Showing 201001 words to 204000 words out of 262297 words

Chapter 68 - Maimoon Hausa Novel Complete

tribe dinsa da kalar fatar sa shi yasa za'a hana shi auren wacce yake so? Menene aibun sa? Yana da asali, yana da addini, yana da ilimi, yana da dukiya kuma shi cikakken namiji ne bashi da tawaya ko kadan amma saboda shi bakar fata ne an hana shi aure duk kuwa da cewa yarinyar shi take so. Nan take ya kira khairat ya gaya mata plan A failed, initiating plan B. Khairat ce ta tsara masa duk yadda tsarin gidan nasu yake shi kuma ya zana, tayiasa bayanin dakin da take da komai. Tayi wa mahaifiyar ta dabara ta saci spare key din kofar gidan ta jefa ta window, ta kira sadiq ta gaya masa shi kuma yazo ya dauka, ta kuma gaya masa exactly a inda ake ajiye keys din gidan. Ana gobe daurin auren khairat Sadiq yazo, bai samu matsala ba saboda su a Saudi Arabia babu burglary dan haka ba wani security. Tunda kowa yasan hukunci babu wanda yake shiga gidan wani. Yana zuwa ya bude kofa da key ya shiga ciki, duk gidan suna bacci banda khairat da take yi masa magana ta waya tana kara yi masa bayanin inda zai bi, a haka har yaje har dakin mamanta ya dauko key din dakinta. Ya fito ya tafi dakinta ya bude, already a shirye take dama dan haka ko magana basu yi ba ta biyo shi da sauri suka fita daga gidan suka shiga motar daya zo da ita, a dakinsa na hotel suka karasa kwana, da sassafe dama yayi musu booking plight suka tafi airport, around 7, jirginsu ya tashi zuwa America. Sun zabi America ne saboda it's a free country, babu wanda ya damu da wani, kuma sun san za'ayi wahalar samun su a can saboda girman ta. Plus England shine guri na farko da za'a fara zuwa neman su. Sadiq bai san ya debo da zafi ba, a saudiyya, ka shiga har gida, kuma gidan masu sarauta, ka sace musu yarinyar da za'ayi bikinta gobe, ka gudu da ita ku bar kasar gaba daya. Chafdi.
Kwanan su daya a America, saboda suna gudun sabawa ubangijin su, suka nemi wani imam suka bukaci a daura musu aure, liman ya nemi waliyyanta khairat tace ita marainiya ce bata da kowa a america, daga ita sai iyayenta kuma iyayen yanzu sun mutu kuma bata taba zuwa garin suba ballantana ta san danginta, sadiq ne duk ya tsara mata wannan yace in sunxo ta fada. Imam din ne ya zauna a matsayin waliyyinta, yace duk wani problem da ya tafu da auren ta zo gurinsa, ya zama shine babanta, Sadiq kuma shi ya tsaya a waliyyin kansa, aka daura aure Sadiq ya bada sadaki, mutanen da suke masallacin sune shaidu. Daga nan sukayi signing marriage certificate sun zama islamically and legally married. Daga gurin daurin auren direct airport suka nufa suka shiga jirgi sai Nigeria. Shi sadiq a tunanin sa uban yaki yadda da auren ne saboda yana jin tsoron zuwa neman auren, dan haka yake ganin yanzu tunda yaje ya aikata abinda ya aikata ai shikenan komai ya wuce. Yana zuwa gida da khairat tun kafin yayi wa sarki Abdallah bayani sarkin ya fahimci abinda ya faru, sato khairat sadiq yayi. Sosai hankalin sarki da Yaya ya tashi dan su sunsan menene zai je yazo. Sadiq ya gaya musu cewa ya riga ya auri khairat dan haka iyayenta babu yadda zasuyi dashi, amma sarki ya san cewa auren nata da yayi shi zai kara mayar da case din worst, saboda zasuyi charging dinsa da forced marriage wanda babban laifi ne a saudiyya, sarki Abdallah ya nuna wa Sadiq cewa lallai ya dauki yarinyar mutane ya mayar da ita gidansu, jin haka Sadiq ko amsa bai bashi ba ya kamo hannun khairat suka fice daga palace din. Shi a tunaninsa yama za'a ce ya sake ta ya mayar da ita gida duk uwar wahalar da yasha kafin ya same ta? A gidan wani abokinsa anan Abuja suka kwana, da safe suka kuma hawa jirgi sula koma America. Sun yanke shawarar gwara suyi zamansu su kadai tunda iyayensu sun kasa fahimtar irin son da suke yiwa junan su. Shikenan kuma suna zuwa america aka shiga honeymoon. Rayuwarsu kawai suke yi suna jin su on top of the world, babu mai saka su babu mai hana su, babu abinda suke sai soyayya kamar su chinye junan su, sun zama Americans sosai. Sadiq ya nemi aiki da takardunsa kuma bai sha wahala ba ya samu, suka nemi gidan haya suka kama, khairat taso neman aiki itama amma sadiq ya hana yace albashinsa ya ishe su, su biyu kadai basu ajiye kowa ba.
Wata daya da auren su khairat ta samu ciki, nan fa murna a gurinsu kamar me, Sadiq yana kallon cikin a matsayin hanyar komawarsa gida, idan babansa yaga cewa ya haihu da khairat ai dole ya hakura ya karbe ta da duk wani challenges din da auren nata zai taho dashi. Su biyu suka yi renon cikin su cike da soyayya da kulawa, da watan haihuwar khairat ya kama kuwa sadiq a jiye aikin sa yayi ya dawo gida gurinta yana kula da ita, hana ta yin komai yayi, komai shi yake yi mata, ko ya kuwa yaga ta dan bata fuska sai hankalinsa ya tashi. A haka labor ya zo mata, hankalin sadiq ya tashi sosai gani yake kamar mutuwa zatayi ballan tana da ta fara bashi wasiyyar ya kula da babyn su, ya kaishi gurin 'yan uwanta ya basu hakuri. Kusan akan chinyarsa ta haihu dan zama yayi dirshan akan gadon ya rungume ta yana yi mata alkawarin daha wannan haihuwar ba zai sake bari ta samu ciki ba saboda ba zai sake bari ta sha wannan wahalar ba. Ana haihuwar Sultan sadiq ya karbe shi ya rungume a kirjinsa, ko goge shi ba'a yi ba, dariya kawai yake yi saboda murna, shi a rayuwarsa bai taba ganin kyakykyawan yaro irin wannan ba, ya sunkuyo gurin khairat da ake gyarawa yace "look at our Little Love, He looks just like you". Nan fa suka ninka soyayyar da suke yiwa junan su suka dora akan Little Love dinsu wanda yaci sunan babansa, Abubakar, sukan zauna kawai su saka shi a gaba suna kallo, watan Sultan biyu a duniya Sadiq yaga cewa ya kamata su gwada zuwa gida suga yadda zata kasance, suka shirya amma basu kwashe kayansu ba saboda basu da tabbas din za'a karbe su a gidan. Sadiq ya shiga gida hannunsa na dama dauke da two months old Sultan, hannunsa na hagu kuma rike da Khairat. Da fushi sarki Abdullahi ya taho, yana zuwa Sadiq ya mika masa Sultan wanda a lokacin kwuiya ce dashi amma kawai sai akaga ya tafi gurin sarki yana bangala masa dariya yana ta ba masa fuska, Sarku Abdallah ji yayi ya kasa fadan kuma, niyyarsa yana zuwa ya kora su su koma inda suka fito amma sai ya kasa, wata soyayyar yaron yaji tana ratsa zuciyarsa. Kowa a gurin sai ya koma kallon su, sultan tamkar ya saba da kakan nasa, Khairat da Sadiq sai dariya suke yi suna mamaki. Dole Sarki Abdallah ya karbi surukarsa da jikansa. Aka ware musu dakunan su suka tare, suka tattaro kayansu gaba daya suka dawo gida. Nan take Khairat tayi farinjini a gurin mutane saboda kirkin ta, ba ta iya hausa ba amma koya take har a gurin bayin gidan, bata damu cewa wai ta fita daban a cikin su ba harkokinta kawai take yi tana kula da mijinta da Little Love dinta. Sarki Abdallah ya karbi surukarsa amma a cikin ransa ya san cewa this is not the end of the story. Dole wata rana sai iyayen khairat sun gano inda take, ko kuma ita khairat din da kanta ta nemi zuwa gurin iyayenta. Takanas ya tura kaninsa zuwa Riyadh dan ya bincika masa yaji me iyayen khairat suke ciki, labarin da aka kawo masa sam baiyi masa dadi ba, iyayen khairat sun dauki maganar very serious dan haka ruwa a jallo ake neman sadiq. Charges dinsa suna da yawa, akwai trespassing tunda ya shigar musu gida ba tare da izinin su ba, ga kidnapping tunda basu yarda cewa ita ta bishi ba sun barshi a cewa sace ta yayi, sauran changes din kuma sai an ganta an ga a halin da take ciki, kuma sarki Abdallah ya tabbatar suna ganinta da baby zasu kara da raping da forced marriage, a takaice indai suka kama Sadiq to sai ya biya da ransa. Sarki Abdallah kuwa is not ready to give up his son, tunda dai aikin gama ya riga ya gama. Ya kira Sadiq yayi masa bayanin duk abinda ake ciki, Sadiq ya daga kafada yace "they can't catch me now" sarki Abdallah ya girgiza kansa a ransa yana cewa 'ta yaro mai take bata karko, kuma komai nisan jifa kasa zai fado'. A bangaren khairat kuwa kullum tana tuna iyayenta amma sai tayi sauri ta kawar da tunanin daga ranta, saboda tasan haduwa dasu yana nufin rabuwa da Sadiq da kuma Little Love dinta, wanda bata jin zata iya hakan. Sarki Abdallah yasan tabbas iyayen khairat zasu gano inda take wata rana za kuma su zo neman ta, dan haka kullum yana cikin tararradin zuwan nasu.
Iyayen Khairat basu samu nasarar gano inda take ba sai da Sultan ya shekara biyu a duniya, lokacin shekarar ta kusan uku rabonta da gida. Da daddare suka iso, babanta mahaifi da kanin babanta, a fusace suke gaba dayan su, tun daga bakin gate da suka ce mai martaba sarki suke nema, aka gaya mudu ya kwanta bacci suka ce basu damu ba. Ganin cewa ba kananan mutane bane ya saka daga bakin gate aka yo waya cikin gida aka fada, sarki Abdallah yana ji yasan ko su waye. Da sauri ya fita, yana ganin idan aka bi abin a sannu za'a iya samun maslaha. Amma yana zuwa ya fahimci babu maslaha, dan sun dauki zafi sosai, saboda abin ya bata musu rai da yawa, domin khairat tana daga cikin yara masu tarbiyya a zuri'ar su, wannan nema dalilin da yasa aka barta ta tafi karatu England, suna ganin duk yaron da har ya iya ya hure wa khairat kunne har ta juya wa iyayenta baya to lallai yafi shaidan shaidanci, cewa sukayi sadiq is a devil kuma ya kamata ayi eliminating dinsa a society, bai kamata ace wai shine crown Prince din da zai jagoranci al'umma ba. Sun dau alwashin cewa sai sunyi hanging dinsa sun nuna wa duniya yadda mulki yake a Nigeria, in dai ire iren su ne shugabannin Nigeria to ya kamata a dau mataki a kai. Wannan maganar ta bala'in bata ran sarki Abdallah, dan shi yana ganin cewa dansa ba mutumin banza bane ba, dan duk a cikin 'ya'yansa yafi na'am dashi, his only fault is falling in love with a wrong girl, amma kuma mutane ba zasu duba cewa the girl lead him on ba, in irin wannan case din ya faru koda yaushe laifin namiji ake gani ba'a duba macen, da bata bashi fuska ba da ba zaiyi hakan ba. Da aka taso abdallah da khairat basu san me yake faruwa ba sai da suka shigo gurin tukunna, Khairat da gudu ta juya zata koma uncle dinta ya damketa, kuka take yi kamar ranta zai fita tana kiran sultan da sadiq. Da kyar aka samu masu rike Sadiq saboda neman zauce musu yayi. A lokacin Yaya ta shigo da Sultan ya hannunta wanda bacci yake yi hayaniya ce ta tashe shi, ita Yaya ta shigo da Sultan ne wai tana ganin kamar in suka ga dan zasu hakura su bar masa uwarsa amma sabanin haka, suna ganin sultan suka gane dan Khairat ne dan haka baban khairat yace shima Sultan din tafiya zasuyi dashi, ai Islamically da na uwa ne har sai ya girma sannan zai zaba, wannan kam sarki yace ba'a isa ba, da kansa ya karbi Sultan wanda ya fara kuka ganin ummeen sa tana kuka, Sarki yace babu wanda ya isa ya karbi Sultan, dole suka hakura saboda an fi karfin su. Aka uncle din Khairat ya dauke ta ya fita da ita tana ihu tana kiran Sultan wanda shima kukan yake yana kiran Ummee na, duk da baisan me yake faruwa ba, da sauri sadiq ya kwace daga rikon da akayi masa ya bisu har wajan mota yace "Khairat, I will come for you, no matter what, no matter how long" a take babanta ya juyo ya dawo gaban sadiq yace "then I will hang you, If you ever step on Saudi land, I will hang you" daga haka suka ja mota suka tafi.
Tashin hankali ba'a saka masa rana, inda Allah ya rufa asiri ma da daddare ne duk gidan kowa bacci yake yi. Da kyar aka mayar da Sadiq daki sarki ya saka akayi masa allurar bacci, amma har yayi baccin yana rantsuwa sai yaje ya karbo matarsa. Sultan kuwa bai koma bacci ba dan gaba daya ya rikice shi ummeen sa da daddyn sa. A ranar sarki Abdallah bai koma bacci ba shima, yana lissafin abinda ya kamata yayi. Duk da yasan cewa gaba da gabanta amma kuma ya tabbatar ba zasu iya taba Sadiq a Nigeria ba, amma yana shiga saudiyya ya zama nama. Sannan kuma ya tabbatar cewa sadiq sai yaje.
Tunda assuba ya aika a kirawo masa babban malamin sa da yake saka yayi masa addu'oi idan wani abin ya shige masa duhu a harkar sarautar sa ko kuma a harkar cikin gidansa. Malamin yana zuwa sarki Abdallah ya yi masa bayanin duk halin da ake ciki bai boye masa komai ba. Malamin yayi shiru yana tunani sannan yace "to yanzu Allah ya taimaki sarki mai kake so ayi?" Sarki yace "so nake idan da wani sirri da kake dashi wanda zaka cire masa ita daga zuciyarsa kwata kwata ya manta da ita" malamin yace "akwai Allah ya taimake ka, za'a iya yin hakan. Amma kuma ran sarki ya dade akwai da a tsakanin su, idan an mantar dashi uwar shi kuma dan fa? Duk sanda ya kalli dan dole ya tuna da uwarsa, musamman ma da yake dan da uwar suna kama" sarki ya danyi tunani kadan sannan yace "to ya kake ganin za'ayi? Malamin yace " za'a iya raba su din kamar yadda ka bukata amma kuma ina tsoron abin zai shafi yaron. In akayi aikin, adadin soyayyar da uban yake yiwa dan zai juye ya koma kiyayya. Zai zamanto kamar mun raba da da ubansa ne Allah ya taimake ka, ina tausayin yaron tunda kaga yanzu babu uwa kuma azo ace uba yana tsanarsa ai abin zaiyi masa yawa, tarbiyyar sa nake tunani" Sarki Abdallah ya daga kansa sama yana tunani. Tabbas in aka raba Sadiq da Khairat an shiga rayuwar Sultan. Amma kuma in ba'a raba su bafa? Ya lissafa abubuwan da suke at stake, na farko rayuwar Sadiq din gabadayanta, Sadiq shine sarki yake sa ran zai gaje shi, shine yake sa ran ko bayan ransa zai rike gidan, zai rike sarautar kuma zai rike al'ummar da suke karkashi sa baki daya, ba rayuwar Sadiq ce at stake ba, family name dinsu da family future dinsu gabadaya is at stake, ba family dinsu kadai ba, hatta martabar musulmin Nigeria gabadaya is at stake, ba musulmin Nigeria kadai ba, ita kanta Nigeria martabar ta sai ta ragu a idanun sauran kasashe. Dan in dai suka ka.a Sadiq sai sunyi publishing a international papers cewa ga abinda Nigerian Prince yayi. Sarki ya sauke ajjiyar zuciya ya sunkuyo da kansa yana kallon malamin yace "a yi. Ni kuma nayi alkawarin zan zamarwa Sultan uwa kuma zan zamar masa uba. Zan bashi duk kannin wani gata da ya kamata iyaye su bashi. Insha Allah sultan ba zai yi maraici ba. Ina rokon Allah kuma ya dubi uzurina, ya dubi dalilin da yasa nayi haka, ya yafe min".
Kaico, mai martaba sarki babu wanda yasan gawar fari sai Allah.



Episode Eighty Two : The Light
Like I always say and always emphasize, things are not always what they seem. Duk abinda kake zargi, karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike ka tabbatar, duk abinda aka gaya maka akan wani indai har ba kaine da kanka ka gani ba, kar kayi saurin yanke hukunci akai, kayi bincike sosai first. Never and never judge a book by it's cover, in ba haka ba you might spend the rest of your life regretting.
How far will you go to save your family?
Hakan kuwa akayi. Daga nan sarki Abdallah ya saka akaje dakunan da khairat ta zauna aka kwashe duk kanin kayanta aka rufe dakunan. Gari yana waye wa yasa aka tara masa duk mutanen gidan tun daga kan iyalinsa har bayinsa ya ce ya hane su da ko da ambaton sunan khairat ne a gidan ballantana labarin ta ko wata magana data shafeta. A lokacin da Prince Sadiq ya tashi daga bacci jin kansa yayi fresh, babu abinda yake damunsa, kamar bashi da wata matsala a duniya. Ya danganta hakan da bacci mai nauyi daya samu. Yayi wankansa ya shirya ya tafi gurin mahaifinsa, ya tarar dashi yana cin breakfast, ya gaishe shi ya zauna gefe, mahaifin nasa kallonsa kawai yake yana studying dinsa, sannan yace "Sadiq yau baza a fita gurin abokanai ba ne?" Sadiq ya dan shafa kansa yace "Ranka ya dade yau gida zan zauna, sam yau bana son hayaniya" sarki abdallah yaji babu dadi har cikin ransa. Sadiq ne za'a ce masa ya fita gurin abokanai yace shi ya zashi ba? Sadiq din da kullum in yana gari gidan a cike yake da mutane saboda shi? Bayan ya baro mahaifin nasa ne ya tafi cikin gida gurin yaya, yana shiga palon ta yaga wani yaro yana ta kuka a hannun baba gaji, kallo daya ya yiwa yaron yaji wani irin tsanarsa a ransa, ji yake kamar ya hada daga baba gajin har yaron yayi musu duka ya kore su daga palon amma ya daure zuciyar sa ya wuce ciki, tunda ya shiga Yaya take kallonsa da mamaki har ya durkusa ya gaishe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login