Showing 213001 words to 216000 words out of 262297 words
tayi masa kunci, me yasa shi rayuwarsa take a haka ne? Sam ya kasa samun farinciki tun ranar da ya juya bayansa ya tafi yabar maimunatu a gidansu tana kuka, ba zai iya tuna ranar da yayi farin ciki ba, genuine farin ciki, ba kuma zai iya tuna ranar da wani yayi farin ciki domin sa ba. Hatta mahaifiyarsa kawai yasan hakuri take yi dashi amma bajin dadinsa take yi ba. What did he miss? Moon is over him ya sani amma shi why can't he get over har?
Satin sa daya aka sallame shi daga asibitin, cikin satin nan ya kara zama miserable, dan har 'yar karamar Moon ma tsoron sa take ji dan daga tayi wani abu kadan zai daka mata tsawa, daga asibitin mama cewa tayi ba zasu je gidan sa ba, yaje yaci kansa shi kadai, ta dauki jikarta su kayi tafiyarsu tasha suka hau mota suka koma ibadan. Shi kadai ya koma gidan sa inda yake zaune shi kadai, ya kira number din Amina yafi cikin charbi amma bata dauka ba, yasan in yaje gurinta ma ba fitowa zatayi ba kuma shi din ma yana tinanin mai zai ce mata in yaje din? Ranar daya koma gurin aikinsa sai da ya kori mutum biyar daga aiki, ya bawa wadansu query, gaba daya kowa ma haushi yake bashi, shi kanshi haushi yake bawa kansa. Rannan ya dawo daga office kawai yaki komawa gida, to in ya koma gidan ma me zaiyi a can? ya kama driving yana zagaya gari a hankali fresh air tana kada shi, ya fara tuno kalaman Amina, she said he lost something a rayuwarsa, she advice him to trace back his life yayi finding menene yayi missing. To in zaiyi tracing back ta ina zai fara? Kafin ya koma gida ya yanke shawarar he is taking the next plight to ibadan, tunda anan ne rayuwar sa ta fara, in ma yana da matsala anan ne zai samu solution.
Da sassafe jirgin su ya sauka a ibadan, ya dauki taxi ta kai shi unguwarsu. Ya sauka ya tsaya yana karewa gurin kallo, babu abinda ya chanja, ya kalli masallacin da a da babansa yake limanci, ya tuna da lokacin da suke zuwa masallacin tare da babansa, what has happened? Ya shiga gidan su da sallama, jakarsa rike a hannunsa, mamansa da take wanke kwanuka ta tsaya tana kallonshi da mamaki. Shi kuma gidan yake karewa kallo, babu abinda ya chanza sai tsufa da gidan ya kara yi da lalacewa. Ya tuna da uwar dukiyar da yake tarawa yake ajiye wa a banza, for what? Ya ajiye jakar hannunsa anan tsakar gidan ya nufi dakin da baba ya zauna kafin rasuwarsa, ya tura kofar ya shiga yana feeling kamar zai ganshi akan tsohuwar kujerar sa da alqurani a gabansa, alqurani? Ya shiga dakin sosai yana kallon tarin littattafan addini a jejjere kamar yadda suke kullum. Cikin littattafan nan babu wanda bai haddace from page to page ba. Ji yayi kansa yana juyawa, when was the last time daya bude alqurani ya karanta? When was the last time daya zauna yayi cikakken azkar? When was the last time daya yi istikara ya nemi zabin Allah a cikin rayuwarsa? How did he expect things to go right a rayuwarsa? Ya juya ya kalli mahaifiyarsa da take tsaye still tana kallonsa, ya sani cewa jin dadin rayuwar mutum duniya da lahira yana jingina a jikin how much yake kyautatawa iyayensa, amma shi baya kyautatawa tasa uwar, duba gidan da take ciki duba gidan da shi yake ciki a abuja. Amma ai da ba haka yake ba, da sanda bashi da komai amma dan albashinsa biyu yake rabawa ya kawo mata rabi, lokacin ma tana da miji ba yanzu ba da bata da kowa sai shi. Ya tuna da baban sa da yadda yayi making sacrifices dan yaga ya zama wani abu a duniya, duk kuwa da cewa bashi ya haife shi ba, a karshe ya dauki 'yarsa ya bashi aure, amma me yayi? Sai ya wulakantata, yaki yin biyayya ga iyayensa, ya take maganar su ya nuna musu basu isa dashi ba, har efi ta bar duniya bata ji dadin aurensa ba, ta yaya zaiyi tsammanin rayuwarsa zata tafi masa a dai dai? Ya dauki alqurani guda daya ya bude ya fara buda pages din yana jin wani feeling mai dadi a ransa, how did this happened? When? When did he lose himself? Sai yanzu ya gane maganar Amina, ba wani abu yayi loosing ba sai kansa, he lost himself the moment da yayi deciding yana son yayi kudi dan ya auri Moon, tun daga ranar he became slave to the idea of becoming rich for Moon. Duk da karyar da Amira tayi masa cewa Moon tayi aure amma ya kasa cire hop din cewa zata dawo gurinsa, kuma yana son sanda zata dawo ta tarar cewa he is richer than yadda tayi tsammani. Duk tsahon shekarun nan komai yayi dan ita yake yi ba dan kansa ba. Hatta kaya in ya saka sai yayi tunanin in ta ganshi yanzu what will she think? In tunaninsa ya gaya masa ba zata so kayan ba sai ya cire ya saka wadansu. He became so obsessed in preparing for her to come back to him that he lost himself along the way. Ya ajiye alquranin hannunsa. He found himself now. Everything is going to be alright now.
Mama ta karaso bakin kofar tana kallonsa tace da yarabanci "Seun lafiya kake kuwa? Yaushe kazo gari? Me kake yi a dakin nan?" Ya mike tsaye ya karasa gabanta ya zube a kan guiwoyinsa, yace "Mama dan Allah ki gafarta min. Nayi kuskure a baya, rayuwata gaba daya bata tafiya dai dai. Dan Allah mama ki yafe min kiyi min addu'ah ko Allah zai dube ni ya shiga rayuwata" Tace "my son, ni ban rike ka da komai ba, kullum addu'ah nake maka Allah ya dawo da kai kan hanya. Kuma Alhamdulillah tunda har kazo ka nemi gafara ta to na tabbatar ka fahimci kuskurenka. Allah yayi maka jagora"
MAIMOON
By
Maman Maama
Episode Eighty Six : The Phone Call
Bayan sati daya da dawowar mu daga asibiti, Sultan ya fara saukowa daga emotional height din da ya hau, ya fara accepting Takawa a hankali. A nasa bangaraen kuwa, Takawa kullum sai yazo part din mu, tun ina jin nauyinsa ina baya baya dashi har na saba na fara yi masa surutu in yazo, dan haka duk sanda yazo nice abokiyar hirar sa Sultan bin mu kawai yake yi da kallo, daga baya sai Takawa ya mayar da zuwa gurin mu da daddare al'ada, kullum anan yake cin abincin dare a palon sultan, sai tanzu nake kara jin dadin koyon girkin da nayi, duk da dai har yanzu asma'u tana nan amma hannu bibbiyu yafi sauri. Kullum Takawa bashi da labarin bawa Sultan sai na khairat, Sultan kam sai yayi shiru ya rabu dashi baya tanka masa. Nayi nayi da Sultan ya gaya masa cewa mun sami labarin ta amma yaki. Shi har yanzu fushi yake yi da ita, yace in ta ki neman mijinta saboda taji haushin ya sake ta to shi kuma fa? Ina laifinsa a ciki.
Wata ranar friday da daddare, Takawa yazo kamar yadda ya saba, ni kuma ina ta faman hidimar jera musu abinci akam carpet, sai ga Amir nan ma yazo, ya gaishe da Takawa, suka gaisa da Sultan ni kuma na gaishe shi. Sultan yana ta tsokanar sa suna dariya kamar yadda ya saba, sai Takawa yace "Sultan baka da kunya, Amir fa uba ne a gurinka" Sultan ya bata fuska yace "Uba kuma?" Takawa yace "eh. Mahaifina ne yayi adopting dinsa, dan haka legally kani na ne, hakan ya saka ya zama uba a gurinka" dani da Amir mukayi ta dariya, Amir har da rike ciki, Sultan ya bata fuska yace "wallahi ba'a isa ba" Takawa yace "daga yau baba Amir zaka ke ce masa. Amir duk ranar da bai ce maka baba ba kazo ka gaya min" Amir harda yiwa sultan gwalo, sannan yayi mana sallama ya fita, ina tayi masa mitar yaki tsayawa yaci abinci. Yana fiya na dauko yankakken apple na kawo gaban Takawa ya dauka ya fara ci yana min godiya, idonsa akan sultan yace "me Amir yake ciki ne?" Sultan yace "as far as I know bashi da problem. Amir is the must cheerful man I have ever known, kullum cikin farin ciki yake, sam bai dauki duniya da zafi ba ko kuma wai ya saka wa kansa damuwa akan neman asalinsa. Matsalar da yake fuskanta daya ce, akan neman auren da yake yi, iyayen yarinyar da yake nema sun hana shi aurenta, wannan shi yasa kwanan baya naga ya tayar da hankalinsa amma yanzu ya fara dawowa normal duk da dai har yanzu ba wai rabuwa yayi da yarinyar ba" Takawa yace "wacece yarinyar?" Sultan ya gaya masa sunan mahaifinta wanda yake malami ne a maiguduri, Takawa yace "ka gaya wa Amir, ya gayawa yarinyar ta gaya wa iyayenta, ni zanje har maiduguri in nema masa auren ta, nine waliyinsa" nan take sultan ya washe baki yana dariya, sai ince wannan shine karo na farko da naga sultan yayi wa mahaifinsa dariya, nima kaina sai da naji dadi, Amir deserves more than that, saboda duk wahalar da sultan ya sha a rayuwa tare suka shata, shima ya kamata ace ya samu farin ciki. Amma kuma can kasan zuciyata ina tausayawa kawata Amira, Amir din ma data dan samu gashi ya gudu ya barta zaiyi aurensa, amma kuma banji haushin Amir ba tunda bai taba furtawa yace yana son ta ba ballantana ace ya yaudare ta. Amma duk da haka sai dana yiwa Sultan maganar bayan Takawa ya tafi, kamar bai jini ba daga farko sai kuma yace "why do you care about her ne wai? Ina ruwanki da ita? She is not loyal" nace "she was not loyal. Amma hakan ba wai yana nufin bata yi learning lessons din ta ba. Everyone deserves a chance at redemption" ya sake dauke kai, na saka hannu na juyo fuskarsa gurina nace "pleeeassse" ya kara bata fuska "to wai ke me kike so ayi mata ne? Shi Amir ga wacce yake so, so kike ince masa Amir ka fasa auren wacce kake so ka auri wacce Moon take so?" Nace "ba haka nake nufi ba honey, kasan yadda Amir suke da Amira, na tabbatar ba za'a rasa sonta a cikin zuciyarsa ba kawai dai wancan son ne ya danne wannan. Kuma shi na miji ai mijin mace hudu ne ko?" Yana kallona kuma sai ya fara murmushi yace "ki sani, in dai akayi auren nan sai na gayawa Aisha ke kika ce ayi mata kishiya tun kafin a aure ta" nayi dariya nace "a'a kar ka hada ni da kawata, in dai har akayi auren to dama an rubuta cewa matar sa ce, bani na saka ba, shi aure ai rai ne dashi, ba'a creating dinsa ba kuma a destroying dinsa, sai dai a zama sila".
Washegari weekend, Sultan yana gida tun safe yana zuba mulki, duk yabi ya addabeni kamar zanyi masa kuka, dama kwana biyun nan kamar wanda ake kara tunzurashi a kaina, ni kuma yanzu ga kasala da take damuna da bacci, ko da yaushe a gajiye nake jina duk da ba wani aikin kirki nake yi ba, dan gyaran part din sultan ma mostly yanzu shi yake yin kayansa indai har yana gida sai dai in baya nan. Da kyar na samu na kwaci kaina daga gurinsa nace zan je kitchen muyi girki da asma'u, ina fitowa ko kallon hanyar kitchen din banyi ba na tafi part dina na shiga na rufe kofa harda saka key, duk da nasan cewa a banza nake yi in dai har sultan ne sai ya shigo sai dai in baiyi niyya ba. In kwanciya a gado ko minti daya banyi ba nayi bacci. Ina cikin baccin naji ana min tafiyar tsutsa a kafa ta, na janye kafar aka sake biyo ni, na tashi zaune da kyar nake bude idona dan bacci, na ga sultan a zaune a tsakiyar gadon yana kallona, yace "girkin kenan ko?" Kamar zanyi kuka nace "bacci nake ji Sultan dan Allah ka rabu dani" shima ya kwaikwayi muryata, "weekend ne fa yau. Weekdays ina damunki ne? Wanda ba'ayi da rana ranar aiki shi nake fanshewa da weekend" bai ankara ba kawai saiji yayi na fashe masa da kuka, ya saki baki yana kallona, na fara cewa "wayyo Mommy ki zo ki taimake ni Sultan zai kashe ni" dariya ya fara yi yana kallona ina ta kuka na, sai daya bari nayi mai isa ta sannan yace "kinsan da Mommy zata ganki yanzu me zatace?" Na girgiza kaina ina share hawayena, yace "cewa zatayi 'ke kika ce kina so, da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba'" na watsa masa harara nace "na fasa sonka ai yanzu, bacci nake so" na yunkura zan sauka daga kan gadon ya jawo ni ya dawo dani ya kwantar, yayi min rumfa da jikinsa yace "ba wani abu zanyi miki ba fa kike ta wannan gudun, wani cikin zanyi miki, kinga sai ki haifa min twins" na fara dariya nace "kai wa yace maka haka ake yin twins din?" Ya saka hannu cikin riga ta yace "haka ake yi mana, in aka yi ciki sai a sake yin wani sai a haifi guda biyu" na lumshe ido ina jin abinda hannunsa yake min nace "gaskiya sultan bacci kake yi a biology classes dinka na secondary school" na bude ido ina kallonsa yana min murmushin mugunta ganin yadda jikina ya fara saki, Sultan ya riga ya gane lagona, duk wani guje guje na da waye, he just need to put his hands on me shikenan magana ta kare. Sai da ya tabbatar he got me right where he wants me sannan ya fara raba jikinsa da nawa a hankali still da murmushi akan fuskarsa, naga cewa da gaske tashi yake son yi ai kuwa na saka hannu biyu na jawo shi na dawo dashi na hade bakinmu, ina jinsa yana dariya a cikin kirjinsa, a raina nace 'wallahi sai na rama, kayi da 'yar halak'.
Anan daki na yayi wanka, sai naga ya saka kaya kamar mai shirin fita, nace "fita zaka yi ne?" Yace "ba nisa zanyi ba, cikin gida zanje gurin Takawa" naji dadi sosai nace "naji dadi sosai da zaka je gurinsa, shima kuma zaiji dadi" ya zauna a bakin gado yana kallona ina goge ruwa a kaina, na gane magana yake so muyi dan haka na karaso na zauna kusa dashi, yace "ina so muyi magana dashi ne akan Abbas. Ya dage lallai sai ya kore shi daga gidan nan. Ni kuma ina ganin rashin kyautawar hakan, shi Abbas ba laifinsa bane ba, bashi ya zabi yadda haihuwarsa zata kasance ba, ba kuma shi ya zabi yadda za'a raine shi ba, bai kamata ace zai yi paying for his parents crime ba" na saka hannu ina kara kwantar da kwantaccen gashin kansa nace "me kake so ayi yanzu?" Yace "so nake yi Takawa ya kira shi su zauna ya gaya masa gaskiyar lamari da kansa cikin sigar lallami da lumana, ya kuma barshi ya cigaba da zama a gidan nan ya kuma cigaba da zuwa fada, babu wanda zai san abinda ya faru sai mu kadai. Kinga in akayi haka sunan family din da suke ta fighting for zai zama ba'a bata shi ba, kowa zai samu abinda yake so. Masu kirari suna yiwa sarki kirari da uban masu uba uban marasa uba, to gwara ya fara zama uban marasa uban akan Abbas" tunda ya fara maganar kallonsa kawai nake yi, a raina nace 'masha Allah' sai daya gama sannan nace "hakan shine dai dai mijina, am very proud of you. Cikar imanin mutum shine ya so wa dan'uwansa abinfa yake so wa kansa, kasan zafin rashin iyaye shi yasa kake kula iyakacin karfinka kaga babu wanda ya dandana wannan zafin, ko da kuwa mutumin da ya aikata maka sharri ne, cikar mutum shine ya rama mugunta da alkhairi. Allah ba zai taba barinka ta tabe ba sultan" nayi masa kiss a gefen bakinsa, yace "wow" ya juyo sosai ya nuna min bakin ya kashe min ido, na makale kafada ina dariya. Nace "ni kuma ga tawa shawarar; idan kun gama settling wannan maganar, ina ganin ka mayar da Abbas makaranta, yadda zai samu future mai kyau nan gaba, ya koma makaranta ko first degree ya samu ya kammala, in ma ba zai yi aiki ba ya ajiye takardun. Kuma komawarsa makaranta zata saka ya dauke hankalinsa daga kan sarauta yasan cewa yana da opportunities a rayuwa beyond his imagination" sultan ya daga kafada yace "OK, I can see what I can do. Amma in yace baya so kinsan bazan dauke shi aka in kaishi ba"
Washegari suka zauna akan maganar. Abbas did not take maganar lightly kuma ni na fahimce shi, maganar da ciwo. Da kyar Sultan ya shawo kansa dan cewa yayi sai yaga bayan Hajiya, Hajiya kam tayi kuka da idonta, ranar Abbas a gidan mu ya kwana part din baki maza. Bayan sultan ya dawo daga gurinsa ya same ni zaune da hijab ga key din mota a hannuna, ya tsaya rike da labule yana kallona, na langwabar da kai gefe, yace "yau kuma me babyn take so?" Nace "Namiji ne fa ba mace ba. Vanilla flavoured ice cream yake so. Sannan da sponge cake ya sha cream da yawa. Sai kuma tsire mai kuli kuli" dariya yayi sosai ya karaso ya karbi key din ya miko min hannunsa yace "you got it". Muna tafiya a mota muna shan ice cream din mu wayar sultan tayi kara, ya dauka, daga gaisuwar da yake nasan Takawa ne, yaje ya tarar bama nan, budar bakin sultan sai cewa yayi "mun tafi shan ice cream, baby ne yake rigima yace shi ice cream zai sha" na bude baki ina kallonsa, duk inda kake tunanin rashin kunyar sultan ta wuce nan, yace "what? He deserves to know da