Showing 36001 words to 39000 words out of 105783 words

Chapter 13 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

712

tsuru-tsuru tayi tana kallonsa cike  da  tsoro  da  fargaba ga wani irin zazza6i da take ji, lumshe ido tayi ta juya masa baya wayar shi ya ciro dake aljihunshi ya  kira  doctor bugu daya biyu Dr yakub ya dauka sannan ya sheda masa yana buqatar ganin shi, OK ya ce masa tare katse wayar sannan ya kalli inda fatuha take kwance hata gashin kanta jiqe yake, haka  nan  ya  tsinci  kansa  da  tausayinta miqewa  yayi  tsaye  hannuwansa na  zube  cikin  aljihu  yana  karewa  fatu  kallo a hankali ya kai hannu ya d'auki fatuha ita ko sai matsar kwalla take tana  mutsu-mutsu  a jikinsa  cike  da  tsoro tana bashi hakuri banza yayi da ita bai dire ta ko ina ba sai bedroom dinta, saman bed ya direta sannan ya dau ko hand dryer daya ke anfani da ita  fatu  nata  binsa  da  idanuta har  ya jona  hand dryer  jikin soket ya  tako  gabanta gashin  kanta  ya  kama ya busar mata da kanta fatuha ko sai bin shi take da ido AC dakin ya rage ma gudu tare da rufe ta da blanket har  lokacin  fatu  da  ido  take  binsa  tamkar  mutum-mutumi ya koma gefe ya zauna fatuha ko lumshe ido tayi kamar mai bacci.

   Ba'a fi 50 minutes ba sai ga Dr yakub sadiq ne ya masa iso har bedroom dinta, dudubata yayi sannan ya fito da alura da magunguna ya aje a gefe sai da ya gama zuko alura sannan yayi ma fatuha magana, "hajiya ki juya zan maki alura ko dan fever ta sauka" waro ido fatuha tayi ta fara kuka tana  cewa, "dan Allah kayi hakuri wallahi bana san alura" kuka take sosai sadiq ta shiga ba hakuri, banza yayi da ita kamar bai jinta, ohni fatuha yau na shiga 3 ban ta6a tunanin muguntar mai kyau ta kai haka ba duk wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta ,Dr ne ya katse shurun da cewa, "please ki tsaya na maki alura kin ji ba zafi fa kuma ko dan ki samu  sauki masasarar da kike yi kinji" Dr ya ida zancan yana smile fatu  ta  ce, "wallahi bana san alura dan Allah kayi hakuri ka kyale ni" Dr yakub ne ya juyo ya kalli sadiq dake ta latsa wayar shi kamar ba mutun a wajan ya ce, "ka ji mara lafiyar ka bata san alura kuma irin wannan fever sai da alura yake sauka" dago sexy eye's ball's din shi yayi yana qarewa bed din kallo da fatuha take kwance saman bed din cikin isa ya qaraso  ya ce, "fatuha..! shuri tayi kamar bata ji shi  ba sarai yasan tana jinshi, wani sabon rainin ne haka ji yayi dama bai kira Dr din ba ya barta ciwo ya kashe ta inya tashi mamakin  kansa  ma  yake  yarda  ta  isheshi  kallo  yake  koda  yake  yana  yin  komai  ne  saboda  farin  cikin  angel daf da ita ya zo ya zauna tare jawo ta Jikinsa sosai  suke  jin  saukar  numfashin juna  su  da  yarda  zuciyoyin  su  ke bugawa kuka fatu tasa tana cewa, "ni ka kyale ni bana so" banza yayi da ita ya riqe ta gam Dr ya zunkud'a mata alura wani irin kuka ta saki tare da rungume sadiq gam tana kuka  sai da tayi kuka san ran ta sannan ta fara sauke a jiyar zuciya, dan guntun tsaki sadiq ya ja tare da zame ta daga jikinsa fatuha ko yana zame ta ta koma ta kwanta saman bed tana sauke ajiyar zuciya, sannu Dr yakub ya mata sannan ya dau briefcase din shi tare da yima sadiq bayanin yadda zata sha magani godiya ya mashi sannan ya rako shi har bakin kofa yashiga motarsa ya tafi, shi kuma ya koma bedroom din fatuha  ja mata blanket ganin  tayi  baccin  wahala sannan ya fita ita kuma bacci ya sure ta.

   Bangaran su Mom ko sun isa family house lafiya, direct part din Ammi suka fara shiga cikin fara'a ta tarbe su da jin dadi asiya mai aiki ta kira ta kawo masu fura mai sanyi da kayan motsa baki, aiko sakin jiki sukayi suka sha dan Ammi ba irin iyayan mijin nan ba ce mai takurawa surukanta ba  daukar su take kamar ya'ya ta Jidda ta janyo tana mata wasa ta  ce, "yan'mata baba ina baban naki kwana biyu shuru? murmushi jidda tayi ta ce, "Daddy na nan lafiya lau"
        "to madallah kwana ki nake ji majid na cewa sadiq bai ji dadi ba" Mom ce ta ce, "wallahi ko faduwa yayi a toilet"
         "Allah sarki ai abun ya zo da sauki"
     "masha Allah"
"ai yanzu ya warware sosai da tare zamu zo ma"
     "Ayya..! sun sha hira sosai da Ammi daga nan suka wuce part din Umma lokacin baba bai dade da dawowa daga kasuwa ba, baba jan Abba yayi suka shige part nashi suka dasa sabuwar hira abin ka da yan'uwa haka Umma da Mom suka bude sabon shafi na hira Basma ce ta fito sanye da gown ta zo har parlour ta gaida Mom, tare da kawo masu kayan motsa baki sannan ta ja jidda bedroom nata tana mata wasa tare da tanbayarta ina daddy washe da baki jidda ta ce, "yana lafiya lau"
       "ok good idan kun koma gida ki ce masa anuty Basma na gaisheshi" to jidda tace mata, chocolate ta dauko a bedside drawer taba jidda sannan ta cigaba da assignment din ta da datake yi sun dade sosai dan kusan a can su kayi dinner sai kusan 9:00pm sannan suka fito, sai da Abba ya qara leqawa part din Ammi ya gaishe da alhaji sannan suka fito har bakin mota Umma da Baba da Basma suka rako su sannan suka juya cikin gida.

    Fatuha kuwa sadiq na lullube ta bacci ya kwashe ta, ba ita ta tashi ba sai da ake kiran sallar isha'i ko da ta tashi zazza6in ya sauka sai dai jikin ta ba qwari, a hankali ta yaye blanket din jikinta ta shige toilet alwala ta dauro bayan ta gabatar da sallah ta koma saman bed ta kwanta.
          sadiq kuwa bashi ya fito daga gym ba sai  gab da magrib wanka yayi ya tafi masallaci bashi ya dawo ba sai bayan sallah isha'i ko da ya shigo gida yaji ba motsin kowa hakan tabatar masa da su Mom basu dawo ba, bedroom din fatuha ya leqa kwance ya hango ta,  jin shigowar shi yasa fatuha qara yin lamo haskyan dakin ya kunna tuni dakin ya gwaraye da haske, a hankali ya qaraso ya leqa fuskar ta tare da cewa, "fatuha..! banza tayi kamar mai bacci tsaki ya ja ya ce "Nasan kina jina ko? ki tashi ki sha magani kona qarasa ki da bindiga.! tunda dai mutuwar kike so" tuni fatuha ta tashi zaune tana zarar ido maganin ya shiga bale mata ya bata sai da ta sha sannan ya miqa mata fresh milk tace ta koshi wani irin kallo ya wurga mata ba arziqi ta kafa kai ta sanye, sannan ya fita daga d'akin yana fita ta ce ah ashe su sangami ana da kirki har da hada ni da madara mai dadi sannan ta ja dan guntun tsaki ta koma ta kwanta.

   Bayan ya fito daga d'akin fatuha  parlour ya dawo ya zauna tare da lumshe idanuwan shi kamar mai bacci cikin sallama su Mom suka shigo wani irin smile yayi tare da tashi zaune, ya qaraso wajan su jidda ce ta rungume shi tana cewa, "daddy I miss you"
      "miss u more angel kin tafi kin bar daddy shi kad'ai a gida" turo baki tayi ta ce "Daddy Anuty nan bata taya ka hira ba ne ba  ko? ta ida zancan tana 6ata fuska
      "eyya my angel Anuty ba lafiya fever take.! moym da zaman ta kenan saman three sitar ta ce, "me ya sameta sadiq ya ce, "Mom fever take dazu na ganta a parlour zaune tana rawar sanyi shine na kira mata Dr yakub"
      "good baby ka kyauta bari na dubata" Abba da ke haurawa upstairs ya ce, "kice  ina mata sannu" to Mom ta ce tare da shiga ita da jidda, ko da suka shiga a lokacin fatuha tayi bacci cikin tausayawa Mom take kallonta domin sakanita da Allah take son yarinyar daga karshe tayi mata Addu'a suka bar dakin.

   yau ko sadiq shi da kanshi ya shirya jidda, sannan su kayi bacci jidda ko sai missing din Anuty fatuha take sadiq ko dadi ya ji komin banza ta saitu.
Written by
Salma mas'ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REAlHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

45_46

Misalin karfe 6:00am na safe fatuha ta tashi Alhamdulillah jikin nata da sauki, a hankali ta sauko d'aga gadonta ta shiga toilet wanka tayi tare da yin alwala, tana fitowa tasa doguwar riga ta shimfid'a daduma domin gabatar da sallah, kasancewar yau juma'a tana gamawa ta cire rigar ta saka wasu riga da wando mai ruwan zumuwa rigar ya tsaya mata har gwiwa, ba qaramin kyau kayan suka mata ba sai suka fito da shape din ta sosai veil din kayan ta dako sai yar hoda data murza sai lipstick ta sama lips din ta, tayi kyau masha Allah direct part din sadiq ta wuce.
a dai-dai bakin kofa ci birki tana zazare idanuwanta har ga Allah yanzu Sadiq ya fara bata tsoro daurewa tayi a hankali ta murda handle din kofar, parlour ba kowa sai sanyi AC da ke tashi da kamshi a hankali ta qarasa kofar bedroom ta murda a hankali ta tura kanta cike da fargaba sadiq ta hango gaban dress mirror, sanye da bathrobe yana goge gashin kansa da sallama ta qaraso bedroom din, ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana jidda dake zaune saman bed itama sanye da bathrobe da alama da ya gama gyara kanshi zai gyarata washe da baki jidda ta ce, "Anuty..! tare da rugawa a guje ta rungume fatu 6ata fuska tayi ta ce "Anuty ashe baki lafiya shine baki fada min ba? ta ida zancan tana 6ata fuska murmushi fatuha tayi ta ce, "Ai yanzu na warke sauke ranki Jidda ta"
"toh shikenan Anuty" sadiq ko harkar gaban shi yake fatuha kuwa sai binshi take da ido a sace tana mamaki hali irin nasa har ta tsinci kanta da zancan zuci, ohni mutun sai shegen kinibibi kamar mace..! dan gutun tsaki fatuha ta ja tare da daukar jidda suka fita.

Bedroom ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta, sannan ta raba mata gashin kanta gida biyu taja hannun ta suka wuce dining area, Mom da Abba na zaune a dining area cikin nutsuwa ta qaraso ita da jidda ta gaishe su cikin ladabi a tare suka amsa tare da yimata ya jikin, washe da baki tace da sauki jidda ta jama kujera ta zauna sannan ta fara saving nata tana cikin saving nata sadiq ya qaraso dining area gaishe da su mom yayi tare da yi masu peck, sannan ya samu kujera ya zauna masha Allah ya sha kyau har ya gaji, kallo daya fatuha ta masa ta kauda kai cikin tsanarsa amma duk da haka sai da ta yaba kyau irin na sadiq har mamaki kyan sadiq ke bata, anya akwai wanda ya fishi kyau kuwa ta jefawa kanta tanbayar, musanman yau da yake sanye da manyan kaya yayi matukar kyau da kwarjini, tunda ta zo gidan yau ce rana ta farko data fara ganin mai kyau da manyan kaya shada ce sky blue yasa tasha dinki da dark blue zare anmasa irin dinkinnan na sarauta sai hula blue mai ratsin dark blue da kafa ma kansa ta zauna d'ansa, hannu ya kai ya d'au cup ya fara hada tea dan shi mutun ne ba mai san yawan cin abinci ba, bayan ya gama hada tea ya fara sha a hankali Mom ce ta kalle sa tare da cewa, "baby karka ce min yau ma tea kadai zaka sha? lagwabe kai yayi ya ce, "eh..!
"haba baby wai me yasa baka san cin abinci ne uhm" Abba da ke gefe ya ce "Sai kace ba soja ba sojoji da aka sani da cin abinci" shagwabe fuska yayi ya cigaba da shan tea din ganin Mom nata magana yasa shi cin chips din kadan fatuha sai da tabatar jidda taci ta koshi sannan ta kyale ta bayan sun kamala cin abincin sadiq ya dau jidda fatuha na biye da su da lunch box har bakin mota, sannan jidda ta mata peck ta shige mota juyowa tayi ta shigo gida da su Abba ta ci karo Mom ta rako shi riqe da briefcase din shi wuce su tayi ta koma dining area chips ta zuba ma kanta a plate da farfesun kifi bata wani ci da yawa ba saboda har yau bakin ta ba dad'i bayan ta kamala ta fara kokarin kwashe kwanikan, Mom ce ta shigo dauke da fara'a a fuskarta ta ce "Haba fatuha ke da baki da lafiya ina ke ina aiki ki? zauna ki hutu" washe baki fatuha tayi tana qoqarin yin magana Mom ta hanata kwalawa rabi'a kira tayi cikin ladabi rabi'a ta qaraso ta d'urkusa har kasa ta gaishe da Mom Mom ta ce, "yawa rabi'a kwanikan nan zaki kwashe sannan yau ki je ki gyara part din sadiq, saboda fatuha bata jin dadi har" cikin zuciyarta rabi'a bata so Mom ta ce ta gyara part din sadiq ba saboda basa wani shan inuwa daya jiki ba qwari ta kwashe kayan dining area din fatuha kuwa daki ta koma tasha magani bata wani dadi ba bacci ya kwasheta.

A cikin school yayi parking din motar shi tare da zagayowa ya budewa jidda murfin mota, ta fito lunch box din ya miqa mata tare da yi mata peck a kumatu ta ce, "daddy am going to miss you"
"I now angel karki damu anjima idan an tashi ni zanzo daukar ki kin ji angel" murmushi tayi tare da yi masa peck ta shige class yana kallon ta har ta shige, shi kuma ya wuce wajan aiki cike da kaunar diyar tashi.

Ba ita ta tashi daga bacci ba sai karfe 11:30pm ita kanta tayi mamakin baccin da tasha, toilet ta shiga tayi wanka ta fito tare da shafe jikin ta da lotion wardrobe ta bude ta ciro atamfa brown mai ratsin black n white atamfar ta hadu riga da skirt dinkin ya mata kyau sosai y'all zauna a jikinta tamkar an aunata qarewa kanta kallo tayi ta cikin dressing mirror, murmushi ta saki tare da cewa, "gaskiya birni tayi dubin yanda na koma kamar ba fatuha inna ba.! duk wannan zancan tana yinshi ne a zuciyarta, murmushi takara yi tana qoqarin kama gashin kanta bud'e kofar da akayi ne yasa ta saurin waigowa a tunanin ta Jidda ce sai taga Hanan washe baki tayi tare da cewa, "Hanan..! cikin fara'a Hanan ta qaraso dakin sanye take da lace sky green mai ratsin black sai veil dinta white ba qaramin kyau tayi ba ta fito yan'matan sak, zama tayi saman bed tare da cire veil din ta ce, "wash na gaji wallahi" dariya fatuha tayi take ce, "wai kin gaji, aiki me kikayi da kika gaji? murmushi Hanan tayi tare da cewa "Kai fatuha karki ce min wannan uban gashin naki ne?" fari da ido fatuha tayi ta ce, "na Hanan ne.! bugu Hanan ta kai mata cikin wasa ta ce, "kai amma fa kin ji dadi" murmushi fatuha tayi ta ce "Ina Jamal da afra?"
"suna parlour tare da grandma nima tanbayar ki nayi sai grandma ke ce min baki ji dadi ba, shine fa na shigo na maki sannu toh ashe har kin warke kin fara make up" ta ida zancan cikin tsokana, dariya fatuha tayi ta ce "Wallahi naji sauki danma Mom bata barni nayi aiki ba"
"ai ta kyauta wallahi"
"amma yau baki je school ba?
"eh exam muke na JSCE shiyasa ban je ba yau bani da paper Jamal kuma fever yake shiyasa," murmushi fatuha tayi take ce, "ni wallahi ina san makarantar nan sai ma na shirya jidda zata tafi sai naji kamar na bita"
"ai karutu akwai dadi akwai wahala kiyi ma Mom magana mana" smile fatuha tayi tare da cewa toh jidda ce ta shigo bedroom din ta fada jikin fatuha murmushi tayi ta ce "Yan makaranta har andawo kenan?" daga mata kai jidda tayi ta "eh Anuty kin ga daddy ya siyo min ice cream da zamu dawo har da chocolate da yawa kuma fa naba daddy naki ya aje mana" murmushi fatuha tayi ta ce toh a zuciyarta kuwa cewa tayi ta6 wannan daddy naki ai sai ke Hanan ce ta katse mata tunani da cewa bari naje wajan uncle nima na amshi nawa tana fadin tana qoqarin daukar veil din ta zata fita ta ce, "fatuha idan kin gama shirya jidda ki same ni a parlour muyi lunch" toh tace mata bawai dan tasan me Hanan ke nufi da kalmarta na qarshe ba daukar jidda tayi ta shige da ita bathroom ta wanke ta tas sannan suka fito ta shafeta da mai tare da samata gwon pink mai qaramin hannu sai gashinta da ta gyara mata tayi kyau sosai masha Allah.

Direct parlour suka fito Anuty bilki na saman two sitar zaune, Mom na zaune saman three sitar suna kallo gaishe su tayi Mom tayi mata ya jiki ita da Anuty bilki da gudu jidda ta koma wajan Jamal da ke zaune saman daya daga cikin kujerin dining area itama ta zauna cikin fara'a fatuha ta qaraso ta fara saving din su, Hanan dake saukowa daga upstairs tana zunburo baki gaba cikin bacin rai ta qaraso dining area din fatuha ta kalle ta ta ce, "Lafiya naga kamar an bata maki rai ? dan guntun tsaki taja ta ce, "wallahi uncle ne ya bata min rai shi kullun cikin bakin rai maganar arziqi ba taba hada ku dashi" murmushi fatuha tayi ta ce "Yi hakuri kinji zauna mu ci abincin mu idan mungama mu fita farfajiya shan iska"
"yauwa tawa..! abinci suka ci cikin nishadi bayan sun gama fatuha da Hanan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login