Showing 102001 words to 105000 words out of 262297 words

Chapter 35 - Maimoon Hausa Novel Complete

tace "I don't know you anymore, Moon din dana sani ba zata bi saurayi gidan giya ba, Moon din dana haifa na raina ba ita ce wannan a gaba na ba. Just answer the question" sai yanzu sannan hawaye suka zo idona, na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ta sake cewa "just answer the question, tun yaushe yake kaiki bar?" Nace "wallahi mommy ban tana shan komai ba. In baki yarda ba kisa ayi min drug test" tace "OK, ina son ki gaya min komai and I mean everything da ya faru tsakanin ku" nan na fara bata labarin tun haduwar mu dashi a abuja har komawar mu England shima ya bi mu, sannan na bata labarin bina da yayi America da duk abinda ya mu kayi a can amma na cire labarin abinda ya faru ranar da zan dawo, oh no I can never tell her that, sannan na bata labarin dawowar mu Nigeria da plans din mu na kai maganar gaban iyayen mu, na gaya mata kuma abinda ya faru tsakanin su da yaya Habeeb da kuma bin Amir da nayi zuwa gurin sultan. Na kara da cewa "mother, he is not a bad person, he is a good person. Dan Allah ku tsaya ku fahimce shi" ta yi ajjiyar zuciya tace "you are not as smart as we all thought you are, moon he is playing you. Mutane irinsa abinda suke yi kenan, su samu yarinya kamarki su yaudare ta su bata mata rayuwa suyi dumping dinta. Tunanin ki bai taba baki cewa duk wadanda suke zuwa suke baki labari akansa shi ya ke turo su ba?" Na girgiza kaina nace "mother this is for real, wallahi da gaske ne, I trust him" ta mike tsaye tare da ajjiyar zuciya tace "Maimoon, you are no longer allowed to see or talk to Sultan in dai na isa dake" na fado daga kan gadon na rike kafafuwanta, ina kuka nace "Mommy kiyi min rai, mommy wallahi in kika raba ni dashi mutuwa zanyi, purnish me duk yadda kike so dan Allah karki raba mu" ta kwace kafarta taje bakin kofa tace "you really have no idea about your situation. Already munir yayi waya 'yalleman ya gaya musu abinda ya gani jiya, it is just a matter of time kafin baffa ya turo a bincika masa, so you really understand why I want you as far away from sultan as possible? He is who he is and you are who you are" ta bude kofa ta fita ta barni a durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha. I can only imagine yadda Hajja zatayi ta yawo da maganar nan. Allah ne kadai yasan irin karyar da munir ya kara akan abinda ya gani din. Na dafe kaina daya fara sara min.

Washe gari da assuba mommy ta shigo da breakfast a hannunta ta saka ni a gaba na ci, sannan tace in tashi inyi wanka, naje naji na fito na tarar ta ajiye min kaya har da underwears akan gado tace in saka, a raina nace ina zamu je kuma da sassafen nan? Ni dai na shirya na zauna ina kallonta, ta kalleni cikin ido tace "you are going on a journey, ke da daada, ba za ku dawo ba har sai kin manta da Sultan" na durkushe a gabanta nan da nan na fara kuka ina rokonta, ko saurare na bata yi ba, tace it's for my own good, a karshe dai nace mata "mommy, ina son magana da daddy" tace "mun riga munyi maganar dashi, shine ma ya bada wannan shawarar" mommy is a bad liar, in dai tayi karya sai an gane, ina kallon fuskarta nasan daddy bai san maganar tafiyar nan ba. Zata tura ni wani gurin da Allah ne kadai yasan inane, ba tare da sanin daddy ba ballantana wani dan haka Allah ne kadai yasan ranar dawowata. Allah gani gare ka.

When everything seems lost, always have hope. Have faith that God is planning something for you. Believe that God's plan is the best.



Episode Fifty Two : The Journey

Munir, ni mai nayi wa Munir a rayuwa? Kawai dan nace bana son sa? Ai ba yaudarar sa nayi ba, tun farko na gaya masa bana sonsa kuma ni ban saka shi lallai sai ya jirani ba shi yaga dama. Na gane mugun nufinsa so yake yayi ruining reputation dina yadda lallai koda na dage bana donsa sai iyayen mu sun tilasta min na aure shi. Ni kam ban masan me zanyi ba in aka aura min Munir. Ina nan a durkushe a gurin ina hawaye har ta dawo, daga bakin kofa ta tsaya tace "let's go" na kuma rike kafarta "mommy dan girman Allah ki bani wayata, wallahi ba sultan zan kira ba, mommy dan Allah ko Hafsat ki barni inyi magana da ita" ta hade rai tace "am not stupid Moon, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba, in dai har zan baki waya menene amfanin kaiki wani gurin. Tunda har kika san ki fita daga gidan nan ki tafi gurin saurayi ai zaki iya komai moon. Moon daga bar fa aka dauko min ke kina warin giya. Moon kece fa har da daukar saurayi ku tafi wani kasar. Duk abinda nayi miki har kina da bakin rokona mercy. In dai har ni na haife kiba zaki kara ganin yaron nan ba har abada. Kuma in dai har ni lawyer ce sai na tabbatar yaron nan yayi jail time saboda ya zama darasi a gare shi da sauran masu hali irin nasa" sautin kukana na kara, tashin hankali na shine jin tace sai ta rufe sultan, sanin halin mommy i know she is not bragging. "Mommy kiyi min rai dan Allah karki taba Sultan, dan Allah ni kiyi min komai, laifi nane, ni naje gurinsa bashi yazo gurina ba, he needs help mommy not more suffering. He will loose himself completely idan ya rasa ni kuma aka rufe shi" ta karaso inda nake tana kallona, ni kuma na sunkuyar da idona kasa tace "did you have sex with him?" Na dora hannayena aka na rusa wani sabon kukan tace "answer me, did you? How many times?" Kuka kawai nake na kasa bata amsa, mommy ta riga tayi nisa duk abinda zance mata ba zata saurare ni ba. Tace "ba zaki amsamin ba sai na kira Walid ya nakasa min ke tukunna? Did you?" Na girgiza kaina da sauri "no mommy, never" ta jima tana kallona kafin tayi deciding gaskiya nake fada, tace "tashi mu tafi" nace "ban dau kaya ba ai" tace "no need, na hada miki already" na juyo na kare wa dakina kallo, sannan na fita ta biyo ni a baya. Babu kowa a palo, haka ta tisa keyata muka fita waje, daada na gani a tsaye gaban motar mommy, baya mommy ta saka na ta rufe kofar ta zagaya zata shiga drivers seat. Yaya Habeeb na hango ya fito daga part dinsu da gajeran wando da singlet, daga dukkan alama jogging zai fita, tsayawa yayi da sakakken baki yana kallon mu muna shiga mota, wannan shi ya tabbatar min da cewa suma basu san da wannan tafiyar ba, da sauri ya karaso "Moon ina zaku je" bani da amsar da zan bashi sai kawai na daga masa hannu alamar 'oho' ya karasa gurin mommy tun kafin ya karasa ta watsa masa harara, ya juyo ya sake kallo na sai kuma ya juya da sairi yana kwalla wa ya Walid kira, tun kafin ya shiga part din nasu mommy ta ja motar dan haka ya tsaya kawai yana kallon mu, munje gate na juyo naga ya Walid ya fito shima ya tsaya yana kallon mu fuskarsa dauke da mamaki.

Titi babu kowa dan haka mommy ta ke kwarara gudu san ranta, ta gaban palace muka wuce, na kalli gate din ina lissafin ko Sultan yana ciki? Na lumshe idona knowing this is the closest I can get to him. Airport muka je, a raina nace kasar zamu bari kenan gaba daya. Muna zuwa muka fito muka shiga waiting room muka zauna, ni dai bance musu komai ba, sai da aka fara kiran flight naji an kira Niamey sai naga sun mike, zuciyata naji tayi min fari kal, dan dai Niamey ai bani da problem, wato mommy gidan su zata kaini kenan, ina zuwa zan karbi waya a gurin cousins dina na can in kira daddy in kira Sultan. Na mike da kwarin jikina, amma ban saku fuskata ba dan kar ta gane ban damu da zuwa Niamey ba. Wata jaka ta miko min tace "ga magungunan ki nan kullum zaki rinka shan dai dai" na duba naga magungunan hawan jini nane, watk mommy tasan sai jini na ya hau shine ta dauki precautions. Na rungume ta ina hawaye nace "am sorry I failed you mother" ta dan shafi bayana kadan sannan tace "it's ok, Allah ya kiyaye hanya" daganan ko fuskata bata kalla ba ta juya ta fice daga gurin. A jirgi hankali na a kwance muke tafiya, ni ce har da bacci, dan nasan 'yan Niamey sosai dan haka bani da matsala. I will come back to Nigeria in less than a week. Hmm

11 na safe a Niamey tayi mana, muka dauko kayan mu muka fito, muna fito wa na fara wara idon ganin motar da zata dauke mu, dan nasan duk sanda muka je Niamey wani cousin din mommy ne yake zuwa daukan mu, babu shi babu alamar sa. Taxi naga daada tana tsayarwa, na karasa gurinta naji suna magana da mai taxi din da yaren da ban sani ba, abinda na fahimta kawaj shine kudin da ya gaya mata, kudi ne masu yawan gaske, ya fito ya fara zuba kayan mu a mota, nace "daada ina zamuje ne?" Tace "zaki gani ne ai" nace "daada ko ma ina zamuje mu fara zuwa gidan su Ahmodou mana mu gaisa, kinga sai mu huta acan" bata kulani ba ta tura keyata cikin mota sannan itama ta shigo. Tun muna tafiya ina gane titunan da muke bi har muka fara shiga inda ban sani ba, daga baya muka dau hanyar barin gari, ni maimunatu na shiga uku, ina zamuje ne? Ni in banda Niamey ban taba zuwa wani gari a Niger ba, na sake cewa "daada ina zamu je ne?" Direct tace min "Tahoua" na kwantar da kaina a jikin window ina kallon jefi jefin bishiyoyi suna wucewa, Tahoua, nasan sunan garin amma a iyakacin sani na bamu da 'yan'uwa acan. Lallai mommy da gaske take, na danyi murmushin takaici nace a raina 'tace bazan dawo ba sai na manta da Sultan. Bata san sai da ya dauke ni shekara biyar ba kafin in chire Ibrahim daga raina ba? Sultan kuwa nasan kuwa nasan zan tafi dashi ne a raina zuwa kabari na' a haka bacci ya dauke ni, can naji daada tana tashina, na dauka munzo ashe tsayawa mukayi sallah, cikin sahara, dan gurin da muka tsaya ko 'yan bishiyoyin babu, ni dai a tsorace nayi sallar na koma mota. Bayan mun kuma daukan hanya daada ta dauko wata food warmer da soyayyun kaji a ciki ta hado min da ruwa da lemo ta miko min, na diba na zubawa drivern na mika masa. Ni lemon kawai nasha dan sam bakina babu taste.

Sai bayan magrib muka isa Tahoua. It is worse than I imagine. Gidan da muka je gidan kasa ne rufin azara, cikin wata chakudaddiyar unguwa. Ji nayi gaba daya hankali na ya kuma tashi, yanzu mommy tana nufin anan zan zauna har sai ranar da ta waiwayoni? Muna shiga muka tarar da wata tsohuwa tana kirki a itace, da mamaki ta taso ta tari daada, suka rungume juna suna ta murna, ni dai 'yar kallo ce, ta kaimu wani daki mai dan girma wanda ko siminti babu sai kasa. Ta shimfida mana tabarmar karauni muka zauna na gaisheta tana kallona tace "tubarkallah, daada ina kika samo 'yar kyakykyawar yarinya haka?" Daada tace "diyar bintou ce fa" tace "hidijan, yanzu bintou ke da diya kamar wagga?" Daada tace "laa wagga ita atta hudu" matar tace "alqur'an daada wagga ya kamata a amra mata dan'uwa ta zamna a Niger" ina jika na mike nace "ina ne bandaki zan zagaya?" Matar ta taso ta rakani, shaddar kasa, na kasa tsugunnawa na fito nayi alwala nazo na tayar da Sallah. Ina yin sallar isha na shimfida zanina na kwanta na lulluba da hijab dina, ba bacci nake ba, so nake inji hirar su daada dan insan halin da nake ciki, ga mamakina ko zance na basu yiba, labarurrukan da kawai suke yi suna dariya. A cikin hirar naji daada tace ai akan hanya muke, tsayawa mukayi mu huta, Agadaz zamu je. Zumbur na mike daga kwancen da nake nace "Agadaz daada? Daada Agadaz fa karshen duniya kenan?" Cos haka muke cewa sanda muna yara. Daada ta harare ni tace "dama ba bacci kike ba ko?" Nace "dan Allah daada Agadaz zamu? Wa muke dashi a Agadaz? Mommy ma da kanta tace bata taba zuwa ba saboda nisan garin? Daada me laifi na har ya kai girman haka?" Sai kuma kuka. Ina jin matar tana ta yiwa daada tambayoyi amma bata ce mata komai ba, aka kawomin abinci naki ci, daada ta dauko min magani na ta bani tasa lallai sai da na sha. Ranar sam banyi bacci ba, ga gajiya ga tunani, da zarar baccin ya daukeni kuwa zanyi ta mafarke mafarke, most of them na Sultan ne kuma duk basu da dadi. Daga karshe dai na tashi zaunr na hade kai da gwuiwa nayi ta rera kuka na. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan insan halin da Sultan yake ciki. Ni kaina ina tsoron zuciyarsa. Sai ya hargitsa garin Abuja gaba daya. Sai gab da assuba sannan nayi bacci, cikin baccin naga sultan a cikin gidan mu yana bi daki daki yana nemana, yana bude dakin mommy ta dauko bindiga ta harbe shi. Na farka a tsorace ina ta jero adduoi. Naji ana kiran sallah na tashi nayo alwala nazo na fara nafiloli ina ta jero wa Sultan addua, ni ban damu da kaina ba, duk abinda mommy zatayi min nasan ba zata taba chuta ta ba, amma shi bashi da kowa sai Allah. Mommy lawyer ce, zata iya creating case against him wanda dole alkalin ya dauke kansa daga ganin cewa dan sarki ne ya rufe shi, babansa kuwa ko dan yatsa ba zai daga ba ballantana ya damu. Hope dina kadai shine daddy, shi kadai ne zai taka wa mommy burki. Amma bansan shi kuma yadda zai dauki al'amarin ba, saboda shi daddy baka ta ba gane inda ya sa gaba saboda kwarjinin sa. Ana yin assalatu na tashi daada sannan na tayar da sallar, na idar ina azkar naji tana gayawa matar ta aika a samo mana mota shata. Karfe shida muka shiga motar, kawar daada ta hado mu da kunu da kosai wai ma ci a hanya. Motar hilux ce saboda sahara. Muna baya ni da daada kayan mu kuma suna gaba tare da driver. Tun karfe shida muke tafiya har karfe uku na yamma sannan muka tsaya muka yi Sallar azahar da la'asar muka cigaba da tafiya. Lallai Agadaz akwai nisa, nayi baccin har na gaji, nayi tunanin har kaina yana neman bugawa. Ko bishiyoyin ma babu, inka leka ta window yashi kawai zakayi ta gani babu iyaka. Daada tayi tayi dani inci abinci naki ci. Rabona da abinci tun wanda mommy ta takura min naci ranar da zamu taho. Mun daga nesa na hango garin. Babban gari ne babu laifi amma ko irin 'yan kauyukan kan hanya din nan babu kawai sai dai ka ganshi a gabanka a tsakiyar sahara. Muna shiga garin daada ta gaya wa drivern in da zai tsaya, ya tsaya amma maimakon inga mun fito sai naga mun zauna a mota muna jira, can sai ga wata katuwar Jeep ash color ta tsaya a kusa damu, wani saurayi ne ya fito ya kara so windon da nake yace "baki daga Nigeria?" Hausar shi tas kamar dan kano. Na dauke kaina kamar ban ji shi ba dan ni kowa ma haushi yake bani. Daada ce ta amsa masa da murmushinta tace "eh mune, mustapha ne ko musbahu?" Yayi dariya yace mata "Mustapha ne daada" ya kalleni yace "Hafsat ko Moon" ya sake bawa iska ajjiyarsa. Daada ta kama fada ni bama abinda take cewa nake ji ba, ya bude min kofa shima yana magana amma bana gane me yake cewa. Ina fitowa daga motar jiri ya debe ni sai kasa. Da sauri ya zo zai rike ni na daga masa hannu nace "Don't touch me" ni na manta ma 'yan Niger basa turanci, amma ga mamakina sai naga ya ja baya yace "just trying to help" daada ta zagayo da sauri ta rike ni muka tashi tsaye, muna tashi kuwa nayi mata wanka da amai, babu komai a cikin aman nawa sai ruwa. Sama sama nake jinsu suna ta yi min sannu. Daada tana cewa "bata taba yin tafiya me nisa irin wannan ba ne shi yasa, kai wannan gari naku da nisa yake" ni dai aka sakani a mota na kwanta ina jin dadin sanyin ACn motar. Ina jin alamar muna tafiya amma babu damar in dago kai in kalli gari saboda jirin da nake ji. Naji horn kuma naji an bude gate, daganan naji mun tsaya. Daada ta riko ni muka fito tare, inajin saurayin yana yiwa wata yarinya French sai naga tazo ta kamani itama muka shiga cikin gidan. A palo suka kwantar dani akan doguwar kujera. Mustapha ya sake aiken yarinyar sai gata da cup din tea mai zafi ta kawomin, na karba nace "graciers" na ringa kurba a hankali har sai da na sanye. Sai a lokacin na samu idon kallon palon. Yana da girma kuma an cika shi da kayan alatu, daga dukkan alama mutanen gidan basu da matsalar kudi. Daada ta shigo daga alama sallah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login