Showing 114001 words to 117000 words out of 262297 words

Chapter 39 - Maimoon Hausa Novel Complete

mata? Abu daya ya saka zai rabu da ita shine yasan babu yadda za'ayi tayi harming Moon dan haka kamar yadda tace she is safe ya yarda she is safe din. Maganganunsu da Sultan ya fara dawowa dasu baya yana bin su daya bayan daya, maganar farko daya kamata yayi looking into itace ta yadda Moon ta zabi Sultan har tace ya zo yaga babanta, yasan halin Moon kuma ya yadda da ita, in dai har tace ta zabi sultan than there is something about him da ta gani, something good. Ya shiga bedroom dinsa ya dauko laptop dinsa ya kunna, the first place da ake samun information ya shiga, internet, amma duk abinda ya gani akan Sultan are not good, but why will Moon choose him? Shi abinda ya gani ma zai iya cewa gwara Munir akan Sultan, ya girgiza kansa, hakkin ubane ya samo wa 'yarsa miji na gari, yes Sultan indai labarin daya bashi gaskiya ne to negligence ya jawo ya zama abinda ya zama, amma wannan ba zai saka shi kuma ya dauki 'yarsa ya bashi ba. Emails dinsa ya duba yaga sun taru, kwana biyun nan he was very busy baya samun duba mails dinsa. Ya tashi yaje yayi sallah isha ya dawo, daya bayan daya ya fara bin emails din yana karantawa, bai jima ba yazo kan nata, "please daddy look into this" ya duba date din ya ga ranar da tabi Sultan bar ne amma da safe, ya bude document din data yi attaching, it is an amazing write up akan sultan, ta fara da tarihinsa, almost duk labarin da sultan ya bashi sazu, tayi bayanin duk bad characters dinsa, so she knows duk mugayen halayensa amma ta zabe shi? Sai kuma ta fara wani bayanin da daddy bai gane ba, a totally different side of Sultan, tana bayanin wadansu halayen wanda babu wanda zaice sultan yana dasu, tana dauko kowanne mugun hali data fada a baya tana justifying abinda yasa ya zama haka, tayi bayani akan yadda yayi rayuwa a america da irin yawan mutanen da ya rike tun a lokacin da ya kamata shi kansa ace rike shi ake yi, she then mentioned the orphanages, anguwannin talakawa a Abuja da Sultan ya rike, he is a hero to them, mutanen da ya samarwa aiki, yaran da ya saka a makaranta, talakawan da yake ciyarwa kuma duk ba tare daya nemi ko da godiya ne daga gare su ba, tace "he told me that doing something good makes him feel good, and that's what he wants, not people's praises" a karshen rubutun kuma tace "I believe this character a good person, but this life conditions makes him look bad in his eyes and the eyes of other people, but deep inside him he is good, very good"

Daddy ya zama speechless, ya rasa tunanin me zaiyi, internet ya koma ya fara searching abubuwan data fada akan sultan amma bai ga ko daya ba, me hakan yake nufi? Amma yasan 'yarsa, she will not lie like this, especially not to him, amma me yasa babu wanda yasan sultan da wadannan halayen data lissafa sai ita kadai? Sai kuma yayi tunanin halin mutane, they only see what's on the surface, dan haka kallo daya zasu yi wa Sultan suyi tagging dinsa as a bad person shi kenan kuma, su kuma wadanda yake good to mutane ne da basu da say a cikin al'umma, dadin dadawa kuma shi kansa sultan din bai yarda cewa shi mutumin kirki bane kuma he is set on anything da zai bata wa babansa suna. Sai da kan daddy ya fara ciwo sannan ya tashi ya je ya kwanta, har yanzu mommy bata zo ba, ya yanke shawarar he is going to ignore her for now, har sai ya gama binciken sa akan sultan.

Washe gari sai 12 ya sauko saboda jiya bai yi wani baccin kirki ba. Kuma yau ma tunda ya tashi yake making phone calls na meeting din daya shirya, yana yin breakfast ya dauki Walid a mota suka fita. Farko court din da mommy ta shigar da kara ya fara zuwa yace an janye karar dama misunderstanding ne kuma an samu fahimta. Private investigators ya hada har mutum goma, task din su shine yana son sanin komai akan Sultan, komai, including labarin rabuwar iyayensa. Sun charging dinsa kudi da yawa amma money is nothing to daddy dan haka ya signing musu check, half now half kuma sai sun gama aikin. Exactly one week aka kawo masa report dinsa, ranar har gari ya waye bai runtsa ba, hatta school report din duk kanin makarantun da Sultan yayi sai da aka kawo wa daddy. Komai na Sultan sai da daddy ya sani har abubuwan da ita kanta Moon bata sani ba. Sanda ya karanta ainahin dalilin rabuwar iyayen Sultan sai da ya dafe kansa yace "ya Salaam" gari na wayewa ya kira Walid yace "ka kira Sultan kace ina son ganin sa da yamma"

A bangaren sultan kuwa tun da ya bar gurin daddy gida ya koma ya shiga part dinsa ya kori kowa ya rufe kofa, he misses Moon sosai, dama zai samu ko muryarta yaji da yaji dadi, amma babu abinda zai yi dole ya jira kamar yadda daddy yace masa, tunda yace he will call then he will call din tunda baiyi kama da karamin mutun ba. Matsalar daya ce shine bai san abinda zai gaya masa in ya kira shi din ba, it will either be the end of his life or the beginning of his life. Jiran kuma anan za'a samu matsala, jira bashi da dadi ballantana ga mutum mai zuciya irin ta sultan. Kwana daya kawai duk yabi ya tayar da hankalinsa, he badly want a drink amma yana tsoron kar yasha daddy kuma ya kira shi, ko kuma ace moon tazo, ya tuna rokon da tayi masa akan kar yasha, menene ma abinda tace masa yayi instead? Ce masa tayi ya karanta alqurani. Ya tashi a hankali ya bude drawer da yake zuba books dinsa, anan yake aje alquranin sa tun wanda kakansa ya bashi, yana yawan daukoshi ya karkade ya mayar ya ajiye, karantawar ne dai baya yi. Ya dauko ya dawo kan gado ya zauna ya bude page din farko ya karanta fatiha. Ita kadai ya karanta yaji wani dadi a ransa, ya tuno sanda yana yaro a gurin kakansa wani lokacin tare suke karatu saboda kullum kakansa yana ce masa yana son yaji yana karatu saboda yadda yake lankwasa harshensa irin na larabawa. Ya ajiye al'quranin ya shiga toilet ya yo alwala ya zo ya shimfida sallaya yayi sallah raka'a biyu, sai kawai ya samu kansa da yin addu'a, abinda da ba yayi, ya roki Allah ya kawo haske a cikin rayuwarsa duniya da lahira, ya kuma yiwa Moon addu'a Allah ya kare ta a duk inda take sannan kuma Allah ya sa allkhairi a al'amuran su baki daya, daga nan ya jawo alquraninsa duk surorin saman sun bace masa duk da cewa da ya iya amma rashin karantawa yasa duk sun zube, na kasan dai ya iya su sosai saboda kullum yana karantawa a sallah. Nutsuwar da ya samu sai yaji tafi wacce yake samu idan yasa giya, ji yake kamar wani assurance na cewa everything will be OK. Tun daga ranar ya samu abinyi, baya zuwa ko ina yana daki sai dai a kawo masa abincinsa nan, kullum sai Amir ya shigo ya duba shi su dan taba hira ya fita, sosai Amir yaji dadin changin abokin nasa dan bai dauka zai taba zama calm akan rabuwarsu da Moon ba, Sultan ya bawa Amir labarin duk yadda sukayi da daddy nan suka hadu zaman jiran kiran daddy. Sai da akayi kwana takwas sannan kiran ya shigo, lokacin amir yana game da wayar Sultan, wayar ta fara ringing amir yace "wow, is this who I think it is?" Sultan ya kalli screen din yaga 'Walid' da sauri ya warce wayar ya daga da sallama, ba tare da Walid ya amsa ba yace "Daddy says to come after Asr" daga nan a katse wayar. Sultan ya jima yana kallon wayar a hannunsa, duk jiran da yake yi kuma sai yaji gabansa yana faduwa. Ya gayawa Amir abinda walid yace, ya tashi ya fara neman kayan sakawa, sai yau yayi nadamar rashin dinka manyan kayan da bayayi, da sam bai damu da duk irin shigar da yake yi ba amma yau sai yaji yana son yayi shigar kirki, da kyar ya samu kaya wadanda basu kama jikin sa ba. Amir yace zai rakashi, nan sultan ya kora masa warning kar ya saka matsatstsun kaya kuma ya tabbatar baya warin sigari, baki kawai Amir ya saki yana kallon Sultan, he is really changing, yace "since when did you care wanne kayan na saka?" Sultan ya bata rai yace "just do as I say kuma ka tabbatar ka cire wannan sarkar in ba haka ba bazan tafi da kai ba"

Da yamma suka je gidan, a palon baki aka sauke su aka kawo musu drinks da snacks, sultan da baya barin abinci amma yau sai ya samu kansa da kasa cin komai, so yake kawai daddy yazo yaji abinda zai ce masa. Basu jima ba daddyn ya fito cikin shiga ta alfarma kamar kullum, yana shigowa suka mike tsaye duk har sai da ya zauna sannan suka zauna suma tare da gaishe sa, ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya kalli Amir yace "Amir ko?" Amir ya gyada kansa, haka kawai yaga daddyn yayi masa kwarjini. Shima daddy ya karanta labarinsa da duk abinda Sultan yayi masa. Ya jima yana kallon Sultan wanda ya sunkuyar da kansa yana jiran abinda zaice, can daddy ya bude baki yace "Sultan, zaka iya dawowa nan gidan ka zauna a gurina?"



Episode Fifty Six : What You Sow

Sultan ji yayi maganar wani iri, sam ba abinda yayi tsammani ba. Ya jima kansa a kasa kafin yace "daddy bansan me zance ba" daddy ya gyada kai yace "I understand. Kafin ince zan baka Moon ko ba zan baka ita ba, dole ina so inga how far you can change, dan haka nake son chanza maka environment zuwa gurina. Amma da akwai sharadi, indai har ka amince zaka dawo gidannan dole zaka bi sharuddan zaman gidan nan, na farko babu yawo, zaka iya fita iyakacin cikin gari amma in dai zaka bar gari sai na sani kuma sai na amince, a cikin garin ma duk inda kake in lokacin cin abinci yayi zaka dawo gida saboda tare muke cin abinci a gidannan breakfast lunch dinner duk tare muke ci, kuma duk inda kake 9pm tayi maka a gida, babu wayon dare. Sanna the most important thing, ba zanyi tolerating koda single drop of alcohol a gidan nan ba, kuma koda a waje kasha ba'a gidan nan ba zan sani kuma ni kadai nasan hukuncin da zan yanke maka. I also want a total change of friends daga gareka, Amir will still be your friend of cause amma shima in naga bashi da niyyar chanza hali dole zan raba ka dashi, ga Walid nan shine sabon friend dinka zan kuma gaya masa kar inji kuma kar in gani a tsakanin ku. Abu na gaba kuma gida na ba gidan 'yan dambe bane, ko da wasa kar inji ance ka daki wani a cikin 'yan aikin gidan nan, tsakanin ka dasu ya zama girmamawa da mutunta juna. Next thing is you will need a change of wardrobe, saboda kamar yadda nake yawo da Walid haka zan ke yawo da kai kuma ba zan ke shiga da kai cikin mutane da wannan shigar a jikin ka ba. Wadannan sune sharudai na, in kaga zaka iya yarda dasu then you are one step to getting Moon, in kuma kaga ba za ka iya ba shikenan sai ka chire ta a ranka Allah ya hada kowa da rabonsa" da sauri sultan ya dago yana kallon daddy wanda shi kuma ya dora kafa daya kan daya ya daiki jarida yana kokarin budewa, alamar ya gama magana kenan. Sultan wani iri yake jinsa, wani irin feeling mixed with kunya, tunda yake ba'a taba ce masa 'yi kaza ko kar kayi kaza ba' amma yau gashi daddy ya wanke shi tas kuma a matsayinsa na surukinsa to be. Da sauri Sultan yace "daddy na yarda, ni kam na yarda da duk sharudan" daddy ya ajiye jaridar yace "madallah da wannan hukunci, gobe da safe zanje fada da kaina zan nemi alfarmar dawowarka gidan nan a gurin mai martaba sarki" Sultan ya girgiza kai yace "ba zai ce komai ba, ba zai noticing ma bana gidan ba" daddy yace "whatever, hakkin sane a gaya masa, kuma ni da kaina zan gaya masa. Yadda muka yi dashi Walid zai kira ka ya gaya maka. You can go now" Sultan ya kasa tashi, shi maganar bata ishe shi ba, shi da za'ayi ta masa fada so yake yi, can ya dan taba Amir yayi masa rada "ask him ina Moon take" Amir ya dan yi gyaran murya yace "daddy ko zamu samu ganin Moon kuwa" ba tare da ya kallesu ba yace "you will see her when the time is right" still sultan bai tashi ba, he have one more question, ya matsa gaban daddy sosai yace a hankali "daddy, dan Allah a cikin informations din da kake dasu, I want to know, did my parents.... " sai kuma ya kasa karasa maganar, daddy ya ajiye takardar hannunsa sa yace "ina jinka" sultan ya hadiye yawu yace "did my parents marry before...... Did they marry kafin su haife ni?" Daddy ya jima yana kallonsa ya kasa magana, tausayin yake ji har cikin ransa, jin daddy bai yi magana ba yasa Sultan ya mike tare da cewa "thank you daddy, dama ina so ne kawai in sani, I always thought wannan shine dalilin da yasa babana baya sona" daga haka yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa daddy ya kira sunan sa, ya tsaya ba tare da ya juyo ba saboda wani irin zafi da yake ji a ransa, daddy yace "sultan iyayenka sunyi aure kafin su haife ka, you are a legitimate child, abinda ke tsakanin ka da babanka is totally different from haihuwarka" Hmmm

Kamar yadda daddy ya fada haka ya aikata, washegari yaje fada akayi masa iso gaban mai martaba sarki, bai yi tsammanin zai gane shi ba amma sai yaga ya tare shi sosai da fara'a da wasa da dariya yace "Muhammad baka da kirki, ace kana garin nan da iyalinka amma ba ka zuwa mu gaisa? Kasan ni nauyi yayi min yawa bazan iya ziyarar abokanai ba" daddy yayi murmushi yace "Allah ya taimake ka ai ni ma ba zaman garin nake sosai ba, kuma in dai nazo to abubuwa sukan yi min yawa har sai na koma. Amma ayi min afuwa, in sha Allah zan ke lekowa lokaci zuwa lokaci" Har palon da yake barkar manyan bakin sa ya saka aka shiga da daddy, nan suka zauna gaba dayan su akan carpet suka fara hirar yaushe gamo da labarin karatun su da friends dinsu wadanda yanzu kowa ya kama gabansa. Daddy yayi mamaki sosai yadda yaga takawa ya zage sosai yana hira da dariya, saboda shi ya dauka maganar da zasuyi formally zasu yi ta maybe a gaban mutane ma, ashe dai Sadiq din is still the same person da ya sani kawai dai nauyi ne ya hau kansa yanzu. Anan suka zauna har aka kawo musu lunch sam daddy bai lura da yadda lokaci ya tura haka ba, he totally can't believe cewa wannan elegant mutumin shi yayi raising Sultan. Da kansa mai martaba yayi serving dinsu a plate daya suka ci, suna cikin ci Abbas ya shigo a nutse yazo ya gaishe su sosai sannan ya fada wa babansa sako cikin girmamawa ya fita. Daddy yayi noticing wani abu, Abbas totally baya kama da Sultan, ba zaka taba cewa 'yan uwa ne ba. Sai da suka gama sannan daddy ya gyara zama yace "Allah ya taimaki sarki magana ce ta kawo ni. Akan dan mu Sultan" daddy ya fada yana kallon fuskar takawa, abinda yayi tsammani kuwa shi ya tarar, just mentioning sunan sultan ya goge dukkan fara'ar dake fuskar takawa, komawa yayi kamar bai taba dariya ba. Yace "Wani abun yayi?" Daddy yace "babu abinda yayi ran sarki ya dade, ina neman alfarma ne in da hali ina so ya koma gida na da zama" Takawa yace "saboda me?" Daddy yace "ba wani abu kawai mun hadu da shine sai naga kusan sa'an yaron wajena ne walid shine sai naga ina sha'awar in hada su a gurina for sometimes, in ka amince of cause" Takawa yayi shiru yana shan lemon hannunsa, har daddy ya fitar da ran cewa ba zai yi magana ba sai kuma yace "you can do with him as you wish. Kawai dai ka tabbatar duk abinda ya aikata maka kai ka jawo mu babu hannun mu a ciki, kuma ka tabbatar duk abinda yayi kar ka danganta shi da mu" daga haka ya ajiye cup din hannunsa ya mike tsaye yace "in ka kammala da akwai servants a waje zasu raka ka motar ka. Na gode da ziyara Allah ya bar zumunci"
I
Da yamma Sultan yaji wayar Walid da sakon sarki ya masa maganar daddy, Sultan sam ya kasa tantance me yakeji a ransa, few things dinsa ya dauka ban da kayan sawa tunda daddy yace baya son irin su. To shi yanzu ina zai iya saka wata shadda ko yadi ne kam. Bashi ma da tailor. Yana zuwa gidan ya tarar da walid da Habeeb suna jiransa a compound, direct part dinsu suka wuce dashi fuskokinsu babu yabo babu fallasa dan sukam sam basa murna da wannan hukuncin na daddy. Four bedrooms ne dama a part din, sai palo mai hade da dining duk da dai ba mafani suke da dining din ba sai dai in bakon da ba za'a shiga dashi main palo ba. Walid ya bawa sultan key din daki daya da kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login