Showing 27001 words to 30000 words out of 105783 words
cikin riga da skt na uniform nata sosai tayi kyau masha Allah ta fito parlour can kuma sai tayi murmushi ta haura sama cikin sand'an.
Sadiq na Shiga daki saman bed ya fada tare da lumshe ido, yana maida numfashi a hankali wata irin tsanar fatuha na ratsashi ware sexy eye's dinshi yayi tare da tashi tsaye, ya je gaban fridge ya bude ya curo fresh milk ya sha sannan ya fara jin zuciyar shi ta daina kuna, ya tashi ya cire uniform dinshi yashiga toilet....
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red opare-speed_dial_yn_=H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com
35_36
A hankali ya murda handle d'in kofar toilet ya zura kafar shi ji kake suuuu gwajaf yayi fad'uwar yan bori, fatuha da ke maqale bakin kofa ta kasa kunne jin fad'uwar sadiq ya sata bushewa da dariya har da rawar tanbola dan shauqi, bud'e kofar tayi ta shigo bedroom tana shigowa ta qara fashewa da dariya, saboda zaman da sadiq yayi a qasan toilet qarasowa tayi bakin kofar toilet din, a hankali sadiq ya dago sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata dariya ta kuma saki tare da bala masa harara ta ce, "ah mai kyau ansha qasa..! dariya ta kumayi tare da gyara tsayuwa ta ce, "toh mai kyau bari na kirama hajiya ta kirama mai d'auri saboda nasan ka goce koka kare dan ba karamar faduwa nasan kayi ba" ta qara bushewa da dariya, sadiq ko cije lips yayi yana jin wani irin rad'ad'i da tsanar fatuha na ratsa sa, kenan ita tasaka masa mai a toilet dan ya fad'i kallon banza ya wurga mata yana qoqarin tashi amma ya kasa wani irin rad'ad'i qugunsa ke masa dan ba karamar fad'uwa yayi ba sosai yake jin rad'ad'i a kugunsa, cije lips yayi ya zauna dan baya iya tashi dariya fatu take saki ganin yarda yake cije le66e yana rinrintse ido ta ce, "Kwarankwatsi baka iya tashi Qur'an ka bugu ba kad'an ba qila ma ka kare ko ka goce", dariya ta kumayi ta nuna idanuwan ta da yatsu biyu sannan ta nuna idon sadiq wanda ke binta da kallon tsana sa'a kawai yake nema ya wawuro ta ya cigaba da duka saboda ya kai maqura iya maqura, daure fuska tayi ta ce, "ka tuna turani da kayi d'azu a matatakala na fadi? toh Allah ya isa ba kasan wacece fatuha ba ko? kaje kauyan wudil ka tanbayi *wacece fatuha diyar Baffa jauro qawar fatsima*, sannan ta qara fashewa da dariya ta ce "Kuma daga yau zan fara nuna ma irin kala haukar fatuha, kuma wallahi kasani fatuha ba'a mata abu ta hakura ko ta dangana, d'azuma a lokaci ba hakuri nayi ba shi yasa na rama," ta bala masa harara tana qoqarin fita, sadiq ko wani miyan bakin ciki ya hadiye yana jin wani irin bakin ciki ,ji yake kamar ya tashi ya shaqe fatuha har sai numfashin ta ya kusa daukewa ya sake ta lumshe idanuwansa yayi zuciyarsa na masa suya da tafarfasa tamkar garwashi, yana matukar mamakin yarda bagidajiyar yarinyar bata shakar sa tunda Mom ke kawo masu aiki bai ta6a cin karo da mai aiki irinta ba, alwashi ya d'aukarwa kansa sai ya gyarawa yarinyar zama ko yana korata.
Washe da baki fatuha ta fito daga part d'in sadiq jin zuciyarta take fes tamkar an zuba k'ank'ara sai da ta daidaita kanta sannan ta fara matsar kwallar gulma, bedroom d'in Mom ta nufa tana yarfe hannu a hankali ta bud'e k'ofar d'akin Mom ta hango kwance saman bed tana karanta azkar, cikin nutsuwa ta shigo tana matsar kwalla Mom ce ta d'ago su kayi 4eye's da fatuha murmushi ta saki tana qoqarin tashi zaune ta ce, "fatuha qaraso mana" jikin kofa ta qara maqalewa tana matsar kwallar gulma dakyar ta iya furta, "Mom dama baban jidda ne ya ce na kawo masa ruwa ina shiga dakin na ganshi ya fadi a kewaye kuma ya kasa tashi" tana ida zancan ta fashe da kukan munafurci Mom tashi tsaye tayi cikin tashin hankali a rud'a ta ce, "muje bedroom d'in nashi naga ko lafiyar baby" Mom na gaba fatuha na baya tana aika gwalo suka shige part din direct bedroom d'in sadiq ta shige yanan zaune inda fatuha ta barshi yayi-yayi ya tashi amma ya kasa Mom ce ta qaraso tare da kiran sunan shi cikin damuwa ya juyo yana kallonta fatuha na bayan Mom tana matsar kwalla da sun hada ido da sadiq ta aika masa gwallo shikuma ya aika mata harara Mom ta ce, "sannu baby kaji bari mu taimaka ma ka tashi,"
"no Mom ba ku iyawa a miqomin phone d'ina tana saman stool na kira *ola* da *Sunday*" cikin sauri Mom ta miqa masa wayar fatuha na gefe ra6e zuciyar ta fes.
Bugu daya biyu *ola* ya daga kiran sadiq, sadiq ya sheda mashi yana neman su, shi da *Sunday* cikin sauri suka qaraso bedroom din, ganin su Mom tsaitsaye yasa jikin su *ola* yin sanyi hango sadiq su kayi zaune a toilet yayi zaman yan'bori a hankali *ola* ya qaraso tare da gaida Mom cikin hausar su wadda bata fita amsa masu tayi sadiq a hankali ya ce, "*ola* taimaka min na tashi kai da *sunday*"
"OK boss" Sunday da ola suka taimaka ma sadiq ya miqe suka d'aurashi saman bed Mom sai sannu take masa itama fatuha sannu ta masa wani irin mugun kallo ya mata, ya kauda kai Mom ce ta ce, "baka ji fatuha na ma sannu bane" lumshe ido yayi tare da ware su ya ce, "ban ji ba.! ya qara maida idanuwan shi ya rufe, wayar shi Mom ta curo ta kira doctor yakub ba ayi minti 39ba sai ga doctor yakub riqe da briefcase din shi ya shigo, fatuha ta masa isowa har bedroom din sadiq gaida Mom yayi sannan ya shiga duba sadiq tare da tataba inda ya bige sannan yayi yan rubuce-rubuce, gyaran murya yayi ya ce, "Alhamdulillah buguwa ce amma bai goce ba kuma bai kare ba, abin ya zo da sauki" murmushi Mom tayi tare da hamdala, sannan doctor ya bashi magani da ze shafa da kuma na ciwon jiki sannan yayi ma su mom sallama ya tafi, Mom da fatuha kuma suka fita.
cikin cool voice nashi sadiq yace da ola ya taimaka ya kai shi bathroom ya watsa ruwa amma ya fara goge man da ke zube a toilet sai da ola ya wanke toilet din tas sannan ya taimakawa sadiq ya shiga toilet, ola na bakin kofa yana jiran sadiq yana gama wanka ya kira ola ya taimakamasa ya fito ko da ya fito ola ya fito masa da jalabiya milk bayan ya gama shafe jikin shi da mai sannan ola ya taimakamasa ya shafa masa magani sannan yasa jalabiya ya koma saman bed ya lumshe ido ,ola ne ya 6alo magani da ruwa ya bashi ya sha yana gama sha ya lumshe ido bacci mai nauyi ya d'auke sa, ola ya koma saman sofa ya zauna Sunday kuma ya kwashe kayan da suka baci da mai ya fita.
Fadawa gado fatu tayi ta ce, "Wash Qur'an yau nayi aiki inama a ce fatsima na kusa" ta qara bushewa da dariya, ta kalli bed jidda na kwance tana sharar bacci dariya tayi ta ce "Allah sarki angal wato(angel) yau na naqasa baban ki sai hakuri angal na san in zafi yayi zafi har sunnan ki sai ya fada" ta kara fashewa da dariya tare da rausayar da kai to ce, "Amma fa gaskiya ban duba masa ba" ta ida zancan tana cire kayanta ta shige toilet tayi wanka d'aure da towel ta fito lokacin jidda tatashi, murmushi tayi ma jidda tare da d'aukarta dan lokaci 4:00pm saura malamin jidda ya kusa zuwa wanka ta mata a tare suka fito suka shirya sallah su kayi saboda anata kiraye-kirayan sallah bayan sun gama sallah fatuha ta rako jidda har waje lokaci har malam ya zo ji tayi itama tana sha'awar karatun, cikin gida ta juya tare da shiga bedroom din Mom, Mom na zaune saman daduma karasowa tayi tare da murmushi ta tanbayi Mom itama tana so ta fara zuwa malam na qara mata karatu Mom ta ce, babu komai ita ma ta je washe da baki ta fita, taje wajan malam itama ba laifi fatuha ta d'an san sururi da yawa sai dai karatun nata ba tajweed shine kad'ai ya d'an bata karatun ba laifi sunyi karatu sosai inda fatuha ta nutsu tana ta karatu, dan wannan malamin ba karamin malami bane.
Bayan sun gama karatu misalin karfe 6:00pm suka shigo gida cikin farinciki, Mom na zaune saman three star tana kallo abba na gafenta gaishe su tayi cikin nutsuwa sannan ta shige daki jidda kuma ta fada jikin Abba tana zuba masa surutu kiran sallar magrib ne ya sa Abba tashi ya wuce masallaci, jidda kuma ta shige bedroom lokacin fatuha ta fito daga toilet daure da alwala, murmushi fatuha tayi ta ce, "Jidda yi maza kiyi alwala kiyi sallah kiyi ma baban ki addu'a, bai da lafiya kinji" waro ido jidda tayi ta ce, "Anuty me ya samu daddy" take Ida zancan tare da rugawa wajan kofa zata fita, jawo ta fatuha tayi ta ce, "yi hakuri mu fara yin sallah sai na kai ki kinji jidda" toh tace mata tana matsar kwalla fatuha kuma na lallashin ta.
Bayan sun gama sallah fatuha ta shirya jidda cikin night dress din ta blue n white wando da riga ba qaramin kyau su kayi mata ba, ta ja hannu ta suka wuce part din sadiq.
Suna Shiga suka samu ola zaune saman sofa, sadiq ma zaune saman bed, yana shan coffee da gudu jidda ta fada jikinsa tana kuka ta ce, "daddy..! lallashin ta ya shigayi yana cewa, "angel menene yake damun ki? bata fuska tayi ta ce "Daddy ashe baka da lafiya shine baka fada min ba? ta ida zancan tana matsar kwalla sadiq y'all ce, "sorry angel lafiyar daddy qalau, waya fada maki daddy bai da lafiya? fatuha ta nuna da ke manne jiki kofa kamar ka ce tak ta arce wani irin kallon tsana ya gefa mata tare da qaqaro murmushi yayi wa jidda yana kallonn fatuha ya had'e rai tamkar yayi bindiga ya ce, "angel na rasa yadda akayi grandma ta samomaki new Anuty mahaukaciya" ya ida zancan yana kallon fatuha ido cikin ido, kauda kai tayi tare da turo baki gaba angel tattoo ce, "daddy new Anuty ba mahaukaciya bace ba"
"injiwa ya ce maki ba mahaukaciya ba ce" fatuha ko wani irin tsoki ta ja tare da jan kofar bedroom da karfi ta fita lumshe ido sadiq yayi yana tunanin irin hukuncin da zaiyi ma fatuha in ya tashi...
written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167refid-52&red opare-speed_dial_yn_=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com
37_38
Fatuha bedroom ta shigo tare da yin sallah isha'i saboda tana da alwalata, bayan ta gama sallah ta rage kayan jikin ta yar rigar bacci tasa wadda yanzu ta zamar mata jiki, idan batasa ba ko bacci bata iyawa kanta ta qarewa kallo ta cikin mirror ita kanta mamaki kanta take saboda ta wani qara haske, da kyau sannan komai na jikin ta ya ciciko rufe idanuwanta tayi tare da ware su, ta sauke su kan qirjinta wanda yanzu ya fara cikowa sosai, murmushi tayi tare da jin kunya ta bar gaban dress mirror din ta fada gado tare da yin addu'a lumshe idanuwanta tayi sadiq ne ya fadu mata a rai tayi sauri ware idanuwan ta tare da sakin dariya, saboda duk lokacin da ta tuna da zaman yan borin da sadiq yayi sai ta dara a haka har bacci ya kwashe ta.
Duk juyi dayayi sai ya zabga tsaki saboda bacin rai ola ne ya juyo ya ce, "boss are u ok? lumshe ido yayi ya ce, "Yes.!
"ok good night boss if u need something talk to me please," ok tare da juyawa ya gyara kwanciyar shi a hankali ya shafa gashin jidda sannan ya lumshe ido, daya lumshe ido fatuha yake gani tana masa dariyar qeta wata irin iska ya furzar mai zafi daga bakin shi ba abinda zai hana shi yima fatuha horo mai tsanani, wanda ko wani aka ce tayima irin cin kashin da ta masa ba zatayi marmarin maimaitawa ba, tsaki ya kuma ja saboda takaici a haka har baccin barawo ya d'auke shi.
*Asuba ta gari..*
Tunda asuba fatuha ta tashi saboda tasan in yau bata tashi da wuri ba Allah kad'ai ya san jarabar da sadiq zai mata, d'an tsaki ta ja can kuma tayi murmushi ta ce, "ko ba komai ina ganin mai kyau Qur'an naji dadi..! sannan ta shige toilet tayi wanka tare da yin brush da dauro alwala tayi sallah sannan tasa uniform komawa tayi ta zauna saman bed tana kallon agogo karfe shida take so ta shiga part din sadiq.
Ba laifi daya tashi sallah asuba kafar ta saki tunda har ya taka bada taimakon ola ba, toilet ya shiga yana shiga abinda ya faru jiya ya fara dawo masa kamar yanzu, murmushi yayi ya ce, "fatuha baki ji" sannan ya qara jan tsoki yana mamaki yarda ya rike sunan ta ya dauro alwala tare da yin wanka ya fito ko da ya fito jalabiya white yasa ya tada sallah yana gamawa ya koma ya kwanta saboda har yanzu jikin nashi yana jin shi wani irin.
Bud'e handle din kofa tayi ta fito direct part d'in sadiq ta wuce kai tsaye, bedroom ta shige kallo daya tayi ma d'aki ta hango ola kwance yana ta share bacci har da munshari saboda dad'i, dariya ta so ta kubuce mata ta guntse dariyar kallon bed tayi sadiq na kwance rungume da jidda murmushi tayi a hankali ta qarasa tare da leka fuskar sadiq ta ga dai bacci yake cikin dubara ta shiga janye jidda daga jikin sa, hannu ta ya kama a tunanin shi jidda ce zaro ido waje fatuha tayi tare da fara matsar kwalla a tunanin ta tashi yayi jin baiyi magana bane ya sata lumshe ido a hankali ta zare hannu ta ta d'au jidda suka fita, direct bathroom ta dire jidda ta fara yi mata wanka , washe da baki jidda ta ce, "Anuty good morning"
"ta6 ke kika san wannan" dariya jidda tayi ta ce, "ina kwana fa nake nufi Anuty"
"aiyo aini ban sani ba, a ina ake koya maki wannan abun wai? washe baki jidda tayi ta ce "A school "
"aiyo wai makarantar da zaki yanzu? daga mata kai jidda tayi Alamar eh, murmushi fatuha tayi tare da daukar jidda suka fito bedroom ta dire ta saman bed tare da janyo lotion tana shafa mata tana cewa, "kai Amma gaskiya yarannan nada dadi jidda zaki rinqa koya min ko? murmushi Jidda tayi ta ce, "Anuty kije daddy ya fara koya maki nima ai shi ya fara koya min" ta ida zancan tana washe hakura, fatuha zaro ido tayi ta ce, "ta6 lallai yarinya har yanzu baki san bak'in halin ubanki ba Qur'an..! wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta, washe baki fatuha tayi ta ce, "ah ni nafi son ki koyamin kinji kinga daddy aiki yake zuwa ko" daga kai jidda tayi tare da cewa, "toh Anuty zan koya maki" murmushi fatuha tayi tare da zurawa jidda uniform suka fito dining area lokacin su baba jummai sun gama jera komai bud'e kololin ta fara marfesun kaji ne da soyanyan chips da egg da tea, murmushi fatuha tayi dan tunda ta zo birni ba abinda keyi mata dadi kamar chips shiyasa duk sanda akayi sakin tunbi take taci sosai zuba ma jidda tayi a plate tare da jamata kujera ta zauna, zata fara feeding nata kenan sai ga su Mom sun iso, gaishe su tayi cikin ladabi suka amsa plate ta jawo ta fara saving nasu Mom sai murmushi take ita dai fatuha ta mata ko dan abin dariyar ta, tana cikin saving nasu sai ga sadiq ya qaraso dining yana tafiya a hankali yana dingishi, a hankali fatuha ta kalli qafar wata irin dariya ce ta zo mata saboda yadda yake harba kafar kamar tsangal gumtse dariyar tayi ta cigaba da abinda take shiko sai aika mata mugun kallo yake, cikin nutsuwa ya qaraso wajan Mom tare da yi mata peck a goshi ita da Abba, abba murmushi yayi tare da shafa sumar shi ya ce, "baby ya jiki? shagwabe fuska yayi ya ce, "Abba da sauki"
"good amma dai gaskiya yau baza kaje aiki ba ko? d'an 6ata fuska yayi ya ce, "zani Abba"
"gaskiya baby bazaka office yau ba ka bari zuwa gobe ka warware sosai"
"Abba..!
"shhh..! kawai ka hakura kaji" ya ida zancan yana shafa gefan fuskar sadiq fatuha ko Sakin baki tayi da hanci, ta ce "Ohni sangami duk wani shaqiyanci ya iya, yo in banda iskanci qatoto da shi sai zuba shagwaba yake sai ka ce Jidda, kai kwarankwatsi mai kyau dan bariki ne" duk wannan maganar tana yinta ne a zuciyarta kallon da sadiq ya wurga mata ne yasa ta dawowa hankalin ta ba shiri Jidda ya jawo jikinsa ya ce, "yau daddy ne zaiyi feeding angel so bana buqatar ganin ki a nan" tare da warce spoon din hannu fatuha, Mom ce ta bala masa harara 6ata fuska yayi kamar qaramin yaro ya cigaba da feeding din jidda tana masa surutu, fatuha ko qoqari tashi tayi Mom ta ce,"fatuha aike sauki kika samu zauna ki ci abincin ki kan lokaci" murmushi tayi tare da kad'a kai ta zauna ta zuba