Showing 210001 words to 213000 words out of 262297 words

Chapter 71 - Maimoon Hausa Novel Complete

sannan yace "mace nake so ki haifa, mai kama dake kuma mai halinki, kuma ina son itama take sona kamar yadda kike sona. Maimunatu zan saka mata" nayi sauri na kalle shi nace "maimunatu? Ai sai muyi maka yawa kuma" ya saka dan yatsansa yana zagaye lips dina dashi, abinda yake fara yi lokuta da dama in zai kissing dina, yace "kin taba ganin inda haske yayi wa mutum yawa a rayuwarsa? Gaba daya rayuwata a cikin duhu nake yinta sai da kika zo sannan kika fara haska min hanya, you brought so many blessings to me, uncountable, yanzu ga baby, to menene laifi dan na kira ta da moon itama, kogi ma ai baya kin dadi" naji dadin maganarsa amma nace "idan hasken yayi maka yawa kuma ai sai ya kashe maka ido ka kasa gani sosai" yace "sai in saka sunglasses" a tare muka yi dariya, abinda nayi tsammani shi ya biyo bayan dariyar tamu, hot kiss, wanda naji shi tun daga kafata har kaina, ganin yana neman zarcewa ya saka na ture shi nace "a asibiti fa muke baka da lafiya" ya shagwabe fuska "ni na warke ai" nace "to in ka warke ka bari a sallameka in munje gida koma menene za'ayi sai ayi, amma yanzu in wani ya shigo fa? Besides kai da baka da lafiya so kake ka karar da sauran karfinka ko?" Bai kula ni ba ya koma ya kwanta irin yaji haushin nan. Banyi aune ba kawai bacci ya dauke mu a haka, daga ni har shi.

Karar wayata ce ta tashe ni daga baccin nayi sairi na mike na sauko ina gyara kayana da sukayi squeezing, na dauka naga Amina ce, ni nama manta tare muka zo da ita. Na dauka da sallama tace "Moon dubiyar kenan? To albishirinki wallahi Mommy da Daddy har da Takawa sun shigo sun ganku" nace "na shiga uku Amina dan Allah da gaske kike?" Tace "wallahi Takawa dai ya shigo, su Daddy kuma yanzu suka zo suka turo ni, na ganku na koma, yanzu ni me zance musu" nace "gani nan fitowa, tunda basu ganmu ba da sauki, Takawa kuwa ba haduwa mukeyi ba ballantana in ji kunyarsa" na kalli sultan naga ya tashi yana kallona, nace "su Daddy sunzo suna waje, an ce Takawa ma ya zo amma ban sani ba ko yana nan ko ya koma" ya tashi zaune yace "then dazu ba mafarki nayi ba kenan" nace "yes Sultan, ba mafarki kayi ba". Na nemo rigarsa na saka masa, yana tayi min complain yunwa yake ji, Allah ya taimake ni su Mommy sunzo da abinci, dan haka suna shigowa na bude na fara zuba masa, dama Sultan ba kunyar Daddy yake ji ba, gwara ma Mommy, ya zauna ya fara cin abincinsa nima Mommy ta matsa min lallai saida na zuba naci. Muna nan tare dasu, Sultan ya ware suna ta hira da Daddy wanda shima naga ya dan sakarwa sultan din, Amir ya shigo, ya gaishe dasu Daddy, nan yake bamu labarin yadda yaje ya kira Takawa da abinda ya faru bayan zuwan Takawan, muka kalli juna ni da Sultan, Amir ya cigaba da cewa " kowa yayi mamakin me yasa yayi fainting, the doctor said he need rest wai stress ne, shine aka kaine daki aka kwantar kuma bayan an jima kawai sai gashi ya fito ko manyan kaya babu, ya karbi key din mota ya fice, babu wanda yasan inda yaje sai dazu ya dawo, yazo nan kuma ya koma can inda aka kwantar dashi, yanzu ya aiko akayi kirana yace inzo in yima sultan knocking ince ya tashi ya ci abinci yayi sallah" muka sake kallon juna ni da Sultan, Daddy yace da Amir ya koma ya gaya wa mai martaba sarki cewa sultan ya tashi har yana cin abinci ma, kuma ya gaya masa jikin sultan da sauki ya kwantar da hankalinsa. 'Yar karamar dariya sultan yayi sannan yace "he doesn't care, kawai drama yake playing" nan take Daddy yayi kansa da fada "ba drama ba koma menene yake playing he is your father, dole kayi respecting dinsa" dama Daddy da dan sauran fushin sa akan abinda sultan yayi, nan ya wanke sultan tas da soso da sabulu, Sultan bai sake magana ba. Bamu ankara ba sai ji mukayi anyi knocking kofa an shigo, Takawa ne da kansa a tsaye a bakin kofa, ya saka babbar riga yanzu, da hula a kansa babu rawani. Fuskarsa babu dariya, idonsa akan sultan. Wani kwarjini naga yayi min sosai, lallai sultan anan ya samu kwarjinin sa. Daddy ya fara kokarin gaishe shi amma sai muka ga ya mika wa Daddy hannu sunyi musabaha, ya karaso cikin dakin duk muka tashi muka fara gaishe shi banda sultan da yake kallon kasa, Amina ta kwashe kayan da muka gama cin abinci ta fita Mommy ma ta bita a baya, na tashi nima zan bisu amma Sultan ya rike hannuna ya dawo dani baya, Daddy ya kalle mu bai ce komai ba shima ya fita. Ya zama saura mu uku, na danyi dariya nervously na kuma kokarin fita amma sultan yaki ya saki hannuna kuma har yanzu kasa yake kallo. Takawa yayi gyaran murya yace "Maimunatu dan bamu guri zamuyi magana" Sultan yace "she is not going anywhere, duk abinda zaka fada min ka fada a gabanta" na kalleshi ina tunanin baiji fadan daddy ba kenan, nace "sultan? Takawa ne fa" yace "you are not going anywhere, in ba zaiyi magana a gaban ki ba ya fita" irin rikon da sultan yayi wa hannuna kamar zai balla ni da kuma yadda naga jikinsa yana rawa ya saka na fahimci ba wai ya hana ni fita ne saboda ya bata wa Takawa rai ba, a'a he is nervous, bai taba zama daga shi sai babansa sunyi magana ba, he needs my support. Na zauna akan kujerar gefensa ina kokarin mu hada ido amma yaki bari in kalli cikin idonsa. Takawa ya karaso gaban gadon sultan ya dan tsaya yana kallonsa, sai kuma naga ya zauna a bakin gadon wajan inda kafafuwan Sultan suke, ya saka hannu yadan bude bargon, ya fara shafa kafar sultan a hankali kamar mai matsa masa kafar, ya fara magana "my Little Love, you are just as strong and brave as I thought you will be. Bansan yadda zaka dauki maganganun da zan gaya maka ba amma ina son ka sani, duk abinda zan gaya maka shine gaskiyar abinda ya faru, kuma abinda zan gaya maka shi zai zamanto amsar tambayoyin da kake yiwa kanka kullum a kaina da mahaifiyarka" nan ya fara zayyano mana labarin da ya saka na saki bakina ina kallonsa, babu wanda yayi magana a cikin mu har ya gama maganar sa, tun daga haduwar su da khairat har dauketa daga gidansi da yayi da auren da sukayi a America, har labarin haihuwar sultan da kuma dawowarsu Nigeria, yadda rabuwarsu ta kasance da abinda Sarki Abdallah yayi bayan rabuwar tasu, aurensa da Hajiya da asalin labarin Abbas, yadda ya dawo hankalinsa yau da kuma sakin da yayi wa Hajiya dazu. Ya cigaba da cewa "ka sani Sultan, ba zan iya dawo da hannun agogo baya ba kuma bazan iya biyaka abinda kayi missing na kulawar iyaye ba, amma daga yau zan nuna maka me ake kira da soyayyar iyaye. Ina nema wa mahaifina gafara a gurinka a bisa abinda ya aikata, kuma ka sani, bayayi hakan bane dan son ransa ko dan ya cutar damu ba, a'a yayi hakan ne saboda yana ganin shine zabin da yafi dacewa a lokacin" ya mike tsaye kamar zai fita kuma sai ya tsaya ba tare daya juyo ba yace "you are no longer the little love I know, you are a grown up man now, kayi tunani akan duk abinda na gaya maka, sai ka yanke hukuncin da kaga ya dace" ni dai da ido nake binsa har yakai bakin kofa sai ya juyo muka hada ido, ga mamaki na sai naga yayi min murmushi sannan ya fita. Na dawo da hankali na kan sultan wanda har yanzu idanuwansa a kasa suke, I can't imagine me yake ji a ransa a yanzu, maganar is hard to digest, I only know that he needs a hug right now dan haka abinda na bashi kenan, a shoulder to cry on, na hau kan gadon na rungume shi idona yana fitar da kwalla, da sauri shima ya rungume ni kamar zai balla ni, sai jin saukar hawayensa nayi a bayana, nima kukan nake yi sosai. Rayuwar sultan kadai ta isa ta zama darasi ga dukkan mai tunani, komai yayi farko yana da karshe kuma ance mahakurci mawadaci ne watarana. Na fara rarrashinsa ina bubbuga bayansa a hankali, nace "shhhh it's over, komai ya wuce, everything is going to be alright".

Da daddare aka sallame mu, direct gida muka tafi. Ga mamakin mu har muka tafi Takawa yana asibitin, amma yana daya dakin sai dai ya turo amir ya ga me Sultan yake yi ya koma ya gaya masa. A motar Amir muka tafi gida, da escort a gaba, sai motar mu sai motar Takawa sannan sauran motocin. Yau sai ga Takawa a gidan mu, shine har cikin bedroom din Sultan, sai daya jaddada min lallai in tabbatar yaci abinci sannan ya rage masa AC n dakin ya tafi. Sultan duk ya zama wani shiru shiru, kuma na fahimce shi, abubuwa ne da yawa suka faru kusan a lokaci daya, yana bukatar lokaci yayi adjusting ya san menene abinyi. Abinda nayi ni kuma a bari na shine na bar maganar ban yi masa ba, na barshi ya shirya da kansa yayi min maganar sai in bashi shawarar da nake ganin ta dace.

Washegari maman Ibrahim ta zo Abuja, a ranar kuma ya farka, he is very lucky babu wani serious internal or external injury daya samu, yana farkawa ni ya fara tambaya if am OK, aka gaya masa am fine, sai yace Amina ta kira mu nida Sultan ta bamu hakuri akan abinda ya faru, yasan laifinsa ne, shi yayi pushing Sultan har ya tura motar sa rami, shima kansa bai san menene ya saka shi ya bi mu a baya ba, Amina tana gayamin a waya a raina nace 'destiny ne, da ace bai bimu ba, abindaya faru bai faru ba, da Sultan bai yi rashin lafiya har sihirin da aka yiwa mahaifinsa ya karye ba' Amina ta tambaye ni ko zan zo in duba shi nace sai na tambayi sultan, Sultan kam yadda yake very emotional nasan bama zan fara mentioning sunan Ibrahim ba, dan haka ban ma tambayeshi ba. Washe gari Amina suka zo min ita da little Moon, sosai yarinyar ta kwanta min a raina, nace "what is your name" tace "Moon" nace "really? Nima sunana Moon" tayi dariya nace mata "can I call you namesake?" Tace "yes". Daga yadda Amina take yiwa yarinyar na kara tabbatarwa cewa Amina is in love with Ibrahim, naji dadin hakan kuma har raina, ina yi musu fatan Allah ya tabbatar musu da alkhairin dake cikin lamarin.

MAIMOON
By
Maman Maama
Episode Eighty Five : Ibrahim
Happy Birthday Oluwaseun Ibrahim Adeniran. May you forever be happy. Kar ka chinye cake din kai kadai dai.
Ibrahim
Last thing da ya gani kafin motar sa ta fadi shine fuskar Moon, and she looks so scared. Sanda motar sa ta fadi babban tsoron sa shine ba mutuwa ba, tsoronsa shine kar wani abu ya sami Moon because of him. A lokacin daya dawo hankalinsa abinda ya fara tunawa shine Moon, Allah dai yasa babu abinda ya same ta, dan haka kalmar daya fara furtawa itace "Maimunatu" muryar mamansa yaji a kusa dashi tana yi masa magana, sannan kuma yaji shigowar wani namiji yana tattaba shi, mutumin ya bude idonsa ya haska masa wata karamar fitila, daga nan kuma ya koma bacci. Sai daya farka for the second time sannan ya fahimci kwanansa uku a asibiti unconscious, ga maman sa da little moon sun zo daga ibadan, amma ita maman sa abinda aka gaya mata shine accident yayi, ba ta san dalilin accident din ba, dan haka ya san bata da labarin ko Moon taji ciwo ko bata ji ba. Doctor ya saka ya kira Amina, wacce tun da ta kai shi asibiti kullum sai ta je ta duba shi, haka ma Daddy, doctor ya gaya wa Amina cewa ya farfado kuma yana nemanta, ba'afi awa daya da wayar ba sai gata tazo. Sosai ta nuna murnar ta daganin ya dawo hayyacinsa, ta ringa yiwa doctor din tambayoyi akan lafiyar Ibrahim din har sai da ta fahimci babu wani muhimmin concern dangane da lafiyar tasa, shi kam Ibrahim kallonta kawai yake yi yana murmushi, sai da doctor ya fita sannan yace "har haka aka damu dani dama ni ban sani ba?" Tace "no, ba damuwa nayi da kai ba. Naso ace ka balla spinal cord yadda ba zaka sake bin mata da miji ba" yace "yes you are right. Nasan banyi dai dai ba, komai yayi min ni na jawo wa kaina, I was just scared he would hurt Moon" tace "matarsa ce fa? In ma menene zaiyi mata ina ruwanka? Kuma ma Sultan will never hurt Moon. Yanzu gashi sanadiyyar abinda ya faru sunyi rigima, har ya kwanta a asibiti ma. She is pregnant fa. You ought to get over her by now" yace "I am over her. Abinda ya faru nima ban san ya akayi ya faru ba and am sorry na jawo problem a tsakanin su. Is she OK?" Tayi ajjiyar zuciya ta zauna a kujera tace "yes she is fine" yace "please can you go to her ki bata hakuri on my behalf? Ki basu hakuri ita da mijinta" ta bata fuska alamar bata son zuwa, ya marairaice murya, "please kinga bani da lafiya fa. Take little Moom with you in suka ganta sai sufi hakura". Har ran Amina bata so zuwa ba, ita a ganinta menene kuma na zuwa wani bada hakuri? Ai kamar kokarin tayar da magana ne kuma, aikin gama ya riga ya gama, daga Ibrahim har Sultan kowa jikinsa ya gaya masa shikenan magana ta wuce sai dai fatan a kiyayi gaba kuma. Amma sai ta yarda zata je din to put his mind at ease. Ta dauki little Moon suka tafi tare. Moon ta tare su sosai kuma taji dadin ganin takwararta amma kamar yadda Amina tayi tsammani sam ba ta ga alamar soyayyar Ibrahim a tare da Moon ba, sai care da mutunta juna, tace mata zata zo ta duba Ibrahim amma ita kan ta Aminan ta san fada kawai Moon tayi ba zuwan za tayi ba. Ga zasu taho Moon ta hada kaya da yawa ta bawa takwararta suka dawo asibiti gurin Ibrahim.
Suna shiga dakin suka tarar Ibrahim ya tashi zaune suna magana da mama, Amina ta durkusa ta gaishe da mama wacce ta amsa mata da fara'arta, daga nan mama ta fita ta basu guri suyi magana. Ba tare daya kalli Amina ba yace da little Moon "sweetheart menene wannan a leda kika samo haka?" Ta karaso gurinsa tana washe baki tace "namesake dina ce ta bani" ya karba yana dubawa "wow duk wannan naki ne ke kadai, bata baki komai ki kawo min ba?" Tace "ba abinda ta bani in kawo maka" yace "kuma bata ce tana gaishe ni ba?" Tace "eh bata fada ba" ya dauki yarinyar ya dora a cinyarsa, yana shafa kanta "sweetheart yau kinga namesake dinki ko? How do you find her?" Tace "she is beautiful and nice" yace "yes sweetheart she is the nicest person I have ever known". Amina ta ajiye ledar hannunta ta juya zata fita, sai a lokacin ya tuna tana gurin, yace "wait" bata juyo ba yace "Maimunatu Please" chak ta tsaya kafin ta karasa kofar, ta juyo a hankali tana kallonsa, a nutse ta fara magana "I am not Maimunatu, I am Amina" ya tsaya kawai yana kallonta dan shi bai ma san ya kirata da Maimunatu ba sai data fada. Ta kalli little moon akan cinyarsa tace "Moon je ki nuna wa Mama kayan da kika samo" da sauri yarinyar ta dauki ledar ta fita da gudu. Bayan ta rufe kofa sukayi shiru suna kallon juna, yace "am sorry, I didn't meant to hurt you, ban san ya akayi bakina ya kauce ba" tace "cut it. Dalilin da yasa ka tura mu gidan Moon kenan wato, because deep down you you still love her, duk abinda kake fada min cewa you are over her duk ba haka bane ba, kace baka san dalilin da yasa kabi su a baya ba amma ni nasan ka bi su ne saboda har yau baka hakura da ita ba. To bara in gaya maka wani abu, she is more than over you. Tun kafin tayi aure ta daina sonka ballantana yanzu. She is happily married. She is not coming back to you. The sooner you get this into your head the better for you. Am not maimunatu am Amina, duk da mun hada jini da ita hakan ba yana nufin feelings din mu da halayen mu daya ne ba. Duk da munyi kama da ita ba hakan yana nufin zan iya rikidewa in zama ita ba. I am my own person. I can't be a substitute for someone. You lost something a rayuwar ka, ka koma baya kayi tracing may be You will find it. I dan kuma baka samu abinda kayi loosing ba then I pity your soul" ta juya ta fita.
Ibrahim ya dafe kansa tare da cewa "ya salam" ya koma da baya ya kwanta akan gadon. "What is wrong with me dear God" duk abinda Amina ta fada gaskiya ne, sai da ta fada kuma sannan ya kara tabbatar da cewa gaskiya ne. He enjoys being with her only because in yana tare da ita sometimes yana jin kamar yana tare da maimunatu ne, amma kuma yasan ba maimunatun bace ba. Amma kuma mai take nugi da he lost something, tana nufin yayi loosing maimunatu? But ai that's obvious, to menene yayi loosing?. Gaba daya ji yayi ya kasa sukuni, duniyar duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login