Showing 57001 words to 60000 words out of 105783 words

Chapter 20 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

722

hawaye kallon ta sadiq kawai yake yana mamaki irin tausayi na fatuha gabaki d'aya tabi ta rude tunda taga bai da lafiya lumshe ido yayi tare da warewa ya sauke so a kanta ya  ce, "insha Allah fatuha zan daina kinji" murmushi ta saki mai hade da kuka-kuka ta tashi ta shiga toilet din sadiq shi kuma ya bita da kallo ruwa ta d'ebo a babba boll na  roba tasa towel a ciki ta dawo d'akin har yanzu idanuwan sadiq na kan fatuha ko qif tawa bayayi, sai da ta qaraso gaban shi ya lumshe ido aje boll din tayi a gefen bedside drawer idanuwanta  taf  da  hawaye cikin nutsuwa ta shiga matse towel din a hankali ta nufo towel din goshin sadiq ta fara dadanna masa kamar yadda inna ke mata idan tana masasara,  ko ina na jikinsa take  bi inda ke bude tana danna masa towel din a hankali fever ta fara sauka shi kanshi Sadiq yaji dadin jikinsa sai dai dan dumin da jikin yayi bacci ne ya fara fisgar shi kafin ka ce me bacci ya kwashe shi, sai fatuha dake ta faman dannamasa towel.
      A hankali ta fara gyangyadi dan ta fara jin bacci, sai bacci ya fisgeta sai firgigit ta tashi ta cigaba sai da bacci yaci karfin ta, ta fada fadadan qirjin sadiq bacci ya kwashe ta.

         Kiran sallah asuba ne ya tashi sadiq a hankali yake bude sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha da ke bacci male-male a qirjinsa gashin kanta ya baje saman qirjinsa ta  kankame sa, matsar da gashin kanta yayi gefe yana qarema fuskar ta kallo, har mamaki wayau irin na fatuha yake gata qarama amma sai dai tana da halin manya, kasa  dauke  idanusa  yayi  kanta, yunqurin tashi yayi yaji ta motsa komawa yayi ya lumshe ido yayi  lamo kamar mai bacci.
         tashi fatuha tayi tare da ware ido ganin  ta  jikin  sadiq  kwace a  zabure ta  mike  tsaye ta ce "Nashiga uku yaushe bacci ya kwashe ni? wayo Allah na da mai kyau ya tashi ya ganni dana bani" hannu ta kai goshin sadiq jin ba zafi yasata sakin ajiyar zuciya ta  furta, "Alhamdulillah jikin yayi sauki bari nayi sauri na d'auro alwala" part din ta bari ta wuce nasu.

      Alwala kawai ta dauro ta gabatar da sallah, bayan ta idar ta tsaya lazumi da bita qaratun ta saboda anjima da rana malam zai amsa.

     Fatuha na fita sadiq ya ware idanuwan shi tare da ta6e baki ya yunqura zai  tashi  yaji hannu shi yayi zafi, sai a lokacin ya tuna da ledar ruwan da aka qara masa har ruwan ya qare ga hannu ya kunbura, ya manta shaf bai cire ba yaye blanket din jikinsa yayi ya shiga bathroom sai da yayi wanka ya fito sanye da bathrobe da qaramin towel a hannu shi yana goge sumar shi da hannu daya, saboda  d'aya hannu namasa
zafi  sosai.

    Lokacin yayi dai-dai da turowar kofa waigowa yayi yana kallon kofar, fatuha dake bakin kofa itama shi take kallo tana  hamdallah  ganin  ya  warware kauda kai tayi tare da cewa, "ina kwana.! amsa mata yayi babu yabo babu falasa qoqarin fita take ya ce "Fatuha.! juyowa tayi tana kallon sadiq wanda shi ma ita yake kallo ya ce "thanks for the caring" murmushi fatuha ta saki duk da bata ji abinda yace karshe ba ta gane mai yake nufi da Kalmarsa ta farko  qarasa fita tayi shi kuma ya cigaba da aikin  gaban shi.

     Yau ma kamar jiya har yanzu rabi'a bata zoba har hankalin fatuha ya fara tashi da rashin  zuwan nata, shara tayi da wanke-wanke sannan ta fera dankali ta soya ta juye a kuloli tare da kwai sannan ta daura ruwan zafi ya tafasa ta juye kamar yadda rabi'a keyi, haka tayi har su ola sai da ta basu nasu, amma har yanzu lamarin rabi'a na bata mamaki zuba kayan abincin sadiq tayi a tray ta aje a dining area sannan ta shige bedroom ta cire kayan baccin dake jikinta ta shige bathroom tayi wanka tana fitowa mai ta shafa tasa material  red mai ratsin golding a jiki masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba, daure gashin kanta tayi da yar kibiyar soke gashi sannan ta fesa turare  mai kamshi sannan ta fito daga bedroom,

       Direct dining area ta wuce ta  dau tray din  kayan abinci sannan ta wuce part din Sadiq, a hankali ta tura kofar bedroom din kishingide ta ganshi saman bed yana sanye da riga da wando riga mai dogon hannu red mai ratsin black sai jeans blue ba qaramin kyau yayi ba, fuskar nan tashi tayi fayau cikin sallama fatuha ta shigo, amsa mata yayi a taqaice aje tray din tayi a stool,

      Sannan tace, "Mai kyau ya jiki ?" amsawa yayi cikin cool voice dinsa, "jiki da sauki fatuha"
       "to Allah ya qaro sauki" sannan ta zauna saman sofa tana facing din sadiq wayarsa ce dake saman bedside drowe ta fara ruri hannu ya kai ya dauka sunan da ya gani jikin screen din wayar ya sasa smile,

   Daga daya bangaran Aunty bilki ta ce, "Hello baby, ya kake ?"
       "lafiya lau Maman Hanan"
  "ya naji voice naka wani iri?
"yanzu na ta shi daga bacci" ya fada a taqaice, murmushi tayi daga d'ayan bangaran ta  ce, "bari na baka jidda tun jiya  take matsamin tayi missing naka kai da fatuha" smile sadiq yayi wanda ya bayana fararan hakuran shi miqawa angel wayar Aunty bilki tayi ta  ce, "daddy.!
    "yes my princess,"
"dadd I miss you"
      "miss you more angel"
"daddy yaushe zaka zo d'auka na?
    "sai end of this week angel"
   "yeee daddy love u dadd ina Aunty fatuha?
    "gata nan kusa dani"
"please daddy ka bata muyi magana I miss her"
     "ok Angel lemme give her.

     Fatuha dake zaune saman sofa sai smile take saboda ta gane da jidda sadiq yake waya, saboda da ita kadai yake waya yana smile ko Mom miqa mata wayar yayi ta kara a kunne cike da jin dadi ta ce, "Jidda.!
      "na'am Aunty" dan bata fuska fatuha tayi hakan ya  fito mata da sak yarintar ta ta  ce, "jidda haka ake ki tafi ki barni ni kadai a gida dan Allah ki dawo kin ji,"
      "laaa Aunty baga daddy ba baya tayaki wasa? ai daddy ya iya wasa" dago ido tayi ta kalli sadiq da shima din ita yake kallo ta hadi wani yawu tace cikin zuciyar ta gaskiya jidda ba hankali ina ni ina wasa da sangami mtww Aunty da jidda ta ce ne ya maido da fatuha daga dogon tunanin da ta tafi sun dade sosai suna waya da jidda har mamaki fatuha take yadda suka dade kamar ba kudi ake dibaba.

      Miqawa sadiq wayar tayi tare da qoqarin bude kulolin abincin dake saman stool, saving nashi ta shiga yi chips n egg sai farfesun yan ciki dake ta zuba kamshi ni kaina ganin qoqarin fatuha nake dan yanzu baza ta wuce 14 years ba, bayan ta kamala saving din nashi ta miqamasa plate din hade da fork amsa yayi yana qoqarin daukar fork din da hannu amma ya kasa saboda hannusa yayi tsamin, daurewa yayi zaiyi ta maza ya ci da hannu kan dole amma ya kasa fatuha na lura da yadda yake matsawa kansa taimakamasa tayi ta amshi plate din sadiq ya bita da kallo debo chips din tayi ta kai masa baki duk da tana gudun tsinki na sadiq aiko taci za'a ba musu ya amsa haka ta cigaba da feeding din shi yana amsa har sai da chips din ya qare sannan fatuha ta saurara masa, shi  kansa  ya  ga  qoqarinsa  na  cinye  abincin  raban  daya  ci  abinci  kamar  haka  har  ya  manta, tana qoqarin qaromasa, zaro ido sadiq yayi waje ya ce, "fatuha wazai ci wannan?
"kai mana"
   "lallai to wannan din dakyar na daure na  ci shima, anfada maki kowa irin kine acici" harara fatuha ta aika masa tana qoqarin tashi riqe hannu ta yayi ya ce, "sorry.!  Sororo fatu  tayi  ji  abin  sadiq  ya  ce,  murmushi ta saki sannan ta dau plate din chips din tana ci.

      Rayuwa na tafiya komai na gudu kwanakin da sadiq ya dauka yana rashin lafiya duk wata dawainiyarsa fatuha ce kulawa  fatu ke basa sosai  na  ban  mamaki, hakan yasa wata irin shaquwa ta shiga tsakanin su da sadiq a yanzu jin fatuha yake kamar qanwar shi hakama itama fatuha kusan yanzu kullun suna tare sai dai idan ya tafi aiki ko masallaci, yanzu sosai fatuha ke jin dadin gidan haka shima sadiq duk wani tunani da damuwa ya ragu ba kamar da ba, har wata yar qiba yayi saboda fatuha bata barinsa da yunwa ko  damuwa  duk  wani  farin  cikinsa  ya tattara  kan  fatu  kuma ya  kasa  gane  mai  hakan  ke  nufi, dan yanzu kusan ita ke  feeding din shi duk wani abinci tana bashi tana masa hira har ya cinye bai sani ba yanzu  sosai  captain  yake  dariya  har  kyakyatawa  kullun fatuha sai tasa sa dariya da labaran ta haka rabi'a ma ta dawo ta amshi aikin ta ashe itama fever tayi.

     Daririkun dake tashi  a dakin sadiq ,ya sani tura kofar kar ayi ban dani fatuha ce sanye da rigar sadiq ta uniform na wajan aiki ala dole sadiq take  kwaikwaya yarda yake  da dariya Sadiq ya saki  tare da matsowa kusa da ita ja mata hancin yayi tare da cewa "Fatuha baki ji ko?" dariya ta saki ta ce "Mai kyau ai haka kake yi idan kasa uniform" ta ida zancan tana qoqarin fita daga bedroom din riqe hannu ta yayi ya ce  "Anjima ki shirya zamu je dauko angel" tsale tayi tare da rungume sadiq tana dariya shima din rungume ta yayi yana smile dan sakin sadiq tayi ta ce "Wallahi da jidda bata nan gidan ba dadi"
      "ko.!
"eh mana"
  "ok oya kije ki shirya ki cire min kaya" bata fuska sadiq yayi ya ce, "2days dinnan kin fara rai nani Allah," turo baki gaba fatuha tayi ta ce " Yi hakuri" smile Sadiq yayi ya ce, "wannan bakin naki ya iya ba da hakuri kuma ya iya rashin jin" zame wa tayi daga jikin sadiq  ta fita tana saukowa downstairs ta hango baba jummai na shigowa da kaya niqi-niqi wani irin ihu ta saki ta ruga da gudu wajan ta ta rungume ta, sadiq da ke qoqarin shiga toilet ya fito da sauri ya rife part din shi chak ya tsaya a up stairs yana mamakin rashin hankali na fatuha guntun saki yaja ya juya, a  tunaninsa  wani  katon abune  ya  faru har  sai daya  rasa  nutsuwarsa  ta  wucin  gadi ajiyar  zuciya  ya  saki.
        kallo baba jummai tabi fatuha da shi kirjinta  na  dukan  tara-tara tana mamakin rigar da ta gani jikin fatu  gashi ta wani  sauya  tayi  6ul6ul  wani miyau  ta  hadiya  makwat ta danyi murmushi  wanda iya Karshi le66anta  fatuha ta katse mata tunanin da cewa, "baba shikenan sai ki tafi ki barni  ni kadai a gida nan?
Baba  jummai  ta  ce, "dan Allah yi hakuri fatuha wallahi hidimomine suka min yawa kuma bada niyar dadewa naje ba, niyata nayi kwana biyu na dawo"
      "toh shikenan bari nayi sauri nayi wanka dauko jidda zamuyi daga gidan Aunty bilki"  toh baba ta ce tana  kara  tsuma  da  danasanin  barin  fatu  gidan  basu  tafi  tare  ba  ashe jidda  ma  bata  nan  wani  abu  da  hadiya  mai  daci fatuha ta wuce bedroom baba jummai ta bita da kallon tuhuma Allah ya rufa asiri ta  furta  jiki  a mace sannan ta dau ledar tsarabar kayan miyan datayi ta shige kitchen.
Written by
Salma mas'ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_* [email protected]

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

65_66

Bayan ta tsala wanka ta shafe jikin ta da lotion mai kamshi da sanyi dadi, riga da sket tasa na atamfa mai ratsin pink green blue masha Allah kayan sun mata kyau, sai suka qara fitowa da haskyan ta daura dan kwali tayi ya zauna sosai a kanta, ta jawo green veil din ta sa sannan ta zura takalman ta black tare da fesa turare, bayan ta kamala ta fito daga bedroom parlour ba kowa sai kamshin girki baba jummai da ke ta tashi.

Part din sadiq ta wuce a hankali ta bude kofar parlour, ba kowa sai sanyi AC dake tashi cikin nutsuwa ta nufi bedroom ta burda handle din kofar tsaye ta hango sadiq gaban dressing mirror yana sanye da blue riga mai gajeran hannu sai blue jeans ya gyara sajan shi yayi luf-luf haka sumar kanshi ta kwanta yayi kyau sosai har ya gaji juyowa yayi su kayi ido hudu da fatuha kashe mata ido yayi ya ce, "kallon fa? murmushi tayi ta kauda kai tana qoqarin fita ya ce, "wallahi kika fita ban zuwa da ke" make kafada tayi tare da qarasa shigowa murmushi yayi ya ce, "Good girl" yana qoqarin saka mabalin rigar shi bayan ya kamala ya dauki car key dinsa da wayan shi dake bedside drawer ya nufo inda fatuha take ya ce, "inyee yan'mata ansha kyau ashe dai yan kauye sun iya gayu" dariya fatuha tayi ta rufe fuskar ta tana aika masu wani irin kallo tattausan murmushi yayi ya ce, "oya tashi mu tafi" a tare suka fito daga part din shi lokaci yayi dai-dai da fitowar rabi'a zata tafi gida kallo tabi so da shi tana mamaki yaushe sadiq ya fara wannan wasan chab ta furta, koma dai minene ai fatuha yarinya ce akan yan'matan dake masa layi kumama ko giyar wake yasha abinda take tunani ba shi bane dan babu abin sadiq zaiyi da fatu watsar da zancan tayi tare da yin gaba fatuha ce ta kira sunan ta, rabi'a waigowa tayi a dan tsorace tare da sakin murmushin da iyakar shi la66anta fatu ta ce, "har zaki tafi?
"eh wallahi na gama aiki na kuma dama gashi baba jummai ta dawo"
"toh ki gaida gida"
"gida zai ji" fatuha ta sakai ta fita.

Suna fitowa kallo ya koma kansu ola jiki na bari ya nufo sadiq har qasa ya gaisheshi Emeka da Sunday duk sai da suka kwashi gaisuwa, sannan ya bude murfin mota ya shige haka ma fatuha ya ja motar suka bar harabar gidan, cikin nutsuwa yake driven din waigowa yayi ya kalli fatuha da tarakufe guri daya ya ce "Fatuha.! Cikin tattausan muryarsa
ta ce, "na'am.!
"yau anfito bude ido ko? dan smile tayi ta ce, "tunda nazo birni wannan ce fitana na biyu"
"ai gara haka saboda bana son to much of yawo, uhm kina san karatu? saurin d'aga kai tayi sadiq ya ce, idan na saki school kina so" jinjina kai fatu tayi cike da farin ciki, "zaki iya karatu kina kulla da angel zaki iya? saurin d'aga kai tayi ga farin ciki shinfide a fuskarta ta ce, "insha Allah" murmushi sadiq ya saki mai taushi ya ce, "insha Allah zan saki kin ji," lokacin yayi dai-dai da tsayawar motar su bakin geta din gidan Aunty bilki horn yayi mai gadi ya bude masu ya kunna hancin motarsa.

Dai-dai parking space yayi parking tare da kashe motar, fatuha ta 6ale murfin mota ta fito shima ya fito yana gaba fatuha na bayansa knocking din kofar sukayi baba larai ce ta bude masu washe da baki har qasa ta gaishe da su sannan ta basu hanya suka shigo, cikin sallama Aunty bilki da ke parlour zaune saman three sitar tana kallo washe da baki ta amsa tana cewa, "sannu da zuwa baby" saman two sitar ya zauna fatuha kuma ta zauna a qasa kusa da sadiq tare da gaishe da Aunty bilki, cikin fara'a ta amsa kwalawa baba larai kira tayi ta kawo masu kayan motsa baki aiko ko 5 minute batayi ba ta dawo riqe da tray cike da kayan motsa baki ta aje gaban Sadiq, kallon fatuha yayi dake zaune gefan shi a qasa tayi shuru itama shi din take kallo harara ya aika mata ya ce, "tashi ki zauna a kujera" Aunty bilki smile tayi ta ce, "aiko dai tayi zaune qasa abin ta, ni ban ma gane ta ba wallahi, naga ta girma sosai raban dana ganta tunda su mom suka tafi yau kusan 2month kenan, jiyama mukayi waya dasu Mom insha Allah ranar Friday zasu dawo tare da yaya jawad"
"aini fushi nake da su sun barni ni kad'ai a gida ai sun kyau"
"dama shagwabar ka ta ishemu ya kamata ka zo kayi aure haka naga har wata yar qiba kayi" fatuha dake zaune saman one sitar ce ta kalli sadiq shima ita yake kallo ji tayi gaban ta ya yanke ya fadi da furicin Aunty bilki kauda kai tayi tana jin jikita yayi mugun sanyi Kallon ta Aunty bilki tayi ta ce, "na aiki su Hanan ne amma yanzu kinga sun dawo" bata ida rufe bakin ta ba suka shigo da gudu angel ta fada jikin daddy murmushi Sadiq ya saki jidda ta ce, "daddy I miss you"
"miss you more angel" kissing d'in kumatunta yayi itama tayi masa Hanan cikin fara'a ta nufi fatuha Basma kuma na gefe tsaye tana satar kallon sadiq kasancewa ta zo hutu gidan Aunty bilki, gaishe da sadiq sukayi ya amsa a takaice sannan Hanan taja fatuha suka wuce dakin ta angel kuma na maqale da daddy.

Suna shiga d'akin Hanan Basma ta cire mayafin kanta ta fada saman bed, itama Hanan bed ta hau fatuha kuma ta zauna saman sofa Hanan ta ce, "laa fatuha baki zama saman bed"
"a'a barni a nan ma yayi wallahi"
Hanan ta ce, "Basma kinga wadda nake fada maki mai gashin nan" d'ago kai tayi ta kalli fatuha ta d'an yi smile ta ce, "sannu ki fa"
"yauwa" cewar fatuha hira suka shiga zubawa kasancewar duk sa'anin junane amma dai Basma ta dan girme su dan yanzu ita SS2 zata Hanan kuma SS1 kunsan a tare suke komai da Hanan da basma duk da Basma Aunty ce a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login