Showing 141001 words to 144000 words out of 262297 words
kowanne bafulatani ne zai yadda ya bawa bayarabe auren 'yarsa ba. Ganin irin yadda hankali na ya tashi ne yasa ta fara lallashina, tace in ban yarda ba zata kawo min sample din IV daurin aurenki kafin in bar gari. Ta gaya min cewa duk 'yan gidan ku suna England yanxu ke kuma kina 'yalleman. Anan ta karbi number ta da niyyar zata kawo min IV din. Daga gidan su Amira da kyar na samu taxi ta kaini hotel na kwana, ranar nayi kukan da ban taba yin irinsa ba a rayuwata, na tausaya miki na tausayawa kaina saboda ina ganin soyayyata ce ta jawo miki aka miki auren dole aka kaiki kauye aka katse miki karatun ki, alhalin ga 'yaruwarki can a England tana karatun ta. Washegari da ciwo na tashi dan ko fitowa ban iya yi ba har Amira tazo da yamma ta kawo min IV din, naga sunan ki da sunan wani Abdulaziz a matsayin mijin. Ganin ina kokarin in mutar mata a hannu yasa ta kira mai taxi suka kaini asibiti, a take aka kwantar dani dan sosai nake neman rasa numfashina. Kwana na uka a kwance Amira tana ta dawainiya dani, ranar dana warke nayi mata godiya nace zan tafi, amma dan Allah she should at least call you and let you know cewa I came back like I promised. Ina komawa ibadan na yiwa baba karya nace na samu Daddy yace yanzu kina karatu in bari sai kin gama tukunna. Mama tana gurin ashe ta gane karya nake yi. Rashin lafiyar ce dai bata barni ba dan tunda na koma ina kwance. Ban san ya akayi mama ta bincike kayana taga IV din da Amira ta bani ba. Bata ce min komai ba har na samu sauki na koma lagos. Ashe bayan na tafi ta nuna wa baba IVn ta gaya masa cewa yarinyar da nake so anyi mata aure, kuma wannan shine sanadin duk wannan ciwowwukan da nake. Ba tare da baba ya sake bi ta kaina ba ya yanke shawarar daura min aure da efi, a cewarsa macece kadai zata saka in manta da ke. Sam babu wanda ya gaya min labarin za'a yi min aure har aka daura ban sani ba, sai da uncle dina na Lagos ya je daurin auren ya dawo sannan ya kira ni ya gaya min, ranar naga tashin hankali, na gaya masa sunyi mistake, ni bana son efi ba zan iya zaman aure da ita ba dan a matsayin kanwa na dauke ta. Ya gaya min lallai in shirya in tafi ibadan inje ayi biki in taho da amaryata. A dole na shirya amma maimakon in tafi ibadan sai na zarto Abuja, direct gidan ku naje, wannan karon na tarar gidan da alamar mutane a cikin sa, ban shiga ba wannan karon a waje na tsaya sai da wani yaron gidan ya fito sannan na tambayeshi ko kina nan? Sai ya ce min ke baki zo ba, amma sauran mutan gidan sunzo, abinda na fahimta a lokacin shine mutan gidan sunzo daga England ke kuma baki zo ba tunda kina 'yalleman. Wannan shi ya goge min duk wani sauran doubts akan auren ki. Na tafi gidan su Amira, wannan karon a gida na same ta. Na gaya mata yadda mukayi da yaron gidan ku tace min eh ke kina 'yalleman, 'yan gidan ku ma sunzo suna ne saboda haihuwar da kika yi, har ta nuna min hoton babyn a wayarta. Ta gaya min cewa kunyi magana da ke kince mata in na sake zuwa ta ce min I should move on, ke kinyi moving on nima I should do the same thing. Zancen haihuwarki ba kara min tayar min da hankali ya kuma yi ba dan ina zuwa ibadan na zube wa mama a tsakar daki, mama hannu ta dora aka tana rusa kukan ta shiga uku danta zai mutu. Babane ya saka ni a gaba da nasiha da addu'a da fada har na dan samu na saki raina. Nan aka fara shirye shiryen biki. Sosai baba da mama suka kashe kudi a bikin nan a niyyarsu ta son suga sun faranta min rai. 'Yan uwana duk sun zo daga side din babana, side din baba da kuma side din mama, kowa was there to make me happy. Bana so in nuna musu kamar wahalar banza suke ji dan haka na ware sosai tamkar na karbi auren har aka yi biki aka gama. Bayan an gama biki ne mama tace mu tafi Lagos tare da efi sai nayi mata bayanin cewa bani da gida a lagos nima a gidan uncle dina nake, amma tunda a lokacin kudi suna shigo min sosai, inna koma Lagos zan sayi gida sai inzo in dauke ta, a haka muka rabu dasu na tafi Lagos. Na sayi gidan kamar yadda nace amma fir naki dauko efi. Nace ni bana son in ci zalinta kuma ni bazan iya zaman aure da ita ba. Sai da Efi ta shekara guda da aure akan ta amma tana zaman gida. Kwata kwata ma na daina zuwa ibadan saboda kar ayi min maganar tafiya da ita. Gashi arzikina kullum karuwa yake yi. Rannan kawai akayi min waya cewa baba babu lafiya, ba shiri na tafi ibadan, kwana na daya da zuwa Allah yayi masa rasuwa. A lokacin nasan mutuwar uba tunda sanda mahaifina ya mutu bani da wayo. Bayan komai ya lafa nace zan tafi, mama ta saka ni a gaba har da kukan ta akan lallai in tafi da matata, yanzu bata da kowa, ba uwa ba uba, ga mijin da dashi da babu duk daya, duk ta lalace ta fita daga haiyacinta. Kukan da mama tayi min ne ya saka na tafi lagos da efi".
Muna zuwa lagos na kaita gidan uncle dina na kama gaba na, ban kuma komawa ta kanta ba. Muna yawan yin waya da Amira, nakan kira ta inji ya kike da su Hafsat, kullum tana ce min lafiya lau kuke, tace hankalinki a kwance yake yanzu baki da wani problem. Kullum tana min maganar ya kamata in ajiye maganar ki a gefe in san me nake ciki a rayuwa amma sam na kasa. Ina waya da ita ne saboda she was the closest thing i have to you. Rana daya kawai sai ga mama tazo Lagos, nan naga bacin rai a gurinta data fahimci abinda na aikata. Efi cewa tayi ta hakura da auren, ita a raba auren kawai duk son da take yi min ta hakura. Mama kuma tace ban isa ba tunda bani na haifi kaina ba. Dole efi ta dawo gidana ta tare. Mama ma anan ta zauna tare da mu ta saka mu a gaba" yayi shiru for the first time tunda ya fara magana. Na kalleshi naga yana kallon can gefe. Ya cigaba da cewa "a duk zaman da muka yi da efi bazan iya tuna ranar da na ganta cikin farin ciki a dalili na ba, ta samu gangar jiki na, amma zuciya ta da ruhina ni kaina basa tare da ni ballantana in bata. I kept blaming iyayen mu da suka hada auren duk da cewa sun san bana sonta. Ba kowanne namiji ne zai iya rayuwar aute da matar da baya so ba. Bamu dade tare ba ta samu ciki, cikin yana girma mama ta dauko ta suka dawo ibadan ni kuma nayi zamana a lagos. A ibadan ta haihu, anan kuma Allah ya karbi ranta a gurin haihuwa. Allah yaso zamuyi sallama nazo kawo musu kayan da mama tace in siya, ina xuwa ta fara labour na kaita asibiti, tana haihuwa jini ya balle mata wanda shine sanadin ta. Inda Allah ya taimake ni na nemi gafarar ta kafin ta mutu da nasan alhakin ta bazai taba barina ba. Bayan na koma lagos naji duk zaman garin ya ishe ni, da kadan na fara sayar da business dina ina dawowa nan garin, a hankali na gina wannan gurin na sayi gida sannan na dawo garin nan da zama. Bayan dawowa ta garin nan na fahimci cewa Amira still have something for me sai na yanke alakar dake tsakanin mu saboda ban taba jin son ta a raina ba, ban taba jin son kowacce mace a raina ba bayan ke. Ina yawan bin hanyar gidan ku with hope wai ko wata rana zan ganki koda kuwa daga nesa ne. Rannan kawai naje unguwar sai naga gate din gidan a bude, kamar ana biki a gidan. Nayi packing daga dan nesa ina jin dadin maybe zan ganki. Na kira Amira a waya nace mata nazo gidanku na tarar ana biki, sai tace min bikin Hafsat akeyi. Ta fito ta same ni tace ta gaya miki nazo kince please in tafi kar mijinki ya ganni, tace kince you are happy with your life and I should leave you alone" ya sake yin shiru yana kallona, fuskarsa tana nuna irin bacin ransa. Ya cigaba da cewa "tun daga ranar ban sake zuwa gidan ku ba. Nayi concentrating akan business dina. Amira tasan ina garin nan amma bata san me nake yi ba, she had no idea nan guri nane, dan haka da kuka zo bata taba tsammanin zata ganni anan ba"
Tun da ya fara maganar nake hawaye har ya kammala, ya tashi ya je gurin water despenser ya debo ruwa a cup ya dawo ya miko min na karba na shanye ina jin dadin yadda sanyin ruwan yake sanyaya zuciyata. Maimakon ya zauna a kujerar daya tashi sai ya hau kan table din gabana ya zauna, exactly yadda yake yi sanda muna makaranta. Na dago kai na kalle shi, he was grinning from ear to ear. It is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Involuntarily na kai hannuna kan zoben Sultan na fara wasa dashi. A hankali Ibrahim yace "it is alright now, we are together now" a hankali na far girgiza kaina hawayen fuskata yana karuwa, ya saka hannu zai dago fuskata na matsa baya. Nace "married or not married, ba dai dai bane kake taba ni ba, ka sani kuma" yayi dropping hannunsa a sides dinsa, yace "bani naki labarin inji, what have you been doing all these years" a hankali na fara magana nace "I waited for you, for five years, I waited" yace "six, almost seven" nace "I met someone after five years of waiting for you" nayi shiru ina kallon yadda yanayin fuskarsa ya fara chanzawa, yace "what? Who?" Nace "it doesn't matter who" ya sauko daga kan table din ya koma wajan ruwa, this time kansa ya zuba wa yasha, sannan ya tari wani ruwan ya zuba a kansa, ya juyo yana kallona da wani yanayin da bazan iya fassarawa ba, nayi sauri na dauke kaina dan ba zan iya juran kallonsa a haka ba. Yana daga tsayen yace "do you mean to tell me that you are in love with someone else?" Na yi shiru ina jinjina kalmar love, in nace love sai inga kamar na rage darajar what I feel for Sultan, it is more than love, na gyada kaina a hankali nace "yes" da sauri ya karaso gaba na ya durkusa "maimunatu please, please don't say that, zuciya ta zata iya bugawa please" na runtse idona ina jin zafi a raina, I hate to hurt him like this amma dole in gaya masa gaskiya, nace "I loved you, but not anymore" ya mike da sauri ya fara safa da marwa a office din yana cewa "you don't mean that, dan dai bana nan ne, you still love me, i know you do, I just need you to give me a chance in dawo miki da soyayyata" ya sake dawowa gaba na "maimunatu please ki sake bani chance" na sunkuyar da kaina ina kallon zoben Sultan a raina ina ayyanawa idan da ace sultan ya san inda nake kuma yasan tare da wa nake, zai iya harbo igwa ta tarwatsa building din gaba daya, a hankali na sake magana nace "there is no time, bikina saura kwana goma" da karfi yace "what?" Na gyada masa kai, ya sake mike wa ya buga hannun sa a table din yace "NO" da dan karfi. "No Maimunatu, destiny brought us together today. Da Allah baya so mu kasance tare da ba zai kawo ki office din nan yau ba. Da in zamu hadu ma sai da auren ki tukunna. Please call off the wedding" na girgiza kaina da sauri nace masa "not possible. I can't do that. Ko da ma ace bana son wanda zan aura ai bani nake bada kaina ba, an riga an bashi ni, an gama komai, bazan taba zuwa in ce bana son auren sa ba. It doesn't work like that" ya sake tsugunna wa kamar zai dora hannayensa a kan lap dina nayi sauri naja kujera ta baya, ya dora hannayen aka, sannan ya shafo fuskarsa. Idonsa ya sauka akan zoben sultan da nake ta aikin murzawa. Ka kalle ni yace "his ring?" Na gyada masa kai, ya sake cewa "who is he?" Na sake amsa masa "it doesn't matter" kamar amsar tambayar sa sai waya ta ta fara kara, a tare muka kalleta, 'my sultan' a hankali ya furta "sultan" ban dauki wayar ba saboda bazan iya yin magana da Sultan a yanzu ba, har ta gama ringing ta katse ya sake kira, nasan halin Sultan in yaso abu, bazai daina kira na ba har sai na dauka. Na mike tsaye, Ibrahim ma ya mike yace "please don't go" na kalle shi for some seconds sai na juya zan tafi, hijab dina ne ya jawo wani frame din hoto daga kan table din ya fado kasa, na durkusa a hankali na dauki hoton ina kallo, wata yarinya ce zata yi shekara uku a duniya, naga fuskar Efi a fuskarta amma idon Ibrahim, she looks very cute a cikin English wears tana murmushin da yake bayyana cleft chin dinta just like her father's. Nace "she is very beautiful" ya zagayo ta bayana yana kallon hoton yace "yes she is, just like the Moon I named her after" da sauri na juyo na kalleshi, yace "yes, sunan ki na saka mata, maimunatu, and I call her Moon" da sauri na hadiye kukan daya taho min, her mother died giving birth to her, but he named her after me. Daya frame din da yake kan table din na dauka, numfashina ne ya tsaya chak, hoton mu ne nida Ibrahim, duk bama dariya, fuska ta kamar zanyi kuka, yana tsaye a bayan class din mu ni ma ina tsaye a kusa dashi, na dan kwantar da kaina a kafadar sa shi kuma ya juyo kadan yana kallona. I remember sanda aka dauki hoton, Hafsat ce ta dauke mu da wayar ibrahim ranar da zamu bar makaranta. We were so young then, and so much in love. Na kalle shi da sauri naga yana murmushi, it is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Na ajjiye pic din da sauri na yi hanyar waje ina jinsa yana cewa "maimunatu please" exactly yadda yake cewa in yana ya son ya lallabani in yi masa wani abu. Da bibbiyu nake hada stairs ina sauka, idona almost a rufe na fita na doshi motar sultan da nazo da ita, na bude na shiga nayi mata key, a lokacin na hango shi ya fito daga building din yana nemana. Nayi baya na fita daga packing lot din ina ganin sa ta mirror yana kallon motar, yayi noticing sunan da aka rubuta a gurin number "Sultan 2" .
Sai da nayi nisa da building din sannan na sauka daga kan titi nayi packing, na kifa kaina akan steering na kama kuka, what hurt me the most is the fact that Amira can betray me like that. Sometimes, the person you trust the most will hurt you the most.
Masoyan Maimoon ina gaishe ku baki daya, nima kuma ina sonku irin sosai dinnan. Ina ganin sakonnin ku ta WhatsApp da Facebook, masu bina private da masu turo wa ta group. Ina so ku fahimci abu biyu. Na farko Moon guda daya ce ba za'a raba ta a bawa kowa ba, dan haka dole wani ya samu kuma dole wani ya rasa. Dan haka at the end dole wani zai ga kamar ba'a kyauta masa ba. Abu na biyu kuma shine, tun kafin in fara rubuta labarin Maimoon na riga na tsara yadda zai kasance, yanzu kawai details din nake filling, kada wani yaga kamar labarin ina rubuta shine yadda zan farantawa wani. Idan kuka cigaba da bin Maimoon na tabbatar muku karshrn labarin zaiyi satisfying kowa insha Allah. Duk da dai ance shi dan adam ba'a iya masa.
I so much love you all
Episode Sixty Four : The Past and the Future
Na jima a haka ina kuka mai tsuma zuciya, jikina har rawa yake yi. Why is my life almost so complicated, me yasa komai ni baya zuwa min da sauki. I hate hurting Ibrahim. Ya sha wahala sosai akan soyayyata, he deserves happiness from me now, but I can't give it to him because it is not mine, it belongs to somebody else. Ina jin wayata tana ta ringing, kira na wajan goma kenan, amma ba zan iya dauka ba saboda ba zan iya magana ba. Da zuciya ta da kaina gabaki daya sun toshe kaina sam babu wani abinda yake fahimta, abinda nake tunawa shine naga Ibrahim, kuma soyayyata da na gani a idonsa ta ninka wacce na san yana yi mini a da kafin mu rabu. A hankali na fara abinda na saba yi indai ina so in saisaita tunani na, na fara kiran sunayen Allah daya bayan daya idona a runtse, a hankali nutsuwa ta fara shigomin kuka na ya fara tsayawa. Na bude ido na ina kallon titi, gari ya fara duhu dan tini anyi sallar magrib. Na fara tunani straight. So Ibrahim did came back like he promised he would. Saura kwana goma bikina, bikina da Sultan. Ibrahim har yanzu yana so na, yana sona fiye da yadda ya soni a baya. But ya dawo rayuwata a