Showing 21001 words to 24000 words out of 105783 words
haka take gani, Washe baki tayi ta juyo tana kallon baba jummai ta ce... "Baba jummai dama ashe aljanna kike zuwa? Baba jummai dariya tayi ita da driven ta ce.. "a'a fatuha nan ba aljanna bane birni kenan"
"kai amma kwarankwatsi kinyi da kika zo dani dafa tare da fatsima kikaso zuwa ko?
"ke da kikaita kuka baki san zuwa"
"Qur'an yanzu ina san birnin 😃.! ta ida zancan lokacin yayi dai-dai da isowarsu katafarin gate din gidan Alhaji Ibrahim, zanso kuga yanda fatuha ke zarar ido.😂
Dai-dai parking space drive yayi parking baba jummai ta kwaso masu kayan su fatuha dai na maqale da ledar ta, ta gari yayi zafi.
Katafarin parlourn gidan suka shiga, qauyanci wajan fatuha ba'a magana dan ko zama taqiyi saboda tayals sai da baba jummai tayi da gaske sannan ta zauna saman carpet tana ta zara ido.
Mom ce ke saukowa daga upstairs cikin murmushi ta ce, "ah sannu da zuwa baba jummai" tare da qarasowa parlour da zama saman two star tana facing d'in su baba jummai d'in ta ce, "ya hanya? tana murmushi.
"Alhamdulillah," baba jummai ta ce, "oh tare da yarinyar kuka zo kenan gaskiya naji dadi" fatuha dake ra6e jikin baba jummai ta gaida Mom cikin girmamawa, baba jummai ce ta washe baki ta ce, "Ai diyar qanina ce jauro"
"a'a ki ce min yar tashi ta yi girman haka"
"aiko dai hajiya" Sunyi hira sama-sama inda fatuha ke ra6e jikin baba junmai tana qarewa gidan kallo tare da santinsa.
Lafiyayan abinci Mom ta basu shinkafa da miyar kaji wadda taji coslow kauyanci ko wajan fatuha ba'a cewa komai, saboda bata ta6a cin irin abinci ba dan haka ta saki tinbi ta ci har da sid'e kwano da qari, Baba jummai dadi taji dan taga fatuha ta saki jikinta.
Bayan sun gama cin abinci Mom ta kai fatuha d'akin jidda ta gwada mata toilet da duk yadda zatayi anfani da komai na toilet d'in tare da ciro mata uniform din yan'aiki farar Riga da skirt dai-dai gwiwa.
ba laifi fatuha duk abinda Mom ta gwada mata haka tayi..
wanka sosai tayi ta dirje jikinta tare da wanke kanta da shafo, masha Allah gashin fatuha har gadan baya sai dai rashin kulla da shine yasa duk ya cure gu d'aya amma hakan bazai hanaka ganin kyan gashin ba,d'aure da towel ta fito, Mom na zaune saman sofa tana jiran fitowar ta, koda ta d'ago kanta Mom d'in, tayaba da kyau irin na fatuha, Hakan yasata yin murmushi ita ko saitahau sunne kai Mom ta katse ta da cewa, "Ah har kin fito? D'aga mata kai tayi alamar Eh , uniform din Mom ta d'auka ta bata ta ce, "ga wannan kayan kullun su zaki rinqa sawa akwai su da yawa cikin wardrobe ranar Friday ne kadai zaki sa kayan gida suma akwai su cikin wardrobe, na ki kuma anfidda su waje sannan in kayan sunyi dati ki aje su akwai mai wanki zai wanke maki su ya goge" Washe da baki fatuha ta ce, "toh.!
Mom har takai bakin kofa ta dawo tare da cewa, "gobe ki shirya za'a kaiki wankin kai" to tace tare da yima mata godiya Mom na fita ta shafe jikin ta da mai tare janyo kayan da Mom d'in ta aje mata a saman gado farar rigar ta fara janyowa ta saka amma sai da tasha wuya sannan ta iya balle ma6allin rigar, dai-dai gwiwa rigar ta tsaya mata kallon rigar fatu tayi ta furta a fili "Kwarankwatsi gidan ga gidan yan'iska ne yo jifa yadda rigar ta min" skirt din ta janyo ta sa tana sawa taga ya tsaya a gwiwa shima ta ce, "kut amma Qur'an mutanan sun rainani yo in ban da iskanci haka zanbi gari qafafu bude ta6 bilahilazi ban fita haka" guri ta samu tayi zamanta tana ta kunfar baki tare da jero Allah ya isa.
Mom dake zaune parlour jin fatuha shuru bata fito ba yasa ta leqo dakin zaune ta same ta har bacci ya fara neman d'auketa saboda gajiyar tafiya, ta6ata tayi tare da cewa "Fatuha.! Nanta ware manyan idanunta Mom tasakar mata murmushi take ce, "hala kin kasa sa kayan tashi kiga yadda ake sawa" nan Mom ta shiga gwada mata masha Allah kayan sun mata kyau duk da fatuha tsine wa kayan take a zuciyar tare da jin haushi kayan.
Bayan Mom ta gama gwada mata ta bata d'ankwali ta rufe kanta ruf kamar wadda tayi acuci yadda kan ya gwada, sannan ta ja ta suka je parlour suka zaune saboda Sadiq sun fita da jidda shan ice cream.
Bayan sun gama shan ice cream suka biya shoprite ya siya wa jidda new Teddy's masu kyau da kayan wasa jidda ko sai murna take a gajiye suka dawo gida, Sadiq na d'auke da jidda a hannusa yana mata cakulkuli tana dariya *ola* na bayan su riqe da kaya cikin sallama suka shigo, Mom na zaune tana kallo fatuha na gefan ta a takure, a ahankali Sadiq ya qaraso jidda na maqale a jikin sa ya kai ma Mom peck a kumatu, Mom ce ta murmusa ta ce, "baby har kun dawo?
"yes Mom" sweet voice din Sadiq ne ya doki dodan kunnan fatuha ta waigo baki bud'e tana qare masa kallo shi da jidda sakin baki tayi a zuciyarta ta ce, "dama ashe ina da raban ganin yan makka kai baba jummai kwarankwatsi kin dubamin, duk wannan zancan da take idanun ta na kan su jidda, dagowar da Sadiq zaiyi su kayi 4 eye's da Fatu harara ya wurga mata saboda yarda ta tsare sa da idanu ya kauda kansa ya ce, "wannan wacece bata iya gaisuwa ba sai kallon" murmushi Mom tayi ta ce "wadda zata dinga kulla da jidda ce diyar qanin baba jummai ce" kallon fatuhan yayi wadda ke kallon su bata dauke ido ba baki sake harara ya qara banka mata sannan fatuha ta ankara ashe harara yake aika mata aiko itama ta fakaici idon Mom ta banka masa harara har da murgud'a masa baki, sakin baki baki captain sadiq yayi yana mamakin wannan wacce mara kunyar mai aiki ce Mom ta samu wadda bata da kunya haka har lokacin tana banka masa harara a fusace ya tashi ya ce, "keeeee!! Ni sa'an kine..! Kike kallo na haka? Mom da ke zaune ta ce "Sadiq lafiya yarinya na zaman zamanta ka fara yi mata bala'i ka bari mana ta kwana biyu sannan ka nuna mata bakin halin naka, wai me yasa kake haka ne baby? fad'a Mom ta masa sosai cikin zafi rai ya bar parlour sannan ta shiga ba fatuha hakuri washe da baki ta ce "ba komai" Mom ta gwada mata jidda ba qaramin dad'i fatuha taji ba zata kulla da balarabiya bayan Mom ta gama yi mata bayani sannan taqara mata da batun zata riqa gyara part din baban jidda sosai fatuha taji dadin hakan.
a cikin zuciyar ta kuwa cewa ta ke Qur'an daba balarabiya ba ce da wallahi bani kula da Ita, shi kuma wancan balaraban ni zaiwa iskaci wai dan yana da kyau. Qur'an gyara mai zama zanyi bilahilazi duk wannan maganar tana yin tane a cikin zuciyar ta.
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
https//,mobile.facebook. com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&_yn_=H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
29_30
Mom ce ta haura upstairs ta bar jidda da fatuha zaune a parlour ,a hankali fatuha ta matso kusa da jidda washe da baki tace "Ya sunan ki?" smile jidda tayi tare da fad'a mata sunan ta, sun dad'e a parlour zaune sannan jidda ta ja fatuha suka koma bedroom d'in jidda, jidda ta fara kwaso wa fatuha kayan wasa, washe da baki fatuha ta amshi teddy tana cewa, "kai Al Qur'an birni dad'i garai yanzu saboda Allah ji wanga halita duk wasa ake da ita kai jama'a" jidda ce ta katse mata zance da cewa, "Anuty garin ku ba wannan teddy ne? nima daddy ke siyo min" dariya fatuha ta fashe da ita ke kekika san wani Daddy mtsss, kuma me Anuty da tedil (teddy)? jidda dariya tayi ta ce, "Aunty ba sunan shi tedil ba sunan shi teddy, Anuty kuma idan mutun ya girme kane sai ka dinga ce masa Anuty"
"aiyo ai mu a kauyen mu yaya ake cewa ko gwaggo, Ah wanga suna Qur'an dad'i garai haka birni ya ke" jidda dai washe baki take tayi ta samu yar'uwa kamar ta me shegen surutu.
Haka suka rinqa zuba hira tare da wasa ita dai fatuha, zuciyar ta fes dan a ganin ta ta samu gurin zama kiran sallah magrib ne yasa suka tashi, fatuha tayi alwala tare da jidda sannan suka fito dan gabatar da sallah.
Bayan sun gama sallah suka dawo parlour, parlour ba kowa sai baba jummai da ke ta jera abinci ita da rabi'a washe da baki fatuha ta gaida baba jummai da rabi'a, baba jummai ce tac e, "Ah fatuha anware kenan?" dariya kawai tayi "toh ga abinci nan idan kuna jin yunwa ku zo ku ci ki tabatar kin ba jidda ta ci ta koshi" inji baba jummai, "toh.! kawai fatuha ta ce mata sannan baba jummai da rabi'a suka shiga kitchen.
Kamar jira take su shige tayi tsale ta haye kujera dining area dakyar ta iya bud'e kulolin farfesun yan'ciki ne sai dafafan doya da miyar kifi, tunkan ta fara ci miyan bakinta ya tsinkewa, zubawa ta fara yi sai da kwanan ya kai har baki sannan ta tsayar da zubawa, jidda ko sai zaro ido take tana mamaki irin ci na sabuwar Aunty ta,
lol.
Washe baki tayi ta ce, "Yauwa jidda sauko muci dan Qur'an ban iya ci a saman wannan abin," haka ko akayi suka sauko qasa suka fara ci, fatuha na ci tana zaro ido saboda dadi kuma ba wai qaramar loma take ba haka zata dauko doya biyo ta turawa kanta ta kuma turawa jidda.
Zaune yake saman sofa da alama daga wanka ya fito, shafe jikinsa yayi da lotion mai kamshi, yana gamawa ya feshe jikinsa da turare mai sanyi dad'i, wardrobe ya bud'e ya ciru 3quarte black sai fara t-shirt hannu rigar dai-dai tamatsa ba qaramin kyau yayi ba bodybuilding nasa yafi gwanin ban sha'awa da birgewa gashin nan nashi ya kwanta abin sha'awa luf-luf, ahankali ya kama handle d'in kofar part nashi ya fito.
Cikin natsuwa yake sakowa daga upstairs, sanye yake da bakin Sweet yayi masifar yi masa kyau, fatuha da jidda na zaune a k'asa ga plate a gabansu sai loma fatuha ke tura wa jidda, dan ita har ta koshi kuma da hannu take bata abincin, a fusace sadiq ya qaraso tare da dakawa fatuha tsawa "Keeee.! Are you mad? you are very stupid" futaha ko ware ido tayi washe da baki ta kalle shi tace, "Ta6 kai ka san wannan gwalangwatsin Qur'an" sannan ta cigaba ta d'irkawa jidda doya jidda ko sai amsa take hankali kwance, lumshe ido sadiq yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi daka mata wata tsawar yayi ya ce, "Dan ubanki baki jin nane? uban waye yace kiyi feeding angel da hannu ba spoon ne eeeh?" Turo baki gaba fatuha tayi ta ce, "yo ni ban san inda fida (feeding) take ba ashe ba'a yaye taba Qur'an ban sani ba" sannan fatuha ta ce da jidda "shine kika saki tinbi ina ta dirka maki abinci,to ta yaye kanta sai ka zubar da fida(feeding)lol.
Wani irin baqin cikine ya turniqe sadiq ya qara wurga mata harara , aiko itama ta rama tana cewa, "yo a kan me mutun tunda na zo gidan su sai aika min harara yake, ba dan nayima Hajiya Alkawari zan zauna da ita iya wuya ba, da sai nace banyin aikin ko ana dole ne, kama gode wa Allah saboda Kuna kama da larabawane shiyasa na tsaya da bilahilazi da tuni nayi tafiya ta aha" tare da gyara tsayuwar ta, sadiq ko baki ya saki yana mamaki irin wannan iskancin da kauyanci tare da tsantsar rashin kunya da rashin tarbiya irin na fatu wanda ko girman sa bata gani, tsawa ya kuma daka ma fatuha wadda tasa yan'hancita katsawa "dan ubanki ni sa'an kine ni eeeeeh? ido fatuha ta qara zarowa, sannan ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi duk sanda na qara magana wannan dan banzan bakin naki ya maida min sai na fasa shi" ya qara wurga mata harara sannan ya sa hannu zai d'auki jidda, ihu fatuha ta saka hakan yasa sadiq juyowa yana mata kallon wulaqanci, "Qur'an ba inda zaka da balarabiyan nan kwarankwatsi, ko na fada ma hajiya tunda ita ta bani ita" dariya abin ya kusa ba ma sadiq amma sai ya d'aure ya wurga mata harara, a rayuwarsa bai ta6a ganin mara kunya irinta ba yar kauye wadda bata jin ko tsoron sa.
Mom dake bedroom taji ihu fatuha hakan yasa ta fito da sauri, ganin sadiq d'auke da jidda fatu na gefe tana ihu yasa mom qarasowa, harara ta aikawa sadiq tare da cewa, "Lafiya fatuha? me kuma ya miki?" turo baki tayi ta ce, "Yanzu saboda Allah hajiya ba ke kika bani wannan balarabiyar ba, na kulla da ita, to shine wai daga yaga ina bata abinci ya hau zagina har da ce min wai fida take sha" hajiya ko dariya abin ya bata saboda ta gano abinda fatuha take nufi, sannan fatuha ta ce, "To shine hajiya yasa hannu zai d'auke min ita Qur'an ban yadda ya maido min abuta" murmusawa hajiya tayi tana konshe dariyarta ta ce "Yi hakuri fatuha ai baban ta ne shiyasa"
"aiyo toh shine hajiya bai iya fada min dan girman Allah, ki ce ya ban yarinyar dan Qur'an sonta nake" tare da matse kwalla, Mom ko dariya abin ke bata sadiq ko mamaki abin ke ba shi yau shida d'iyar sa za'a masa qarfin hali, Mom ta ce, "Toh shikenan sadiq bani jidda idan ta mata wanka sai ta kawo ma ita, ai shikenan anraba rigama ko fatuha? sadiq 6ata fuska yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi.
Haka sadiq ya miqa wa Mom jidda tare da haurawa sama, sannan ya d'au alwashin sai ya gyarawa wannan yarinyar zama dan yaga alamar da rashin kunya tazo.
Fatuha ko washe da baki ta amshi jidda, jidda ko sai raba ido take gashi cikin ta ya cika dam kamar yayi magana......
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
https//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial&_yn_=H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITRESFORUM.com
*rip rip this page is for you my lovely one so enjoy the page this na for u no be so*😉
31_32
Washe da baki fatuha ta amshi jidda ta wuce da ita bedroom ta cire mata kaya, direct toilet ta shige da ita sai da ta wanke jidda tas sannan suka fito.
Wash Fatu ta ce, tare da cewa, "Ah bilahilazi birni tayi yanzu dubi sau biyu ina sab'e ki, ko gajiya bakiyi da wanka kamar kwad'o" jidda ce ta washe baki ta ce "Anuty daddy baya son dati shiyasa, always yake min wanka yayi ma kansa"
"uhm..! ta6e baki fatu tayi ta ce, "yo ke ki kasan wannan," washe baki jidda ta kuma yi ta ce, "baba na fa nake nufi Anuty"
"aiyo wai wannan baban naki ai dole yake wanka daga ganin shi ya cika tsirfa"
"daddy nawa"
"uhm shi fa, ke ni wani mai ake shafa maki idan anmaki wanka" smile jidda tayi ta d'auko mata lotion d'in ta mai kamshi fatuha ta amsa tana jujuyawa ta ce, "ah'ah wanga farin mai haka fa? yo ai wannan kamar turare ne" jidda ce ta fashe da dariya ta ce, "Anuty ba turare bane maine ga turare na chan saman dirss mirror wanda daddy ya siyo min a uk,"
"tir qashi me kuma uk? washe da baki jidda ta ce, "wata qasa ce haka"
"a'a ha shi baban naki har shawagi yake qasa-qasa ta6 kinga matso na shafe ki da mannan kar yaji shiru ya zo ya min tijara dan na lura dan ta kife ne baban naki" haka ko ta shafe jikin jidda da lotion tare da anyana man a ranta ita ma ta gama shafa basilin dan ita yanzu ta zama yar birni.
Sai da ta gama shafe jidda da mai tsaf sannan jidda ta gwada mata inda night dress din ta suke kar ku ga abu komai fatuha ta gani sai ta mai sharhi, bayan ta gama shirya ta tsaf, sannan ta d'auke ta dan kai ta d'akin baban nata wanda tayi ma laqabi da sangami.
Direct part din Sadiq suka wuce a hankali ta murd'a handle d'in kofar ta shiga, jidda tana ta zuba mata surutu, tana shiga parlour ta saki baki da hanci bata san sanda ta dire jidda ba a qasa wani irin sanyi dad'i ne da kamshi ya doki hanci ta kasancewa sadiq mutun ne mai san sanyi da kamshi, shiyasa part d'in shi yafi na kowa sanyi a gidan, washe baki tayi tana qarewa parlour kallo saboda iya kar had'uwa parlour ya hadu.
Jidda ko bedroom ta shige da gudu lokaci sadiq ya fito daga wanka, sanye yake da bathrobe hannu shi riqe da towel, yana goge gashin kan shi jidda ta ruga ta rungume sa ciki