Showing 93001 words to 96000 words out of 262297 words
yanke shawarar ba zai gaya wa babansa ba saboda yasan ba zai shiga maganar ba. Ya yanke shawarar samun uncle din shi Galadima, amma first sai ya fara ganawa da daddy na. Ni kuma na yanke shawarar samun uncle Aliyu in yi masa bayanin komai akan sultan, na yanke wannan shawarar ne saboda sanin halin daddy na, he is too smart, idan nace shi zan yiwa bayani har sai ya tono abinda bai kamata ya sani ba. Sai after ten sannan Sultan ya tafi. Ina shiga gida na tarar da mommy da Amina jigum jigum a palo sun saka uban kaya a gabansu, na karasa nima ina kallon kayan, kayan da sultan ya lodo min a America ne, dama yace zai yi shipping dinsu nan, ashe ya riga ya turo su shine yanzu ya aiko dasu cikin gida ba tare daya gaya min ba. Na samu guri na zauna ina lissafin ta ina zan fara bayani. Mommy ta ce "shi Abbakar din naki ce masa akayi in za'a zo zance tare da kayan lefe ake tahowa?" Daga ni har Amina dariya muka yi, nace "mommy kayan lefe kuma?" Tace "to in ba lefe ba wadannan uban kayan na menene? Ki kirawo shi tun kafin yayi nisa kice ya dawo ya dauki kayansa. Kema kinsan in daddyn ku yana nan ko da wasa babu wanda zai shigo masa da wadannan kayan cikin gidansa" na lankwasar da kai nace "mommy tsaraba ce fa ya taho min da ita daga America. Kuma yanzu idan na mayar masa shi namiji yaya zai yi da kayan mata? Kuma ba'a nan kasar ya saya ba ballan tana ya mayar musu" ta kalle ni tace "wato tare kuka hada plan din ku kenan. Ke kika ce ya sayo miki kenan?" Nayi dariya nace "wallahi mommy bani na roke shi ba, kuma ni bansan ma ya aiko da kayan nan cikin gidan nan ba, ko gaya min bai yi ba" ta sake kallon kayan tace "to yanzu ya kike so ayi dasu?" Amina ce tayi zumbur tace "ni dai bara in fara zaban rabona" nan ta baje kayan tana zaba, nace da mommy "kinga yanzu na huta da siyan kayan tsaraba in zamu tafi Nigeria" dama mommy ta san halina na kyauta, duk sanda zamu je Nigeria sai na kusan yiwa account dina tas saboda kowa sai na sai masa wani abu, tun daga kan tsofaffi zuwa kan jarirai, Hafsat har mamaki take yi yadda akayi nasan kowa a familyn mu duk kuwa da cewa ba tare muke ba.
Tun daga ranar kullum anan gidan Sultan yake dinner kuma sosai muke kara shakuwa da juna ni dashi, ban taba tunanin cewa wani mutun zai iya yiwa wani irin son da muke yiwa juna ni da Sultan ba. Wani lokacin a gidan Hafsat muke haduwa amma sam yanzu na daina binshi yawo, ko zamu fita ma sai dai tare da Amina ko kuma da driver. A duk sanda muka hadu a gidan Hafsat in dai Zayed yana nan sai ya ta yiwa Sultan tambayoyi akan a ina yayi karatu kuma a ina yake aiki da dai sauransu. Ni har kunya nake ji tunda anyi tambayar nan ba sau daya ba ba sau biyu ba amma Sultan sam baya nuna damuwar sa sai dai yayi ta bashi amsa. Rannan dai bayan sultan ya fita sai Hafsat tace "Darling wai me yasa kake ta yiwa Sultan wadannan tambayoyin ne?" Zayed yace "wallahi na rasa dalili, kullum na ganshi sai inji tamkar na sanshi, kuma na rasa a inda na sanshi, sam babu wani guri da muka gadu dashi" Hafsat tace "kasan wadansu haka suke, kama ce kawai, maybe kasan wani mai kama dashi ne" Zayed ya girgiza kansa yace "I know him or someone that looks like him from somewhere, I just cant place my finger on it" .
Kwanci tashi har lokacin bikin nuraddeen yazo. Nan muka shirya inamu2 sai Nigeria, Sultan ya riga mu yin gaba saboda wani aiki daya taso masa. Kwana biyu muka yi a Abuja muka wuce 'yalleman. Abinda nake tunani kuwa shi ya faru dani dan kowa muka hadu sai ya tambaye ni "yaushe ne naku bikin?" Ni dai kawai da dariya nake bin su. Munir kuwa kamar jela haka yake bina duk inda nayi, mutane kuwa da sun ganmu sai suce "our next amarya da ango" ni kuwa haushi kamar ya kashe ni. Kuma wai duk da muna tare amma haka nake ganin sa a gurin 'yammata, da karya da akuya kowa ya gani indai da skirt a jikinta to sai ya bita, sai dai in ya ganni ya maze kamar bashi bane ba. Sultan kuwa rikice min yayi wai lallai sai ya taho gurin bikin, a cewarsa ai shikenan sai ya gaida duk uncles dina kuma 'yan'uwana ma duk sai su gan shi, da kyar na hana shi, kuma nasan abinda yake damunsa shine yasan dole muna tare da munir, sau da yawa in muna waya in yaji muryar namiji sai ya tambayeni "waye wannan?" Sultan akwai kishi, ni har tsoro yake bani, na hana shi bina 'yalleman saboda bana son haduwarsu da munir dan ba za'a kwashe da dadi ba, na fison sai naje gurin iyayena formally kafin su hadu. Masha Allah anyi biki lafiya an gama lafiya, nayi ta yiwa 'yan'uwa rabon kaya kamar yadda na saba, nuraddeen ya gina gidansa mai kyau anan 'yalleman din inda nan zasu zauna shida amaryarsa, muna zuwa ganin gida kuwa na saba da amaryar dan itama mai son mutane ce, nan muka yi exchange din number. Ana gama biki uncle Aliyu ya kira ni palon waje, ni nasan kwanan zancen kuma na shirya. Ina shiga na ganshi shida uncle Rufa'i na gaishe su na zauna a kasa. Uncle Aliyu yace "maimunatu kinsan dalilin kiranki da nayi?" Na gyada kaina. Yace "to ya muke ciki?" Nace "Uncle da akwai wani, ina son kusa masa rana yazo ya gaishe ku. Na so ya gaida daddy tun a England amma kuma basu hadu ba, insha Allah daddy yana dawowa zai je ya same shi sai kuma yazo gurin ku kuma" Uncle Rufa'i yace "madalla, Allah ya sanya alkhairi. In yazo mun ganshi kuma zamu saka ayi bincike a kansa. Kin tabbatar shi kike so" na sunkuyar da kaina bance komai ba, yace "to Alhamdulillah. Shi kuma munir ya kuke ciki dashi?" Nace "Uncle shi Munir ai na riga na gaya masa, shi ne dai yaki hakura har yau. Ni dai uncle wannan din dai..... " yace "wannan din dai shi kike so?" Nayi shiru. Uncle Aliyu yace "kar ki damu Maimunatu, babu wanda zai miki auren dole, maganar munir zamu san yadda zamuyi da ita yadda ba za ta bata zumunci ba. Shi wannan da kike magana akansa ya sunan sa? A ina yake? Dan waye shi?" Nace "sunansa Abbakar Sadiq, A abuja yake" na danyi shiru sannan nace "dan sarkin Abuja ne" uncle rufa'i yace " ah, kice da princess muke magana" na rufe fuskata ina dariya. Uncle Aliyu yace "ban san 'ya'ya nawa ke ga maimartaba ba, amma nasan akwai wani dan sa fitinanne. Whatever dai ki kai shi gurin yaya ambassador din in ya dawo, tunda shi ya fini sanin kan Abujan. Allah yayi miki albarka" nace "Ameen, nagode uncle" .
Bamu bar 'yalleman ba sai da su daddy da yaya Walid suka zo tukunna, kwanan su biyu sannan muka koma Abuja gaba daya. Ranar da muka koma a ranar Sultan ya zo. Duk gidan a hargitse yake saboda ana general cleaning da ake yi dan haka a mota naga Sultan. Ina shiga da sallama yace "look what you have done to me" na kalle shi sama da kasa nace "me nayi kuma?" Ya nuna min wuyansa, baki ga ramar da kika saka ni nayi ba" nayi dariya nace "ni banga wata rama da kayi ba Sultan, gashi nan kayi wani fresh da kai har da ajjiye tumbi" da sauri ya shafa cikinsa, ganin yana kokarin daga shirt dinsa nayi sauri na dauke kaina ina dariya, yace "please dan Allah tumbi nayi?" Nace "wasa nake maka fa" ya wani bata fuska "amma wannan ai mugun wasa ne, kinsan kuwa yadda bana son tumbi? Amma ke kinga yadda ki ka yi kiba kuwa? Dama ku fulanin nan haka kuke da wayo,sai ku tafi ruga kuje kuyi ta cin dadi,kuci kaji,kuci zabbi, kusha nono" nace "kuma muci kwai ba. Karka damu indai 'yalleman ce har sai ka gaji da zuwanta" daga nan muka koma hirar yaushe gamo, na bashi labarin yadda muka yi da uncle Aliyu, yace "daddy fa?" Nace "tare da shi muke yanzu, zan tunawa mommy ta gaya masa, sai ya baka rana ka zo" shi kuma ya bani labarin ya samu maigirma galadima da maganar, yaji dadi sosai kuma yace in dai ance ya turo iyayensa to yazo direct ya gaya masa, shi zai yi masa komai. It's like everything is falling in place, matsalata daya yadda zanyi convincing daddy ya karbi Sultan, amma shima na samu solution, project din da na rubuta akan sultan zan bashi, in yaki yadda kuma ince masa yayi bincike.
Da daddare na samu mommy na tuna mata maganar Sultan nace ta gayawa daddy, tace zata gaya masa amma yace mata gobe zai koma England, da akwai wadansu takardu da zai cike amma ba zai dade ba zai dawo. Naji babu dadi amma we are ready to wait. Washegari tunda na tashi nake jin zuciya ta babu dadi. Irin feeling din da mutun yake ji idan something is wrong, nayi ta tunani ko zan tuno wani abu da nayi ba dai dai ba amma na kasa tunawa, sultan na kira na tambaye shi if he is alright, kuma daga muryarsa na gane bashi da wata matsala, jin yadda nake jin babu dadi yasa yace zai zo da yamma. Yamma nayi na shirya cikin doguwar riga purple mai ratsin pink nayi rolling pink veil, ina gama shiryawa sultan ya kira ni yace yazo, part din su ya Walid na saka aka bude masa ya shiga sannan na fita, ina shiga palon na tarar dashi ya bude fridge ya dauko drink yana sha, na tsaya ina kallonsa nace "wannan wanne irin bako ne? Daga zuwa zai bude wa masu daki fridge" ya juyo ya kalleni dan bai san ma na shigo ba, yace "waye bakon? Ni a gidan nan ai sai dai in sauki wadansu" na shiga na zauna tare da gaishe shi, ya amsa sannan ya zauna akan center table din gurin yana kallona, yace "so... What's the problem?" Nace "I don't know, kawai dai ina jin ba dadi ne, I just want to confirm if you are alright" yayi murmushin nuna jin dadin sa yace "am OK, I really am. Maybe akan tafiyar daddy ne kike feeling bad, tunda ba dade wa zaiyi ba ai babu problem ko?" Na kirkiro murmushi nayi masa. Nan ya zauna yake ta bani labarai da zasu saka ni farin ciki, in no time kuwa sai gani na ware ina dariya sosai. Yana cikin bani labarin Amir yayi wata budurwa kanuri sai kawai ji muka yi an bude kofar palon, a tare muka dago kai muka kalli kofa, ya Habeeb ne a tsaye, yadda muke kallon sa shima haka yake kallon mu, Sultan ya mike da murmushi ya doshe shi yana mika masa hannu, kallo daya yayi masa ya wuce shi ya karaso inda nake zaune a daskare, ya nuna sultan ya hannu yace "Moon me wannan yake yi a gidan nan?" Na bude baki amma na kasa cewa komai ganin yadda kamannin yaya Habeeb suka juye "I asked you a question, me wannan yake yi a gidan nan" murya na rawa nace "gurina yazo" na kalli sultan naga mixed expression a fuskarsa, na sake mayar da kallona kan yaya Habeeb wanda har yanzu ni yake kallo, yace "amma ya muka yi dake, you told me he is not your type that you are just using him for your project, ko? Rasa amsar da zan bashi nayi, na sake kallon Sultan, he is getting angry, nace "yaya Habeeb please don't do this" yace "don't do what? Ke fa kika cemin da kin gama using dinshi for the project zakiyi masa kafa, that's exactly what you told me, kuma yanzu kin gama so banga dalilin da yasa zaki cigaba da ganin sa ba, i see no reason why you should waste his time any longer" yana fadin haka ya juya ya koma gaban sultan ya tsaya yace "look man, this should be the last time da zan ganka tare da kanwata, you are not her type, ita da kanta ta fada, she was just using you for her project kuma ta gama, so ala raka taki gona" gaba ki daya kamannin sultan sun chanza, idonsa ya rikide ya zama jajawur, bai ce da yaya Habeeb komai ba sai ya karaso inda nake, da sauri na mike tsaye nace "Sultan listen to me, abinda ya fada ba haka bane, you of all people know I love you" ya Habeeb yace "bullshit" wani irin juyi sultan yayi ya danki wuyan ya Habeeb yayi baya dashi ya hada shi da bango, a zabure na karasa gurin na fara kokarin kwace yaya Habeeb nan da nan hawaye suka fara zuba a idona, hawayen da Sultan ya gani a idona ne yasa ya saki Ya Habeeb shi kuma duk da shakar da yasha amma bakinsa bai mutu ba, yace "kai kana tunanin kowa mahaukaci ne irinka? Waye kake ganin zai dauki 'yarsa ya baka?" Ya juyo kaina yace "ke kuma ki sani, am going straight to mommy" daga haka ya juya ya fice.
Kujera na samu na zauna na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ina jin Sultan ya kuma dawowa ya zauna akan center table din gaba na. Yace "Maimunatu me mutumin can yake cewa ne? Do you really told him cewa am not your type?" Na bude fuskata amma ban kalle shi cikin ido ba, ya sake cewa "what project was he talking about? Did you really write a project on me?" Nace "Sultan listen to me, duk yadda ka dauki maganar nan ba haka take ba... " ya katse ni "did you write a project on me? Yes or No" nace "yes, but... " da sauri ya mike yasa kafa ya daki kujerar kusa dani, nima na mike nace "Sultan ka saurare ni mana, I never meant to hurt you, ina taso in gaya maka ban san yadda zaka dauki maganar ba" ya juyo yana kallona, a hankali ya karaso inda nake tsaye, ya matso sosai har sai da ya hade goshin mu guri daya sannan cikin murya mai kama da rada yace "fuck you, and fuck your damn project" rintse idona kawai nayi hawaye yana zuba dan nasan babu abinda zan ce masa ya saurare ni. Ban bude idona ba sai da naji rufe kofar sa. Da sauri nabi bayan sa, kafin in fita daga palon har ya shiga motarsa ya tayar, a guje ya fincike ta dan Allah ne kadai ya taimaki mai gadin mu dan sauran kadan sultan yayi ciki dashi.
Episode Fifty : Munir 2
Nabi motar da kallo har ta fice, ji kaina nake a cushe cos babu wani tunanin da yake tafiyar min dai dai. Kamar daga sama naji kara mai kama da accident din mota a waje, ko ba'a gaya min ba na san Sultan ne, bansan lokacin da naje bakin gate ba kawai nima gani na nayi a gurin, motar Sultan na gani ta daki bishiyar da take opposite din gidan mu, ji nayi tamkar zuciya ta ta fado kasa, ina ganin masu gadi suna tafiya gurin amma ni ji nayi kamar an daskarar dani, ga mamaki na sai naji ya yi wa motar key yayi reverse da ita tare da tarwatsa mutanen da suka tafi kayo masa dauki, gaba daya gaban motar yayi damage amma a haka ya sake figarta ya yau titi. Yana tafiya masu gadi suka fara surutu, 'wai yaron nan me yake kawoshi unguwar nan ne kwanannan? Kar fa yazo ya tattaka mana yara a banza kuma babu mai daukan mataki a kansa" ni dai jiki a sanyaye na koma gida. Sai da na kama hannun kofar shiga palo sannan na tuno da ya Habeeb da kuma alkawarinsa na gaya wa mommy. Ga mamaki na sai naji babu wani tsoro a zuciya ta, gwara a yi ta ta kare kowa ma ya huta, dan ni yanzu ban damu da kome za'ayi min ba, nafi damuwa da halin da Sultan yake ciki, I fear he might hurt himself, ni kuwa nasan ba za'a taba yimin wani physical damage ba. Na murda kofar na shiga da sallama, babu kowa a palon sai ya Habeeb, fuskarsa sam babu rahama a cikin ta, kallo daya nayi masa nayi hanyar kitchen, haushinsa nake ji sosai duk da cewa deep down nasan ba laifin sa bane ba laifi nane, he was only trying to protect me. A kitchen na samu Asma'u, cook din gidan nace "Ma'u ina mommy?" Tace "Mommy taje unguwa, lokacin kina gurin bakon ki, tace in gaya miki sai dare zata dawo" banji dadi ba cos I don't want to delay this any longer. Na sake fito wa na wuce ta gaban yaya Habeeb na hau stairs din part dina. Direct balcony na wuce na saka kujera na zauna. Kamar yau ne na tsaya a gurin nan ina kallon Ibrahim ya fita daga gidan nan ruwan sama yana dukansa. Can't believe it has already been six years. History is repeating it self today. Amma yanzu a shirye nake, I am no longer sixteen years old, I am twenty two. Yanzu ba yarinyar nan bace da ta gama secondary school, wannan double degree ne da ita a second best university in the world. Ba wai zama zan yi in jira abubuwa suke faruwa ba kamar yadda na zauna nayi ta jiran Ibrahim, this time I am going to make things happen. Tashi nayi na koma daki na dauko laptop dina na kunna, email na shiga na rubuta wa daddy sako