Showing 243001 words to 246000 words out of 262297 words

Chapter 82 - Maimoon Hausa Novel Complete

Mahdi is the best husband that you can ever wish for" nan muka rabu da alkawarin next time idan muka hadu zan bata labarin rayuwar makarantar mu da mahdi. Bayan sun tafi na zauna ina tunanin hukuncin ubangiji. Tayi ba dai dai ba a rayuwa amma kuma tayi nadama, mun yafe mata mu da ta bata wa, Allah ma sai ya yafe mata, sannan kuma tazo ta farantawa mahaifiyarta rai ta hanyar bata zabin mijin da zata aura, sai ubangiji yayi mata zabin alkairi ya bata Mahdi, wanda ni a ganina yafi Amir din da da na dauka zasuyi aure, ya kuma fi Abbas din da naso hada ta dashi. Allah kenan.
Ranar sadakar bakwai Ibrahim yazo yi mana gaisuwa, dama Amina tace min yazo dashi akayi jana'iza. Muka fita gaba daya dasu Hafsat yayi mana gaisuwa, sam babu wani special treatment daya bani, idonsa suna kan Aminan sa. A ranar muka taho gaba daya har Daddy, Amina kadai muka bari acan saboda 'yan shirye shirye da zata yi saboda bikin su yanzu saura sati uku. Su inna sun so a daga bukukuwan amma mazan gidan suka ce babu wani abu, sai dai an yanke shawarar Abuja za'a tafi ayi bikin gaba daya a can. Muna zuwa Abuja gida muka wuce, Sultan yayi ta nacin in taho gida amma naki, saboda ba karamin gajiya nayi ba kuma nasan ina komawa gida sai ya karamin wata gajiyar. Da kyar na samu na lallabashi ya hakura ya barni na kwana a gida. Tunda muka sauka a gida daga ni har Hafsat muka baje cikkuna a gado muka yi ta bacci. Washegari bayan sultan ya taso daga office ya biyo muka tafi. Naga duk ya chanja a kwana biyar din da ban ganshi ba, he looks so calm and happy, loneliness din da nake gani kullum a idonsa is now totally gone, a raina nace lallai duk duniya babu abinda yafi iyaye dadi, komai girman mutum, komai arzikinsa, komai yawan matansa da 'ya'yansa, soyayyar iyaye daban ce, ballantana ga sultan wanda da bai san taba, dan haka yanzu kara'i ake masa. Ina shiga motar ya matso ya jawo fuskata ya fara kissing dina, na barshi yayi dan kansa ya hakura, yace "damn it baby girl, I missed you" nace "ina kayi missing dina bayan nasan kana can Ummee tana goya ka da zani" yayi dariya yace "da ace zan tsaya da sai ta goya nin ai" na taya shi dariyar nace "how is she?" Yace "tana can tana shan amarci" na dungure masa kai nace "Ummeen kake gaya wa tana amarci ko?" Yace "in munje zaki gane wa idonki ai".
Muna shiga naga gidan gaba ki daya ya chanza min, gaba daya an chanza masa traditional setting din sa an mayar da shi modern. Part din Takawa in ka shiga ba zaka dauka a Nigeria kake ba saboda haduwarsa, anan kuma ummee take, basu wani raba dakuna ba. Komai wayewar ka in ka shiga gurin sai kayi kallo. Da sauri Ummee tazo ta rungume ni tana min sannu da zuwa, ta sunkuya kusa da cikina tace " Hello dear, welcome back home" daki daki sai da ta shiga dani ta nuna min, master bedroom ne naki shiga, ina suruka ina ganin makwancin surukai?, lol. Part din Hajiya yana nan yadda yake, tana nan kuma har yanzu a ciki, amma kuma a kusa da gurin anyi wa su saratu sababbin dakuna suma, an kawata musu gurin gwanin ban sha'awa. Sultan yana ta tabani wai in tashi mu tafi amma Ummee tana ta zuba min hira, tana tsara min yadda aka tsara bikin Amir wanda za'ayi next week. Ban tambayeta labarin yadda aka mayar da auren su da Takawa ba ita ma kuma bata gayamin ba. Muna ta hira har akayi sallar magrib, sultan ya fita masallaci mu kuma mukayi anan, tare suka dawo da Takawa, ni dai yana shigowa kaina a kasa na gaishe shi, ya amsa min sosai harda tambayata ya karin hakuri, na dago kaina na amsa masa "Alhamdulillah" and he smiled, this is the second time dana taba ganin murmushinsa. He looks different shima, he looks happy, har wani haske naga yayi da wani annurin fuska irin na angwaye. Tare muka ci abincin dare, ni dai duk a takure naji ni. Su kam hirar su suke yi sosai, Ummee sai dariya take yi, she looks so happy, basu da wani problem in the world, komai yayi farko yana da karshe, duk wata wahala da mutum yake sha a rayuwa mai wucewa ce, musamman idan kana kan gaskiyar ka, musamman idan baka zalinci kowa ba, to ka tabbatar cewa ubangiji yana sane da kai, kuma He has a special plan for you. Allah yasa mu dace.
Muna zuwa gidan mu a palon farko na tarar da baba gaji da 'yammatanta, bakunan su har kunne suna murnar dawowa ta, gidan kal kal kamar banyi tafiya ba, ko'ina sai kamshi yake yi. Na zauna duk suka zo suka gaishe ni kuma duk na ambaci sunayensu, suka dauko kayayyaki na suka kai min dakina, zasu kawo min abinci nace musu na koshi. Anan palon na baje dani da cikina muna hutawa, sai da na gama hutawa sannan na tashi na tafi part dina. Ina tura kofar corridor naka duk fitulun gurin a kashe, amma kuma ga haske nan yana fitowa daga kofar da take facing dina, kofar dakin da sultan ya gina a matsayin our baby's room, ni dai a sani na dakin a rufe yake tunda aka kawo ni ba'a taba koda bude shi ba saboda babu komai a cikinsa. Na karasa na tura kofar naji ta a bude, ina shiga naji kida a hankali yana tashi, irin wakokin nan na lullaby. Ido na bude ina kallon dakin, exactly irin dakin da na taba gani a cikin system din Ummee a Riyadh. A zahiri ma sai naga yafi kyau akan hoton. Kadan ne ya rage ban saki kara ba saboda mamaki, hannuna yana rawa na dauko wayata na kira sultan, "sultan baby's room din nan yayi kyau sosai" yace "what baby's room?" Nace "gashi kuwa, an gama an saka komai" da sauri yace "wait a minute, gani nan zuwa" bai fi minti biyu ba sai gashi ya shigo, ina nan tsaye har yanzu a inda nake ina kallon dakin, komai na dakin blue ne, sai shades din ne wani mai duhu wani mai haske, an saka komai tun daga labulaye da capet, baby crib da drawers, da sofa guda daya da breastfeeding pillows a kanta, ga playpen da toys da yawa a ciki, baby swing, baby carrier, trolley, walker, feeders da starilizer, hatta tissues babu abinda babu a dakin, na karasa na bude closet din dakin, nan ma wani mamakin nasha, kayan baby ne fal a ciki, wadansu anyi hanging wadansu an jera su a lockers, kuma abin burgewar shine yadda akayi arranging kayan according to size, from newborn, sai 1-3 months, sai 3-6 months, 6-9 months, haka har 5 years. Diapers da wipes kuwa ina jin sai mun shekara bamu nema ba. Na juya na rungume sultan nace "oh sultan, it is beautiful" yace "I have no idea yaushe aka hada dakin nan" na dan cika shi ina kallonsa nace "nasan waye, Ummee ce" ji nayi kawai babu abinda nake so irin inga na haihu na fara kula da baby na, har wata kwallar dadi naji tana bin idona, ya ilahi, bansan ta inda zan fara gode wa Allah ba. Na saka hannu ina shafa lallausan bargon da aka shimfida akan crib din, a lokacin ne ido na ya hango pictures din da aka rataye a both sides din gadon, daga hannu dama hoton wani baby ne, na dauka ina kalla, sultan ne yana baby, with his red lips, ya tabe baki irin yadda babies suke yi in zasu yi kuka, dariya na kama yi, yazo ya karba shima yana dariya, na lakuce masa hanci nace "daga gani dama kai rigimamme ne kana baby" ya dauko picture din barin hagu shima yana kalla, ni ce nima ina baby, nayi murmushi dimples dina duk biyun sun lotsa, ya saka hannu yana shafa fuskata a hoton, nace "see? In dai babyn nan yayi rigima to kai ya dauko" ya ajiye hoton ya juyo yana kallona yace "idan kuma yayi surutu fa? Da shagwaba, da son jiki?" Nace "oho, wannan kuma bansan wa yayo ba" ya jawo ni jikinsa ya rungume ni ta baya yana dan juyi damu yace "kin san lissafi nake yi yau in kin huta gobe zamu fara shiga kasuwa siyayya?" Nace "ai mu yanzu 'yan gata ne, komai yi mana ake yi" ya yi murmushi yace "yeah, you are right. Ni fargaba ta daya, kada a haifi babyn nan su dauke mana shi su hana mu" nayi dariya nace "shikenan sai mu bar musu shi mu haifi wani". Hmmm kawai yace min. Na dauko waya ta nayi dialing number din Ummee, sultan ya gani yace "ke cikin daren nan zaki kira mata tana dakin mijinta" na harare shi, tana dauka nace "oh Ummee, it is beautiful" tayo dariya tace "har kun gani kenan, do you like it?" Sultan ya zuro kansa yace "we love it Ummee and we love you" ina jiyo dariyar Takawa a background, a raina nace 'dama yana dariya?' Ummee tace "we Love you too sweethearts. Yanzu saura abu daya ya rage" nace "Ummee komai komai ya kammala babu abinda yayi saura kuma" tace "akwai. Addu'ah. Addu'ah ita zamu saka yanzu a gaba muyi tayi ba dare babu rana. Allah ya sauke ki lafiya ya kawo mana new little love lafiya" sultan yace "what? Ummee sunana ne fa?" Tace "daga ranar da aka haife shi za'ayi maka retire, amma before then, you are still our little love, so enjoy it while it last" mukayi dariya a tare, tacigaba da cewa "maimunatu daga yanzu ki dage da cin dabino sosai, sannan kike cin abinci sosai kuma mai kyau wanda zai kara miki karfi da lafiya. Sannan abu na karshe ki tabbatar kullum wayarki tana kusa dake kuma ki tabbatar akwai kudi a ciki kuma akwai chaji. Hospital bag din ku tana gurina, na hada miki kayanki dana baby wanda zaku bukata a asibiti. Allah ya sauke ki lafiya." Sultan yace "Ameen" nima na fada amma a raina, ya karbi wayar ya kashe. Ranar a dakina muka kwana, sultan sai da ya karbi dukkan bashin daya ke bina, nima kuma haka, dan nima ina son mijina. Na kwanta a jikinsa ina shakar kamshin sa da nayi missing kwana biyu, ya taba cikina da yake ta mutsu mutsu yace "kai fa na lura kiriniya ce da kai, to ka sani, wannan wasan bana yara bane ba, ga playpen dinka can Ummee ta sayo maka da toys dinka, sune abokan wasan ka ba mu ba, idan Mommy da Daddy suna yin wani abu yara basa zuwa gurin" nayi dariya ina shafa kansa nace "idan bai yi kiriniya ba ai sai Allah ya tambaye shi" ya dan bata rai yace "yarinyar nan naga alama kinga gurin kwana na shi yasa kika raina ni, zanyi maganin ki ne, dan kinka yanzu ina dan daga miki kafa ko? I will be back to my normal self and sai kin raina kanki" kafin muyi bacci na tambayi sultan "wai Ummee ta dade a garin nan ne har ta shirya dakin can?" Yace "watanta daya da sati daya a Nigeria yanzu" sannan ya bani labarin abinda ya faru bayan tafiyar mu daga Riyadh.

Episode Ninety Six : The New Bride
Riyadh; bayan tafiyar su Moon;
A hankali Ummee ta juya ta koma cikin gida, tana shiga palon kawai taji gaba ki daya ta tsani gidan kuma, ta tsuguna anan bakin kofar tana jin hawaye yana fitowa daga idanunta. Ta jima a haka sannan taji karar wayarta kamar daga sama, da bata yi niyyar tashi ta dauka ba dan she is in no mood for chitchat, sai kuma tayi tunanin ko moon ce zata gaya mata wani abu, dan haka ta tashi da sauri ta karasa gurin yawar ta dauka, number din Nigeria ta gani, bata san number din ba amma jikinta ya bata ko waye, ta ajiye wayar bata dauka ba a ranta tana cewa 'duk laifin ka ne ai, muna zaman mu ka jawo gashi nan sun tafi sun barni ni kadai' ta zauna akan kujera tana lissafin abinda zata yi kuma, sai ta sake jin karar wayarta, wannan number din ce dai, Sadiq ne, tun da suka rabu ranar nan da daddare a abuja shekaru talatin da suka wuce bata kuma jin koda muryarsa ba sai dazu. Da taso shi kamar rai, son da ya saka har ta guji iyayenta ta aikata abinda bata taba tunanin zaya iya aikatawa ba, amma ta aikata saboda shi. A lokacin daya aiko mata da takardar saki kuma ji ta yi a ranta kamar duk duniya babu wanda ta tsana kamarsa, amma duk da haka duk tsahon shekarun nan, babu wani namijin data taba kalla da sunan namiji, ga larabawan nan, kyawawa na ajin karshe, amma duk kallon mata take musu a idonta, bata jin da akwai wanda zata iya sakawa a matsayin data sakashi a da. Sai kuma ga Maimunatu tazo mata da labarin cewa duk abinda ya faru baya cikin hankalinsa, sakin da yayi mata ma bai ma san ya sake tan ba, asali ma, bai ma san da ita ba all these years. Ga kuma labarin wahalar da sultan yasha a hannunsa. Sai ya zama ta kasa tantance taka mai mai me take ji a dangane dashi. Shin haushinsa take ji, ko tsanarsa tayi ko tausayinsa take ji. Wani kiran ya sake shigowa, ta daga wayar a hankali ta amsa, ta saka a kunnenta amma kuma sai ta kasa magana, to me zata ce masa? Shima daga daya barin maganar ya kasa, sun jima a haka suna sauraren numfashin juna, shekara talatin ba kwana talatin bane ba. Ya lumshe idonsa yana picturing dinta a ransa, sannan murya cikin makogwaronsa yace "how are you, Khairat?" Taji kiran sunan ta da yayi har cikin ranta, da akwai wani tone da yake kiran sunan ta dashi wanda shi kadai ne yake kiranta da hakan, all those thirty years melted in her heart. Ta dan gyara muryarta kadan dan kar ya fahimci yana da wani effect a kanta yace "They are gone, sultan and Moon, bansan inda suka tafi ba" yace "Sultan is a big boy, He will take care of them. Am asking how are you" ta goge hawayen idonta tace "am fine. Am a strong woman now. I have been taking care of myself for thirty years, I can take care of my self now, I don't need you" bai damu da abinda tace ba yace "then why are you crying?" Tayi shiru dan bata dauka zai gane kuka take ba, ya sake cewa "why are you crying, Khairat?" Nan take kukan ya taho mata gaba daya, tayi tayin kayanta bai hana ta ba, har da sheshsheka, sai da ta gama kayanta ta goge hawayenta sannan ya sake yin magana, muryarsa tayi masa nauyi sosai, yace "do you want me to come?" tace "I want my son. I want Sultan. I am tired of living alone. Sultan yayi fushi sun tafi sun barni ni kadai. Ban san inda suka tafi ba" kamar baiji abinda ta fada ba ya sake maimaita tambayar da yayi mata "do you want me to come?" A hankali tace "yes, yes I want you to come" yace "then I will come, I will come for you like I promised. Am sorry I kept you waiting" tace "Sultan ban san inda suka tafi ba" ya dan jima yana tunani sannan yace "zan saka a duba su anan airport din, duk inda zasu je dai nasan jirgi zasu hau, in kuma basu hau jirgi ba to suna cikin kasar nan. Daga nan zamu san inda suka tafi sai mu neme su a can" ta gyada kai kamar yana kallonta, yace "shikenan hankalinki zai kwanta ko Ummeen Little Love?" Bata ce komai ba, yace "I will come to Riyadh jibi insha Allah" ji tayi zuciyar ta ta fara bugawa da karfi, ta kashe wayar tana kallon screen din wayar, jibi? Two days kenan? Anya kuwa zata iya ganin sa? Ya yake yanzu? Ta tuna cewa yanzu shi sarki ne, yayi aure bayan rabuwarsu har ya haifi yara biyu, how much has he changed? Is he still the Sadiq she knows ko kuma ya koma total stranger?
A cikin kwana biyun da tayi tana jiran zuwansa har sai da ta rame saboda tunani, wani lokacin sai zuciyarta ta gaya mata ta kirashi kawai tace masa kar yazo yayi zaman sa, tunda in yazo ma mai zai yi mata? Babu wani abu a tsakanin su yanzu, ta tabbatar babu sonsa yanzu a zuciyarta, bata jin haushinsa dai irin da amma bata sonsa, duk sanda tayi wannan tunanin kuma sai ta tsaya ta tambayi kanta, anya kuwa? Amma kuma tana da tabbacin cewa shi babu wani abu a ransa a game da ita, zai zo ne dai akan maganar dan su, amma koma menene a tsakanin su is now over. Ya gaya mata yayi tracing su sultan, dan haka yanzu bata da fargaba a kan su, tasan they are safe. Ranar da zai zo ta gyara masa guest room, amma kuma sai ta tsaya tana tunanin bai kamata ta sauke shi a gidan ta ba tunda ita kadai ce a gidan, sai kuma tayi tunanin mai yasa take wannan tunanin a kansa bayan babu komai a tsakanin su. Bai gaya mata karfe nawa zai baro Nigeria ba dan haka bata san karfe nawa zai sauka ba, ita kuma bata tambayeshi ba, so she get ready, sits down on the sofa and waited, with her hands between her thighs. Akayi asahar ta tashi tayi sallah ta dawo ta zauna, akayi la'asar ma haka, magrib tazo itama ta wuce, sai da taji ana kiran sallar isha sannan hawayen da take ta rikewa ya fara gangarowa daga idonta, he is not coming, he is never coming. Ta mike a hankali ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login