Showing 51001 words to 54000 words out of 105783 words

Chapter 18 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

713

kuka idanuwan ta cike da kwalla taf, shigewa mota sukayi jidda sai daga mata hannu take har sai da motar su ta bar harabar gidan sannan ta shige gida da gudu ta fada saman three sitar ta saki kuka mai tsuma zuciya.


Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com

         
            57_58
    

Godiya ta musanman gare ku mosayan ❤ wannan novel ina jin dadi 💃🏼yadda kuke comments🤓 a kan wannan littafi hakan ya nuna min ana mugun tare 🤝🏽 wannan shafin naku ne.

      Sai da fatuha taci kuka ta gaji sannan ta tashi ta shige kitchen, ta bude fridge ta ciro fruit  ta wanke ta dawo parlour tana ci tana kallo har bacci barawo ya kwashe ta.

    A dai-dai bakin gate ya tsaya tare da yin horn shitu mai gadi ya taso ya bude masa gate, washe da baki ya shiga gaisheda sadiq, sannan sadiq ya sako hancin motar shi cikin gida Jamal dake filin gida yana ball ya saki murmushi ya biyo motar yana murna dai-dai ta parking din motar yayi a parking space tare da bude murfin motar tunkan ya budewa jidda motar, tayi sauri fitowa ta washe ma Jamal baki small dad Jamal yace tare da fadawa jikin sadiq murmushi Sadiq yayi tare da d'aga shi sama yana mashi wasa, dauke da shi ya shigo parlour tare da yin sallama Aunty bilki na saman three sitar zaune Hanan na saman one sitar cikin sallama sadiq yayi washe da baki Aunty bilki ta amsa tare wurga mai harara, sosa keya yayi tare da zama Hanan da ke, zaune a kujera ta gaisheshi a taqaice ya amsa mata tare da kallon Aunty bilki cikin wasa ta ce, dashi "Bari kallo na!, ta fadi tana qara aika masa harara dariya yayi ya ce, "Kai sister tunda na kawo ta ai sai ki huce"
     "ban hucewa abinda sai da na dinga binka sannan ka kawo ta"
   "to ayi min hakuri please" toh tace tana kwallawa baba larai kira ta kawowa sadiq kayan motsa baki dauke da tray ta fito cike da kayan motsa baki ta aje masa a gabansa tare da masa sannu da zuwa sannan ta juya ta koma bakin aikin ta, hira suka dinga zubawa shida  yar uwar shi suna cikin yin hirar Aliyu min jin Aunty bilki ya dawo shima zama yayi aka dasa sabuwar hira da shi, basu suka tashi ba saida suka fara jin kiran sallah magrib, alwala suka dauro sadiq da Aliyu  suka wuce masallaci Kasancewa Aunty bilki hutu take shiyasa ta cigaba da kallon ta.

     Sai da aka gabatar da sallah sannan suka dawo gida lokacin Aunty bilki ta shirya masu abinci a dining area, direct can suka wuce dining area Aunty bilki ta shiga saving nasu lafiyayan jallof  taji naman rago da kosulo cikin jin dadi suka cin abinci tare da taba hira bayan sun kamala cin abinci suka dawo parlour suna hira suna kallon news sai wajan karfe 10:00pm sadiq ya baro gidan Aunty bilki.

     Kiran sallah magrib ne ya tashe ta daga bacci bedroom ta shiga tare da shigewa toilet ta d'auro alwala ta gabatar da sallah bayan ta idar tayi zaune saman daduma tayi tsuru-tsuru wani irin tsoran gida take ji da wani fargaba, duk ji take gidan ya isheta tunanin rayuwar ta a kauye ita da fatsima ta shiga yi  har da yan hawayan ta ji take kamar ta rufe idanuwan ta ta ganta a kauyan wudil gabaki d'aya kewar su inna ta dame ta, jan jiki tayi ta hau saman bed bawai dan tana jin bacci ba blanket taja tayi lamo tana matsar kwalla.

      Bala mai gadi dake gyangyandi qara horn yasasa tashi firgigit wangale gate din yayi, yana washe baki qaraso da motar shi yayi dai-dai saitin bala mai gadi tare da zuge glass din window, murmushi yayi ya ce, "malam bala hala har ka fara bacci? murmushi bala mai gadi yayi ya ce, "Wallahi ko shi ke san dauke ni? saboda yar isakar da ake tana kadawa mai dadi sai kaji bacci na fizgar ka" murmushi Sadiq yayi tare da da ciro kudi idan yake ajewa acikin motar  yan' dubu-dubu ko irgawa baiyi ba ya damkawa bala mai gadi tare jan motar, bala mai gadi jerawa sadiq Albarka ya shiga yi da fatan alheri sannan ya soke kudin shi aljihu yana yin parking ya kashe motar tare da jingi da kujerar motar ya lumshe idanuwan shi tare da ware su murfin motar ya bude, tare da samata key yana shigowa parlour haske ya kunna ya gwaraye parlour kallon parlour yayi ba kowa, kashe haskan yayi  a hankali ya qarasa bakin kofar dakin fatuha har zai murda handle din kofar sai ya fasa tare da ja baya ya wuce part din shi, fatuha ko duk wani motsi da sadiq yake a kunnanta take jin shin  lamo tayi kamar mai bacci haka ta dinga zare ido har bacci ya kwashe ta.

      Yana shiga bedroom toilet ya shige ya sheqa wanka ya fito, tsane jikin shi kawai yayi tare da zura kayan bacci yabi lafiyar bed ya kwanta.

     Kiran sallah ne ya tashi fatuha toilet ta shiga tare da yin wanka  tare da dauro alwala daure da towel tafito  Dan karamin towel na hannunta tana tsane jikin ta dashi,   shafe jikin tayi da lotion tana gamawa tabude wardrobe ta  ta janyo wasu riga da sket masu stone's a jiki masu kyau   tana gama sasu ta dauko aftar dress ta aza bisa domin  gabatar da sallah tana idarwa ta koma  saman bed ta kwanta bacci ya qara kwasheta, ba ita ta tashi ba sai karfe bakwai kallon agogwan dake manne jikin daki tayi tare da yin miqa toilet ta shiga tayi brush ta fito tare da sharce sumarta ta kwanta a gadon bayan ta a hankali ta bude kofar daki ta zuro kai ta laleqa taga ba kowa fitowa tayi ta nufi dining area tana qaraso wa taga sadiq zaune cikin shirin shi na unform yasha kyau har ya gaji dago eye's ball's din yayi su kayi ido hudu da  fatu, kauda kai yayi ya cigaba da breakfast gaisheshi tayi ya amsa a taqaice qoqarin barin gun take har ta juya yace "Fatuha.! waigowa tayi hakan yasa iska ta hura gashin kan ta har ya shifi fuskar sadiq lumshe ido yayi tare da ware su a kanta itama din shi take kallo kauda kai yayi ya ce "Ki dawo kici abincin ki" washe baki tayi tare da jan kujera ta zauna saving din kanta tayi tare da janyo plate din gaban ta Sadiq kallon ta yake ta qasan ido hannun hagunta tasa ta gyara gashinta da iska ke yawo da shi ta zura hannun ta, cikin plate ta fara cin abincin, chips ne da farfesun kifi wani irin dadi ya mata sai kada kai take tana ci sadiq mamaki qazantar fatuha yake, cin abinci da hannu ko wankesu batayi ba kallon ta yake sosai dagowar da zatayi da kanta ta  kai wata lomar sukayi 4 eye's murmushin karfin hali ta masa tana qoqarin boye hannu ta dan kwata-kwata ta manta yana wajan kauda kai yayi tare da daukar briefcase din shi kallon shi fatuha take tayi rau-rau da ido ko kallon ta baiyi ba yasa kai ya fice, ture plate din tayi take nan taji abincin ya gundire ta, kwashe kwanikan tayi ta kai kitchen a nan ta ci karo da rabi'a na aiki gaisheta tayi ta amsa cikin fara'a taya ta aiki fatuha ta shiga yi tun tana  hana ta har ta kyale ta, kusan tare sukayi komai na launch sannan suka jera a dining area bayan sun kamala fatuha ta shiga rokar rabi'a kar tatafi ta barta ita kad'ai aiko taci sa'a rabi'a ta tsaya taji dadin hakan sosai, dan haka ta wuce part din sadiq ta gyara shi tas ta dawo parlour suka cigaba da hira da rabi'a ko da aka kira sallah azahar  tare sukayi sannan su kaci abinci, sai kusan qarfe hudu rabi'a tayima fatuha sallama, fatuha bata ji dadi ba amma hakanan ta hakura ta zauna kiran sallah la'asar ne ya sata shiga bedroom ta shiga toilet tayi wanka tare da alwala saboda yau tasha aiki ba laifi wata hadadiyar riga da isket ta kuma sawa, hijabinta ta zura tayi sallah bayan ta gabatar da sallah ta cire hijabin ta dawo parlour, jin zaman parlour ya isheta ta yasa ta fita farfajiyar gida su ola da Sunday ne da sauran yaran sadiq suketa shawagi a gidan resting chair ta samu ta zauna tare da jingina da kanta ta lumshe ido wani iska ke kadawa mai dadi da sanyi, Sunday ne ya zuguro Emeka dake ta kallon fatuha har yana lashe baki ya  ce, "hey Emeka stop looking at her, mind ur business this girl past ur level  na Oga consin sister be that"
     "I don't now fa amma this girl na beautiful"
    "Oh u no go stop looking at her I will tell  Oga"
     "sorry Sunday haba kar muyi haka da kai"  Emeka ya fadi cikin hausar sa mara dadi Sunday ya  ce, "leave me alone" Sunday ya fada
      "sorry lemme leave the place ma" Emeka tabirim bala mai gadi ya koma duk abun nan da sukeyi fatuha bata sani ba.

      Yau yasha aiki sosai wajan a office sai kusan yama likis sadiq ya nufo gida, yana zuwa bakin gate horn yayi bala mai gadi ya wangale masa gate ya kunno hanci motar shi, hango fatuha yayi harabar gidan  saman resting chair gashin ta ya bage kusan rabin qirjin ta duk waje suke domin riga da isket ne ajinta sun  dan matse ta sosai  dakyar take numfashi,  Emeka da ke gefan bala mai gadi sai kallon ta yake, yaransa sadiq yake  bi  da  kallo  wayanda  ke  harabar  gidan  kusan  rabin su  hankalinsu  na  kan  fatu,  take  farin  cikinsa  ya  d'auke lumshe ido sadiq yayi tare  da  ware  su yana ji wani  abu  mai  zafi  yana  masa  yawa mota ya  ja da karfi dai-dai parking space yayi parking ko dai-daita parking  baiyi ba ya fito cikin zafin rai fatuha dake kishingide ya nufa cikin zafi rai ya daka mata tsawa da  cewa, "me kike  a  waje  mai  ya  fito  dake? sadiq  ya  rintse  ido  yana  ta  masifa ganin  fatu  ta  tsare  shi  da ido  duk  ta  rud'e  sam  ta  kasa  gane  masifar  me  yake  mata mara  dalili  cike  da  masifa  sadiq  ya fisgota ba  shiri  tayi  masauki  bisa fafadar kirjinsa tana  sauke  numfashi  cike  da  tsoro  yanayin  sadiq  matse  mata  hannu  yayi sai  huci  yake   kamar  zai  hadiyi  zuciya  ya  mutu  saboda  masifa, ware ido tayi tare da saka masa kuka saboda  masifar  da  sadiq  yake  yayi  yawa janta  ya shigayi tana  rike  hannusa  tana  kuka  tana  cewa,  "mai  nayi  kuma  mai  kyau  Allah  banyi  komai  ba" ya cigaba da janta  cikin  zafin  rai  sai da ya zo parlour  yayi wurgi  da  ita saman kujera har sai da kanta ya bigi kujera kuka ta qara saki tana kallon sadiq dan bata san laifin data masa ba,  shima  d'in numfashi  yake  saukewa  cike  da  6acin rai cije  lips  yayi  yana  jin  wani  suya  a zuciyarsa  mara dalili, kallon ta yake ido cikin ido matsowa yayi daf da ita har tana jin saukar numfashinsa idanusa sun  kad'a  sunyi  jawur  rintse  ido  fatu  tayi  tana  kuka  mara  sauti hannu  yasa  ya matse mata fuska cikin daka tsawa yace "Uban waye yace ki fita waje haka? ya fadi a tsawa ce har cikin kanta sai da taji tsawar da sadiq ya mata runtse ido tayi tana girgiza kai tana kuka sakin fuskar yayi ya ja gashin kanta har saida ta saki qara tare da rushewa da wani sabon kuka cikin  daka  tsawa  sadiq ya  ce, "idan na qara ganin ki kin fita farfajiyar gidan nan baki sa hijabi ba sai na kona gashinan" ya ida zancan tare da matse mata fuska da karfi kuka ta kuma saki tana kallon sadiq wani irin tsanar shi na fizgar ta, lumshe ido tayi tana jin zafi da radadin, wani wawan tsaki sadiq ya ja tare da tura ta  ta bige da kujera sannan ya dau briefcase din shi ya haura sama da  sauri tamkar  zai  tashi  sama, kuka ta saki  mai ban tausayi.

     Yana shiga parlour shi ya wurgar da briefcase din shi ya zauna bisa kujera tare da lumshe ido, yana  sauke  ajiyar  zuciya wata zuciyar ta ce masa "Kai sadiq ina ruwan ka da harkata? idan ma tsirara zata dinga yawo me ruwan ka? runtse ido ya kuma yi" wata zuciyar tace masa "Ko dan saboda tarbiyar diyar ka ka taka mata birki? saboda duk abinda tayi shi jidda zata kwaikwaya?" duk wannan zancan a zuci yake kiran sallah magrib ne ya tasheshi bedroom ya shige ya rage kayan jikin shi agurguje yayi wanka, yana fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jallabiya a hankali yake sauko wa daga upstairs, inda ya bar fatuha har yanzu nan take tana kuka jin alamar tafiya ya sata dago jajayan idanuwanta  ta kalli sadiq, sadiq ma kallon ta yayi  tare da aika mata harara ya ja  tsaki mtss ya fice, kuka ta kuma saki sannan ta ja jiki ta shige daki tana alwala tana kuka har ta gama, haka tafito ta zura abaya tana idar da sallah ta cigaba da lazumi   har sai da aka kira isha'i ta tashi tayi sannan ta ja jiki ta koma bed ta cigaba da raira kukanta kanta har ciwo yake mata amma dan jaraba takasa daina kukan.

  bashi ya dawo gida ba sai bayan sallah isha'i, yana shigowa parlour dining area ya wuce yana b'ude kulolin yaga alamar fatuha bata ci abinci ba dogon tsaki yaja tare da rufe kulolin, Kwala mata kira yashiga yi shiru ba'a amsa ba dan haka cikin nutsuwa ya nufi dakin fatuha ya murda handle din kofar can saman gado ya hango fatuha cikin cool voice din shi ya ce mata " Yanzu dan iskanci
kina jina  kikayi   banza dani? tayi shiru bata tanka masa ba, rashin yayi mugun bacci dan haka ya daka mata wani uban  tsawa  wadda ta sata zabura ta sauko daga bed tare da fashewa da wani sabon  kuka😭, harara ya aika mata ya mata nuni da ta biyoshi, bin shi take har tana sarke kafa dining area ya isa itama taja ta tsaya ya  ce, "oya wuce kici abinci" a takaice tace masa ta koshi, wata tsawa ya kuma daka mata jiki na bari tana kuka ta fara zuba abincin dan kadan ta zuba, wani irin kallo sadiq ya wurga mata tare da yin magana cikin daure fuska "Haka kike zuba abinci eeeh?"  kuka tasa tana  mamakin  yarda  sadiq  ya  karanci  cin  abincin ta tare da cigaba da zuba abincin har ya kai bakin plate din, tana qoqarin qara zuba wani sadiq ya matse hannunta da karfi har sai da ta saki qara, saboda ya lura bata da niyar daina zuba abincin kuka ta  saki  tare  da  zaman  dole, juya abincin ta shigayi ta qasaci  sai kuka, cikin  murya mai sauti sadiq ya ce "Ko kiyi ma matune shuru! ko nasa alburushi  na bula maki kai kowama ya huta, kuma abincin karki ci ki bari na tashi tsaye Allah danne ki zanyi na dura maki har da plate din" cikin hawaye fatuha tashiga dura abinci har tana jin kamar zatayi amai amma sai da ta cinye shi tana gama ci tayi qoqari tashi cikin sauri sadiq dake saman kujera dining area ya lumshe ido kamar me jin bacci, har tayi nisa ya ce "Fatuha..! juyowa tayi tana kallon shi hawaya da ke maqale a idanuwan ta suka gangaro bisa kumatunta tayi  kala  tausayi  baby face  nata  yayi  jawur, wani irin yerr sadiq yaji ajikinsa   kallon  ta yashiga yi kamar yau yafara ganinta har wani  langwa6e kai  yake  yana  kankance  ida yakara Kiran ta akaro nabiyu   "Fatuha..! gaban tane ya yanke ya fadi kuka ta kuma saki tare da dawowa ta durqusa gaban shi tana rera wani saban kukan, a hankali sadiq ya kai lallausan hannun shi ya cigaba da gogema fatuha hawayan ta, lumshe ido tayi tare da ware su kan  sadiq dake  kallonta, yana gama goge mata hawayan  ya mata alama da  ta tafi har tayi gaba ya ruqo hannun ta  juyowa tayi da sauri idanu  ta  waje  tana  sauke  numfashi  da  sauri  da  sauri domin ita yanzu yafara bata tsoro,  langabar da kai yayi ya ce,    "Fatuha please kukan ya isa  haka"  kallon shi take shima din haka,     wasu sabin hawayan ne suka qara zubowa wani irin kallo sadiq ke bin ta dashi ya koma abin tausayi kamar bashi ba  hakan yasa fatuha hadiye wasu hawayen, smile yayi tare da sakin ta cikin sauri ta shige daki tare da fada wa saman  bed.
        shima sadiq upstairs ya haura cike da farinciki dashi kansa mamakin haka yake..... Hmmm kayi bayani Sadiq😘.

Written by
     salma mas'ud nadabo

Edit by
    Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
  ★we are the beat★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_* [email protected]

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                   59_60

       Tun ranar da fatuha tasha maqara ta shiga wasan 6uya da sadiq, kwata-kwata bata bari su had'u dan ta lura aljanu gare shi, lol ko gyaran part nashi za tayi sai ta bari ya tafi office haka shima bangaran sadiq bai wani damu da rashin ganin na ta ba, saboda yasan lafiyar ta lau of cos yana ganin part nashi fes.

      Fatuha da rabi'a sun wani qara shaquwa musanman yanzu rabi'a bata tafiya gida sai 4, shiyasa fatuha ke dan jin dad'in gidan ita dai burin ta bai wuce ace su Mom sun dawo ba ko Jidda dan ta gaji da zaman kad'aici, ku san tare suke aikin ma yanzu dan fatuha yanzu ta fara gogewa da girke-girke dan yanzu kusan abinci gidan ita ke yin shi duk da rabi'a na hana ta.

   

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login