Showing 102001 words to 105000 words out of 105783 words

Chapter 35 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

724

mu a haka ba, rayuwa kenan" rungume juna sukayi tare da  hade bakin su suka furta, "Allah ya bar mana zumincin mu har ya'ya da jikoki ameen Fatsima" harara ta aika ma fatu ta ce, "ke mijina ya hana fadin wannan suna," dariya sukayi tare da cewa, "sannu mai miji" a haka suka isa wajan kamun  kasancewar sune manya-manyan qawayan amarya hada-hada kawai suke biki yayi biki su Zara da Nana ma sai da suka zo ansha biki sosai sai kusan yamma likis suka dawo, gidan mami suka wuce direct.

        Da sallama suka shigo angel dake zaune da friends nata ta qaraso ta rungume fatuha ta ce, "Mom a I miss you"  
          "miss you more dear, kin manta da mamanki tunda biki ya kama ko? to ai gashi nan ni na biyo ki bana iya hakuri kimin nisa" fatuha ta fada tana shafa kanta smile tayi  ta ce, "Nima haka Mom" ja mata hanci fatu tayi sannan ta koma cikin friends din ta.

          Shirye-shirye na zuwa dinner suke, cikin material lace green and black yan'matan amarya, amarya kuma ta shirya cikin black lace mai ratsin white, sosai sun fito sunyi kyau musanman da suka sha make up, cikin  motaci na gani na fada aka zo kwasar yan matan amarya, fatuha ko motar sadiq ta shige, lallausan murmushi sadiq ya sakar ma fatu ya kama  hannu ta yana murzawa a hankali cikin salo yana sakin murmushi yasha kyau har ya gaji yana sanye cikin shada milk tasha aikin hannu,  kamshin turaransa na fizgar fatu ya  ce, "My wife kinyi kyau masha Allah" smile fatuha tayi ta ce, "na gode hubi, kai ma kayi kyau har na ji kishi kar mu je yan mata su dinga kalle min kai" fatu ta fada tana d'an 6ata fuska yar dariya sadiq ya saki yace, "ni ba mai kallo na mijin mace daya daga fatu na rufe" murmushi ta sakar masa mai cike da sakonni sannan ya ja mota hannu sa daya na maqale dana fatuha.

              Hall ya cika maqil anata gudanar da biki, inda abun ya zama abin sha'awa da birgewa amarya da Ango sunyi kyau har sun gaji, kasancewar bikin masu hannu da shuni ne  manya-manyan ya'ya masu hali da masu fada aji sun halara, fatu da sadiq kam sun zama abin kallo dan sadiq baya iya boye irin son da yake ma fatuha koma a inane nuna mata so yake, sai nan yake da ita haka aka gudanar biki, ayi ciye-ciye da lashe-lashe  naira tayi kuka dan anyi barinta sai dai mu ce Allah ya bada zaman lafiya.

          Da misalin karfe 10:00pm taro ya watse sadiq ya wuce da fatuha gida, maqale qafa tayi ita baza ta koma gida ba ya maida ta gidan mami, cikin yan'mata amarya fir sadiq yaki saurarata haka ta cika taf kamar ta fashe, horn yayi mai gadi ya wangale geta ya kunna hancin motarsa cikin gida yayi parking a parking space, kashe motar yayi ya bude murfin motar fatuha ko zaune tayi tana qoqarin fara raira kuka Allah ya gani gidan Mami ta so kwana ba gida ba, zagayowa sadiq yayi ya 6ale mata murfin motar ganin fatu bata da niyar fitowa sadiq ya dauke ta kamar baby ya shiga da ita gida sai rigima take zuba masa har da kuka dakyar ya lallashi fatu ta saurara masu sukayi baccin dare.

   Washe gari

   Yau d'ibin mutane suka sheda daurin auran Dr yakub da Hanan    akan sadaki naira dubu dari, zuciyar Dr yakub fes sai washe baki yake da ka gansa kasan yana cikin farin ciki, ana kamala daura auran Dr yakub yaji alat a account dinsa kallon sadiq yayi tare da sakar masa murmushi sannan ya masa godiya,  bayan  kamala biki ango ya dauki amaryar sa sai airport inda Hanan ke ta zuba kuka.

            Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dad'i inda sadiq ke bama fatuha kulawa sosai, yanzu haka sun fara exam, alhamdulillah exam din ta zo mata da sauki, cikin ta ya dan fito.

     Murna suke sosai na ganin cewa yau sun gama paper, sosai fatuha ke jin dad'i a gaskiya bata da abinda zata ce ma mai kyau ya gama mata komai a rayuwa, ko da ta fito sadiq ne ya zo daukar ta, kasancewar Saturday ne ya zo weekend gida cike da farin ciki ta qarasa gaban motar ya 6ale mata murfin mota ta shiga, su Zara ko d'aga mata hannu su kayi tare da yimata alqawarin sai sun zo ranar suna.

       Kallon ta sadiq yake cike da so a hankali yake driving cikin nutsuwa har suka iso gida, shi da kansa ya bude mata murfin mota wata hadadiyar mota ta gani mai tsadar gaske sabuwa dal  Lexus toyota fake a harabar gidan su, kallon sadiq tayi ta ce, "Habibina munyi baqine?" d'aga mata kai yayi tare da janta suka shige ciki suna  shigowa parlour, parlour ya dauki sautin, "happy birthday to you fatuha" cike da farin ciki fatu ke bin su da kallo wasu kyalkyali suka fara zubowa a jikinta da flowers kallon sadiq take da mamaki peck ya sakar mata a goshi ya furta,  "happy birthday my wife🎂.!  jan hannuta yayi gaban cake shida angel dan kusan ita ta hada komai, sosai farin cikin fatu ya kasa 6oyuwa dan ba qaramin dadi ta ji ba sai smile fatuha take tare suka hada hannu suka yanka cake din, parlour ya dau tafi, gutsuro cake din sadiq yayi ya bata a baki itama ta amsa ta bashi sannan angel ta bata itama ta ba angel, pictures sukayi sosai yan'uwa da abokan arziqi suka bata gift da yawa, daukarta sadiq yayi cak ya maido ta harabar gida a je ta qasa yayi ya rungume ta, ta baya tana facing din motar dazu ya ce, "Rufe idanuwan ki love" lumshe ido fatuha tayi sadiq ya ce, ta bude tana budewa taga car key wani irin ihu fatu ta saki tana kallon car key kame da baki, juyowa tayi ta rungume sadiq tasa kukan farin cikin, shafa bayanta sadiq yake a hankali ya zame jikinsa yasa hannu ya goge mata hawayan dariya ta saki tare da sakar masa peck  ta ko ina tana cewa, "thank you hubi thank you.! dariya su majeed suka saki shi da fatima, murfi motar ta bude ta shiga yana mai tsananin farin ciki sannan ta kule motar suka dawo cikin gida sadiq ya mata alqawarin kafi ta fara zuwa university zai koya mata driven.

   Bayan kwana 2
               ***
Shirya kaya fatuha take cikin trolley a yanzu cikin ta zai kai 4 month, sadiq ne ya jawota jikinsa ya zaunar da ita shi ya cigaba da hada kayan, sai murna take kasancewar wudil zasu daga nan su wuce abuja, yima sadiq kwana biyu bayan ya gama hada kayan cikin trolley, ya ja trolley din zuwa parlour ya kiran Sunday, ya amshi kayan ya kai su boot sannan sadiq ya leqa bedroom din angel itama ta gama hada na ta kayan, smile tayi ta ce, Daddy.! ta masa peck ta miqa masa trolley dinta, amsa sadiq yayi ya ce, "Angel kin sa komai da kike buqata  ko? Dan karki manta wani abu" d'aga kai tayi ta ce, "Yes daddy"
       "good girl idan zaki fito ki kashe AC da komai na bedroom din" ok tace tare da nufar AC zata kashe sadiq ya fita ya ba Sunday trolley jidda ya kai boot komai sun gama hadawa, sun shirya tsaf sai tafiya  fatuha na sanye cikin  atamfa dinkin bubu dinkin ya zauna ajikinta das ya mata kyau sosai cikinta ya fito,  kanta ya sha dauri wadda ya dace sosai ta fito matar manya da ita tana yafe da mayafin daya dace da kala kayanta, tayi kyau har ta gaji ta qara haske, rike da wayarta iPhone 6 Angel ta fito daga bedroom suna video call da Jamal tana sanye cikin lace riga da sket dan yanzu ta fara zama yan'mata kashe wayar tayi ta biyo bayan su Mom suka fita a tare, da kansa sadiq yaja motar, sai da suka fara zuwa gida, haka Mom ta hada masu tsaraba sosai ta masu Allah ya kiyaye hanya ita da Abba kana suka kama hanyar zuwa wudil.

        Da misalin karfe 2:00pm suka isa wudil cike da murna fatuha ta shige gida ita da angel, da gudu angel ta fada jikin inna dariya inna ta saki ta ce, "oyoyo mutanan birni sannu ku da zuwa, yau tafiyar harda yan'mata? kwabe fuska fatuha tayi ta ce, "Angel dan kin fini sauri ko shine kika rigani" dariya sukayi a tare sannan suka shige parlour haka inna ta dinga nan da su sadiq ko tunda ya sauke su ya wuce gidan gona wajan Baffa ya taya shi aiki sai hanasa Baffa yake acewarsa daga zuwansa baya fara da aiki ba, sai yamma liqis suka dawo. 
           gaishe da inna sadiq yayi sai zuba masa albarka take sannan ya wuce masaukinsa, wanka kawai yayi yana tsane jikinsa fatuha ta shigo da kulolin abinci ta aje masa sannan ta amshi towel din hannusa  tana goge masa jiki, jawota jikinsa sadiq yayi sosai yana facing nata cike da so a hankali ya kai hannu kan cikinta ya ce, "Ya babyna? smile fatuha tayi ta ce, "Yana cikin koshin lafiya"
   "Are you sure? d'aga masa kai, rage tsawansa yayi dai-dai cikin fatu ya kasa kunne saitin cikinta yana murmushi saboda baby sai motsi yake peck yama cikin tare da miqewa  fatuha ta taimaka masa ya shirya kana tayi feeding nasa tuwo shinkafa miyar kuka tasha manshanu da naman rago sosai yaji dadin abincin.

      Angel ko tana wajan inna suna shan hira, Idan ta bugo wani shirman inna ta biye mata, dan inna jin take tamkar jikarta haka itama angel sakin jiki take da inna sosai.

         Qoqarin fita fatuha take Sadiq ya riqe ta ya langwabe kai  ya ce, "my love," shafa gefan fuskarsa fatu tayi ta ce, "Na'am" shagwabe fuska sadiq yayi ya ce, "Please ki kwana anan?" zaro ido waje fatuha tayi ta ce, "Ta6 ba ruwana nama ji da wannan abin kunyar" ta nuna cikin ta dariya sadiq yayi ya hade goshin su waje guda ya ce, "Ai na halal ne ko kin manta?" lumshe ido tayi a hankali sadiq ya lallubu bakin ta yana kissing, sun dau lokaci mai tsaho suna tsotsanar la66an juna su sannan ya sake ta yana maida numfashi, smile fatuha tayi ta ce, "I love you"
      "Love you more" kana fatu ta fice da sauri, barbaza sumar kansa sadiq yayi tare da furzar da iskar bakinsa mai sanyi ya furta, "always loving  you fatuha..! Sannan ya kwanta.

        Kwanan su fatuha biyu a wudil, ta zagaya gidajan yan uwa da abokan arziki, hada kayan su suke zasu wuce, fatuha ji take kamar karsu tafi haka dai ta gama hada kayan, inna sai sa masu albarka take tare da yi masu addu'a samun zaman lafiya mai daurewa, sadiq ko albishir ya masu daya biya masu kujera haji murna wajan fatuha ba'a magana, haka ta dinga zuba ma sadiq godiya haka su Baffa da inna sannan ya fido kudi masu yawa ya aje masu dakyar ya samu Baffa ya amsa, sannan itama fatuha ta baje masu tsaraba laces da atamfa da shada da ta siya masu sosai su inna sun ji dadi sannan suka dau hanyar abuja fatuha har da yar kwallanta ita da angel.

      Sai  dare suka iso abuja, katafarin gidan nasu ya hadu fadin tsaruwar gidan ma bata lokaci ne, dan yafi na kano ko ta ko ina, duk inda ka waiga a gidan yaran sadiq ne sojoji da yawa kamar a barak haka suka shigo da kayan su kasancewar sunci abinci a hanya, sallah kawai su kayi angel ta shige dakin da sadiq ya gwada mata a matsayin nata dakin ya hadu dan yafi nata na kano kyau nesa ba kusa ba.

         Haka suma dakin su fatuha ya hadu iya kar haduwa, har kauyanci sai da fatuha tayima sadiq dariya kawai yake mata saboda komai tayi birgeshi take.

     Washe gari

Bayan sun kamala komai sadiq kwashe su zuwa yawo, sosai sun sha yawo inda sadiq keta kula da fatuha yana bata kayan gina jiki wanda zasu taimaka mata ta haihu cikin koshin lafiya.

   3 month letters

     Sosai cikin fatuha ya girma dan har Mom ta ce sadiq ya maido ta kano, kasancewar tun hutun da suka tafi basu dawo ba, saboda cikin yanzu ya kai wata na takwas, ba yarda sadiq ya iya ya amsa da toh dan baya so tayi nisa da shi.

       Shi da kansa ya hada masu kaya  sannan ya kai masu boot itama fatuha ji take za tayi missing nashi, sannan suka dau hanyar kano, suna isa kano gidan Mom ya wuce da su lokacin itama fatima ta dawo  gida ita da Basma saboda Mom ta ce baza su je gida ba, a wajan ta zasu haihu har suyi arba'in, dadi ta ji ganin su sai damuwar ta ta ragu kwana sadiq daya ya juya abuja cike da kewar fatuha.

    Akwana a tashi ba wuya wajan Allah, su fatuha yau da naquda suka tashi majeed Mom ta kira a waya ta sheda masa halin da suke ciki, driver ya  wuce da su asibiti, labour room aka wuce da su, su uku sun dade suna naquda, sosai hankalin Mom dana Umma ya tashi su Abba na kwantar masu da hankali, ko da sadiq ya iso gari daga  airport asibiti kawai ya wuce yana isa lokacin yayi dai-dai da haihuwa fatuha ta sili6o baby boy din ta Fatima ma boy ta haifa, Basma baby girl masha Allah yaran masu kyau, musanman fatuha gabaki daya baby sadiq ya d'auko kamar yayi kaki ya aje haka suka dinga murna kankace me asibitin ya cika da yan uwa.

      A hankali sadiq ya qaraso bakin gadon da baby ke kwance yasa hannu ya daukesa yana kallo, "masha Allah.! Ya furta a hankali yana smile tare da kallon fatuha hannuta ya kama ya sakar mata light kiss a hannuta Sadiq ya ce, "Thank you my wife da kika bani wannan farin cikin"Angel ma murna ba'a magana kwana su d'aya aka sallame su family house aka wuce da su.

      Sosai suke samu kulawa tare da wanka da shan abubuwa masu gina jiki,  ranar suna anyi shagali ba dan k'adan ba, inda dan fatuha yaci sunan Abba Ibrahim ana kiransa da aslam,
D'an majeed yaci su baba khabir ana kiran shi da Walid, diyar Khaleed taci suna Khadija ana kiranta da Nana.

      Suna yayi suna inda aka dinga narka kudi kamar ba'a so, anyi ciye-ciye da lashe-lashe an raba sabeniyas sannan taro ya watse kowa ya tafi gida cike da farin ciki aka bar masu jego.

        sosai Mom ta zage tana gyaran ya'yan nata inda suke ta shan gyara  jikin da tsimi wani irin kyau da sheqi suke  zubawa, baby's kuwa sunyi wayau gasu yan duma-duma saboda suna samun ruwan nono sosai kullan angel na maqale da Aslam sai fatuha zata bashi nono sannan angel ke bata shi, dan wani irin son duniya ta daura mashi, bata da  lokaci kowa sai na Aslam.

      Sanye da qaramin towel ta fito daga bathroom tana goge gashin kanta da qaramin towel, gaban dressing mirror ta tsaya tana shiryawa lotion ta jawo zata shafa, ta hango sadiq ta cikin mirror lallausan murmushi ta sakar masa a hankali ya qaraso ya rungumeta ta baya sanyayar ajiyar zuciya ya saki yana shinshinar kamshi jikinta lumshe ido fatuha tayi tana amsar sakonin sadiq, dan ba qaramin kewarsa tayi ba qoqarin zame towel di'n jikinta yake ta riqe tana kallonsa ta cikin mirror, lumshe shanyayun idnusa yayi ya ce, "Please..! yana qoqarin zame hannuta dake saman towel din kasa magana fatu tayi har sadiq ya samu nasara zame towel din rintse ido tayi tare da waigowa ta shige jikinsa, daukar ta cak yayi ya daura saman bed ya fara aika mata sakonni da zafi-zafi lokaci daya suka fice hayacin su, gani zasu lula yasa na silale na fice.

        Shiryawa take cikin atamfa riga da sket cike da shagwaba ta ce, "Habibina gaskiya ka tashi ka fita bana so Mom ta zo ta gan ka, tana ganin ka zata gane" ta ida zancan tana parking  gashin kanta smile sadiq yayi  ya rungumeta sosai ta baya can kasan makoshi ya ce, "Uhm my love baza ta gane komai ba kinji"
      "da gaske" daga mata kai sadiq yayi alamar eh tare da ciro wasu takadu daga aljihusa ya miqamata, wani irin tsale fatuha tayi ta qanqanme sadiq dan murna ba komai  bane yasata farin cikin ba sai admission na north west university data gani.

      Da sauri fatuha ta fita tana kwalawa Mom kira, fitowa tayi daga kitchen ta ce, "na'am fatuha" fadawa tayi jikin Mom tare da nuna mata admission murna Mom ta tayata tare da yima sadiq godiya sosa keya yayi angel itama fitowa tayi riqe da Aslam amsarsa sadiq yayi yana mashi wasa, haka su fatima suka dinga taya fatuha murna.

    3  years letters

      Sosai fatuha ke maida hankali a karatun ta tana karanta law yanzu haka tana level 2, Aslam yayi wayau sosai dan har tafiya yana yi ba ida baya zuwa zai kai  2years ga surutu  tsiya komai ya gani sai ya tanka, angel kuma na SS2 an fara zama yan'mata sosai.

       Yauma kamar kullun a  gajiye ta dawo daga makaranta tun safe taje school sai 5:00pm suka gama lectures, a gajiye likis ta dawo gida ga wata irin kasala dake damunta, Aslam ne ya sako daga jikin baba asabe rugo da gudu ya fada jikin fatuha, daga shi sama tayi tana chabesa yana dariya  zaunawa tayi saman three sitar tare da gaida baba asabe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login