Showing 261001 words to 262297 words out of 262297 words

Chapter 88 - Maimoon Hausa Novel Complete

Sultan ya shigo da sallama, na juya nayi masa alamar yayi a hankali kar ya tashe su, ya karaso ya zauna a kusa shima yana kallonsu, yace " Hmmm, they are beautiful, aren't they?" Nace "They are perfect" na tashi tsaye ina mammatsa masa kafadar shi da wuyansa, ya sauke ajjiyar zuciya yana kwanto da kansa a cikina, nace "wai Sweetheart yaran nan wanne tribe ne su?" Ya dan bata fuska yana kallonsu yace "oho, waya sani ne, menene ma'anar tribe din ma gaba daya? Menene kuma amfanin sa?" Nace "babu, bashi da wani amfani sai gurin rarraba kawunan al'ummar musulmi. Mutane sun kasa gane wani abu, we are atronger if we stand together, amma in muka rarrabu anan zamuyi falling easily. Yanzu kamar yaran nan, suna da jinin hausawa, larabara, fulani da buzaye, to wanne tribe ne su? A hakikanin gaskiya basu da tribe amma da mutum ya kallesu yasan they are perfect, ni a ganina mixed din su ne ya kawo perfection din su. Basu kadai bama, duk yaron da aka haifa a auratayya tsakanin two different tribes in mun lura zamuga yafi both tribes din kyau, wannan shi yasa duk duniya halfcast sunfi kowa kyau. Anya kuwa wannan ba wata hanya bace da ubangiji yake nuna mana cewa in muka hade kan mu a guri daya sai munfi samun kyakykyawar rayuwa akan in muka rarrabu?" Sultan ya jawo ni muka fada kan gadon yayi juyi ya mayar dani kasansa yace "maimaita abinda kika ce akan halfcast" nayi murmushi ina shafa fuskarsa nace "kunfi kowa kyau a duniya. Kafi kowa kyau a duk mazan dana taba gani a duniya, ba larabawa ba ba turawa ba, ba Africans ba koma wanne kabila ne banga wanda ya kamo kafar ka akyau ba" yana murmushi yace "ban yarda da wannan theory din ba miss psychologist. Saboda nasan ban kaiki kyau ba" nace "believe me Sultan ka fini kyau, ni macece kai kuma namiji ne. The most amazing thing is your skin, I love it" na fada ina saka hannuna cikin rigarsa ina shafa muscles din da suke rudani tun farkon gani na dashi. Ya juya fuskarsa yana kallon yaran da suke bacci a gefen mu, ya daga ni sannan ya dauke ni yace "let's go to my room sai ki maimaita abinda kika ce kiga yadda zan yi dake" muka fita muna dariya gaba daya.
Washegari ya dawo daga office ya tarar dani a palo ina feeding Basma, Bassam yana tsaye akusa dani yana wasa da toy car dinsu, yana jin muryarsa ya yar da motar hannunsa ya tafi da 'yar koyon tafiyar da suka fara yi zai tare shi, ya fadi ya sake mike wa, Sultan ya karaso da sauri ya daga shi yana juyi dashi a tsakiyar palon, Basma ta sake ni itama ta sauka daga jikina ta tafi, ita ma ya dauke ta yana tsalle dasu suna ta dariya, nace "to ni kuma fa?" Ya juyo yana kallona yace "naki special ne" sannan ya ajiye su a kasa ya durkusa a gabansu yace "albishirin ku, yaye ku za'ayi" na bata fuska nace "ai basu isa yaye ba, ka bari ko fifteen months suyi mana" ya karaso gaba na ya ajiye min wasu takardu, na dauka ina dubawa, naga takardun visa ne da kuma plight ticket zuwa Maldives, na mike da sauri na makalkale shi ina murna, ya daga ni sama nima irin yadda ya yiwa twins ya ringa juyi dani, yaran suka saki baki suna kallon mu, ya sauke ni yace "I promised I will take you back, didn't I? Gwara mu tafi yanzu tun kafin ki fara aiki ki zama busy. Amma ki sani, yanzu ba ki da ciki dan haka kiyi shiri na sosai" na harare shi nace "wancan zuwan ma da nake da cikin me aka fasa" yace "to wannan will ve double. You better get ready" na rungume shi kamar zan shige jikinsa nace "I can't wait, Darling. I love you so much Sultan" ya zagaye ni da hannayensa yace "I love you too, MyMoon".
The End
But remember, every ending is just another beginning.
Alhamdulillah .
Na sadaukar da littafin Maimoon ga duk wanda ya karanta shi. Ina fatan duk wanda ya karanta yaji dadi ko kuma ya karu da wani abun to yayi min addu'ah, Allah ya bani dacewa a duniya da lahira.
Littafin Maimoon kyauta ne, duk wanda ya sayar min ta hanyar bugawa ko kuma a document ya sani Allah yana kallonsa kuma zai tambayeshi.
Da akwai lessons da na saka a littafin Maimoon, wanda nasan in dai har mutum yana biye to zai karu da one thing or another. Amma babban abinda nake so mutane su dauka shine to not judge a book by it's cover, things are not always what they seem, duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to there is a story behind him, kowa da akwai labarin sa, kowa kuma da akwai dalilin da yasa yake yin abubuwan da aka ga yana yi. Akwai mutane da yawa a duniya kamar Sultan, suna nan a cikin unguwannin mu da lungunan mu, deep inside them mutanen kirki ne sosai amma yanayin rayuwa shi ya mayar dasu yadda suke, wadansu zaka gansu suna shaye shaye, wadansu sun zama 'yan daba, wadansu ma sata suke yi, amma da zamu zauna dasu mu tambayesu labarin rayuwarsu da sai mun zubar musu da hawaye, ba wai zabin sune ya saka suka zama haka ba, rayuwa ce ta mayar dasu hakan. Babban abinda zamuyi musu shine mu nuna musu soyayya, no matter how small, you have no idea how mu much a little love can change someone's life. Allah yasa mu dace.
Godiya mai yawa ga dukkanin masoya littafin Maimoon, ba zan taba mantawa da soyayyar ku gare ni ba. Ban taba tsammanin Maimoon zai samu karbuwa irin haka ba, musamman saboda kasancewarsa littafi na na farko, na fara da zero followers na gama da over ten thousand followers. Alhamdulillah. Ku sani duk ina sane daku, nasan sunayen most of you, kuma duk comments dinku ina karantawa kuma ina jin dadi.
Maman maama novels na WhatsApp na matan aure, you guys are always making my days, jazakumullahu bi khair. Maman Ahmad da jama'arta, Surayya ta hannun daman Sultan da Hannatu ta hannun daman Ibrahim, ina fatan kun gaisa kamar yadda sultan da Ibrahim suka gaisa. Nafisa Usman, R-sulym, ummu khulsum, Aishas (we have many), Fatimas, Ummis, Hadizas, Umaira, Saiham, Yagana, Nafeesa, dama sauran wadanda ban kira ba duk ina godiya.
Jinjina ga Umar Faruk (sadauki) wanda shi ya kirkira kuma ya tabbatar da kafuwar both WhatsApp and Facebook groups na maman maama novels, I will forever be greatful. Hayatuddeen, Aisha Tafida, Dr MB, Fadila, Haleema yuguda, Amina, Aysha, Rabiat, Abu Muhammad, da sauran wadanda ban kira sunan su ba, ina godiya for keeping the WhatsApp group lively. Ina jin dadin programs din ku na dare, kuma ina karuwa sosai, Allah ya bar zumunci.
Jinjina ta musamman ga constant Facebook followers of Moon, musamman
Abdul A A Rasheed wanda zan iya cewa shine first fan dina kuma ya cigaba da bin littafin maimoon har karshen sa. Ahmad, Salahuddeen Dama, Sadiya Usman Aliyu,
Yagana Babakura, Fadyla Ingawa , Ummi Ummusalma,Zeeta Aliyu , Aisha Aysha Muhammad Deejarh Muhammad , Bashir Muhammad Rahama , Maimuna, Nafisat Usman Tafida, Jamila Jibril , Nafisat Saleh , Muktar Ahmad, Hadiza UssainAdamu , Abdoulmaleeck Saleh, mata mutanenmu na amana, Ummu Kaltume Aminu , eve mohd, Abdulmajeed,
Zainab M Alhassan , Barkhe, It's B Y Ibrahim, da sauran wadanda karancin lokaci ba zai bar ni in fadi sunan su ba, ba wai dan ban san dasu bane. Allah ya bar zumunci, Ameen.
Maybe zan cigaba da rubutu, may be not, amma ko da zan cigaba din to ba nan kusa ba. Kamar yadda rana daya na tashi na fara rubuta Maimoon haka maybe wata rana zan iya tashi in fara rubuta wani.
Nagode
Alhamdulillah.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login