Showing 6001 words to 9000 words out of 262297 words
ya dawo inda nake zaune ina zane na yace. "Tell me more" murmushi nayi sannnan na fara kwararo masa bayani tun daga kan yadda earth core take da yadda rocks suke melting su zama lava, yadda mantle da crust suke budewa har lava din ta fito earth surface. Daga nan na koma kan bayanin different types of cooling and solidification na lava din yadda yake producing different kinds of rocks. Sannan na dawo kan shi obsidian din, cooling process din da yake forming dinshi, dalilin da yasa yake black and shiny, composition dinsa, life span dinsa da amfanin sa a gurin mutane. Nafi 30minutes ina magana kuma at the same time ina cigaba da drawing dina. Tunda na fara magana ajin yayi tsit babu wanda yayi magana har na gama. Gamawa ta yayi dai dai da gama drawing dina. Sai da na karewa drawing dina kallo na tabbatar na gama sannan na dago kaina na kalle shi ido cikin ido tare da cewa " Is there anything more you want to know, SIR?" Na fadi kalmar sir din nima cikin challenge. Sai da wajen 30sec ta wuce sannan ya iya magana yace "wow, that is very correct. No, there is nothing more. U have said it all".
Kamar hadin baki, yana gama fadin haka aka buga bell din break. Books din mu duk muka rufe muka fice daga class din. Sai da mukayi nisa sannan na juyo na kallo class din mu naga yana nan a tsaye a inda muka barshi ya saka hannayensa cikin aljihun wandon sa yana kallon kasa. "He must be feeling like an idiot" na fada ina murmushi. Amira tace " Ai kin wanke mana shi tas, I wonder ta yaya zai yi facing din mu tomorrow morning for maths" Hafsat tace "and they said I am the cruel one". Dariya muka yi muka tafa ni da ita, nace "ai ba cruelty bane, he asked me a question and I answered him. He then asked me to tell him more, so I told him more" wata kawarmu Hasiya tayi joining din mu tace "baki da kirki Moon. You told him more and more. By the way, how do u know so much? Ni dai nasan ba'ayi mana duk wannan a aji ba" Nayi murmushi nace mata a cikin holiday na karanta, nasan za muyi shi a wannan term din. Nayi forming note a kan shi, in kina so kizo ki karba ki copying " tayi min godiya ta wuce. Amira tace "Tabdi ai ni babu abinda zai saka inyi karatu a cikin hutu, hutu fa akace, we are suppose to huta a cikin hutu"
Episode Seven: The Thin Tall Man
Washe gari first period muke da mathematics. Dan haka tunda na shirya nayi breakfast sai na dauki jotterta, calculator, sannan na duba syllabus naga abinda ya kamata muyi yau sannan na fice sai library. Ina zuwa na tarar librarian din ma zuwanta kenan. Ko gama cleaning library din ba'ayi ba. Na samu guri na jira har suka gama sannan na shiga. Miss Martha, librarian din mu ta tambayeni ya akayi banje class ba, na amsa mata da cewa teacher din mu bayanan kuma inada assignment da nake so in karasa. Ina shiga mathematics section na wuce, na debo textbooks din calculus har uku sannan na samu secluded guri na zauna na fara calculations dina hankalina a kwance. Saboda ina ganin a haka sai nafi ganewa akan ace wannan yaron ne zai koya min. Double period ce damu dan haka a lissafina zaiyi one hour 20min. Ina yi ina duba agogon hannuna har naga one hour ta wuce saura 20mins kenan. Hankali na gaba daya yana kan calculations dina saboda sosai nake jin dadin product rule din da nake yi a lokacin. Ji nayi tamkar ana kallona, da sauri na dago kaina tare da cire earpiece din kunnena. Ido muka hada dashi ga mamaki na sai naga ya sakar min murmushi. Daga dukkan alama ya jima yana kallona. Nayi saurin dauke kaina tare da sunkuyar da ido na kasa ina mamakin ganin shi a nan bayan nasan ya kamata ace yana class dinmu yana koya musu maths. "Mind if I join" ya fada cikin muryarsa mai sanyi. Ba tare da na sake kallonsa ba na ce "no". Kujerar kusa dani ya ja ya zauna. Ta ke naji na shaki kamshin sa. Na dan matsar da kujera ta kadan saboda kafadan shi da naji yana taba tawa. A hankali ya fara yi min magana wanda na tabbatar da ace da akwai mutun a kusa dani bazai ji me yake cewa ba. " Why aren't you in class" "am sorry" na fada a takaice. "Sorry for what" ya fada tare da adjusting kujerar sa yadda zai fuskance ni sosai, na kara jan kujerata baya sannan nace "for not attending your class". Murmushi mai sauti yayi sannan yace" it is not my class, it is OUR class, we are all suppose to be participating in it". Yayi shiru sannan ya kara da cewa " by the way, we miss u in class today. The class was exciting though, but I thought it would have been more exciting if u were there. So I asked of u and was told to check the library. And here u are. So, why are u here?" Ya tambaya yana kallon cikin idona. Na dauke kaina ina inda inda cike da jin kunyar abinda nayi. Ya saka hannunsa ya juyo da fuskata gare shi muke kallon juna, cikin muryar rada ya ce min "you think I am not good enough to teach you, right?" Kunya ce ta kamani, nayi sauri na kwace fuska ta daga hannunsa, nasa hannaye na na rufe idona cikin kunya nace masa "no" da dan karfi. Ga mamakina sai kawai naji ya kama dariya nima bansan sanda na fara dariyar ba. Sai da muka dena dariyar sannan ya dauki jotter din da take gabana tare da cewa " let's see what you have been doing for the past one hour" ban ce masa komai ba. Sai da ya gama studying abubuwan da nayi sannan yace " wow, we were in class tying to solve some few problems while you are here already done with the term. Na zaro ido nace "am not done with the term sir, am not even close" ya rungume hannayensa a kirjinsa, abinda na lura cewa dabi'ar sa ce. Yace " you are special, do you know that? Nayi sauri nace " no sir, am not. Kawai dai ina da son karatu ne" na fada ina kokarin kare kaina. Kallona kawai ya tsaya yana yi chike da rashin fahimta. Sai a lokacin na kalleshi sosai. Ba bahaushe bane. Na sunkuyar da kaina. "What tribe are you?" Ya tambaye ni cikin sanyin murya wadda itama by now na fahimci hakan yanayinsa ne. "Fulani" nace ina wasa da 'yan yatsuna. Yace " but what you just spoke is Hausa, right?". Nace "yes" yace " so u are Hausa Fulani " na girgiza kaina alamar a'a. Bai sake min wata tambayar ba. Can ya ce " I am yaroba. I am from Ibadan, Oyo state. My name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun. Will you do me the honor of been my friend? " ya miko min hannunsa alamar shaking. Na gado kaina na sake kallonsa. Fatarsa ba mai haske nace kamar tawa ba kuma baka bace ( wankan tarwada). Dogo ne sosai sannan siriri ne dan bashi da kiba sam amma kuma straight bayansa yake tsahonsa bai sa ya rankwafa ba. Yana da doguwar fuska da dogon hanci da yalwataccen gashin gira. Bakinsa mai dan fadi ne mai dauke da siraren lips wadanda a yanzu suke dauke da murmushi. Fuskarsa tana zagaye da siririn saje da dan karamin gemu a habarsa. Fararen glasses be sanye a idonsa wadanda suke lumsassu kamar na maijin bacci. A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da cewa " I am Fulani from Jigawa State. My name is Maimoon Muhammad Dikko. Yes, I will like to be your friend and I am sorry for missing OUR class today" " it is OK friend" ya fada yana sauke hannunsa ganin bani da niyyar shaking dinsa. Agogo hannuna na kalla, ga mamakina sai naga next period har tayi nisa. Da sauri na mike ina harhada takarduna hankalina duk ya tashi. Shima ya mike tare da daukan jotter da nayi calculations yace 'I will look this calculations over if you don't mind" "no problem" nace ina sauri duk hankalina yayi class. A bakin kofa ya sameni ina signing out. Ina fita ya biyo baya na, sai a lokacin na sake lura da tsahonsa, dan gabaki daya na a kirjinsa na tsaya. "See u tomorrow" na fada bayan mun fita daga libraryn. "See u in CLASS tomorrow" yace yana jaddada Kalmar class din. Da sauri nayi gaba dan bana so ya cigaba da bata min lokaci tunda already nayi latti a class din English. Ina shiga Aunty grace ta fara tuhumata akan daga ina nake, inda ni kuma na bata amsa da cewa ina library ina assignment ban san cewa har lokaci ya wuce da yawa ba.
Saida aka fita break sannan na tambayi Hafsat ya akayi a lokacin maths. Ta be baki tayi tace "ina ruwanki, ke da kikayi tafiyarki kika barmu da wannan dogon mutumin" nace "sorry tare da langwabar dakai, ta harare ni ta dauke kai alamar har yanzu fushi takeyi. " is he good? " na tambayeta. Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace "you will find out tomorrow, we have him double period da safe" " oh my God Moon, he is so good, ban taba enjoying mathematics irin na yau ba, I really did enjoy it. Wato dalla-dalla yake bin komai kuma sai ya tabbatar kowa ya gane sannan zai yi gaba. Gaskiya Moon kinyi missing " inji Hasiya wacce ta dawo kusa da desk dina fuskar ta kamar gonar auduga. Na mike tsaye na dubi sauran 'yan class nace "OK people, tomorrow, I will give the Thin Tall Man a chance" "Thin Tall Man?" suka kusan hada baki. Nace "yes" matter of factly, "baku ga yadda yake bane? I think the name fits him perfectly". Dariya ajin ya dauka gaba daya, inda ni kuma na bawa Hafsat hannu muka kashe muna kyalkyala dariya. Amira na hango ta gefen idona fuskarta dauke da bacin rai.
Episode Eight: The New Imam
Muna hostel da daddare Amira tazo dakin mu ta sameni nayi wanka ina shirin yin bacci, ta zauna a bakin gadona. Da yake yanzu mun zama seniors ba bunks ne damu ba. Still dakin mu daya da Hafsat da wadansu Christians su biyu Naomi da Abigail. Mu hudu ne a dakin mai dauke da gado hudu, lockers hudu da kujerun karatu kowacce da table dinta guda hudu, sai fridge guda biyu. Dakin babu tarkace da yawa da yake Hafsat akwai tsafta kuma duk ta fimu girman jiki hakan yasa ta zama kamar Senior din mu. Babu wanda ya isa yayi kazanta. In kaga Hafsat tana bamu order sai ka dauka ba class din mu daya ba. Muna da toilet din mu guda daya a dakin wanda muke sharing mu hudun, kuma kullum twice cleaners suke zuwa su wanke mana shi duk da ba wani datti yake yi ba. Masifar Hafsat ma ba zata barmu muyi kazantar ba.
Ina tsaye ina kallon fuskata a mudubin jikin locker din Abigail Amira ta shigo dakin sanye da dogon hijab har kasa tare da sallama. Ina ganinta nasan har ta kwanta ta taso. Ta cikin mudubin nake kallonta har ta zauna a kan gadona tace "kai Moon wannan bargon naki da laushi yake, wannan inna kwanta a kansa ai ba zan iya tashi daga bacci ba" na juyo ina fuskantar ta nace ' ko kina so in bar miki ne, u can take it if you want. Ina da wani" da sauri tace " a'a wannan ai sai in kasa tashi sallah asuba" muka yi dariya baki daya. Hafsat dake kwance kan gadonta tana karanta novel tace "Amira wai da gaske yasaiyadin mu ya tafi umrah?" Amira tace "eh wallahi Hafsat, shine ma maganar da nazo muyi. Ya tafi umrah, sai nan da at least a month zai dawo. Na taho na zauna kusa da Amira nace " to fa, yanzu me ake ciki kenan Amira? Waye zai ke janmu sallah kuma wa zai ke yi mana dori? Amira a lokacin itace mosque prefect dan haka duk wasu bayanai akan harkar addini a gurinta a ke samu. Tace "senior master dai yace they will find a solution. Maybe da assuba in muka je sallah zamu ga new face" na dafe kai nace "oh God, I don't like these changes da muke samu wallahi" Amira ta gyara zama tace "change is sometimes good Moon. Dama maganar da nazo muyi kenan, karki damu kanki da wadanna changes din har su zo suyi affecting dinki negatively, please Moon, give the change a chance, ki daure, you might even like it. Bana so gobe idan munje masjid kinga new imam ki yi loosing interest akan karatun ki. Kinga kun kusa sauka ke da Hafsat. Kada kizo karatun ki ya koma baya kuma. Muka kalli juna nida Hafsa wacce yayi her usual side looped smile tare da whispering "she likes you" na tashi daga dan kashingidar da nayi nace "I like you too Amira. Kuma insha Allah babu abinda zai samu karatu na, besides, I have u". Amira tayi sauka tun kafin tazo school din. Shi yasa run muna jss ni da Hafsat muke daukan karatu a gurinta. Tana dariya ta mike tana cewa "ni din bayan in muna karatun wasa kike yi. Da haka ta mike tare da wishing din mu good night, tayi sallama dasu Abigail sannan ta tafi dakinsu
Ajiyar zuciya nayi nayi rigingine ina tunano abubuwan da suka faru a ranar. Na fahimci cewa abinda nayi ban kyauta ba. Ya kamata in bawa Thin Tall Man chance kamar yadda Amira ta fada kafin in ce bana son teaching dinsa. Abinda nayi na kin shiga class dinsa is very wrong, za'a iya furnishing dina akan hakan. Amma duk da haka bai nuna min bacin ransa ba sai ma neman sulhu da yayi dani. Kafin inyi bacci ranar sai da nayi alkawarin insha Allahu gobe zanyi making up for my mistakes.
Washegari kuwa kamar yadda muka yi tsammani hakane ya faru. Mukaji muryar diff liman yana jan sallah. Muka yi joining har aka idar sannan muka tafi class din da ake mana islamiyya. Muna zazzaune muna bitar karatun mu na baya sai gashi ya shigo ajin. Duk da cewa akwai duhun assuba amma class din tar yake da fluorescent light wacce take a kunne. Kallonsa na tsaya yi cikin mamaki. It is the thin tall man. Jallabiya ce a jikin sa ash color sai bakin dogon wando da bakar hula a kansa. Idonsa babu glasses. Ya shigo ya rufe kofar tare da jingina a jikinta, ya ringume hannayensa a kirjisa tamkar mai jin sanyi. Daya bayan daya ya ringa binmu da kallo har idonsa ya kawo kaina, muna hada ido nayi saurin sunkuyar da ido na kasa. Gyaran murya yayi na dago kaina kawai sai naga ya yi min murmushi nima kuma sai na samu kaina da yi masa murmushi. Na sake sunkuyar da kaina kasa a karo na biyu. Ya sake yin gyaran murya tare da cewa "I was asked by the senior master to guide you through your Islamic studies before your mu'allim returns from his pilgrimage" ya tako a hankali ya jingina da jikin board yana facing din mu sannan ya cigaba da cewa "I don't know how you guys do it, do u have a class monitor or something?" Duk muka amsa masa da "yes" sannan ya bukaci da ta tashi tayi masa bayanin yadda tsarin karatun mu yake. Nan Amira ta tashi cikin nutsuwa ta fara yi masa bayani dalla dalla tare da nuna masa time table din mu. Yana sauraronta attentively yana gyada kai alamar fahimta. Sai da ta gama sannan yace " with your permission, I will like to make some changes. Instead of group progression I will like it to be individual so that we will carry everyone along. Because of the time factor, we will add night classes to the early morning ones so that we will have enough time. I will discuss this with your Senior master to see if its OK to have the night classes". Ya zagayo gabana ya dauki alqur'anin da yake bude a gaba na ya duba inda muka tsaya sannan ya mayar ya ajiye yace " I don't think we can start today, the time has already run out, we will insha Allah start tomorrow. Maassalam to u all" duk ajin suka amsa masa da "bissalam" banda ni wacce haka kawai naji na zama uncomportable saboda tsayawar da yayi a kusa da seat dina. Duk iskar da zan shaka sai na shaki kamshin jikinsa da scent din after shave dinsa.
Episode Nine: Give Me a Chance
Geography lecture din da muka yi was very interesting. Sai yanzu na fahimci abinda Hasiya take nufi lokacin da tace yana bin komai dalla-dalla. He makes sure He carries everybody along. Yana making references da abubuwan da na fada rannan yana kara buda su dayi mana bayani using simple terms wanda ko the most stupidest person zai gane. Anan na kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa, komai nasa a hankali yake yinsa. He is very gentle, bashi da hayaniya sam.
Toward the end of the class sai ya bamu classwork, kowa ya rubuta abinda ya fahimta a game da topic din yau for 10mins. Kowa ya dauko takarda ya fara rubutu, ni kuma na duba takarduna na rasa fullscap sheet, sai na juyo gurin Hafsat nayi mata alama da hannu akan ta bani paper, take mutuniyar tawa sai ta makale kafada tare da murguda baki. Takaici ya ishe ni gashi time yana tafiya. Sai na juya gurin Amira. Kafin Amira ta fallo min sai naga an ajiye min paper a gaba na, na daga