Showing 12001 words to 15000 words out of 105783 words
ke ma in zaki ci ki zo muci nasan kishi kike mun ware ki ke kad'ai" murmushi inna tayi ta zauna suka cigaba da kalacin..
****
Misalin karfe 1:00pm flight d'in su Alhaji ya sauka Kano, a hankali yake takowa ta matatakal jirgin da ka gansa kaga babba mutun sanye yake da shada blue babba riga anmata aiki da dark blue zare sosai d'inkin ya haushi yayi kyau.
sadiq na jingi ne jikin motarsa black Benz kasancewar shi ya zo d'aukar Abba, qad'an-qad'an ya duba agogo d'ago kai yayi yana kale-kale can ya hango Abba washe baki yayi ya qarasa da sauri ya rugume Abba ya ce, "I miss you.!
"Miss you more Son" tare da shafa masa gefan fuskarsa bud'e masa murfin moto yayi ya shige shima ya zagaya ya shige driver ya jasu.
Mom ce zaune a bedroom saman sofa tasha danqareran leshin ta green mai ratsin white flowers, anmata bubu da leshin mai kyau tasha d'auri ture kaga tsiya gashin ta ya leqo sai kamshi ke tashi ba qaramin kyau tayi ba.
dai-dai parking space driver yayi parking Alhaji ya fito shida sadiq yaran sadiq sai qamewa suke tare da kwasar gaisuwa wajan Alhaji, Washe da baki suka shigo gidan cikin sallamar su, Jidda da ke zaune a palour suna wasa da Jamal qanin Hanan d'an Bilkisu, da gudu Jidda ta rugo wajan grandpa ta rungum sa ita da jamal d'aukar su yayi yana cewa "Ah'ah my little grandchildren kun girma musanman angel, Angel me daddy ke baki? kin qara girma" Dariya tayi ta ce, "grandpa kullun daddy sai ya bani fresh milk da safe"
"good girl yanzu kin fara cin abinci kenan? washe baki tayi.
Mom ce ke takowa downstairs a hankali d'auke da murmushi a fuskarta, A hankali alhaji ya daga kai ya hadiya wani miyau mukut yana binta da mayen kallo (ohni salma tsohuwar zuma tatashi lol) Katse masa tunani tayi ta hanyar cewa, "Abban sadiq sannu da zuwa"
"Yauwa"
ya hanya?
"Alhamdulillah"
kun zo kun fara cika grandpa da surutu ko? Cewa aunty bilki da fitowar kenan daga bedroom washe baki su kayi su duka Anuty bilki ta ce, "oya ku wuce kuyi wasa"
Hanan ce ta zunboro baki ta ce, "Momi nafa girme su ni ai bana wasa"
"Toh yayi uwar mata"
Mom ta bushe da dariya tare da jan hannu alhaji suka wuce bedroom.
Ita da kanta ta taimaka masa ya cire kayansa ya shige wanka inda yake ta zuba mata soyayyya.
After 1hour Alhaji ne ke sakowa daga stairs shi da Mom sanye yake da jalabiya milk ya fito sak bafulatani glass na manne a fuskarsa dining area suka wuce lokacin kowa ya halara.
Mom ta jaa ma Abba kujera ya zauna itama ta zauna, Mom ta fara serving nasu lunch cuscus ne da miyar dankali taji kaji sosai aciki sai lafiyayan so6o mai sanyi ta zuba ma Abba cikin nutsuwa suke lunch inda sadiq ke feeding Jidda da Jamal.
****
Bayan sun gama kalaci fatuha ta kwashe kwani kan ta wanke, ta wuce gidan su fatsima suka wuce rafi, tafe suke suna tsokana dan har yanzu da suka fara irgandangi ba dai tsokanar su kayi ba, fatsima ce ta ce, "Fatuha kalli wancan ba d'an maigari bane da kandala"
"Qur'an shine ta6 aiko ya ja ma kanshi tona asiri taho mu qarasa"
Dan mai garine da kantala mai tallah suke aikata masha'a bayan bishiya da sauri su fatu suka qarasa cikin d'aga murya fatu ta ce, "asirrin ku ya toni bilahilazi kamar a gaban mai gari" cewar fatuha bala cikin sauri ya fara maida zariyar wandon shi yana zare ido kandala ta fara gyara riga zata d'au tulun ta .. Fatuha ta kada baki ta ce, "Qur'an ba inda zaku mun kama kwartaye ehe"
"keeee!! Ni sa'an kine zanci uban ku fa yana magana cikin borin kunya
Yar shewa fatu tayi ta ce, "bilahillazi Bala ka raina mana wayau mun Kama ku kuna iskanci shine dan baka da kunya zaka zagemu, toh Qur'an sai mun tona, dama rana nan na d'auki gyadar kandala tamin raini wayau to zan je na fad'a ma malam abinda kike in kin fito tallah..! Kwala kandala ta fara matsewa tana ba ma fatuha hakuri shima bala haka har ya masu Alqawarin zai basu murtala sannan suka hakura, suka tafi suna dariya.
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Blood sister deeja
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
17_18
After lunch sadiq ya kwashi su jidda da Hanan da Jamal zuwa shan ice cream sosai sunje yawo daga nan ya wuce dasu munjibir park, cikin jin dadi suke wasan su duk inda ka kalla a wajan yara ne da manya ke hutawa har ma turawa, resting chair ya samu ya zauna yana Kallan su Jidda yadda suke wasannin su cikin nishad'i daga nesa kuwa yan'mata sai yaba kyansa suke da tsarin shi wasu mamaki su kar dai ace duk yaranan nashi ne, dan iya kar haduwa sadiq ya hadu wasu ma sai jan su Hanan suke a jiki dan su samu damar yi ma sadiq magana ganin ba wasa a fuskarsa ya suka hakura basu suka bar munjibir park ba sai gab da magrib.
Dai-dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu jidda, Jamal kuma na kafadar sa yaran shi yayi ma alamar su kwaso kayan dake cikin motar su biyo shi da su, haka ko akayi suka kwaso kayan ba komai bane sai kayan zaqi kala-Kala da teddys da kayan wasa da ya saima su.
Anuty bilki na zaune a parlour saman three star Hanan ta rugo take fada jikinta ta ce, "Momi.!
"yeee yan'matan Momi sun dawo" bata ida rufe bakin ta ba sadiq ya shigo yana Cesar, "Ah sister ke kadai ce a parlour Mom fa?
"tana part din Abba"
"ok.! ina baba jummai?
"Tana kitchen"
"ok Hanan kira min rabi'a ta amshi kayanan ta kai maku su d'akin angel"
"OK uncle" rugawa tayi kitchen ta Kira rabi'a.. sanye take da farar riga mai dogwan hannu sai mini skirt da alama wannan kayan unform ne na yan'aiki.
Har qasa ta duqa ta gaishe shi tare da amsar kayan ta wuce da su bedroom d'in Jidda sadiq ya ce, "sister ni zan wuce masallaci may be sanda zan dawo kin tafi"
"Ai kwana zanyi a gida" waro ido yayi ya ce, "Gidan naki fa" yar shewa aunty bilki tayi ta ce, "ka manta mai gidan baya nan sai gobe zan koma"
"oh haka har yanzu bai dawo ba?
"eh.!
sannan sadiq ya sa kai ya fi ce zuwa masallaci.
*****
Duk wata gona dake da bishiyar mangwaro sai da suka leqa suka tsunko nunanu, daga nan suka biya wajan shafi'u mai rake suka amso bashi, acewar duk sanda bala dan mai gari ya basu murtala zasu biyasa bayan sunyi tafiya mai nisa fatsima ta ce, "Kai wallahi na gaji"
Fatu ta ce, "ai sai da nace maki mu zubar da ruwan tulun mu zuba mangwarayan mu cikin tulun, idan mun koma gida sai muce biyo mu akayi muka fasa dibar ruwan"
"kwarankwatsi ke dai fatuha wayau gare ki amma kinsan wani Abu"
"a'a saikin fada.!
"qara muje da ruwan Qur'an saboda mun dad'e"
"Haka kuma fa ga wancan Malam D'alha d'in sai sauri ya ke yaje ya fara zalinci"
"ke dai bari" ta qara gyara tsayuwar tulun ta
"kinko iya qarin jiya fatuha?
"hehe yo tun yaushe na iya shi, Ke nifa Malam D'alha ne baimun ba shiyasa bana bashi hada amma Qur'an na iya"
"toh bilahillazi yau sai kin bashi saboda yau ban shirya ma bugu ba, Ko bishiyar nan da muka hau na maqale duwawuna sai zinga yake" Fatuha ta kwashe da dariya ta ce, "Sai ki je gida kiyi gashi da ruwan d'umi Inmaki na maitafasa"
Cikin sallama ta shigo gida inna ta amsa, Inda Sabo ya kamata ta saba da wannan baqin halin na fatuha in ta je d'iban ruwa sai ta shekara bata dawo Ba.
"Inna Ina abinci na?
"yana madafi" kwanan samira ta jawo tuwo ne miya kuka yasha manshanu sai kamshi yake loma daya zuwa biyu tayi, fatsima tayi sallama cikin shirin ta na zuwa makarantar allo, tare suka zauna suka ida cin tuwo zata d'au hijabin ta kenan inna ta leko daga uwar d'aka ta ce, "yanzu saboda Allah fatuha sai na ce kiyi wanka zakiyi kome? raban ki da wanka tun shekaran jiya wuce kiyi wanka nan ku tai makarantar" baki ta turo gaba tana dire-dire "gaskiya inna ki bari sai na dawo nayi"
"Aifa baki fita sai kinyi wanka"
Da kuka da komai fatuha tayi wanka sannan ta fito suka wuce makaranatar allo.
Zaune suke a parlou suna hira cikin ni shadi su Jidda sai wasa suke aunty bilki ta ce, "Ku dai baku gajiya da wasa ko, Ince dazu ba manjibir park kuka je da uncle ba duk wasan da kukayi a can bai ishe Ku ba ko? Oya ku wuce ku shige bedroom kuyi bacci" su duka suka hada baki wajan cewa, "sorry Momi..! tare da lagwa6e kai duka parlou aka fashe da dariya.
Abba ya katse dariyar da cewa, "Yauwa gobe Ina so ku shirya da wuri zamu je family house meeting"
"Toh Allah ya kai mu Alhaji" inji mom sun dad'e sosai suna hira a parlour sannan kowa ya tafi part nashi, Inda su Jidda suka maqale ba su kwana ko Ina sai part din sadiq haka ko akayi da yake shi mutun ne mai son yara.
Bangaran su alhaji ko sosai suke zuba soyayya tare da gwada wa juna su yarda sukayi kewar junasu, sosai alhaji ke gwada ma Momi salan sa daga nan suka lula duniyar ma aurata.
*****
Zaune suke Malam Dalha sai amsar hada yake da zabgegiyar bulala shi a hannu, burin shi bai wuce ya ga su fatuha sun kasa ba ya wanke su da bulalar.
"Ke tashi ki bani taki hada" cikin tsiwa fatuha ta tashi ta fara karanta wa Masha Allah cikin murya mai sanyi da dad'i (ni kaina sai danayi mamaki wai dama fatuha ta iya karatu haka) Malam Dalha ko sakin baki yayi har ta gama sannan ya koma ya zauna gwiwa sage. lol
***
Tsale-tsale suke kamar ba dare ba cikin bedroom d'in sadiq wasan pillow suke haka shima ya shiga cikin su, wasan su ke cikin nishad'i haka shima sadiq ya biye masu shima kamar qaramin yaro suna haka har bacci ya kwashe su.
Ahankali yasa hannu ya bud'e wardrobe ya ciro picture d'in shi da kausar na maqale a qirjin shi a hankali wasu hawaye masu zafi suka zubo masa, yasa bayan hannu shi ya goge, bazai ta6a mance wannan ranar ba bayan sun gama wasan pillow shi da kausar suka je waje suna wasan ruwa, anan su kayi picture d'in da camera cikin sanyin murya ya ce, "I miss you my wife..! yana rungume da pic d'in har bacci ya dauke shi...
Written
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Blood sister deejah
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
19_20
Duk yadda Malam D'alha yaso ya daki su fatuha yau dai bai samu hanya ba har aka tashi.
Cikin sallama ta shigo gida, Baffa na tsugunne yana shanya zogala Washe da baki ta gaishe sa Baffa ya ce, "yar Albarka har kin dawo kenan?
"Eh Baffa na dawo"
"Masha Allah ana dai karatu dai ko?
"Eh Baffa"
"Ai haka ake so.! qoqarin cire hijabinta take ta ce, "Baffa ina inna?
"ayo ai yanzu inna ki ta leqa gida su fatsima baki had'u da ita ba?
"Eh..! bata ida rufe bakin ta ba sai ga inna ta shigo, sun dad'e suna hira sama-sama daga nan Inna ta shige madafi..
***
Bathrobes ne sanye a jikin su jidda suna ta tsale-tsale a cikin d'akin sadiq, a hankali shima ya fito daga toilet kamar wanda ke jin tausayin k'asa babu alamar walwala a tatare da shi kasancewar yau ji yake mutuwar kausar ta dawo masa sabuwa yaran ne suka had'a baki wajan cewa, "daddy morning.!
"morning too my little children" Fridge ya bud'e ya ciro fresh milk ya zuba masu a cup's kowa ya sha.
Anuty bilkisu ce ta shigo part d'in cikin sallamarta ita da rabi'a, sadiq na qoqarin ya shirya su Anuty Bilkisu ta shigo ta ce, "ah bros yaran nan sun hana ka hutawa ko?
"No.!
"oya ku wuce muje baba jummai na bedroom dina tana jiran ko"
"ok Momi..! suka fita a guje ....
Gyaran murya Anuty bilkisu tayi a hankali ta shafa gefen fuskar sadiq wanda ya lula cikin duniyar tunani, A hankali ya dago sexy eye's ball's din shi ya ja numfashi ya ce, "Sister..! tare da d'aura hannun shi saman nata, "baby wai meke damun ka ne uhm? gaba d'aya ka chanza yau a ganka da walwala gobe a ganka ba walwala" hawayan da ke maqale a idanun sa yayi qoqarin mai dawa ya qaqaro murmushi wanda iya karshi lips din sa ya ce, "sister ni fa ba abinda ke damuna"
"Toh shikenan naji mai yasa kake kora masu kula da jidda why? Kafi so ka cigaba da kula da ita da kanka ne? bayan kasan hakan ba zai yuyu ba saboda kana zuwa aiki, ka gani baba jummai ba yarinya ba ce bata iya dawainiyar ku kai da Jidda sai dai na Mom, haka gyaran bedroom naka ka hana kowa yama sai ita mai yasa baby ka chanza? ta ida maganar cikin rawar murya langwabe kai yayi kamar qaramin yaro ya ce, "sis ni fa ban chanza ba kawai dai yan' aikin ne basu ji sis shiyasa, dana aje kudi sai su d'auka baba jummai ce kad'ai bata d'aukar abinda ba'a bata ba, kuma ko aikin basu wani iya ba sai shirme"
"Toh naji yanzu dai ga rabi'a tana parlour ka zata fara gyara ma d'aki daga yau kafin baba jummai ta je kauye ta samoma good girl wadda batada d'an hali" 6ata fuska yayi ya ce, "sis kin.....!
"Shhhh please kayi hakauri for some days baby"
"toh sis" peck ya mata a hannu ta, ta masa a goshi.
Sannan aunty bilki ta cigaba da cewa, "Uhm kayi sauri ka shirya kasan yau akwai family meeting"
"I now gani nan fitowa"
"OK.!
Rabi'a na takure saman one star cikin uniform din ta na yan aiki wanda bata tunanin sadiq ko giya wake yasha bai yarda ta masa aiki saboda so biyu yana kamata zata masa sata, Anuty bilki ta qaraso washe da baki ta ce, "Rabi'a daga yau zaki Fara aiki anan part din na wani d'an lokaci please ki kula saboda na lura ba son aikin naki ya ke ba"
"to.! ta ce tana maida numfashi tare da washe baki, Anuty bilki tasa kai ta fice.
*****
"Fatuha..! Fatuha.!
"Na'am inna"
"zo nan wad'an nan kayan wakika barmawa su raban ki da wanki har kin manta wai yaushe zaki fara tsaf ta ne fatuha eeeeh,? kin fara girma amma kullun rashin jin ki dad'uwa yake, yi maza ki wanke su tas ki shanya" Kuka tasa har da birgima kasa tana cewa, "Qur'an inna ban iya wankin ba alqawalin Allah"
bakin ta inna ta bige ta ce, "wallahi in bakiyi wankin nan ba baki zuwa gad'ar tunda baki san kin girma ba, kuma indai baba jummai ta zo kina ji kina gani zan bayar da tsarabar data yi maki" matse kwalla tayi ta ce, "Toh inna zanyi Qur'an"
"Ah karma kiyi ai ba dole" Inna ta fara tatara kayan zata shige da su daki, jiki a sa6ule fatuha ta amshi kayan ta fara wankin.
*****
Tsaye yake gaban dressing mirror yana feshe jikinsa da turaran intense mai sanyayan kamshi, sanye yake da shirt blue mai dogwan hannu sai jeans dark blue hannu shi maqale da agogo silver na zalla azurfa, farin glass din shi yasa ya fito kamar balarabe ba qaramin kyau yayi ba amma fuskar nan d'aure, qwanqwasa kofar d'akin sa akayi ya juyo tare da furta "yes come in.! rabi'a ce jiki ba kwari kallo d'aya ya mata ya watsar cikin kakausar murya ya ce, "what.?
"Uhm dama kai nake jira ka fita na gyara bedroom d'in" wani irin kallo ya qara wurga mata ya matso gab da ita yana jifanta da kallon tsana ya ce, "Kinsan Allah zan fita ne na dawo wallahi na shigo d'aki na naga banga tsinke ba, huh you will see" fuuu ya ja ya fita ya barta sai 6ari take.
Ahankali ya ke