Showing 3001 words to 6000 words out of 105783 words
nuna mata da baki ta ce, "kin tuna abin da ya mana jiya?
"qur'an ina sane wallahi ai ban yafe mai ba, kawo kunnan ki kiji abinda zan mai" magana su kayi a kunne (wadda ko ni salma banji ba) sannan suka kwashe da dariya fatsima ta ce, "kai fatuha billahilazi hiyasa nake sonki wallahi kin san maganin d'an iska" ta ida zancan tana daukar tulun ta fatuha tayi gaba haka suka jero suna tsokana sannan kowa ce tayi gidan su.
Tana shiga gida inna har ta sheka koko, nata na cikin kwannan samira ta Kafa kai ta shanye baffa ya fito daga uwar d'aka washe da baki ya ce, "yauwa yar albarka har kin gama d'ibar ruwan"
"eh baffa na gama kai nake jira mu tafi"
"to bari na d'ako fatanya na a buka sai mu wuce" to ta ce, ta ruga da gudu ta d'ako hijabin ta suka ma inna sallama suka fita.
*****
Sadiq ne ya fito daga toilet sanye da bathrobe a jikin shi ahankali ya leka fuskar Jidda da ke bacci yana shafa kanta, ahankali ya kai mata kiss a goshi, bud'e ido tayi ta sakar mai murmushi ta ce, "daddy good morning"
"morning sweetheart oya tashi muje ayi wanka"
"tam papa.! d'aukar ta yayi suka shiga toilet ya wanke ta tas suka fito yana mata cakulkuli tana gantsarewa tana dariya ta ce, "daddy please stop"
"naqi dear ba daddy zaki ma wayau ba"
"no daddy ba wayau zan ma ba fa"
"to menene to.!
" uhm wani abu" ta ida tana hada hancin ta dana sadiq, kamar an mintsile sa ya ce, "oya tashi na shirya ki"
"tam papa" mai ya shafa mata ya sa mata jeans blue and pink t-shirt mai kyau da manyan flowers ya raba mata gashin ta gida biyu ba k'aramin kyau tayi ba Masha Allah peck ya mata a kumatu ya ce, "oya wuce wajan grandma, gani nan zuwa dana gama shiryawa"
"to daddy" ta fita da gudu ya bita da kallo shiryawa yayi cikin kakinsa na sojoji tare da gyara sumar sa ba K'aramin kyau yayi ba wow duk inda namiji ya ke to sadiq ya kai, briefcase nashi ya d'auko wanda ke gefen gado tare da ficewa dinning area ya nufa.
"Mom good morning "
"morning son how was your night?
"cool Mom and your's? ya ce tare da kai mata peck kumatu ta ce, "the same"
"good" atsaitsaye yayi break saboda ya kusa makara ya fita yaran shi suka fara qamewa tare da miqa gaisuwa motar shi wadda tasha wanki benz fara mai daukar ido ya shige yaron sa ya rufe suka fice daga gidan.
*****
Baffa da fatuha ne a gona sai aiki suke cikin jin dadi fatuha na ma baffa hira, sosai ya ke jin fatuha a ranshi fatuha ce ta katse shurun da cewa, "baffa zanyi fitsari"
"to fatuha ki qarasa can gefe kiyi kin ji, ki kulla da kafar ki"
"to baffa" ta kutsa kai cikin gona sai da ta tabatar baffa baya hangen ta sannan ta lalla6a ta qara shigewa jejin wani sasak'e icce ta d'iba ta kule a leda, tana dariya ta matse azanin ta baffa da yaji shure ne ya fara kwala mata kira da gudu ta qaraso tana cewa, "baffa gani" tana hakki
"yauwa yar albarka yo Ina kika shige yin fitsarin" baki ta washe ta qara gyara zanin ta hannuta ya ja suka zauna suna cin dumaman tuwon da inna ta aiko masu da shi suna gama ci bacci ya kwashe fatuha baffa ya ce "ikon Allah har kinyi bacci kenan.. ya tashi ya cigaba da aikin shi.
*****
Cikin natsuwa yake aikin shi a office, office d'in Masha Allah sanyi AC sai ratsawa yake sosai, abokin shi majid ne ya shigo dauke da sallama ya ce, "ah big man ashe ka shigo"
"yap tun 8:00am.. hannu ya mika masa suka gaisa ya samu guri ya zauna ya ce, "big man ya Mom and sweetheart?
"lafiya lau yauma rigima tamin zata biyo ni taga uncle majid"
"Allah sarki me yasa baka zo min da ita ba"
"haba wallahi tana zuwa nan zata cikani da to much of surutu"
"uhm kai dai ka sani mutun sai muskilanci"
"naji d'in idan wannan surutun ya kawo ka to ka fita"
"to ban fita tunda ba kaika kawo ni ba" shuru sadiq yayi ya cigaba da aikin shi kiran sallah la'asar ne yasa suka fito su kayi sallah suka koma.
bashi ya dawo gida ba sai 5:30pm part nashi ya shige ya yayi wanka ya wuce bedroom din Mom zaune take sama sofa tana karanta azkar yayi sallama ya mata peck Jidda ce ta rugo ta bashi hug ta ce, "dady I miss u"
"miss u more dear..!
After ya gama lunch ya shirya Jidda da kanshi ya ja hannu ta suka je parking space, yaran shi har sun taso ya d'aga masu hannu alama su kad'ai zasu kaitsaye gidan Anuty bilki ya nufa.
Dai-dai wani madaidaicin gida su kayi parking mai gadi ya wangale masu gate, Masha Allah gidan ya had'u sosai plat ne mai kyau su hannan na filin gida suna wasa ganin uncle sadiq ya sasu rugawa aguje suna mai oyoyo, ya chabe su yana masu wasa tare suka karasa palour Maman hannan na ganin shi ta washe baki ta qwalawa talatu kira ta kawo mai abin motsa baki, dangin su fruit da sauran su har k'asa talatu ta duk'a ta gaishe shi Aunty ta ce, "ah baby yau kai ne a gidan nawa hala Mom ce tace ka zo to yayi" smile yayi ya ce, "oh kina nufi ban zuminci ko?
"kamar hakan dai"
"a'a aunty ke ma kin san bana zaman a naija sosai, but now na dawo Nigeria zanrinqa zuwa har saiki gaji dani"
"toh shikenan Allah yasa da gaske kake"
"haba anuty billy" ya ida zancan yana shagwabe fuska "ohni baby wai yaushe zaka daina shagwaba, duba fa har da d'iyar ka budurwa" dariya ya fashe da ita, "ni dai sister kin samin ido wallahi" sannan ya kora lemo "toh naji na daina"
"uhm wai ina mai gidan"
"bayanan yana dubai"
"ok..
"sai end of this week zai dawo"
"Allah ya maido shi lafiya"
"ameen" hira sukai sosai da yar 'uwarsa Kiraye-kirayan sallah magrib ne yasa suka tashi sadiq ya wuce masallaci.
********
Misali karfe 5:30pm har baffa ya gama komai a gona fatuha na kwance kamar maiyin bacci dare, saboda yasan halin ta in ta kwanta bacci bata san a tashe ta, yasa hannu ya d'auke ta har suka iso gida inna na ganin su ta washe baki, tare dayi ma malam sannu da zuwa tare da kar6ar fatuha da ke sharar bacci d'aura alwala baffa yayi ya tafi masallaci bashi ya dawo ba sai bayan isha'i, lokacin fatuha ta tashi tana cin abinci hira suka d'an ta6a sama-sama sannan suka wuce ma kwantan su Inda fatuha ta matsu gobe tayi dan ta aikata abinda ke ran ta.
*****
Bayan isha'i sadiq ya dawo yayi sallama da sister nashi sannan ya raba ma su hannan tsarabar su, karku so kuga murna wajan su bayan sun fito haka ya biya da Jidda wajan shan ice cream ya mata siyaya sosai sannan suka dawo, tun akan hanya ma bacci ya d'auke jidda dan haka tana kwance a kafad'ar shi cikin sallama ya shigo Mom na palour tana kallo ita da baba jummai, baba jummai ce ta tashi washe da baki tare da amsar jidda shi kuma ya wuce dakin shi yasa ice creams din a fridge.
Baba jummai tana zuwa d'aki tayi ma jidda wanka ta samata night dress nata blue riga dai-dai gwiwa, shima yana zuwa d'aki wanka yayi saboda ya gaji sosai ko da ya fito Mom har ta shinfid'e jidda saman bed kayan bacci shi yasa tare da jawo laptop din shi yana shan coffee ya dad'e yana aiki sannan bacci ya dauke shi.
****
Kiraye-kirayan sallah asuba ne ya tada fatuha bakin ta washe ta ce, "kai narantse da Allah jiya da kyar bacci ya suran yadda na matsu yau tayi, wallahitalahi yau Rabi'u sai ya gane kuran shi qur'an ciki sauri tatashi tayi sallah.
Yau dai ba laifi fatuha ta taya inna aiki sosai ba dan komai ba sai dan tabarta ta fita, saida suka gama komai ta gyara zaman zanin ta wadda kullun jiya na leda na habar zanin ta sannan ta ce, "inna zani gidan su fatsima"
"to fatuha karki dade"
"to inna.. ta fita da gudu gidan su fatsima ta shige inna fatsima na tsakar gida tana wanke-wanke gaisheta tayi ta amsa da cewa, "fatuha ya inna"
"inna lahiya lau"
"ki ce ina gaishe ta inkin koma gida"
"to za ta ji inna, ina fatsima?
"tana uwar d'aka" fatsima da ke shara bacci saman tabarma fatuha ta d'aka mata bugu ta ce, "ke tashi..! firgigit ta tashi "kai fatuha.."
"ke banza tashi muje"
"oh na tuna fa Qur'an ban san sanda bacci ya sure ni ba" dankwalinta ta daura suka fita suna tafe suna tsokana dai-dai wata gona suka ci birki Rabi'u ne gindin bishiyar mangwaro da alamar rake ya gama sha bacci ya dauke sa saboda duk ga abin rake zube, lafewa fatuha tayi jikin bishiyar bedin ita da fatsima suna lekyan shi fatuha ta ce, "fatsima bilahillazi yayi bacci" ta kwashe da dariya "ai sai ya ci uba sa" qulin leda ta ciro daga habar zanin ta ta nufi Rabi'u cikin sand'a ta bud'e ledar ta zuba masa tana k'ok'arin rugawa da guda bayan bedi Rabi'u da ke bacci cikin bacci ya fara jin rad'ad'i na susa ba arziki ya tashi yana soshe-soshe, yayi zuru-zuru su fatuha da ke bayan bishiya sai dariya suke sannan suka fito daga nesa dashi ta tsaya ta kwalamasa Kira ya waigo ta ce, "ai dama na fad'a ma kwarankwatsi ba'a buguna na hakura" fatsima ta bushe da dariya ta ce, "ka je gida mai tafasa tama magani kaji rabe' dagowa yayi idanun shi sunyi jaaa saboda azaba ya ce, "bala'iiiii zan ci uban Ku dama kune kuka fesa min asosa? narantse na sha magani sai na zo har gida na ci uban ku"
"yo zancan banza, ka zo muk'arama wani" injin fatuha taja hannu fatsima suka bargun suna dariya shikuma Rabi'u na soshe-soshe
CAPTAIN SADIQ
👮
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
blood sister deejah
Follow me on wattpad: salmamasudnadabo
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
7_8
Rabi'u yasha wahala sosai idanun sa sunyi jawur sai ihu yake, ado ne zai wuce ya hango shi yana birgima ya qaraso da sauri garesa yana Cesar, "subhanilillah lahiya Rabi'u me ya faru?
"fatuha ce..? yana ihu haka malam ado ya taimaka mai ya kai shi gida jikin nan nashi yayi jawur abunka da bafulatanin mutun, inna maitafasa tana gyaran tafasa taji sallamar Malam ado ta tsame hannu ta dake cikin tafasa ta yafa mayafi ta leka waje ganin malam ado rik'e da Rabi'u ta ce, "lahiya Malam ado me ya sami Rabi'u ni?
"nima dai ban sani ba amma da alama sosa ce"
"toh fa kai ko Rabi'u mai ya had'a ka da sosa garin ya haka ta faru? ta ida zancan tare da riqe haba zani tana matse kwalla cikin murya wanda yasha wahala ya ce, "inna wallahi fatu ce da wannan iskancin"
"bala'i kambuuu alqawalin Allah ban yarda yau sai naga uban ta jauro billahilazi" ta ida zancan tana yarfa hannu sama Malam ado ya ce, "a daiyi hakuri yarinya ce"
"yarinya uban wa? Mai tafasa ta k'arasa maganar da dafe qirji ta ce, "yarinyar da aure yau haihuwa bad'i shegiyar yarinya mai kama da mayu duk ta adabi mutanan kauyan nan da bakin halinta, wallahi Malam ado ban hakura shigo da shi namasa magani na je na samu uban nata, haka aka, shigowa yayi da Rabi'u yayi zuru-zuru aka shinfide shi bisa tabarma.
"Qur'an fatuha baki da mutunci"
"yo ni ta wasa ce ai dama na fad'a maki saura malam D'alha ai qule nake da shi kwarankwatsi"
"hehe kai qawata ina san ki qur'an" fatuha ta washe hak'ora"
Ta ce, "nima haka billahilazi" haka suka dawo gida ko da suka dawo gida fatsima gida ta wuce gidan su fatuha ta shigo da sallama yau zuciyar ta fes take da farin ciki inna da ke shara ta amsa sallamar, ta kauda kai ta ce, "yanzu dan Allah fatuha kin kyauta kenan tunda safe da kika fita sai yanzu zaki dawo? bata idaa rufe bakin ta ba mai tafasa tayi sallama cikin tsiwa inna ta amsa fad'owa tayi cikin gidan da masifa ta ce, "keeeee!! ta cakumo wuyan fatuha inna ta ce, "lahiya mai tafasa?
"lahiya kenan bari uban ta jauro ya zo billahilazi yau ban yarda, kuma duk abinda ya samu d'ana ke ce ni zaki kashe ma d'a har kin isa to baki isa ba" inna sai bata hakuri take amma taqi sakin fatuha wanda tayi wiki-wiki da ido dan tasan tayi, baki ta turo gaba take ce, "ke ki cika ni..! tare da finci ke kanta daga ruqwan da mai tafasa ta mata cike da rashin kunya da tsiwa ta ce, "yo ba d'an naki bane jiya ya bige ni ba, kuma na rama yau" ta ida zancan ta murguda baki "dan uban ki idan zaki rama saiki sa mass asosa? inna ta ce, "fatuha ince jiya ban maki magana ba?
" yo inna jinayi ban iya hakura" ta fada cikin tsiwa haka maitafasa ta gama zage-zagen ta da kumfar baki ta fice acewarta in Malam jauro ya dawo zata zo ta same sa.
*****
"Daddy please muje shan ice cream"
"sweetheart akwai a fridge muje na baki"
"ok papa thank you" ya lakace mata hanci ya ce, "that is my angel" ta washe hakora part nashi ya kaita ya bata ice cream shi kuma ya shige gym room nashi ya dad'e yana gym sannan ya fito riqe da towel a hannu shi yana goge zufar fuskarsa, gefen da Jidda take ya kalla har tayi bacci ahankali ya karasa saitin fuskarta yayi kala tausayi a hankali cikin murya mai sanyi ya ce, "my angel I now you miss your Mom sam baki samu d'umin uwa ba, why KAUSAR me yasa kika tafi kika barni ni da Jidda why kausar..! yana maganar kamar zautace yana share hawayan fuskarsa y'all ce, "I miss you more my wife naso ace yanzu kina ganin angel my wife, dake take Kama sosai naso ace tare zamu bata good caring ya kai lips din shi dai2 goshin Jidda ya mata peck
*Asalin labari*
Malam idi zaunan d'an kauyan Kano ne wato rano su fulanine sosai Allah yayi ma malam idi rufin asiri, dai2 gwargwado yana kiwon shanu sosai, har ma da kaji gashi mutumin kirki shiyasa kowa ya sanshi a kauyan rano, yana da mata tani sosai yake san tani Allah ya basu ya'ya 3 maza 2 mace 1 kabiru shine babba mai bimai Ibrahim sai rukayya.
Zaune suke zaman lafiya cikin kauyan inda lokacin kabiru ke aji shida na secondary, shi kuma Ibrahim aji 5 rukayya na aji 3, sosai suke karatun su saboda Malam idi mai san karatune.
Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau garin rano zaman lafiya yayi qaranci, saboda 6arayi na zuwa su kwashe ma mutun dabobi sannan su kashe ka da iyalan ka, Malam idi ne ya shigo gida cikin sallamar shi tani da ke wanke-wanke ta amsa ta ce, "ince dai malam lafiya"
"wallahi tani kauyan nan ba lafiya" kabiru da ke uwar daka ya leko sukayi tsaitsaye can idi ya yanke shawarar saida dabobin shi su koma birni cikin garin Kano, ba yarda idi ya iya haka ya saida shanun shi cikin ikon Allah ya samu kudi mai yawa ya sama masu madaidaicin gida a rijiyar zaki, sannan yaba abokin shi Malam tanko kudi wanda ke birni ya siya masa shago a kasuwa kwari a zuba komai a ciki.
ya tataro iyalan shi suka dawo cikin garin kano, lokacin Ibrahim ya gama secondary da yake Ibrahim yaro ne mai san karatu result nasu na fitowa ya samu admission a biyuke, idan yake karanta business admin shikuma kabiru ya cigaba da kasuwancin sa tare da mahaifin su sosai suke samun rufin asirin su.
Kwanci tashi asarar mai rai yau Ibrahim ya gama karatun shi inda ya samu aikin kwangila sosai yake samun cigaba, inda ya had'u da Hauwa'u sukayi auran soyayya ankai amarya rijiya zaki kusa da gidan kabiru inda yake zaune da matarsa Aisha tsakanin amarya da Ango soyayya sosai suke zubawa, bayan wata biyu hauwa'u ta fara laulayi sosai take samun kullawa wajan mijin ta da surukar ta, har ma da Aisha matar kabiru lokacin rukayya na FCE cikinta ya shiga watan haihuwa bata wani sha wahala ba sosai ta haihu d'an ta mai kyau sosai ibrahim yayi murna sosai.
Kwana bakwai