Showing 9001 words to 12000 words out of 105783 words

Chapter 4 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

701

da Abban kausar, hakuri yake ta bashi ankan cewa bai san kausar bafa fad'a masa larurata ba sadiq  ya  ce, "ba komai Abba"
  "Toh shikenan Allah ya bata lafiya" 
"Ameen.!!
         d'akin da a kwantar da kausar ya shiga Mom na saman daduma tana lazumi, gaisheta yayi ta amsa a takaice sosai taji dad'in ganin sauyawar sadiq  ba kamar d'azu ba, Kausar ya kalla wanda ke kwance saman gado kamar gawa oxygen ne manne a hancin ta sai jini da ake qara mata, idanuwansa ne suka ciciko da kwalla tabbas yasan ya rasa kausar ya rasa mata tagari,  cikin  zuciyarsa  yake  sanbatu  da  cewa,  why mai yasa zaki mana haka kausar..! hawayan da ke neman zubo masa ya had'iye Mom ce ta katse masa tunani da cewa, "Baby ni zan wuce ka kulla da ita anjima matar jawad shukura zata kawo maku dinner, Son please ka rage damuwa wannan" Mom  ta  fad'a tare da shafa gefen fuskansa kamar jira ya ke hawaye suka fara mai zarya "shhh..! ya isa mana idan kana kuka ita kuma mai zatayi sokake ka tada ma kausar hankaline baby? Girgiza kai yayi tare da d'aura hannusa kan na Mom ya ce, "toh na daina"
   "ko Kai fa idan kasan kuka zaka cigaba dayi to sai mu koma gida Bilkisu ta kwana da ita"
   "Uhm Mom bazan sake kuka ba" wasu sabin hawaye ne suka zuba masa ya  ce, "Mom na rasa yarda zanyi control kai nane Mom nasan sarai na rasa my wife saboda wannan cikin" ya ja numfashi ya  cigaba da  cewa, "Mom kausar bata iya rainun cikin nan, Mom ki duba ki gani ita kanta duk month tana buqatar jini bale kuma yanzu data ke tare da ciki" ya ida zancen hawaye na zubu masa Mom ce ta share kwallan idanu ta ta  ce, "son ya isa haka kayi mata addu'a insha Allah lafiya lau zata raini cikin ta har ta haihu kaji" kai ya gyad'a mata tayi  peck nasa agoshi sannan ta masa sai da safe.

     Gashin kanta ya shafa  ahankali tare da kai mata peck a goshi ya  ce, "Allah ya baki lafiya my wife" sannan ya d'aura kansa saman gadon, a hankali take bud'e eye's balls din ta tasauke su kan sadiq da idanun sa ke lumshe kamar maiyin bacci,  a hankali ta miqa hannu ta saman sumar sa tanajin wani son mijin na ta na qara narke mata a zuciya, a hankali ya dago sexy eye's  ball's din sa ya sauke a kan wife din sa da  suka  canza  launi  saboda  kuka,  murmushi ta saki tana qoqarin tashi zaune ya  dakatar  da  ita  da  cewa, "no ki koma ki kwanta kiji my wife" ya ida zancen yana shafa cheeks nata ya  ce,  "My wife mai yasa kika 6oye min sick naki why? Idanun tane suka ciko da kwalla ta bud'e baki zatayi magana, sadiq  ya  ce, "Shhhh.. ya had'a bakin su waje d'aya yana mata salon sa mai kashe mata jiki..

                            **
           Rayuwa haka ta cigaba da tafiya sosai kausar ke samun kulawa wajan sadiq, inda suka bud'e babina soyayya, soyayya suke sosai kamar su cinye juna su inda duk month sadiq sai ya kaita asibiti an qara mata jini.

   Misalin qarfe 3:00am na dare sadiq kwance kausar na manne aqirjinsa ahankali yasa hannu yana cire mata hula da ke kanta, wadda bata bari ya cire mata, wasu siraran hawaye ne suka zubo masa saboda kusan rabin gashin ta ya zube saboda wannan ciwon, kuka ya sha sosai cikin daran sannan ya tashi yayi sallah ya nemamata samun sauqi wajan Allah, tabbas yasan ya rasa kausar ya rasa wani 6ari na rayuwarsa da irin wannan tunanin bacci ya d'auke shi.

   Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau kausar cikin ta ya kai 9month, sadiq ne akwance yana bacci ya fara jin,  wash.! sadiq.! zunbur ya tashi hankali tashe kai tsaye asibiti suka wuce nurses suka kawo masu taimakon gagawa, gabaki d'aya sadiq ya rud'e har da yar kwallan sa, waya ya curo ya kira Mom ya fad'a mata cikin muryar kuka.
     Zirga2 sadiq ke yi ya kasa zaune ya kasa tsaye, Majid ne ya dafa shi  ya  ce, "cool down sadiq" tare da rugume sa alamar lallashi,  Doctor's ne ke kan kausar sosai suke aikin su dan suga ta haihu da kanta amma abin ya gagara.!!

          Doctor yakub ne ya fitu yana goge zufar face nashi, da sauri sadiq ya k'arasa wajan su da Mom da majid a  tare suka jefama doctor yakub tanbaya  "Ya kausar.?
   "da sauki muna kan bakin qoqarin mu, ga wannan paper captain sadiq kasa hannu kausar ta kasa haihuwa da kanta" jikin shi narawa ya amshi paper yasa hannu aka shiga tiyata tun dare ake abu daya sai da safe suka fito.
     daga Mom har sadiq ba wanda ya rintsa addu'a kawai suke, bayan ta haihu doctor ya sheda masu ta haifi baby girl murna wajan su Mom ba'a magana da sadiq.

      Kwance take a d'aki ita kad'ai tasan rad'ad'in da take ji wasu hawaye ne masu zafi  suka zubu mata tasa bayan hannu ta ta goge, gefen da baby take ta kalla jin an bud'e kofar ya sata d'ago eye's ball d'in ta, wani lallausan murmushi ta saki tana qoqarin tashi,  Sadiq ya qaraso ya  ce, "my wife" tare da kai mata peck a goshi yana qoqarin maida hawayansa kausar  ta ce, "Habibina.! cikin sanyin murya  Baby  sadiq ya d'auka yana  murmushi  ya  ce, "Masha Allah baby mai kyau da ita kamar  ke"
   "habibina..!
"Na'am"
  "ga amanar baby mun na baka please ka kula da ita"
  "shhh insha Allah tare zamu raini baby mu" yana qoqari boye hawayan da ke maqale a idanusa,  hannu ta kai  ta  shafa sajan fuskarsa mai laushi ta ce, "Wani suna zamu sama baby mu? Lallausan murmushi yayi ya ce, "Hauwa'u suna Mom, za'a mata laqabin ta Jidda" Fad'ad'a murmushinta tayi ta ce, "Jidda..! ta shafa cheeks d'in baby hannu ta ya riqe ya sunbata, tarine ya subuce mata jinine ya fara bi mata ta hanci da baki.
      Da sauri sadiq ya mik'e zai kira doctor, hannu sa ta riqe tana girgiza masa  kai  tana motsa baki can yaji jikinta yayi sanyi cikin  wata  irin  murya  rikice  ya  ce,  "Noooo..! Sulalewa k'asa yayi sumame.

Writing by
Salma mas'ud nadabo

Edit by
Blood sister deeja

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM

13_14

Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un duk wani mai rai mamacine yau dai kausar ta rigamu zuwa gidan gaskiya, shi kuma sadiq aka wuce da shi emergency dan bai san inda kansa ya ke ba, dangi sunyi kuka sosai na rashin kausar saboda kausar mutuniyar kirkice.

Yau kusan sati daya kenan da rasuwar kausar sadiq na asibiti sosai yake samun kulawa wajan su jawad da majid, wanda bai ma san suna yi ba, Jawad ne zaune a d'akin asibiti saman three star yana shan coffee yana d'an kallon sadiq dake kwance har yau tamkar gawa, sosai yake damuwa da halin da d'an uwan nasa ke ciki.
A hankali yake bud'e sexy eye's balls d'in sa, abubuwan da suka faru na dawo masa tamkar yanzu akayi su, wani irin kuka ya fashe da shi maitsuma zuciya yana qoqarin tashi ya cire drip din da ke maqale a hannusa, Jawad ne ya taso ya rungumesa alamar lallashi kuka ya qara fashewa da shi yana fisfisgewa kamar zarare yana cewa, "Bros I cant live with out my wife please bros ka barni na bita" ya qara fashewa da wani sabon kukan, ganin abin nashi kamar ba kai d'aya ba ya sa jawad yayi ma d'aya daga cikin yaran sadiq masu tsaron lafiyarsa magana dake tsaye bakin kofa ya ce, "Kiran Dr yakub.
Jum kad'an Dr yakub ya shigo shi da nurse tana d'auke da trayn alururi, dakyar Dr da jawad suka samu suka danne sadiq aka masa alura bacci, sai da yayi kusan 30 minutes yana sanbatu sannan bacci ya d'auke sa Jawad ne ya ce, "Dr Ina fatan dai sadiq ba brain nashi bane ya sami problem ba? ya ida zancan yana matsar kwalla "karka damu kawai mutuwar ta firgi tashi ne amma, insha Allah zai samu sauki daya tashi komai zaiyi normal, Allah bashi lafiya"
"Ameen Dr.

2weeks letter

Sosai Jidda ke samun kulawa wajan Mom da baba jummai da mai aikin ta Mary, sadiq ko duk wata walwala ya daina idan kaga yana smile to Jidda na hannusa, inda ya d'aura mata son duniya nan wani bangare na zuciyarsa kuwa ji yake Nigeria ma ta isheshi saboda ya rasa abar kaunar sa, daga karshe ya yanke shawawar barin kasar bai samu wata matsala ba wajan aikinsa ya d'au hutu sheraka d'aya, Mom ce zaune a parlour sadiq na riqe da jidda wanda bacci ya d'auke ta acinyar sa cikin sanyi murya kamar mai koyan magana da yanzu magana ma wuya take masa ya ce, "Mom Ina san nabi jawad londan idan zai koma"
"toh ai shikenan son"
"Amma Ina san idan zan koma na koma da Jidda, saboda sai hankali na yafi kwanciya" Mom ce ta daka tsale ta dire ta ce bata san zancan ba, ba inda zai tafi da ita duka yarinyar nawa take zai tafi da ita, ba yarda ya iya ya hakura wannan kenan.


CIGABAN LABARI

A hankali ya d'au jidda wanda ke bacci ya kaita bedroom ya kwantar da ita ya shiga wanka, inda yake jin mutuwar kausar ta dawo masa sabuwa sai da ya zubar da kwalla sosai, 30 minutes yayi yana wanka ya fito sanye da bathrobe, A hankali ya kai lips d'in sa goshin Jidda ya mata peck, ware manyan eye's ball din tayi ta ce, "Daddy.!
"oya tashi ayi wanka muje yawo wajan hajiya da Umma" baki ta washe ta ce, "ok daddy.! d'aukarta yayi ya kaita bathroom ya wanke ta tas suna wanka suna wasan ruwa.

****
Yanzu saboda Allah fatuha kin kyauta kenan? ince bana ce ki kyale Rabi'u ba eh?
"yo inna ji nayi kwarankwatsi bana iya hakura"
"Aikin kyauta tunda kin sa maitafasa tamin tanadi kinji d'ad'i saiki zubar da ruwa a qasa kisha" baki ta turo gaba ta ce, "Gaskiya inna baki so na kwarankwatsi Baffa yafi sona" ta ida zancan tana matsar kwalla inna ta ce, "Fatu kenan kin ta6a ganin inda uwa ta haifi d'a tace bata so, Kawai dai halin kine ban so fatuha, ki daina tsokana" baki ta washe ta ce, "yo ahe kina so na kwarankwatsi na daina tsokana amma bilahilazi duk wanda ya shiga gona ta sai ya ci wuya Qur'an" Sannan ta zuri takalmanta ta ce, "Inna na tafi makarantar allo"
"Toh Allah ya shirye ki"
"ameen inna..!

*****
Bayan sun fito daga bathroom ya shirya ta cikin gown maroon mai d'an siririn hannu sai mai dogwan hannu a ciki ya gyara mata gashin ta, masha Allah sosai Jidda tayi kyau kamar d'iyar larabawa, peck ya mata a cheeks ita ma ta masa ya ce, " good girl tayi kyau" baki ta washe ya ce, "oya je ki wajan grandma gani nan zuwa"
"OK daddy" ta ruga da gudu ta fita ya bita da kallo yana smile, shima shiryawa yayi cikin jeans black and red t-shirt mai ratsin black sannan ya maqala ma hannu sa agogo black na zalla fata sai sheki yake, ya zura takalman sa black ba qaramin kyau yayi ba abin ka da farar fata d'an hutu sajan nan nasa ya kwanta luf-luf, a hankali yake sakowa downstair, a parlour zaune ya samu Mom Jidda na zuba mata surutu, cikin natsuwa ya gaishe ta ta amsa sannan yaja hannu Jidda suka fita Mom ta masu a dawo lafiya.

****
Zauna suke suna karatu fatuha tace, "kwarankwatsi na gaji, yo hi haka akeyi ya tasamu gaba ana abu daya"
"Rabu da shi Qur'an nan kadai ya iya a karatun" cewar Fatsima dariya suka kwashe da ita, ashe Malam D'alha ya ji dariyar ya fido so waje yana zare masu idanu ya ce, "Dan buhun uban ku kun raina mutane ko? yau zaku ci uban kune" sai da ya zane masu jikin rad'au sannan ya kyale sun inda suka rinqa jeramasa Allah ya isa.

*****
Dai-dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu Jidda part d'in hajiya suka fara shiga, d'auke da sallama suka shiga hajiya da ke zaune saman two star ta washe hakora tana cewa, "Ah'ah wana ke gani yau, kaine a gidan namu amma yau 6atan kai kayi maigida" Smile sadiq yayi ya langwabe kai ya ce, "Kai hajiya sokike ki ce bana zuminci ko? sannan ya samu waje ya zauna hajiya ta ce, "Dama yi kake? ta ida zancan tare da qwalawa Asiya mai aikin ta ta kawo masu kayan motsa baki "oh ashe da wannan yan neman ka zo" hajiya ta fad'a tare da jan Jidda ta d'aura saman cinyarta sadiq ya ce, "Kawo maki ita nayi ta maki 6ana"
"lallai kam aiko da taci na jaki" su duka suka kwashe da dariya sun dad'e sosai suna hira sannan suka wuce part d'in Umma.
Da sallama suka shiga Umma dake kitchen ta leko ganin sadiq ta washe baki ta ce, "ah'ah yau za'ayi ruwa da qanqara" da gudu Jidda ta ruga ta rungume Umma, Shagwabe fuska sadiq yayi tare da zama yana cewa, "Umma har da ke cikin masu ce min bana zuminci" kamar daga sama ya ji saukar magana "Toh dama yin zuminci kakeyi" cewar majeed juyowa yayi ya dallama majid harara, sanye ya ke da kayan ball green da alama daga ball yake sadiq ya bud'e baki ya ce, "Toh d'an hana ruwa gudu" yar shewa majeed ya saki ya hau upstairs.
Basma ce ta fito qanwar majeed baza ta wuce 15years ba ta gaishe da sadiq ya amsa ta ja hannu Jidda suka je dakin ta, sun dad'e sosai suna hira da Umman sannan ya bi bayan majid.
D'akin majid ya shiga ya zauna saman sofa lokacin majid na wanka, sanye da bathrobe ya fito yana murmushi ya ce, "Ashe ka biyo ni? harara sadiq ya balla masa majeed ya ce, "bani na kar zoman ba rataya aka bani, ka zo sai yi ma mutane borin kunya kake" ya ida zancan yana dariyar shaqiyanci, basu suka bar gidan Umma ba sai isha'i lokacin su Alhaji sun dawo daga kauya.

****
Fatuha da fatsima ne bakin rafi suna shan mangwaro "bilahillazi mangwaron ga zaqi garai" cewar Fatu
"sosai ma Qur'an" inji fatsima fatuha ta ce, "kin san wani Abu na matsu baba jummai ta zo mu ci d'ad'i nifa tsarabar nake mawa"
"ke dai bari fatuha"
"nima wallahi duk cikin tsarabar wannan bak'in abun yafin dad'i" ta washe baki ta ce, chakule ko (chocolate) lol....


Written by
        Salma mas'ud nadabo

Edit by
      Blood sister deejah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄

                                15_16

                   Shirye-shiryan ake sosai kasancewar yau ALHAJI Ibrahim zai dawo daga UK, sosai Mom ke gyara kanta kasancewar Mom irin matan nan ne wanda girman bai hana su gyara kansu wajan miji, abinci ne kala-kala anyi domin abirge Alhaji yau kusan 2week baya nageria.

   
                  "Daddy..! daddy..! please wake up daddy" saman ruwan cikin sadiq jidda ke tsale tana kiran suna sa  sadiq  daya  bud'e  idanusa  dake  d'auke da  bacci ya  ce, "oh no angel so kike daddy yayi ciwon ciki, ash bakya ji ko? Cakulkuli ya shaga  yi mata tana dariya tana  cewa, "daddy stop please" ta ida zancan tana mai da numfashi tsakaitawa yayi da yimata cakulkuli ya  ce, "Uhm my angel mai ya tashe ki haka da wuri har kina so ki hana daddy bacci? bayan kin san today is weekend" ya ida zancan yana langwabe kai ala dole yima jidda shagwaba yake, (ohni salma shi dai shagwababe ne ko da yake d'an auta ne... Lol")  jidda  ta  ce, "uhm'uhm daddy grandpa ne fa zai dawo yau" tana maganar tana wasa da ma6alin rigar sadiq na bacci ya  ce, "Inyee little princess of grandpa" ya lakace mata hanci wangale  baki  tayi  ta  ce, "daddy I miss grandpa"
              "I now angel yau zakiga grandpa har ki gaji ko angel?
              "yes daddy"
                        "oya tashi muje na maki wanka na maki make up kifi su Hanan kyau ko? washe baki tayi sadiq  ya  ce, "good girl..! ya d'auke ta suka wuce bathroom.

                           *****
            "Inna.! inna..!
"Na'am ohni fatuha wai yaushe zaki girma ne Dan Allah? mutun shekara goma shad'aya amma mutun kullun girma yake yana cin qasa"
                 "yi hakuri inna wallahi zanina nake nema inna, wanda baba jummai ta siyo min abirni"
                 "ah yau antuno da baba jummai kenan to zanin yana uwar d'aka na"  Washe baki tayi ta  ce, "eh inna Qur'an na matsu ta zo kwarankwatsi inna"
                 "ai zata zo insha Allah aikin san duk qarshan shekara ta ke zuwa, amshi kwanan ki kaima Baffan ki kinji"
             "to inna.! Baffa na zaune saman tabarma ta aje masa kwanan tare da gaishe shi washe da baki ya amsa da  cewa,  "Fatuha yan'mata.! rufe fuskarta tayi ita ala dole kunyar Baffa take ji  tana  wani  sunne  kai  ta  ce, "Qur'an Baffa ni ba yan'mata ba ce su Tanine yan'mata" yar  dariya  Baffa yayi  ya  ce, "alalai d'iyar Baffan ta ke ma ai yan'mata ce, matso mu ci abincin tare nasan baki ci ba saboda baki iya cin abinci ke kad'ai, kuma inna nasan batayi kalaci ba.
                "toh Baffa matsowa tayi tana cin abincin inna ta shigo washe da baki  tana  cewa,  "Kai dai Malam baka gajiya da shagwa6a fatuha da girman ta amma har yanzu tare kuke kalaci baka bari muci tare"
               "ah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login