Showing 159001 words to 162000 words out of 262297 words
an fasa partyn nan kowa ya tafi a bar masa amaryarsa" ta dauka ta gaya masa ina sallah sannan ta kashe. Ina idarwa nace "ke Amina waye ya baki damar yi min magana da mijina" duk suka kwashe da dariya. Hafsay tace "ina tausayawa angwayen nan yanzu fa dawowarsu daga 'yalleman kenan kuma zasu tarar da wata hidimar ta daban". Bayan munyi sallar isha muka shirya zuwa gurin partyn, a wajen swimming pool za ayi, gurin kato ne amma kuma a zagaye yake, dan madaidaicin swimming pool ne a gurin sai kuma kujeru da aka jejjera. An kawata gurin da fitulu masu color wanda yasa ruwan yake yi kamar shi ma different colors din ne. Kayan da na saka musamman Zayed yayi mana order dinsu daga saudiyya a matsayin wedding gift dinsa, kayan larabawa ne na mace dana namiji, kalar light blue mai kyalli. Nayi rolling mayafin yadda ya rufe rabin fuskata tunda ba'a saui baki ba.
Sai da suka gaya mana sun iso sannan muka fita gurin partyn, kawayena a zagaye dani wai lallai babu mai gani na sai an biya kudi. Suka kaini kan kujerata suka zaunar dani. Hayaniyar da naji ne yasa na fahimci gurin a cike yake da maza abokanan Sultan, a raina nace 'sultan akwai kwashe kwashe shi kam' ina jinsu suna ta ciniki na sai kace wata kaza, har suka gama a take Solomon ya rubuta check ya bawa kawayena, sai da aka basu sannan suka matsa daga gabana na fito fili sosai. Ta cikin mayafina nake leken inda zanga Sultan, tunda aka daura ban ganshi ba, can na hangoshi a tsakiyar abokansa suna ta dariya, fuskarsa kamar gonar auduga, yayo kyau sosai da kayan sa irin nawa. Gurin gaba daya ya hargitse da samari da 'yammata, kusan rabin mutanen gurin a tsaye suke. Ina jiyo amir da sultan suna ta musu, Amir yace tunda an sayi baki sai a bude fuskata kowa ya ganni tunda purpose din taron kenan, a taryi amarya, Sultan kam yace sam babu mai gane masa fuskar mata, ai kowa ya ganni a dinner da luncheon.
Ni dai ina zaune kamar gunki. Wani kamshi dana shaka be yasa zuciya ta ta tsaya ta daina bugawa for some seconds, sannan kuma ta fara bugawa da sauri, Hafsat da take zaune a kusa dani naji ta mike tace cikin muryar rada "what are you doing here?" Muryarsa naji yace "I have come for her" a razane na dago fuskata, Ibrahim na gani a tsaye a gabana, wani jiri naji yana neman daukana 'am I hallucinating?' Yawun bakina gaba daya ya kafe. Na kalli gurin da Sultan yake naga ya juyo yana kallon mu. Ji nayi kamar in tashi in fita daga gurin a guje saboda tsoro. Bakina ya kasa motsi ballantana inyi magana, inajin Hafsat tana masa bala'i murya kasa kasa "ka fita tun kafin su ganka, baka san an daura mata aure bane ba, there is nothing more between you two" maimakon ya fita din sai ya durkusa a gaba na, na kuma kallon Sultan da sauri naga gaba daya attention din su shida friends dinsa ya dawo kan mu. Fitsari ne kawai ban saka a wando na ba. Sama sama nake jin muryar Ibrahim yana magana "Maimunatu, nace miki na hakura ne saboda kince min you will be happy with him, a lokacin ban san wanene zaki aura ba, Maimunatu how can you marry someone like him? Is he blackmailing you or your family? Nasan ba dan kudinsa bane because you have all the money you need, kuma yanzu bayan binciken da nayi a kansa na tabbatar ba dan kina sonsa bane, saboda ni na sanki, nasan ba zaki taba son mutum mai hali irin nasa ba. Maimunatu nazo nan a yau, duk da nasan cewa ba lallai ne ya bar ni in fita daga gidan nan da raina ba amma am ready to die for you in dai har hakan zai kawo karshen wannan auren naki ne. I sacrifice my love so that you will be happy, but now after knowing you won't be happy I am willing to sacrifice myself so that you will be free" Tashin hankali ba'a saka masa rana. Poor Ibrahim. You have no idea what you have done. Hannuna naji ya kama ya saka min wani abu a ciki, sannan cikin rada yace "please Moon, run away" ta baya naga an finciki Ibrahim an mikar dashi tsaye, na daga kaina naga Solomon, kyakykyawan mari ya sauke a fuskar Ibrahim. Na mayar da dubana kan Sultan, kofin da yake hannunsa naga ya saki ya fadi kasa, sannan ya fara takowa a hankali idonsa yana kaina, na mike tsaye ina jiran karasowarsa, Hafsat ce tayi sauri tasha gabana, a raina nace "oh no my dear sister, Sultan will never hurt me" chak ya daga ta ya ajiye a gefe, na daga mayafina na karasa bude fuskata ina kallon cikin jajayen idanunsa. Bazan iya cigaba da kallon abinda nake gani a idon sultan ba dan haka na rufe nawa idon, ya dora goshinsa akan nawa yace cikin muryar rada "who is he?" Na kasa cewa komai, ya kara tambayata "who is he?" Da kyar na tattaro yawun bakina daya bushe a hankali nace "please sultan, not here" kamar baiji ni ba ya sake cewa "who is he" kafin in bashi amsa ya kama hannuna ya cire abinda Ibrahim ya saka min a ciki, na bude idona na kalli abin, shima shi yake kallo. Kallo daya nayi masa na gane menene, pink Handkerchief dina ne dana yiwa Ibrahim reply a jiki all those years ago. Sultan ya bude ya karanta rubutun jiki. "I don't know where the path to the future leads, but I want to find out with you"
Hmm
Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
Ibrahim; 9 hours ago
Ya daga kai ya kalli agogonsa da yake kada karfe goma sha biyu na rana. Ya mayar da idonsa ya lumshe yana jin zafi a ransa. Tun safe yake kwance akan gadonsa, ko breakfast bai yi ba. It is time, yasan yau ne yasan kuma yanzu ne daurin auren Maimunatu dan har katin daurin auren yana dashi. Ya dauko katin yana juyawa a hannunsa, sau nawa za'a bashi katin auren maimunatu ne wai? Kamar yadda ya gaya mata ya hakura, he just want her to be happy, kuma indai happiness dinta will come from wannan auren to dole zai hakura da ita ko da kuwa zai cigaba da zama babu aure har karshen rayuwar sa. Amma tun ranar da yace mata ya hakura din bai samu sassauci na radadin da zuciyar sa take masa ba har yau. Why must his destiny be so cruel ne? Da ya rasa ta ya sha wahala after several years kuma sai gata har office dinsa only for her to tell him cewa bata sonsa yanzu wani take so kuma. Ya mike zaune ya jawo wayarsa ya kira yaronsa ya bashi umarnin ya siyo masa abinci ya kawo masa dakinsa. Ya ajiye wayar yana tunanin wannan abin daya same shi yasan duk alhakin Efi ne. Marainiya babu uwa babu uba aka aura masa amma duk da son da tayi masa haka ya rufe idonsa yayi ta gallaza mata sabida baya santa. Lallai alhaki kuikuyo ne, gashi shima wacce yake so din tace bata sonsa kuma duk da cewa ba tayi treating dinsa kamar yadda yayi treating Efi ba amma zuciyar sa ba karamin zafi take yi masa ba. Shin haka Efi taji itama? Ko kuma taji fiye da haka ma? Ya tuna sunan mijin da Moon ta aura, Sultan, a Prince, ya tabbatar ba zata samu matsala ba tunda at least babban gida zata shiga, gidan daraja, she will be respected in the society. By impulse, kawai ya jawo wayarsa ya shiga Facebook saboda yana son ya rage tunani, yana shiga ya fara scrolling through newsfeed, ya jima a haka kawai yaga hoton Moon tare da wani, ya jima yana kallon hoton saboda irin kyan da yaga tayi masa, yayi sauri ya dauke kansa yana kiran "auzubillah" matar wani ce yanzu, ko kallon mijin nata baiyi ba ya bude labarin kasan hoton. Zuciyarsa ce ta buga da karfi har sai da ya mike zaune, jikin sa ya fara karkarwa, ya sake maimaita heading din labarin "The Drunk Prince of Abuja weds Today" a hankali ya fara karanta labarin, an danyi brief magana akan Sultan, irin halayensa da mutane suka sanshi dashi, sai kuma akayi bayanin yadda bikin ya kasance da irin kudin da aka kashe a bikin. Kafin ya gama karantawa gaba daya gumi ya jika jikinsa, ya fara duba comments din mutane, most of them suna cewa suna tausayawa Moon na 'she looks so young' 'iyayenta sun cuceta' 'poor girl' wadanda kuma basu san iyayenta ba suna cewa 'kudi iyayenta suka gani suka bashi' Ibrahim ya ajiye wayar akan gado ya rike kansa da yake sara masa, ya ilahi, me yake faruwa ne? Mai yasa maimunatu ta auri mutum irin wannan? Ba class dinta bane ba. Ya sake daukan yawar yana ta bincike akan Sultan, anan yaga labarin gang bang da irin abubuwan da suke aikatawa a duk fadin Nigeria. No, no, no, kawai yake maimaitawa "no I will not let Maimunatu destroy her life. But why us she doing this?" Gani yake kamar duk abinda ya faru fault dinsa ne, da ace tun farko bai tafi ya barta ba da duk haka bata faru ba. A ganin sa babu wacce zata auri dan giya tace zataji dadin aure, babu kuma wacce zata auri known criminal kamar sultan tace zata ji dadin aure.
Da sauri ya zura rigarsa ya dau key din motar sa ya fice, yama manta da zancen bai ci abinci ba. Supermarket dinsa ya tafi yayi kamar zai shiga sai ya tsaya, mai gadi yazo ya gaishe shi, yace masa "kasan wani dan Sarkin garin nan kuwa da ake bikinsa yanzu?" Da sauri yace "sosai ma kuwa yallabai, ai wannan babu wanda bai san shi ba a garin nan, tun yana yaro ya gagari ubansa, mai martaba sarku da kansa ya kaishi gidan gagararru, acan ya girma, naji labarin ma har kisan kai yayi a gidan shine suma suka ga ba zasu iya ba suka sallamo shi ya dawo" (kunji mutane ko?hmm) Ibrahim yaji yawun bakinsa gaba daya ya dauke, mai gadin yace "Yallabai Allah dai yasa ba wani abun ne ya hada ka dashi ba?" Ibrahim yace "babu komai kawai labarin bikin naji" daga nan bai shiga ba ya fito da motar sa ya kuma hawa titi, tafiya kawai yake bai san inda zashi ba, mai yasa Daddy ya yarda ya aura wa Moon Sultan? Tabbas da akwai wani abu a kasa. Maybe blackmailing Daddy yake yi, tunda Daddy babban mutum ne, Sultan zai iya hada wata karyar yace idan Daddy bai bashi Moon ba zai fada a gari, irin abinda blackmailers suke yi. Wani gurin cin abinci ya tsaya ya shiga, ya duba agogonsa yaga karfe biyu har da rabi, time is running out, he have to think of something. Dan kadan yaci abincin yaji ba zai iya ci ba, ya tashi yaje gurin biyan kudin sai yaga bayarabe ne cashier din, ya tambayeshi da yarabanci "kasan dan sarkin garin nan da aka yiwa aure kuwa?" Mutumin kamar dama jira yake yace "ni kuwa na san shi, ni da suka hana ni bacci jiya da daddare ba dole in san shi ba?" Ibrahim yace "suka hana ka bacci kamar yaya?" Mutumin yace "ai inda suka yi partyn jiya a kusa da gida nane, shi mai gidan, Solomon, is a known criminal in lagos, ya gagari kowa, he is a kidnapper as well as an arm robber. Gida kawai ya saya a garin nan ya ajiye in yayo barna a lagos sai ya taho nan ya zauna kwana biyu sannan sai ya koma. Jiya a gidansa sukayi partyn su har gari yawaye babu wanda yayi bacci a unguwar nan sabida kida, kwalaben giya kuwa da aka ringa shiga dasu ni dai har kallo na fito yi, da safe makocina ya ce min ta window dinsa yaga ana shiga da mata gidan, mata irin wadanda bana mutunci ba, mu dai jiya Allah ne kadai ya saka va'a kife da unguwar mu ba saboda yawan zunuban da aka aikata a ciki" Ibrahim has heard enough, yayi masa godiya ya fito. Direct gida ya koma, kafin ya karasa gida har ya yanke shawarar abinda zai yi a ransa. He is going to break the marriage, even if it takes his life. Yayi murmushi a ransa, maybe wannan shine destiny dinsa, maybe wannan shine dalilin da yasa Allah ya sake hada shi da Moon few days to her wedding. Yana zuwa gida yayi sallah ya bude locker dinsa da yake ajiye muhimman takardunsa ya dauko handkerchief din Moon daya ke ta ajjiye dashi all those years. Ya karanta rubutunta da still yake baro baro a jikin hanky din "I don't know where the path to the future leads to, but I want to find out with you" ya sake yin murmushi. So, this is it, this is the future, their future, and he will be there for her. Da yake late yayi sallar azahar din sai yaji already ana la'asar dan haka ya sake tashi yayi sannan ya dauko wayarsa. Yasan inya kirata ma ba zata dauka ba. Amma wannan 'yar'uwar tata wacce tayi masa karyar cewa ita yayar moon ce, yama sunan ta? He can't remember. Number din ma bai yi saving ba dan haka yayi ta scrolling call history dinsa har yayi tracing number din, yayi dialing, sai da ya kira wajen sau uku sannan ta dauka, kamar yadda yayi tsammani hayaniya ake tayi, tace masa bata jinsa sosai amma bara ta fita waje ta kira shi. Ba'afi ten minutes ba kuwa ta kira shi, suka gaisa sosai ya tambayeta ya biki tace Alhamdulillah, yace "kuma ku bikin naku na rowa ne ko? Ko gayyatar mutane ma bakwayi" tace "ayyah, na dauka Moon ta gayyace ka ai" yace "a'a, ko daurin aure bata gayyace ni ba. Na so kuma inyi attending ko da event daya ne in yi wa ango Allah ya sanya alkhairi, kuma kinga kema ai da mun sake gaisawa sosai ko?" Ta danyi dariya tace "ai ba'a gama ba, yanzu zamu tafi kai amarya, a can gidan nata kuma zamu yi party da daddare" a ransa yace "perfect, then that is what I will attend" a fili kuma yace "to ban sani ba ko za'a iya gayyata ta can din" ta sake dariya tace "why not, ai har da maza abokan ango. Ka taho kawai bayan Sallar isha, tunda biki ake in kazo palace din zasu barka ka shiga, sai a nuna maka part din amaryar, in kaje can sai ka kirani sai in shiga da kai" yace "kai amma naji dadi sosai, jazakillah bil jannah" tace taba dariya "kai sai kace wani abu na baka? Sai kazo din" ya kashe wayar yana murmushi, sam baya jin tsoro ko fargabar abinda zai je ya dawo. Tsoron da yaji ya kasa tunkarar Daddy shine dalilin faruwar komai, he is no longer afraid, he was a fool, but not anymore. Yana yin sallar isha ya shirya, shi kansa bai san taka maimai me zaiyi ba amma yasan zuwansa gurin a matsayinsa na tsohon saurayin Moon zai bata ran mijinta, tunda dan giya ne ma zai dauka ita ta gayyato shi, hakan kuma zai iya zama sanadiyyar mutuwar auren, shi kuma ko menene zai faru dashi bai damu ba, as long as Moon will be free from this marriage.
Bai sha wahala gurin shiga palace din ba saboda gidan a cike yake da mutane, tun daga gate ya tambaya akayi masa kwatancen inda gidan amaryar yake, da dan nisa kafin ya karasa, yana zuwa yaga gurin a cike da motoci, yayi packing ya fito sannan ya kira number din Amina yace mata gashi yazo, ba'a jima ba ta fito suka sake gaisawa sannan tayi masa jagora zuwa ciki. Suna shiga ya hango Moon a zaune a tsakiyar kawayen ta, sparkling like the moon she is. And he feel like his life doesn't matter any more.
Moon
Na sake rufe ido na ina kokarin saita numfashina tare da kiran "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" repeatedly a zuciya ta. Na bude ido na naga har yanzu Sultan ni yake kallo, jijiyoyin wuyansa da goshin sa sun fito rado rado. Na sake hadiyar yawu da kyar nace "Sultan, this is not what you are thinking" ya kalli handkerchief din hannun sa yace cikin shakakkiyar murya "this is your handwriting. Baki bani amsa taba, who is this man to you? What is he doing here today?" Nayi kokarin rike hannunsa ya matsa baya, cikin rawar murya nace "Sultan not here please. Nayi maka laifi, please ka bari muje wani gurin sai inyi naka bayani". Handkerchief din hannunsa ya dunkule ya jefo min a kirjina, ya juya baya ya koma inda yake dazu. Ban taba ganin bacin rai a fuskar sultan irin wanda nake gani yanzu ba. A hankali na juya gurin Hafsat da take tsaye kusa dani na dora kaina a kafadar ta na fara kuka. Muryar Amir naji yana magana "alright ladies and gentlemen, the party is over, we really appreciate your presence but you all need to leave now" na dago kai ina kallon mutane suna ta fita, friends dina ko sallama basu samu damar yi min ba duk Amir ya tisa keyar su suka fice, Amina da Hafsat ne kadai suka ki tafiya, mazan ma duk Amir ya koresu, amma sai na lura da gang bang ko mutun daya bai fita ba, sai kara samun guri suka yi suka zauna. Sultan na hango shi kadai yana tsaye ya juya bayan sa ya dora kafarsa akan kujera yana shan wani abu a cikin kofi. Gaba na ne ya fadi, oh dear God, no. This is all my fault, tun farko dana bawa Sultan labarin Ibrahim da duk haka bata faru ba. A hankali na fara takawa ina tafiya inda Sultan yake tsaye, na karasa bayansa na