Showing 162001 words to 165000 words out of 262297 words

Chapter 55 - Maimoon Hausa Novel Complete

dora hannuna a kafadarsa nace "am sorry sultan" ya ture hannuna daga jikinsa ya juyo yana kallona da idanunsa da suka fara sauya color zuwa ja, yace cikin daga murya "why? Na sha tambayar ki in akwai wani wanda ya kamata in san da zaman sa amma kika ce min babu" kafin in bashi amsa naji muryar Ibrahim yace "sai ka tambayi kanka me yasa bata ba ka labarina ba, maybe it is because she is still in love with me" nan take idon Sultan ya karasa yin ja kamar garwashin wuta, ya juyo a fusace yace "please somebody should shut up that man for me" tun kafin ya rufe bakin sa kusan mutum biyar suka yi kan Ibrahim suka fara duka, durkushewa nayi a gurin na dora hannu na aka na fara rusa kuka ganin yadda suke ball da Ibrahim ta ko'ina. Banda Solomon wanda yake zaune a gefe ya dora kafa daya kan daya shan abinda yake cikin kofin hannunsa, wanda ko ba'a gaya min ba nasan irin abinda sultan yake sha ne, a cikin gida na ranar da aka kawo ni. Na rike rigar sultan ina kuka guiwowina a kasa "dan Allah Sultan ka kalle ni kaji abinda nake gaya maka, please ka hana su dukansa dan Allah" kamar wanda na kara tunzura shi ya juyo yace min "why? Me yasa ba kya so su dake shi? Saboda abinda ya fada gaskiya ne, saboda still kina sonsa?" Nayi saurin girgiza kaina nace "I don't love him sultan, I Love You, I chose you, I marry you. Menene kuma ya rage?" Cikin fada yace "you marry me sannan kika gayyato tsohon saurayinki cikin gida na?" Ban san sanda na dake shi a kafada ba nace "how can you say that? Come back to your senses Sultan" bai ce min komai ba sai tsayawa da yayi kamar mutum mutumi yana kallona, ta gefen idona na hango Solomon ya taso ya taho inda muke, yana karaso wa ya mika wa sultan kwalbar da take hannunsa, ba musu ya karba, da sauri na na fincike daga hannunsa na zubar da abinda yake ciki a kasa. Solomon ya saki baki yana kallona kafin ya fara magana "ni dama tunda aka bani labarin cewa our sultan has fallen in love with a good girl, nasan cewa we lost him, Sultan din dana sani ba zai zauna ayi masa irin cin mutuncin da aka yi maka ba, this means nan gaba sharing dinta za ka ke yi da sauran samarinta, only God knows su nawa ne, tunda baka san da wannan ba sauran ma ba zaka sanda su ba sai dai ka gansu a kan gadonta" a zuciye sultan ya juya ya kai masa duka yana cewa "shut up, damn you" ya rike hannun sultan yace "in baka son hakan ta faru then end it here, ka nuna min cewa har yanzu baka yi loosing guts dinka ba over a woman" hannunsa ya saka a aljihu ya zaro wani abu, ganin abun kawai ya saka naji wani zazzabi yana neman ya sauko min, Ya Allah intervene. Tunda nake ban taba ganin bindiga ba sai a film amma yau wai gani ga ita a daren farko na na aure. A hannun sultan ya saka bindigar yace a hankali "shoot him between the eyes, in kayi haka sauran babu wanda zai sake zuwa" gaba daya jiki na karkarwa yake yi dan bana jin bakina zai iya budewa har inyi magana. Amir ne ya karaso gurin da sauri fuskarsa cike da tashin hankali yayi kokarin karbar bindigar daga hannun sultan amma Solomon ya ture shi yace "stay out of this" yaje ya jawo Ibrahim wanda akayi wa laga laga, ya ajiye a gaban Sultan yace "Shoot him" na kama hannun sultan daya ke rike da bindigar nace "Sultan no" a hankali sultan ya dago kansa ya kalli Solomon yace calmly "no, I will not shoot him" ya juyo da jajayen idanunsa kaina ya ce "kince min you chose me over him, let's find out in gaskiya kike fada" ya saka min bindigar a hannuna yace "choose again, me or him" kallonshi kawai nake da mamaki, this is not my Sultan, this is someone else's. "Ki zaba, in har kina sonshi then put a bullet in me, in har kuma ni kike so kamar yadda kika fada then put a bullet in him" sama sama na ke jin sauran maganganun, naji Hafsat tana cewa da Sultan "baka da hankali Sultan? Menene hakan kake yi" na daga mata hannu alamar tayi shiru ba tare dana kalleta ba, no body will get hurt again a saboda ni, naji Solomon yana yiwa Sultan masifa "what if she shoots you?" Sultan yace "then so be it" Amir naji a kusa dani yana magana shima "Moon give me the gun" a hankali na fara jero sunayen Allah a zuciya ta, a take naji duk wani tsoro ya kauce min, na fahimci duk hikima ta ubangiji akan abubuwan da suka faru. This is a battle, Sultan's battle, between his good side and his bad side, I am his good side and Solomon and his other bad friends are his bad side. Yanzu na fahimci komai, na fahimci hikimar ubangiji da ya dawo da Ibrahim cikin rayuwata a wannan lokacin. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, it is destiny amma ba destiny din zamuyi aure ba. Allah ya dawo da Ibrahim rayuwar mu ne saboda yana son yayi amfani dashi yayi testing Sultan, wannan duk jarabawa ce, ni kuma zanyi iya kacin kokarina inga na taimakawa Sultan gurin cin wannan jarabawar. I now understand everything and I know exactly what to do. Na gyara rikon bindigar a hannuna, it is heavier than it looks. A hankali na dago idona ina kallon rinannun idanun sultan, na motsa bakina na furta I Love You amma ba tare da sauti ba amma na tabbatar ya fahimci abinda nace. Na daga bindigar a hankali ina kallonta, cikin second daya na juya ta zuwa kaina sannan na lumshe idona na dora dan yatsa na akan trigger kamar mai niyyar harbawa. Exactly abinda nayi tsammanin zai faru shi ya faru, kafin in dora dan yatsa na akan trigger Sultan yazo gurin ya doke hannun bindigar ta fadi kasa, dama ba wani rikon kirki nayi mata ba, tana faduwa ya kankame ni tamkar zai tsaga kirjinsa ya sakani a ciki, jikinsa gaba daya karkarwa yake yi. This is my chance, a hankali na fara yi masa magana, yadda babu wanda zai ji daga ni sai shi "Na zabe kane saboda ina sonka, na aure ka saboda ina sonka, ban gaya maka labarin saba saboda bana son in bata maka rai, amma ina son ka sani, babu sauran sonsa daya rage min a zuciyata saboda zuciyata taka ce. Bani nace yazo ba kuma bansan menene yasa yazo ba. Na ce maka ka hana dukansa saboda nasan cewa kai mutumin kirki ne, kuma mutanen kirki basa rama sharri da sharri, mutane ne masu afuwa masu tausayi, mutanen da ubangiji yake alfahari dasu. Nayi kokarin hana ka harbin sa not because I care about him but because I care about you. Kisan kai yana daya daga cikin manyan laifuka da Allah baya so, bana son ka dauki zunubin sa akan ka. Na juyar da bindiga kaina ne saboda in nuna maka how much I Love You. I Love you more than my life it self". Ya jima yana rike dani sannan ya sake ni ya juya da sauri gurin da Ibrahim yake yace masa " GO. But I swear to God, in na kara ganin ka ten miles close to my wife I Will Shoot you". Hafsat ce da Amina suka zo gurina, na rungume daya daga cikin su ba tare da nasan ko wacece ba. Ina jin hayaniyar gang bang "Sultan ya za'ayi ka bar shi ya tafi?" "Har cikin gidan ka fa ya shigo gurin matar ka, har yana ce mata ta gudu daha gurinka" "lallai Sultan ka zama nusari, you are no longer one of us" Sultan yace "gida na ne, kuma matata ce, kuma ni nace masa ya tafi. Duk wanda yake da problem da decision dina will settle it with me" ta gefen ido na naga Amir yana fita da Ibrahim da ga gurin, sannan kuma daya bayan daya suka fara fita, Sultan ne na karshen fita.

Gurin ya rage mu uku kadai, ni Hafsat da Amina. Idon Amina kawai na kalla nasan taci kuka ta koshi, tace "Moon dan Allah kiyi hakuri, wallahi bansan da akwai wani abu a tsakanin ku ba, da nasan haka zata faru wallahi da ba zan shigo dashi ba" na dafa kafadar ta nace "it is OK. Komai ya wuce ai. I have won" Hafsat ta dauko wayarta tace "yanzu zan kira daddy in gaya masa, gwara ya san matakin da zai dauka tun yanzu. In auren nan ba zai yiwu ba gwara a fasa shi kawai" na rike hannunta nace "me za'a fasa? Already an riga an daura. Menene amfanin gaya wa Daddy in banda tayar masa da hankali da zaki yi? Tun kafin a daura auren nan daga ni har Daddy mun san challenges din da zanyi facing. Tunda har yau na iya controlling Sultan na hana shi aikata mummunan aiki duk kuwa da cewa yana cikin tsananin fushi, duk da cewa a buge yake, bana jin akwai wani abu nashi da ba zan iya facing ba"



Episode Seventy : The Wedding Night 3

Kafin mu dora a inda muka tsaya, bara mu dan taba magana akan abinda ya faru ranar kai amarya.

Abinda ya faru ba laifin Ibrahim bane gabaki daya, Moon tana da laifi haka zalika Sultan. Laifin Moon anan shine keeping secrets in a relationship. Wannan shine babban abinda yake wargatsa relationships, ko aure ko kafin aure. Idan kinsan ko kasan da akwai wani abu da kake ko kike boyewa partner dinki/ka to ku fito ku fada, ko da kuwa abinda zai bata masa/ta rai ne, gwara ya/ta sani daga gurin ki/ka akan suji daga wani guri, idan ke zaki fada kinsan da kalaman da zaki yi amfani, idan kuma wani ne zai fada zai iya ya kara har da gishiri da maggi kuma babu yadda zaka/ki yi ka/ki kare kanki. Wannan kuma shi zai kawo rashin yarda, ita kuma yarda da juna ita ce ginshikin ko wanne relationship.

Laifin Sultan kuma shine na yarda ayi organising party a cikin gidansa, wannan mistake ne babba. Ba tsohon saurayin matarka ba hatta su kansu abokanan ka basu da hurumin shigo maka gida irin haka. Ni a ra'ayina ina against siyan bakin amarya da abokanan ango suke zuwa yi. Kwanan baya anyi ta samun cases na raping amare, ni ina ganin wannan siyan bakin da kuma yawan kwashe2n abokanai zuwa ganin amarya yana daya daga cikin abinda yake kawo wadan nan cases din. Ballantana wanda yake da abokanai irin na Sultan.

Laifin Ibrahim kuma shine da yabar emotions dinsa sukayi controlling dinsa ya yanke hukunci ba tare da bincike ba. Babban mistake din da mutum zai yi shine ya yarda da maganganun mutane. Hear say. Wannan ya kara gishirinsa, wancan ya kara maggi wancan ya kara onga, before you know it gaba daya maganar zata chanza salo. Believe only what you see da idonka, ko kuma maganar da kaji direct daga mai ita, ba wai wani ya gaya maka yace wane yayi kaza ko kuma wane yace kaza ba.

Please guys, be a little softer on Ibrahim. He has gone through alot akan soyayyar Moon. He really deserves a break. Amma naga kowa dariya yake masa. Lol. Ni kam #teamIbrahim nake yi, na hana shi auren Moon ne kawai saboda a haka ne ma'anar labarin zata fi fitowa. Please, I am on my knees ku dan rangwanta masa mana.

Back to the story.
Mun jima muna tattaunawa akan abinda ya faru, anan ne Hafsat ta bawa Amina labarin alakata da Ibrahim, yadda Amira ta raba mu da kuma labarin rayuwar Sultan, Amina duk jikinta yayi sanyi ta kasa maganar kirki. Na durkusa a gabanta na rike hannunta nace "Amina, sam yanzu bana yiwa Ibrahim soyayyar aure, amma still ina jinsa a raina kamar dan'uwana haka nake jinsa. Na tausayawa rayuwar da yayi bayan rabuwar mu kuma ina tausayin halin da yake ciki a yanzu. He thinks he is doing a good thing. He thinks I am in trouble. He needs an explanation. He needs to know the whole truth. Dan Allah Amina ina son kiyi reaching out to him kiyi masa bayani yadda zai gane sosai cewa ni na zabi sultan duk da halayensa. Kiyi masa bayanin cewa sultan is not as bad as people think ge is. Ki bashi duk wannan labarin da muka baki yanzu ki gaya masa cewa na auri sultan saboda ina sonsa, saboda ina ganin soyayyata zata kawar da duk wani mugun hali nasa, kuma so far I have succeeded. Ki gaya masa kyaleshin da Sultan yayi yau alama ce ta cewa he is no longer who he was before" tunda na fara magana Amina take girgiza kanta alamar ba zata yi ba, ni kuma ban daina maganar ba har saida nazo karshe, tace "No, Moon, bazan iya ba, ba zai saurare ni ba, yaudara ta fa yayi ya saka na shigo dashi har cikin gidan ki" na kara rike hannunta nace "please Amina, you are my only hope akan sa, duk da yadda nake son in taimaka masa ba ni da yadda zanyi sai ta hanyarki kadai, please help me as your sister" da kyar na samu tace maybe zata yi in ta huce saboda taji haushin using dinta da yayi. Muna cikin haka Amir ya dawo yace amina tazo ta taya shi su kwashe abincin partyn da ba'ayi amfani dasu ba, wadanda ba zasu lalace ba suka shiga dasu suka adana, wadanda kuma zasu baci Amir ya aika dasu cikin gida. Ni da Hafsat kuma muka shiga ciki muka koma cikin bedroom dina muna cigaba da jajantawa, kafin su Amina su gama sai around 12:30, dan haka dole kwana ya kamasu a gidan. Hafsat ta kira zayed wanda tunda yazo bikin ya kama hotel, kullum da daddare yake lallabowa ya dauke matarsa sai da safe yake dawo da ita, ta gaya masa zata kwana a gida na saboda dare yayi. Sai da duk mu kayi wanka muka yi shirin kwanciya sannan naga sun tashi suna yi min sallama wai wani dakin zasu tafi su kwanta. Nace "saboda me?" Hafsat ta harare ni tace "oho miki, yau ne fa first night dinki, kawai kuma sai muzo muyi dare dare akan gado? In angon ya shigo kuma fa?"

Na kasa basu amsa har suka fice. A raina nace "wannan angon nawa ai Allah ka dai yasan inda yake" nayi tunanin in kira wayarsa inji ina yake amma kuma kar ya dauka wani abin nake nema. Na kwanta ina kallon dakina, karshen kyau yayi kyau, babba ne sosai dan duk girman gadon baifi quarter din dakin ba, babu ce kawai a kayan da ake bukata a daki Daddy da Mommy basu saka min a dakina ba. Komai yaji, komai da akwai except ango. Ina Sultan ya tafi? Na gyara nayi kwanciyata duk jikina yana yimin ciwon gajiya amma sam babu bacci a ido na, nafi 30 minutes a haka sai kuma na mike zaune na jawo wayata nayi dialing number dinsa, switched off, yayi fushi, nasan he has the right na yin fushi dani amma abinda yafi damuna shine abinda zai aikata a cikin fushin nasa, ya Ilahi give me the strength. Number din Amir na lalubo na kira, bugu daya ya dauka da alama bai kwanta ba, sai kuma na rasa mai zance masa, yace "Moon baku kwanta ba? Ko akwai abinda kuke bukata ne?" Nace "amm babu komai, dama ina son inji ko Sultan yana tare da kai ne?" Yace "No, ban ganshi ba, na dauka kuna tare ai" nace "a'a ai tunda ya fita bai dawo ba" na dan yi jim sai kuma yace "OK bara in duba shi" na zauna akan gado na harde kafata ina jiran tsammani, can Amir ya kira ni yace "naje har gate na tambaya sunce bai fita ba, kuma naga duk motocinsa da suke gidan nan suna nan, yana cikin gidan, kin duba part dinsa" na girgiza kai kamar yana kallona nace "a'a ban duba ba" yace "ok, ki duba can" nace "to na gode" sai kuma yace "Moon, he will be alright, Sultan is a tough guy, ya fuskanci abubuwan da suka fi wannan kuma yayi surviving. Idan kin duba baki ganshi ba just kiyi baccin ki, let him be, mostly in yayi zuciya yana rufe kansa a wani gurin ne ya zauna shi kadai har sai ya huce, you will be surprise in yazo zaki ga kamar ba'ayi komai ba" na ce "OK, thank you Amir, really thank you, for everything" yace "you are welcome". Banje part din Sultan neman sa ba, na dauki shawarar amir, I will let him come back on his own. Na koma na kwanta ina tunanin lamarin duniya, kana taka Allah na nasa, na tuna irin threats din da sultan yake min akan first night din mu, amma gashi ranar tazo, kuma anyi auren , kuma muna gida daya amma kuma zamu kwana a separate bedrooms. Na tuna baccin mu na jiya akan balcony da abinda ya gaya min sanda muka tashi, nayi murmushi ni kadai. I don't know a ina Sultan yake yanzu, but I know one thing for sure, he is not going to sleep tonight.

A hankali na bude ido na, ji nayi kamar yanzu na kwanta, amma kuma ina jin a jikina kamar gari ya waye, nayi sauri na kalli window naga haske yana shigowa. Na mike zaune da sauri na kalli agogo, 8:30, inna lillahi, ko sallar asuba banyi ba, na shiga uku, wannan wanne irin bacci ne kuma ko juyi banyi ba. Da sauri na shiga toilet nayo alwala nazo na gabatar da sallah sannan na tashi na gyara gadon dana kwanta na koma toilet nayi wanka na dawo daki, tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login