Showing 165001 words to 168000 words out of 262297 words
kafin in fara shiryawa na kira wayar sultan, still switched off, na shafa mai na shirya cikin lace coffee color, riga da skirt da suka kama jikina suka zauna sosai, na gyara kitso na, na bayan ya sauko har gadon bayana, na gaban ma na sake tufke shi yabi ta saman idona ya sauka a wuyana. Na fesa turare na na fito ina neman dakin dasu Hafsat suka kwana, dakin kusa da nawa basa ciki, na kalle shi naga kusan irin nawa ne amma nawa yafi shi girma. Na fita ta dan corridon da zai fita dani palo na, anan dakin ba'kina yake, na murda kofar na gansu sun ba rarraje suna kwasar bacci, nayi murmushi a raina nace 'sun gaji' na duba agogo naga kusan karfe goma, ni kam yunwa nake ji, na dan daki kafar Amina "ke ku tashi fa, kun ma yi sallah kuwa?" Hafsat ta sake jan bargo, nayi ajjiyar zuciya dan nasan ko nafi kuda naci Hafsat ba zata tashi ba, Amina na takurawa sai da ta tashi tana ta kunkuni wai ita bacci bai ishe ta ba an takura mata. Nan na barta tana kokarin shiga wanka na fita ina zagaya gida, a raina ina lissafin Sultan ne fa yayi min alkawarin zai zagaya dani, nasan lissafin yadda gidan yake a raina dan haka ban wani sha wahala wajen gano part din Sultan ba, na tura main kofar sa naji a bude take, na shiga palon sa, na jima a tsaye ina shakar kamshinsa, unique kamshin da yake sakani lumshe idona kullum na jishi, a hankali nake tafiya ina karewa palon kallo, kusan irin nawa ne sai dai ban bancin arrangement din kayan ciki, na shiga corridor dinsa, shima two bedrooms ne dashi irin nawa amma shi bashi da dakin bakin da nake dashi a palo, instead sai akayi part din baki maza daban wanda sai ka fita can main palo sannan za ka shiga gurin. Bedroom dinsa na farko bayanan, kamar ma ba'a taba shiga dakin ba, bedroom dinsa na biyu kuma ina shiga naga alamar anyi amfani dashi amma ba'a kwana a ciki ba, har da kayan sa da yaje daurin aure dasu akan gado, daga dukkan alama sauri yake ya shirya ya tashi gurin party kuma daga can bai dawo nan ba. Na juya jikina a sanyaye na fita. Ina sultan ya kwana? A main palo naga Amina ta fito suna zaune da Fa'iza suna ta zuba surutu, ina shigowa suka bini da kallo, fa'iza tace "wow, masha Allah, babbar yaya kinga yadda kikayi kyau kuwa? Kowa ya ganki yasan babu tantama amaryace" sai kuma ta leka bayana kamar mai jiran wani ya biyo bayana, sai kuma ta rage murya tace "ina angon? Ina fatan dai ba nan zai fito ba dan takura mana zai yi da harara da tsawa" nace mata "sha kurumin ki, baya nan, ya fita already" ta bini da kallon mamaki tace "ya fita kuma? Wanne irin ango ne haka zai fice da sassafe?" Nace "kinsan abokanan sa da suka zo bikin nan wadansu ma bada ga kasar nan suke ba, to duk yau zasu tafi shi yasa ya fita da sassafe dan suyi sallama" daga dukkan alamu ta yarda da bayani na, tayi ajjiyar zuciya tace "har naji dadi, na dauka har an fara gwadawa amaryar halin, kinsan fa sai kinyi hakuri wallahi, dan indai yaya Sultan ne sai ya saka miki ciwon zuciya, dan wani lokacin inya fice sai yayi kwana da kwanaki bama a san inda yake ba" dariya na mayar da maganar nace "really? Kice za'a samu chanji kenan yanzu. Kar ki damu daga yau duk sanda kike bukatar ganin yayanki kizo nan zaki ganshi, in kinga bayanan to office ya tafi" ta tabe baki tace "to Allah yasa" sai kuma tace "dama Hajiya naji tace azo a kawo muku breakfast shine nace bara in zo mu gaisa in kuma ga gidan sosai. Ga abincin can akan dining an ajiye" nace mata "mun gode, in kin koma ki mana godiya a gurin Hajiya" tace "laah chafdi, yaya Sultan fa duk gidan nan shine dan lelen Hajiya, kinga shi ba'ayi masa fada, ba'a saka shi ba'a hana shi, duk abinda yake so shi za'ayi masa, dan haka in kika ce zaki yiwa Hajiya godiya har sai baki kin ya gaji" muka kalli juna ni da Amina, Amina tace "ashe sultan dan gata ne mu bamu sani ba. To shi kuma daya brother din naku fa? Shi ba'ayi masa gatan?" Fa'iza tace "shi wannan ai sha wuya kenan. Shi fa ko time din kansa bashi dashi. Kullum yana tare da Takawa bacci ne kadai yake rabasu, komai nasa shi yake yi. Shi wannan ma banajin ko budurwa yana da ita. In kinga kuwa fadan da Hajiya take masa komai kankantar abu sai kinyi mamaki" Amina ta cigaba da bugar cikin ta "abin tausayi, kice ko karatu mai zurfi bai samu yayi ba kenan saboda bashi da lokacin kansa" tace "kamar kin sani kuwa, da kyar ya samu yayi diploma ya hakura, Hajiya tace masa menene amfanin karatun? Ai anayin karatu ne saboda a samu aiki ake samun kudi, shi kuwa he got all the money to last him a lifetime, aiki kuwa dama dashi aka haifeshi" Amina zara cigaba da yi mata tambayoyi na girgiza mata kai, na chanza topic din da cewa "ni fa duk wannan hirar da kuke yi ba jin ku nake yi ba, dan yunwa nake ji" daga nan muka tashi muka tafi cin abinci. Muna cikin ci Hafsat ta fito, taci kwalliya kamar ita ce amaryar, tayi joining din mu muka ci abincin tare. Dankali ne da kwai, sai farfesun kaji da farfesun ganda, sai kunun gyada mai dadi wanda ni shi nayi tasha, dan sam baki na babu taste, Sultan ne kawai a raina. Nace da Hafsat "kiyi waya mana a kawo khairat, kar tayi ta kuka" tace "ba zatayi rigima ba, nayi expressing breast milk da yawa na saka mata a freezer, da anyi warming an bata shi kenan".
Ranar tamkar wanda ake sake yin wani bikin a gidan, dan sosai gidan ya cika da mutane mostly 'yan uwan sultan masu son ganin amarya da kuma dakin amarya. Na gode wa Allah dasu Hafsat basu tafi sun barni ni kadai ba, dan su sukayi ta hidima dasu suna zagayawa dasu daki by daki, kowa kuwa sai ya yaba da tsarin gidan. Duk kuma wanda yazo sai Amina ta zuba musu kayan gara da snacks din partyn jiya da ba'ayi ba ta bashi. Ni kuma akwatin lefe na na kayan kyalliya guda daya na bude nake rabarwa. Har magriba muna abu daya. Hafsat tayi waya gida ta gaya musu sai dare zasu dawo saboda baki sun yi min yawa, nan da nan sai ga yammata biyu Mommy ta sake turo wa, suka taho da katan katan na drinks da chocolate saboda yara. Abinci kuwa daga cikin gida akayi ta aiko mana, dan haka ko tukunya bamu dora ba. Sai da mukayi sallar magrib sannan kafa ta fara daukewa. Har lokacin babu Sultan babu labarin sa. Na kira wayarsa har na gaji amma still switched off. Bayan munyi dinner muka hadu muka gyara gidan tas har fa'iza da yake bata tafi ba. Muna gamawa muka zauna muna hira, hafsat ta lura ina ta danna wayata ta sake tambayata a hankali "har yanzu bai kunna wayar ba?" Kai kawai na gyada mata, tace "ki kira Amir, shirun yayi yawa" na sake dialing number din Amir, ya dauka muka gaisa yace "ai nayi niyyar shigowa dazu kuma na hango gidan a cike na fasa" nace "wallahi kam yau gidan masha Allah" nayi shiru, yace "bai dawo ba?" Nace "eh, kuma wayar a rufe" yace "amma da mamaki, kusan 24 hours fa kenan" naji hankali na ya kuma tashi. Yace " I will know what to do, am sure yana cikin gidan nan tunda duk friends din mu da suka tafi a gaba na suka tafi kuma bai shiga motar kowa ba, sannan all his cars are here. Za muyi organizing search party mu nemo shi duk inda ya shiga" nace "to na gode, duk abinda ake ciki dai sai a sanar mana" ina kallon Fa'iza tana kallona tana son ta san maganar me nake yi. Tace "wai yaya sultan ba zai dawo bane har yanzu? Tun safe fa nake gidan nan amma baya nan" Hafsat tace mata "a cikin mutanen kike so ya shigo ya zauna?" Tace "a'a wai dai ko yaya ne ai a gaisa dashi. Gashi har dare yayi kar mu tafi mu barta ita kadai"
Bayan sallar isha Amir ya shigo, muka gaisa, nasan ganin fa'iza ne ya saka bai ce min komai ba, sai ya zauna kamar mai daddanna waya ya turo min text, 'couldn't find him, think we report to the police?" ina karantawa naji wani daci a bakina, amma kuma ina jin a raina cewa duk inda yake he is OK, dan da ace wani abun ya same shi da na tabbatar zanji a jikina. Na dago kai na kalli Amir naga baya kallona, nayi masa reply "bashi da wani secret hiding place a cikin palace dinnan? Kamar gurin da yake zama if he wants to be alone?" Ya amsa min "nan spot din dama shine gurin zamansa, cikin trees, yanzu kuma ya sare su yayi gida a gurin" ina tunanin abinda zance masa kawai naji wani feeling like someone is watching me, and that someone is Sultan, nayi sauri na dago kaina na kalli direction din da nake ji feeling din, bakin kofa, and there he is. Har yanzu kayan jiya da daddare ne a jikinsa, fuskarsa babu murmushi kuma babu bacin rai, idanuwansa tarwai a kaina. Nayi sauri na dauke idona na sunkuyar da kaina kasa, har lokacin babu wanda yasan ya shigo palon. A hankali ya fara magana, daga jin muryarsa kasan ya dan jima baiyi magana ba. Yace "waye ya baku izinin ku mayar mana da gida dandali?" Duk suka juya suka kalleshi da mamaki, ni kuwa har lokacin ban dagi kaina ba. Amir ya mike kamar zai ji tsalle yace "I think what you want to say is thank you for keeping my house alive and keeping my wife company" bai bawa Amir amsa ba ya juya yana kallon fa'iza yace "ke, tashi ki fita" jiki na rawa ta mike tace "to yaya babu driver a kusa" yace "Amir ya kaiki" ya karaso tsakiyar palon inda Hafsat take ta watsa masa harara, bai kula ta ba sai da fa'iza da Amir suka fita sannan yace "waye yace kuzo ku cika mana gida da surutu?" Ta yatsine fuska tace "gida? Ina gidan yake? Ai kasan tun kafin ayi daran akayi kwandi, tun kafin kusan zaku yi gida ni da mijina muke da gida, sau nawa kuke zuwa kuna zamar mana a gida bamu taba yi muku gori ba?" Yace "eh din, amma dai bamu je ranar da aka kaiki munyi bake bake mun hana Zayed zuwa gurinki ba" tace "to ai mu bamu muka hana ka zuwa ba. In baka sani ba ka sani, da Allah da annabi ta roke mu muka zauna ai, haka kawai ni an raba ni da mijina an zo an kawo ni cikin hayaniya an saka min ciwon kai" sun jima suna bugawa da Hafsat, daga karshe tayi zuciya ta tashi ta tafi daki. Ya juyo kan Amina da take ta dariya yace "ke kuma waye ya baki ikon saka kayan da ba naki ba?" Ta kalli kayan jikinta ta kalleshi tace "Allah yaso ma kayan 'yar'uwata ne ba kayan wani ba" yace "ni kuma kayan matata ne, sai ki gaya min waye yafi kusanci da ita" tace "to ai miji da mata suna iya rabuwa, dan'uwa kuwa har bada naka ne" yace "ba dai wannan miji da matar ba" tace "shi yasa naga ka tafi ka barta jiya, sai mu din dai 'yan'uwan nata mu muka zauna tare da ita" yace "sai kuma gashi na dawo yau kuma nace kowa yasan nayi, I need to be with my wife, alone" ta mike itama a fusace tace "in kaga na sake dawowa gidan nan sai kunje har gida kun bani hakuri" ina jinsa yana dariya kasa kasa, kafin ta karasa kofar shiga part dina sai ga hafsat nan ta fito musu da jakankunan su ta mikawa Amina tata tace "muje, gobe ma rana ce ai" har sunje bakin kofa Hafsat ta juyo tace "kuma ka sani, kamar a kunnen Zayed, sai na gaya masa ka koreni daga gidan ka" ya bita yana "haba babbar yaya matar babban yaya, ni na isa in kore ki" ya bisu kamar mai basu hakuri, suna fita ya jawo kofar yayi locking yana dariya kasa kasa.
Har lokacin ban dago kaina ba, jinsa nayi shiru na dan gado kadan sai muka hada ido, nayi sauri na mayar da kaina kasa. Dariya yayi sosai sannan ya karaso inda nake zaune, ya zauna a kusa dani ya dan kwantar da kansa a kafada ta, gashin kansa yana gogar side din fuskata, ya kamo hannuna ya rike yana wasa da zobe na yace "Am sorry love, please forgive me, na bar zuciyata tayi controlling dina na daga miki murya a cikin mutane, sannan nazo na tafi na barki ke kadai a first night din mu. I don't know what came over me wai har ni ne na saka miki gun a hannunki. Wannan shi ya saka na kasa dawowa mu hada ido dake tun jiya, I am so ashame if myself. I don't know what to do with my temper" kasa ce masa komai nayi saboda ni basan ni ya kamat in bashi hakuri bashi ba, ni ce nayi masa laifi, duk abinda yayi yayi ne saboda ransa ya baci, kuma nice na bata masa ran. Jin bance komai ba sai ya sauko daga kan kujerar ya durkusa a gaba na ya dora fuskarsa akan cinyata yace "nayi kneel down, in still baki hakura ba kuma zan yi frog jump" nayi murmushi a raina nace "this is my sultan" na dora hannuna a hankali akan gashinsa kamar mai shirin taba wuta, a hankali na fara shafawa, it feels very soft, softer than I imaging. Ina jinsa ya sauke ajjiyar zuciya tare da kara pressing kansa a hannuna. Na fara magana nima a hankali "ni ba kayi min komai ba ballantana har ka nemi yafiya ta, nice nayi maka laifi, nice nayi keeping secret from you, duk da cewa kai baka taba boye min komai akan ka ba, u have the right to be angry at me, am sorry" ya dago kansa yana kallon fuskata yace "we are even then" ya mayar da kansa ya kwantar, na dan ture shi nace "it is not over though, ina kaje? A ina ka kwana ka wuni ka barni da tunanin halin da kake ciki, babu inda Amir bai duba ba a gidan nan baka nan" yana dariya yace "shi Amir din ne yace miki ya duba ko'ina? The fool. Ina part dinsa fa, ina guest room dinsa" nima dariyar nayi, sai da muka gama dariyar mu sannan nace "you really need a bath" ya langwabe kai "no, I need food first, then a bath and then you"
Maimoon is now on wattpad, follow me at @MamanMaimoon
Episode Seventy One : The Honeymoon
Hmmm let's talk about something kafin mu ziyarci honeymooners. Abinda nake so inyi magana akai shine auren dole. Dan Allah iyaye mu kula mu rage yiwa 'ya'yanmu auren dole. Ni 100% ina goyon bayan auren soyayya gaskiya. Saboda soyayya ita take kawo sacrifice, forgiveness, juriya da kuma jajircewa a cikin relationship. Idan da akwai soyayya babu abinda mutum ba zai iya yiwa partner din shi ba. Idan kuwa babu soyayya to dama kiris ake jira yanzu zakaji an fara rigima. Soyayyar dake tsakanin Sultan da Moon ita ce ta saka duk abinda ya wakana ranar kawo amarya ya zamo ba komai ba. I cikin kwana daya sun manta da komai, babu tuhuma babu gori, amma imaging auren babu soyayya a ciki, mai kuke tunanin zai faru?
Na danyi shiru ina kallonsa ina lissafin anya kuwa ina da sauran abinci a gidan nan? Dan duk warmers din abincin an mayar dasu cikin gida. Dabara ce ta fado min a raina, na dan bata rai nace "aren't you forgetting something?" Yace "No" nace "kara tunawa dai" ya danyi shiru har yana sosa kansa alamar tunani sannan ya sake cewa "ni babu abinda na manta" na marairaice fuska nace "Kaza" ya maimaita "kaza?" Nace "yes now, ba ango yana shigowa da kaza ya kawowa amarya ba?" shima ya marairaice yace "please don't tell me yanzu sai na fita siyan kaza" nace "sosai ma" ya harde kafafuwansa yana kallona ni kuma na dan bata rai ina kada kafa irin lallai sai anyi min abinda nake so, dariya naji ya dan yi sannan yace "just tell me babu abinci a gidan inje in siyo, ba sai kin wayance da zancen kaza ba, I know u can't cook, but what you are forgetting is that, I can" ya mike tsaye ya miko min hannunsa yace "zo muje muyi girkin tare" babu musu na kama hannun na mike muka tafi kitchen, muna zuwa ya daukeni chalak ya dora akan worktop din kitchen din yace "sit here and watch" sai kuma ya tsaya yana tunani, ya bude fridge ya juyo yana kallona yace "kaza kika ce kina so ko? To kin samu, kazar amarcinki bata siyarwa bace ba, ni zan gasa miki da kaina" ni dai kallonsa kawai nake yi naga ya fito da kaji manya guda biyu, ya wanke su yazo ya hada spices sannan ya shafe su dashi, ya ajiye su a gefe, ya dawo ya dauko attaruhu da albasa ya wanke ya miko min yace "yanka min wadannan kanana kanana" nace "with pleasure" na dauka na fara yayyankawa. Ya kunna gas ya dora ruwa kadan, ya zuba gishiri da mai, yana tafasa ya zuba taliya. Sannan ya dauko kajin ya sakasu a griller ya kunna yaya setting time. Har lokacin yankan attaruhu nake yi, ya