Showing 24001 words to 27000 words out of 105783 words

Chapter 9 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

706

da  farin  ciki  ta  ce, "daddy..! wani irin murmushi ya saki tare da shagwabe fuska ya ce, "uhm ni fushi nake da angel" tare da d'aukar ta ya zaunar da ita saman bed ya cigaba  da  cewa, "shine saboda kinyi new Anuty kika manta daddy ko angel? shagwabe fuska ita ma tayi tare da d'aura hannu ta saman cheeks d'in sadiq ta ce, "sorry daddy" ta marairaice kamar za tayi kuka, dariya yayi tare da fara yi mata cakulkuli, dariyar su  jidda  ta ankarar da fatuha washe da baki ta nufi kofar bedroom ta bud'e a hankali ta shige, zaro ido tayi  waje tana kallan d'akin baki bud'e tana  cewa, "kai Amma wanga gida ya had'u kwarankwatsi yanzu gobe ni zan gyara wanga gurin," baki ta qara washe wa duk wannan maganar tana yin tane cikin zuciyarta, sadiq dake ma jidda cakulkuli tana dariya jin kamar an bud'e daki  an shigo yasasa da gowa a hankali,   ya sauke sexy eye's ball's din shi kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata ita dinma shi take kallo tana aiyana irin kyau na sadiq a zuciyarta "ta6 amma dai sangami ba qaramin kyakyawa bane Qur'an" washe baki ta kuma yi  ta ce "Amma fa sai bakin rai kamar fir'auna tir da wannan hali wallahi ga kyau ga bakar zuciya, ko da yake na kusa maganin shi ai," daka mata tsawar da sadiq yayi ne yasa ta dawowa daga dogon tunanin da take tayi wiqi-wiqi da ido, "you are very stupid ina maki magana kin yi shiru ehhh ? are u deaf or what" tsawar da sadiq ya daka wa fatuha har wani fitsari taji ya taho mata gadan-gadan ganin yana nufo ta yasa ta bud'e kofar tafita daga d'akin da gudu sai da taje dai-dai kofar parlour ta bud'e baki yadda zai jita ta ce, "Allah ya isa mugu kawai" sannan ta bud'e kofar ta ida fita a guje sadiq dake bakin kofar bedroom yana jin ta lumshe ido yayi yana jin wani irin tsanar fatuha na ratsashi da mamakin rashin kunyar ta ,a hankali ya ja jikinsa ya koma saman bed lokacin jidda har tayi bacci shima kwantawa yayi tare da kara masu gudun AC  ya ja masu blanket.

        Tana isa d'aki ta kulle da makuli gudun kar sangami ya shigo wato sadiq, toilet ta shige da gudu tayi fitsarin data matse saboda tsabar tsawar da sadiq ya daka mata shi ya haifar mata da fitsarin dole, tsoki ta ja tare da cire kayan jikin ta tayi wanka sai da ta wanke jikin ta tas sannan ta  d'auki k'aramin  towel ta daura ta fito, rigar baccin da Mom ta gwada mata ta ciro ta sa duguwar riga ce pink mai manyan follows milk rigar ta wuce gwiwa ba qaramin kyau tayi ma fatuha ba, ita kanta sai da ta yaba kyan rigar sannan ta kwanta saman bed tare da janyo blanket ta lullu6e ko 2 minutes ba tayi ba bacci ya sureta.

           ASUBA TA GARI
       
       tsaye yake gaban dress mirror yana shiri cikin uniform nashi kasancewa yau Monday ba qaramin kyau yayi ba, kofar bedroom ya kalla tare da jan tsaki sannan ya kalli bed jidda na bacci.

      Bangaran  Fatuha ko yau bacci har da munshari ba ita ta tashi ba sai 6:00am, cikin sauri ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan tayi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba  tayi sauri ta zura uniform din ta, kasancewa Mom ta fada mata jidda na zuwa school shiyasa take shirin cikin sauri cikin sauri ta nufi part d'in sadiq dai-dai bakin kofa tayi tsaye gaban ta na dukan uku-uku saboda ta tuna artabun da suka sha da sangami jiya kawai shahada tayi tare da qundun bala ta bud'e kofar ta shiga tare da yin sallama,  ba kowa parlour hakan yasa ta murd'a handle d'in kofar bedroom sadiq ta hango tsaye gaban dress mirror a hankali  ya dago sexy eye's ball's din shi wani irin kallo ya wurga mata tare da jan tsoki, cikin  tsawa ya ce "Yanzu ne time din da ya kamata ki shigo eeh?  baki san tana zuwa school bane, koko rashin sanin muhinmanci ilimi yasa kika zauna baki zo ba eeh? nuna ta yayi da yatsa  ya ce, "as from to day karki qara kai wannan time din baki zo ba stupid girl kawai" duk da bata san Kalmar da ya fadi aqarshe ba amma jikin ta ya bata zagin ta yayi sai da ta fakaici idon sa sannan ta bala masa harara tare da d'aukar jidda daga saman bed zata fita da ita har ta kai bakin qofa, ya kara daka mata tsawa ya ce "Kin makarar da ita yanzu Kuma ina zaki kaita? oya wuce ki mata wanka a bathroom d'ina" wiqi-wiqi da ido fatuha tayi dan ita bata san me ye bathroom ba, wata uwar tsawa ya kuma daka mata y'all ce, "oh waike wace irin yarinya ce ehh ki kai ta ban d'aki na kiyi mata wankan yar qauye kawai mtss, saura kuma inkin je kinmin kauyan ci" jiki ba kwari fatuha ta shiga toilet din ba laifi dan kauyanci da tayi kadan ne sannan tayi ma jidda wankan, tana mata tana zuba mata surutu d'auke da ita ta fito sannan ta zauna da ita saman bed sadiq na zaune saman sofa yana kallonsu  shafe jikin jidda tayi da mai sannan ta dau uniform din jidda zata sa mata nan fa kar ku ga zare ido dan ta rasa ta inda zata samata rigar saboda gown ce irin mai kamar biri da wando d'inan tayi tsuru-tsuru, sadiq jan tsaki yayi tare da fisge rigar ya shiga sama jidda fatuha duk tana kallon yadda ya ke samata sai da ya gama shirya jidda sannan ya mata peck ta  ce, "daddy good morning"
      "morning too angel how was ur night,?
    "cool daddy"
   "good" fatuha ko sakin baki  tayi tana kallon su.

    Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan sadiq ya d'au briefcase din sa, fatuha kuma ta d'auki jidda suka sauko downstairs Mom da Abba na zaune a dining area har sun fara breakfast cikin ladabi sadiq ya gaishe su haka ma fatuha da jidda Mom ce ta kalli fatuha washe da baki ta ce "Ya kwanan baqunta?" murmushi fatuha tayi tare da jama jidda kujera ta zauna cikin natsuwa ta shiga saving din jidda abinci,  da ta gama sai ta zauna shima cikin dari-dari  sannan ta sa hannu cikin plate d'in wata irin tsawa sadiq ya daka mata wadda tasa fatuha fara matsar kwalla, cikin kakausar murya yafara cewa "Wai bana ce maki ki daina feeding din angel da hannu ki bane eeh" Mom ce ta kalle shi tare da wurgamasa harara take ce, "baby wai me yasa ka ke haka ne eeh" fada ta masa sosai sannan shima Abba ya dasa da cewa,  "Kai haka ake a rayuwa? kai kullun cikin zafin rai sadiq wai me yasa baza gyara halin ka bane eh baby? kullun ciki  rigima  da  masu  aiki" shiru sadiq yayi tare da aikawa fatuha harara ita ko tayi kamar bata gani ba sai ma gwalo da ta aika masa cikin nutsuwa suka gama breakfast.

     Briefcase din sa sadiq ya d'auka fatuha na d'auke da jidda suka fito harabar gidan, haka fatuha ta rinqa zare ido tana qarewa yaran sadiq kallo *ola* ne ya qaraso cikin sauri tare da amsar briefcase din sadiq ya kai masa mota fatuha na biye ta shi suna zuwa gaban mota fatuha ta aje jidda cikin mota , zata juya sadiq ya fisgota ta fado jikinsa, da sauri ya ture ta tare da taka mata qafa da booth din kafar shi ya murzashi sosai, jin za tayi ihu yasa ya matse mata baki da hannun shi da karfi yana kallon ta ido cikin ido ,idanun fatuha sun cika da kwalla taf saboda ita kad'ai tasan azabar da take ji, ture ta yayi tare da nunata da yatsa ya shige motarsa har zai tada yajiyo muryarta tana magana da yake ahankali take magana shiyasa baiji abinda take fadi ba, kwafa yayi ya tada motar suka bar harabar gidan, fatuha ko Allah ya isa ta shiga jeramasa tana  kuka tare da shigewa  gida a guje.
Written by
         Salma mas'ud nadabo

Edit by
      Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_yn_=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

      *👏🏼Godiya ta musanman ga masoya na ❤ina jin dadi addu'ar ku ta fatan alheri😍 nima ina son ku ana mugun tare*🤝🏽

*Wannan shafin nakune masoya na asha karatu lafiya*❤

                        33_34

       Parlour ta qaraso tare da share yar qwallar da ya taru a idonta, Mom na zaune saman three star tana kallo juyowa tayi cikin murmushi tare da kallan fatuha, ita ma fatuha murmushi tayi tare da fara kwashe kayan abinci da ke dining area Mom  ta  ce, "ah fatuha da kin bari rabi'a ta zo ta kwashe" washe baki tayi tare da cewa, "barshi kawai hajiya" Mom murmusawa tayi tare da cewa "Ni ko fatuha da kin daina ce min hajiya nan da yafi! Ki rinqa kira na da sunan da sadiq ke kira na" murmushi fatuha tayi tare da cewa, "toh.! sannan ta kwashe kayan ta kai kitchen Mom kuma ta cigaba da kallon ta tana ayana wasu abubuwa a ranta, tana fituwa direct part d'in sadiq ta wuce ta gyara part d'in sosai,  tana gamawa ta shiga toilet shima toilet d'in sai daya sha wanki dan fatuha gyara tayi bana wasa ba, tana gamawa ta washe baki tare da zama saman sofa tana qarewa d'akin kallo hotan sadiq ta hango manne jikin bango tangameme shi da kausar sunyi murmushi.

     A hankali ta qaraso wajan hotan tare da washe baki tana kallon hotan ta  ce, "ohni ashe sangami na murmushi, ah ji yadda ya washe hakora dan Allah ai da haka yake kullun daya fi kyan gani" murmushi tayi tare da d'aura hannuta saman pic din ta ce, "uhm gaskaya kana da kyau Qur'an" chan kuma sai ta bata fuska tare da cije lips dinta dariya tayi sannan ta ce, "Kwarankwatsi zaka zo ka same ni wallahi ba kasan *wacece fatuha ba yar gidan Baffa jauro*" sannan ta bala wa pic din harara  ta fita daga part din.

   Tana sakowa downstairs ta shige bedroom dita wanka ta kumayi, tana fitowa ta shafe jikin ta da lotion tana shafa lotion din tana washe baki tana  surutu da  cewa, "Qur'an wanga mai sanyi garai ga kamshi, wallahi birni tayi" sai da ta gama shafe jikin da mai tas  sannan ta sa wasu uniform din.
                    
                                **
      Cikin school yayi parking tare da fituwa ya budewa jidda murfin mota smile ya mata me sanyi, sannan ya ciro mata lunch box  dita ya miqa mata, 6ata fuska jidda tayi tare da cewa "Daddy am going to miss u daddy" saman kanta ya  shafa  tare da cewa "Sorry angel soon za'a tashi aiko? sai inna dawo gida sai muje shan ice cream ko my angel" washe baki tayi tare da yi mashi peck sannan ta shige class yana kallonta har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shige mota yatafi.

       Bayan ta gama shirin ta tafito parlour ba kowa sai kamshi da ke tashi na girki, kitchen din ta nufa tare da sallama baba junmai ke girki sai rabi'a na gyara salat murmushi tayi tare da gaishe su washe da baki baba jummai ta amsa tare da cewa "Yar albarka kin zo taya ni aiki ne?" daga kai tayi alamar  Eh, can kuma fatuha ta bata fuska tare da cewa, "baba wai ina kike kwana jiya kika barni ni kad'ai," washe baki baba jummai tayi tare da cewa, "aini fatuha banan nake kwana ba a gida na nake kwana sai da safe na zo" turo baki fatuha tayi ta ce, "gaskiya baba yau binki zanyi,"
     "ah ba za'ayi haka ba ki zauna nan nima ai gidan bacci ke kai ni" baba jummai ta shiga lalla6a fatuha.

    Taya su aiki tashiga yi sosai can baba jummai  ta miqawa fatuha kwano ta d'ebo  man da za'a soya kaji a store, wani irin murmushi tayi tare da shiga store d'in nan ta zuba a kwano tare da qule wani a leda tasa a aljihun skrit d'in ta ta fito, sannan tayi ma baba jummai sallama ta koma parlour  ta cigaba da kallo tanayi tana washe  baki, Mom ce  ke saukowa daga stairs sanye da mayafi da car key a hannu ta kallon gefan da fatuha take tayi tare da cewa "Oh na manta, nayi da ke jiya zan kai ki gyaran kai wallahi na manta gashi yanzu fita zanyi" murmushi fatuha tayi ta ce, "ba komai gobe maje,"
    "toh shikenan idan na  manta ki tuna min please" toh ta ce mata tare da rakota har bakin kofa sannan ta koma parlour ta cigaba da kallo.

Tana kallo har bacci ya kwashe ta a parlour, cikin bacci taji ana sallama tashi tayi tare da ware  idanuwan ta ta sauke su kan  Anuty bilki, ware ido ta kuma yi tana qarewa Anuty bilki kallo dan tabbas tayi mata kama da sadiq sai dai sadiq ya fita kyau sosai qaqaro murmushi tayi bakin ta na rawa ta gaida Anuty bilki, zama tayi tare da amsawa tayi ma fatuha murmushi fatuha  ta  ce, "uhm hajiyar ba ta nan ta fita? murmushi Anuty bilki tayi ta ce, "ai na sani munyi waya yanzu zata dawo ba dad'ewa zatayi ba" fatuha kitchen ta shige ta fada ma baba jummai anyi baquwa lemo ta zuba mata a tray da kayan motsa baki tare da ce mata gata nan zuwa taga baquwar, Anuty bilki ko kayan jikin ta ta rage tare da haurawa upstairs dan ta watsa ruwan , fatuha na zuwa parlour taga ba baquwa sai Afra da ke bacci saman kujera baba jummai ta qwalawa kira ta fitu a rud'e ita ma Anuty bilki da shigar ta bedroom kenan ta sauko, turus baba jummai tayi a parlour tana  cewa, "lafiya fatuha me ya faru" bakin  fatu  na  rawa  ta  ce, "baba wallahi baquwar ce ban gani ba gashi ta bar yar ta a nan" Anuty bilki ce ta qaraso, da  murmushi  a fuskarta baba  jummai ta  ce,  "ah wai Bilkisu ki  ka  gani kike  nufin baquwa ai yar gidan ce amma tayi aure ganin gida tazo yi" murmushi fatuha tayi ta ce, "Aiyo aini ban sani ba shiyasa" itama Anuty bilki dariya tayi sannan ta haura sama tare da ba  fatuha afra ta kula da ita kafin ta fito.

        Misalin karfe 12:00pm jidda ta dawo school ita da Jamal, kasancewar school d'aya suke da yan'yan Anuty bilki cikin murna fatuha ta tare su , kasancewar fatuha me son yara ce, ta ja jidda da Jamal bathroom ta masu wanka suka fita tas, sannan ta sa masu kaya ta zo da su dining area suka ci abinci sannan ta dawo parlour da su suna dan ta6a hira sama-sama duk  cewa  kusan  rabin  hira  duk  shirme  yafi  yawa, can sai ga Hanan ita ma ta dawo daga school washe da baki ta qaraso ta fad'a jikin Anuty bilki take ce, "wash Mom am tied"
        "sorry sweet je kiyi wanka ki canza kaya" fatuha ko washe baki tayi tana qarewa su Hanan kallo, tsakanin Hanan da fatuha kunsan sa'anin ne shiyasa tunda ta shigo fatuha ke kallon ta hakan sai yasa ta tuna da fatsima kwalla taji ta zo mata gaskiya ta san tayi kewar su inna da fatsima d'aki  ta shige tayi kwanciyarta Hanan ce ta shigo ta shige toilet tayi wanka sannan ta fito d'aure da towel suna hada ido da fatuha tayi murmushi take ce, "sannu ki"
         "yauwa" fatuha tace mata, nan Hanan ta fara janta da hira sama-sama, Hanan dama kawa take  so  gashi ta samu aiko nan hira ta barke tsakanin su idan fatuha ta fadi wani abu Hanan tayi dariya sosai har cikin ta ya kule.

    Sai yamma likis su Hanan suka tafi, har bakin mota fatuha ta rako su ita da jidda, kamar kar su tafi saboda fatuha taji dadi hirarsu da Hanan.

     Bayan sun tafi suka koma bedroom din  jidda, taci gaba da zubama fatuha surutu can kamar  an mintsili fatu ta tashi ta koma parlour kad'an-kad'an  ta leqa waje.

     Motar sadiq ce ta kunno kai cikin gidan, wani irin murmushi fatuha tayi tare da yin sauri da haurawa, upstairs part d'in sadiq ta shige direct toilet din shi ta shiga ta fido da man da ta kule a leda ta juye shi qasan toilet d'in sannan ta fito tana dariya tana waigen part din ji tayi ta fada jikin mutun, idanunta ta zaro cikin tsoro da fargaba, tayi  lamo tana jiran aradu, wata irin tsawa sadiq ya daka mata tare da ture ta, ta tafi tagalgal zata fadi ya fisgota tare da qanqance idanu yana kallonta, fatuha kuwa har ta fara matsar kwalla, cikin kakausar murya ya ce "Ke wace irin mahaukaciya ce? ya karasa zancan da murya mai sauti wanda yasa fatuha sakin kuka saboda a iya rayuwar ta ba wanda ya ta6a mata irin wannan ihu haka  ko  tsawa, kuka take sosai tana girgiza mai kai janta ya cigaba dayi har sai da ya kai ta last stairs sannan ya ban kada ta ta fadi qasa tayi zaman yan bori nunata yayi da yatsa tare da cije lips din shi ya d'au briefcase din shi ya shige part nashi fatuha ko kuka tayi san ranta dakyar ta tashi saboda qugun ta ya riqe bedroom ta shiga tare  da shiga toilet dan watsa ruwa ta  gasa  jikin  ta  dan  ba  karamar  buguwa  tayi  ba, bata jima ba sosai ta fito d'aure da towel ta shirya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login