Showing 249001 words to 252000 words out of 262297 words
zanen sultan dana taba yi, exactly irin wancan sai dai a wannan ma na kara abubuwan da na kara a wancan. Ina cikin zanen sultan ya shigo, ya zagayo bayana ya tsaya yana kallon zanen yace "hmmm, wannan shine plan dinki?" Nace "yes" ya kalli zanen yace "ni fa nace miki shape din kaina ba kamar mangwaro bane ba. So kike ki rage min kasuwa dan kar wata ta shigo ko?" Kalmar watan daya fada naji ta daki kirjina, kawai sai na hango shi a idona tare da wata, na ajiye pencil din hannuna na rufe computer ta na mike tsaye, ina jinsa yana yi min dariyar ganin yadda na bata raina amma ko kallonsa banyi ba saboda wani haushinsa da nake ji. Ya rike hannuna yana kokarin juyo dani in kalle shi amma naki, ya rabu dani ya rungume ni ta baya ya saka kansa a wuya na yace "fushi kika yi Love?" Bance masa komai ba, yace "wasa fa nake miki" nace "I know, but it still hurts" yace "rikon da kika yi wa zuciyata Moon bana jin da akwai wacce take da karfin karbarta a hannunki. My heart was made to love you, only you. I was born to love only you. Ban taba son wata ba kafin ke kuma bazan taba son wata ba bayan ke. Only you" ya juyo dani yace "to yimin murmushi mana in gani" na sunkuyar da kaina ina son in dan kara tsahon fushin nawa, chakulkuli ya far yi min, nan take na fara dariya har kamar zan fadi, yayi saurin rike ni ya hada da jikinsa shima yana dariyar. Muka juya muna kallon zane na, yace "to taya zaki raba wa mutane? Binsu za kike yi gida gida kina basu?" Nace "Nope, am going to use a helicopter" bude baki kawai yayi yana kallona.
Amir na kira a waya na gaya masa duk abinda nake so, wajan azahar yazo muka sake yin maganar dashi, na cire pages din dana keso na bashi a flash, na dauko kudin dana san zai bukata na bashi amma yaki karba ya tafi. Da daddare sultan yana gurin Takawa ni kuma ina zaune ina cin abincin da Ummee ta aiko min dashi sai ga wayar Mommy, na dauka na gaishe ta tace "Moon mai ya faru ne?" Nasan maganar da take nufi amma nace "Mommy akan me fa?" Tace "The whole of Abuja is on fire akan sultan. Yanzu friends dina sunfi uku da suka kira ni suna tambayata" a raina nace 'sako na ya isa kenan' a fili kuma nace "me ya faru ne Mommy" tace "dazu da yamma helicopter yayi ta yawo a gari yana watso takardu, unguwa unguwa, takardun zanen project dinki" sai kuma tayi shiru, jin bance komai ba tace "Moon, did you do it?" Nace "yes Mommy" tace "why?" Nace "Mommy just ke da abokan aikin ki a office ku shirya, you will have alot of cases this week".
Hakan kuwa akayi, kusan duk garin Abuja lungu da sako, unguwannin masu kudi da kuma unguwannin talakawa babu wanda bai samu sako na ba. Nan take 'yan jarida suka samu abinyi, sultan kin zuwa yayi office a satin, Takawa kuma yace a rufe gate din palace kar abar wani dan jarida ya shigo. Kamar yadda nayi tsammani, talakawan duk da sultan yake taimakawa, wadanda nasan labarinsu da wadanda ban sani ba, haka suka ringa fitowa suna gaskata maganganuna na cikin takarda ta, wadansu ma shi kansa sultan ya manta dasu, haka aka ringa dauko dukkan files dinsa na gurin police ana resolving cases din. A haka har zancen orphanages dinsa ya fito shima, 'yan jarida kam sun samu abin yi, nan suka dukufa bincike har suka tonawa dan majalissar da yace shine yayi orphanage din asiri. A satin, kusan duk jaridar daka dauka hoton sultan ne a front page dinta, anyi masa title 'Our Prince' wadansu kuma su rubuta 'Our Lion'. Sultan kam har yanzu bai ce komai ba, in ma na kunna TV ana maganar sai ya chanza channel. Ni kam babu abinda nake yi sai godiya ga ubangiji da yasa plan dina ya zama successful. Sultan's name is now clear a cikin mutane. Babu wanda in sultan ya wuce zai zage shi, ko an samu mai zagin ma, to kuwa tabbas za'a samu masu kare mishi. 'Ya'yana ba zasu tashi ana musu gorin babansu was a criminal ba. Wannan kenan.
Satin biki ya kama. Gidan mu ya chika kamar yadda aka saba in za'ayi biki. Ballantana wannan da yake bukukuwa ba biki ba. Hatta zainab din ya walid an dauko ta an dawo da ita abuja, anan za'ayi bikin baki daya. Hafsat ta dawo gidana, tace can yayi hayaniya da yawa, dan haka daga nan muke shiryawa mu fita tare. Sultan ma tunda bikin yazo kullum suna tare da su Ya walid, amma kuma hankalinsa gaba daya yana kaina, dan badan ummee ta saka baki ma ba da ba lallai ne ya barni zuwa bikin bama gaba daya. Yanzu ma kuma babu kwana, sai dai inje in wuni da daddare in dawo gida. A tare muka hada amaren mu da angwayen mu muka kama su rana daya duk a gida. Akayi mothers eve ranar thursday, ranar friday kuma za'ayi wuni, Saturday a yi daurin aure, da yamma akai amare sannan da daddare ayi dinner. An kai dinner din dare ne saboda ana son Fadila amaryar ya Habeeb ta samu damar halarta itama. Tun a ranar Thursday da daddare na lura kafafuwana sun fara kumbura, nasan wannan normal ne ga mai tsohon ciki musamman kuma ga hidimar biki da muke yi, dan haka da daddare na kwanta da wuri na dora kafata akan pillows, sam ban nunawa sultan ba saboda ba karamin aikinsa bane yace bazanje ranar wuni ba, ranar wuni muka shirya da sassafe muka fita, aka wuni ana shan shagali, sai dare sannan muka dawo gida. Muna zuwa gida Hafsat ce tayi min maganar yadda kafa ta ta kumbura suntum, tace "Moon you should stay home tomorrow, ki huta, daurin aure ne sai kai amare, dinner da daddare za'ayi kafin nan kin huta" nasan gaskiya take gaya min, I already have high bp, wannan kumburin nawa is not normal edema, it may be pre-eclampsia, amma sai nayi tunanin ai in naje goben ba wani abun zanyi ba, zama kawai zamuyi, in za'aje kai amare da dauko amarya zan iya zama na inki zuwa, sai da daddare in je dinner. Na riga sultan kwanciya dan haka na rufe jikina bai ga kumburin ba, kuma da sassafe ya fita, zasu fara zuwa bauchi daurin auren yaya Habeeb sannan a dawo abuja a daura na ya Walid da na Amina. Banbi shawarar Hafsat ba saboda ina ganin babu yadda za'ayi in zauna a gida bayan ana can ana shagali a gidan mu. Sultan yana tafiya nabi Hafsat muka tafi gida. Komai lafiya lau yake tafiya har aka yi daurin aururruka aka gama, aka zo hidimar kai amare. Dama already wadanda zasu dauko Fadila sun riga sun tafi, sai aka tafi kai zainab tunda ita ta gida ce ba sai an jira anzo an dauke ta ba. Basu dade da tafiya ba sai ga masu daukan Amina sun zo, nan fa kallo ya koma sama, duk aka fito compound ana kallonsu dan wani sabon bikin suka bude, sun yi shigar su irin ta yarabawa sunyi kyau sosai, sun taho da kaya sukace a bawa Amina ta saka, ina daga kwance naga kallo zai barni dan haka na mike nima na fita, wata 'yar matashiyar budurwa ce tazo ta tsaya gaban Amina ta karanta wata doguwar takarda mai dauke da dogon jawabi akan irin soyayyar da Ibrahim yake yi mata da alkawarin da yayi na zai rike ta amana, inta amince to ta bisu su tafi, in kuma bata amince ba to ta zauna a gida. Daga haka ta mika wa Amina hannu, Amina ta saka hannunta a cikin na yarinyar, nan take guri ya kaure da murna. Hayaniyar gurin ce tasa naji kaina yayi wani mugun sarawa, na rike kan da sauri, ganin babu wanda ya lura dani ya saka na lallaba na koma daki, ina duba hannayena naga sun kumbura suma, na kwanta akan gado na lumshe ido na ina jin ciwon kaina yana karuwa ga kide kiden da akeyi tamkar a cikin kaina suke kadawa. Na lalubi wayata na kira Hafsat amma wayar tana ta ringing bata dauka ba. Na koma na kwanta. Cikin hikimar ubangiji aka daina kidan, ina jin karar motoci alamar an tafi kai amina itama. Take naji gidan tsit dan kusan babu kowa a manya, babu kuma wanda yasan ina dakin, kowa zai dauka na tafi kai daya daga cikin amaren. Na danji kan ya rage ciwon, na tashi na nemi jakata na sha magungunana sannan na koma na kwanta. Take bacci mai nauyi ya dauke ni. Muryar Mommy ce ta tasheni, tana tabani tace "Moon dama kina gida? Ya akayi kika zauna ke kadai? Da wani abun ya faru fa?" Ni dai bance mata komai ba, tunda wani abun bai faru ba ai shikenan. Har yanzu akwai ciwon kan, na tashi zaune ina rike kaina Mommy tana ta jera min sannu, na kalli agogo naga har anyi magrib, dan haka na shiga toilet nayo alwala, ina dawowa dakin na kalli fuskata a madubi naji gaba na ya fadi, gabaki daya fuskar ta kumbura, na kalli hannayena naga har kyalli suke. I really need to go to the hospital right now amma bana son in tayar wa da mutane hankali ana cikin biki. Na tayar da sallah, nayi magrib da isha gabaki daya, ina kallon mutane sai shirin tafiya dinner sukeyi amma ni kam nasan wannan dinner din babu ni a cikin ta. Na koma nayi kwanciyata. Mommy ta shigo ta samu guri ta zauna tana kallona. Nace "Mommy baki fara shirin tafiya ba?" Tace "Moon ina zanje baki da lafiya? In naje ma ba zanji dadin dinner din ba, dan hankali na biyu zai rabu" sai naji babu dadi a raina, dan nasan kawayen Mommy da yawa zasu je gurin kuma za'ayi ta nemanta, nace "Mommy kiyi tafiyar ki kawai, ai ba wani abin ne yake min ciwo ba, kawai dai ina bukatar in huta ne shi yasa ba zanje ba" ta jawo pillow tana murmushi tace "nima ina bukatar hutun ai" nayi murmushi, dan nasan babu abinda zan gaya wa Mommy wanda zai saka ta tafi gurin dinner din nan ta barni a gida, God bless our mothers. Hafsat ma ta shigo tayi tayi Mommy ta tafi ita ta zauna amma Mommy taki yarda. Ni dai daga nan na koma bacci. Karar waya ta ne ya tashe ni, na duba naga 'my Sultan' na dauka ina jin ciwon kaina yana karuwa, yace "Moon baki fa lafiya me yasa baki kirani ba?" Ji nake kamar a cikin kaina yake maganar, nace "ai muna tare da Mommy, babu wani abu, kayi zamanka in an tashi sai kazo mu tafi gida" yace "you dey craze? Ya zanyi in zauna anan babu ke? Am coming right away" daga nan ya kashe wayar. Mommy tana zaune tace "zuwa zaiyi?" Nace mata "eh, dama ki shirya, in yazo kawai sai mu tafi gida ke kuma sai ki tafi gurin taron" ta gyada kai tace "bara yazo din tukunna sai in shirya. Ina baba gajin ki? Anan gurinki take kwana ko?" Nace "eh, anan take kwana. Ummee ma ta karo min wata baba Sa'a". Muna tare da Mommy sultan ya aiko a gayamin yazo, Mommy tace ace masa ya shigo dakin, ita kuma ta fita ta tafi nata dakin. Ina kwance ya shigo, ya tsaya a bakin kofa, na tabbatar ya lura da yadda jikina ya kumbura, yace "menene yake miki ciwo yanzu?" Nace "ciwon kai ne, sai jiri da nake ji inna tashi" ya karaso ya zauna a bakin gadon ya taba wuyana yace "your temperature is also high. BP din ne ko?" Na gyada masa kai. Yace "dama abinda nayi ta lissafi kenan. Wannan hayaniyar da zirga zirga is not good for you" na kirkiro murmushi nace "an gama ai. Babu dadi idan aka ce banzo ba, Amina babu abinda bata yi min a bikina ba. Ga su ya Walid suma ba zasu ji dadi ba" ya bata rai yace "da baki zo ba duk zasu fahimta, ai sunsan condition dinki" bance komai ba na rufe idona, dan maganar ma karamin ciwon kan take yi. Mommy tayi knocking ya tashi ya bude mata, ta shigo tana kallonsa tace "zaku tafi ne ko anan zaku zauna?" Yace "gwara mu tafi can din dai tunda yafi shiru zata fi hutawa sosai" tace "hakane, dan ana dawowa daga gurin dinner wanda bashi da high bp ma sai nashi ya tashi" ta jiyo tana kallona na dan yi mata murmushi nace "bye Mommy" tace "bye-bye, sai munyi waya" sai da muka ji tashin motar ta sannan sultan ya kama ni na mike tsaye muka fita, a hankali muke tafiya saboda jiri da nake ji, daga karshe ma dai dauka na yayi ya sakani a mota, ya zagaya ya shiga ya kunna motar yana kallona, na kirkiri murmushi nayi masa shima ya mayar min, amma nasan nashi murmushin bai kai zuci ba. Ya kama hannuna daya ya rike a hannunsa daya, yayi intertwining fingers din mu ya dora akan gear sannan ya tura hannayen mu a tare muka saka gear muka fara tafiya a hankali, hankalinsa rabi akan titi rabi akaina, hannunsa daya akan stirring wheel daya a cikin nawa. Na kwantar da kaina a jikin kujera ina jin dadin kamshi da sanyin motar, amma maimakon inji bp dina yana sauka sai naji yana kara hawa, na kalli sultan na tina da ranar dana fara ganinsa, a hankali naga ya fara zama dishi dishi, this is my worst fear tun sanda na samu ciki, preeclampsia, a raina nace 'ko yanzu na tafi, at least nayi wani abu a rayuwata".
Episode Ninety Eight: My Baby
Pre-eclampsia rare ciwo ne na masu tsohon ciki. Shine ciwon da yake saka mata convulsions (jijjiga) during labor. Alamominsa sune matsanancin hawan jini, kumburi, jiri, matsanancin ciwon kai, sensitivity to light, blurred visions etc. Matan da suke at risk of samun ciwon sune wadanda already suke da hawan jini kafin su samu ciki, wadanda mahaifiyar su ko sister din su ta taba yi, yara kanana da suka samu ciki da wuri ko kuma manya wadanda shekarun su suka ja sosai. In kina da ciki kuma kika ga kina da wadan nan alamomin dana lissafa a sama to kada ki yarda ki fara labor, it is very deadly, za'a iya rasaki ko babyn ko duk ku biyun, ko kuma ki samu wani mugun ciwon, wani lokacin har hauka ake haduwa dashi. In baiyi tsanani ba kuma cikin ki bai tsufa sosai ba, ana iya control dinsa, in yayi tsanani best solution shine ki tafi asibiti ayi miki aiki a cire babyn. Shikenan.
Na rintse idona ina lissafa condition dina, a take na yanke shawara. Na bude idon na sauke su akan sultan, a hankali nayi magana "sultan stop the car" ya dan kalle ni yaga am serious sai yasa signa yayi packing a gefen titi. Ya juyo gaba daya yana kallona "Moon menene? What do you need? Jikin ne?" Na danyi masa murmushi kadan nace "asibiti zaka kaini ba gida ba" ya dan tsorata kadan "is the baby coming?" Na girgiza masa kai, "asibiti zamuje, za suyi min aiki su fitar da babyn" a take naga tashin hankali a rubuce a fuskarsa, na rike hannunsa sosai nace "don't do this sultan please, I need your support and strength. Please don't freak out" ya dan nutsu kadan yace "me yasa kika ce zasu yi miki aiki? Kince kuma ba labor kike ba" nan nayi masa bayanin duk situation dina da risks din da naje facing. Sosai naga hankalinsa ya tashi, ya daki stirring wheel da hannunsa yace "damn it, I hate that Ibrahim" na bata rai nace "Ibrahim bai dora min ciwo ba Allah ne ya dora min. Ba akaina aka fara ba ba kuma akaina za'a gama ba. Tunda na samu ciki lafiya lau nake, ko mugun laulayi banyi ba, wadansu matan daga ranar da suka samu ciki ba zasu samu lafiya ba har sai sun haihu. Wadansu matan talauci ya saka ko abinci mai kyau basa samu a lokacin da suke da ciki, wadansu matan basa samun medical care, wadansu matan zasi hadu da ciwo irin nawa amma basu san menene ba kuma su zo su fara labor a haka, a karshe su samu matsala koma su mutu gaba daya. Amma ni na samu komai, komai da nake bukata na samu, abinda nake bukata a yanzu shine support dinka, together we will get through this" ya dan nutsu ya dakata yana kallona, na mayar da idona na rufe inajin kaina tamkar zai rabe gida biyu, ga wani jiri da nake ji duk da cewa a zaune nake. Naji hannun sultan yana shafa fuskata, na dan bude idona ina kallonsa, na rike hannunsa da yake kan fuskata nace cikin sanyin murya "I need you to be strong" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "yanzu me zamuyi" nace "asibiti zamuje. Amma please bana son ka kira kowa, Mommy da ummee in suka zo zasu kara min pressure ne. We can do this alone. Everything is going to be alright" da hannu daya ya dauko wayarsa yayi dialing, na fahimci doctor na yake kira, yana dauka ya fara masa bayanin abinda nace masa da kuma symptoms dina, banji mai doctor din yace masa ba yace "alright, we are on our way" ya kashe, hannun na yana cikin nasa ya kunna motar yayi reverse muka dau hanyar hospital, na koma na kwanta na rufe idona. Sama sama naji shigowar mu asibitin, naji sultan yana gayawa doctor a waya cewa gamu mun iso, hannunsa daya a rike da nawa dayan kuma ya saka yana shafa fuskata, na dan bude ido da niyyar in kalleshi amma hasken fitulun cikin asibitin ya saka na mayar da idona na rufe ba tare dana