Showing 39001 words to 42000 words out of 105783 words
suka kwashe kwanikan sunka kai kitchen sannan suka fita farfajiyar gidan domin shan iska.
Saman resting chair suka zauna, suna dan taba hira fatuha ba qaramin jin dadi gurin take ba saboda har da yan shuke-shuke lumshe ido tayi ta ware su Hanan ta ce, "kai fatuha karki ce min wai bacci kike ji"
"ah ba bacci nake jiba kawai wajan yamin ne ina san guri kamar haka, shiyasa sanda nake akauye kullun muna bakin rafi ni da fatsima" murmushi Hanan tayi sun dade sosai a filin gida suna hira kiran sallah magrib ne ya tashe su a wajan suna tafe suna hira, sadiq da ke qaqorin fitowa zai je masallaci sanye da jalabiya milk fatuha bata lura da mutum ba tayi kansa ba tayi masauki ko ina ba sai saman fafad'an kirjinsa rintse ido fatu tayi tana zare ido tayi lamo a kirjinsa tana jira taji saukar aradu saboda tuni hancinta ya mamaye da kamshinsa, wata iri tsawa sadiq ya daka mata wadda yasa yan hanjin ta katsawa tayi baya zata fadi ya tarota cikin zafin nama idanusa waje kamar yarda fatu ta zaro nata duka waje kirjinta na bugawa da sauri da sauri, sakinta sadiq yayi da sauri Hanan ko take ta kama gefe jikin fatuha ta rabe, harara ya aika masu su duka cikin 6acin rai ya ce, "stupid girl's kuna tafiya kuna kalle-kalle baku kallon gaban ku mtss..! sannan ya sa kai ya fita, sauke ajiyar zuciya Hanan tayi ta ce, "ba dai jaraba ba mtss, sannu fatu indai uncle ne haka yake kullun cikin bakin rai da hargowa" fatu data dauke wuta na wucin gani murmushi tayi ta ce, "ni zan fada maki haka..! sannan suka shige cikin gida.
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
47_48
Bayan su idar da sallah parlour suka dawo suna kallo, kitchen fatuha ta shiga anan ta iske baba jummai tana farfesun yan'ciki gaishe ta tayi cikin sakin fuska ta amsa mata tare da yimata ya jiki, da sauki ta bata amsa tana qoqarin bude fridge fruits ta debo ta zuba a boll na glass tare da wankewa sanna ta dauko wuka parlour ta koma Hanan da ke zaune saman one sitar ta duro qasan carpet tare amshe wuqar hannu fatu ta ce, "Bari ni na yanka fruit din, kinga ke bakida lafiya" harara fatuha ta aika mata ta ce, "waya ce maki bani lafiya? lafiya ta lau inda za'a auna mu qilama na fiki lafiya" dariya Hanan tayi ta ce "Wasa kenan" tare da cigaba da yanka fruit din sai da ta gama yanka fruits din sannan ta maida wuqar ta dawo parlour suka fara cikin fruit din cikin jin dadi suna kallo suna taba hira.
Anuty bilki ce zaune saman sofa Mom na saman bed zaune aunty bilki ta ce, "Mom yanzu sai yaushe zaku dawo?
"wallahi ban sani ba amma nasan sai mun kai 2weeks tunda shi wancan zuwan da yayi sai da yayi kusan 3weeks" shagwabe fuska Anuty bilki tayi ta ce, "amma fa gaskiya Mom zamuyi missing naki wallahi" murmushi Mom tayi tare da cewa, "kanku bazan zauna ba naqi bin tsohon mijina ba, akan wani dalili zan barshi kullun yana zuwa uk ni ina Nigeria ni mai ya'ya, ya'yan da suna gidan miji," dariya Anuty bilki tayi ta ce, "kai Mom..! harara ta wurga mata ta ce, "kinga idan takuramin zakiya tashi ki ban gu kona samu na cigaba da hada shirgi na,"
"Mom wato kaya zaki kwasa da yawa kenan?
"laaaa yau Allah ya kawo mu 'ya na tirtse uwar ta dan zatayi tafiya da uban ta, toh kaya zan d'iba da yawa kika bata min rai wallahi har wata sai muyi" ta ida zancan tana bude bedside drawer baqar leda ta curo ta ce, "yauwa ga wannan tun wancan satin na so na aiko baby ya kawo maki, to ban samu dama ba" washe baki Anuty bilki tayi ta ce, "kai Amma fa Mom naji dadi Allah yasa wannan maganin irin wancan ne gaskiya wancan naji dadin shi" murmushi Mom tayi ta ce "Ai ina tunanin wannan yafi wancan, dan wannan dan sudan ne"
"amma fa na gode Mom kamar kinsan gobe zai dawo"
"toh ai shikenan daya garin da madara ake sha duk dare shi kuma dayan da zuma ga turaruka nan masu kamshi idan kina anfani da su ko cup kika riqe sai yayi kamshi," washe baki Anuty bilki tayi ta ce, "thank you Mom kamar kin san Abban Hanan nasan kamshi sosai wallahi"
"ah daughter waye baya san kamshi? sai dai idan mutum bai samu ba kamshi na da muhinmanci sosai daughter, ko kamshi kika riqe to wallahi kin riqe mijinki a hannun ki," haka Anuty bilki ta dinga jerawa Mom godiya agogo ta kalla kusan 8:30pm ta ce, "Mom bari muzo mu lalla6a mu tafi gida dare ya fara yi, ba dan gobe Abban Hanan zai dawo ba da mun kwana wallahi,"
"ai ko ba bazai dawo gobe ba ban zan bari ki kwanar min gida ba, ke kullun kika zo yini sai ki bige da kwana, ai hakuri ake a zauna har miji ya dawo ya same ka ba wai ka kwaso kafa kazo gida ba" mayafinta ta janyo da handbag dinta ta tura bakar ledar ciki fitowa sukayi daga bedroom din Anuty bilki na gaba Mom na bayan ta suka sauko daga upstairs sai da ta iso parlour ta yafa mayafin ta, su Hanan da ke zaune parlour suna shan fruit Anuty bilki ta qaraso ta ce, "Hanan ku tashi mu tafi dare nayi" bata fuska Hanan tayi ta ce "Momi na fa dauka sai 9:00pm zamu tafi "
"ai kin san bana san driven din dare ko? kuma ba da driver nazo ba" Hanan bata so su tafi yanzu ba da ba exam suke ba da nan zata kwana fatuha ma haka bata ji dadi ba saboda idan Hanan ta zo tana de6e mata kewa Anuty bilki ce ta katse masu tunani da cewa "Hanan yima baba jummai magana zamu tafi ta baki afra" bata ida rufe bakin ta ba sai ga baba junmai riqe da hijabin ta a Hannu afra na goye a bayan ta washe da baki ta ce, "ah kuma har kun fito yanzu na ke cewa bari na kawo maki Afra, yau nama yi daran tafiya da yake na tsaya yima mai gida farfesu," Mom ce ta ce, "ku dai baku ji baby ya sata farfesu ke kuma kin miqa mata diya tana ta fama ga afra da shegen kuka"
"ba komai ai kuma ko kukan ba tayi ba"
"Allah ya taimake ki shi kuma baby bayan yasan baki wuce magrib shine zai daura maki wahala" murmushi baba jummai tayi tana qoqarin miqawa Hanan afra, dariya Anuty bilki tayi ta ce, "Mom da kin bar shiga tsakanin baba jummai da baby ko ka shiga kai zaka sha kunya" murmushi Mom tayi aunty bilki ta ce, "to ai sai mu wuce tare sai na sauke ki gida baba"
"toh shikenan" tare suka fito fatuha na kusa da Hanan sunata zuba surutu jidda na riqe da hannu Jamal duk suka rako su filin gida, Anuty bilki na qoqarin bude murfin mota sadiq ya shigo tsayawa tayi tana sakin Murmushi qarasowa yayi ya ce "Sister har zaki tafi? na dauka kwana zakiyi ai" ya fadi cikin zolaya, harara ta maka masa ta ce, "baby ka rainani wallahi" dariya yayi ya ce, "baba har dake zasu tafi da niyata na kai ki,"
"ah ba komai" Hanan dake kusa da fatuha sai turo baki take sadiq ne ya kalle ta tare da aika mata harara ya ce, "sister na kusa fara cima Hanan naga kwanan wani rashin ji ke damun ta,"
"ni ba ruwana wannan tsakanin ku ne,"
"toh shikenan" raurau da ido Hanan tayi tare da cewa, "uncle sorry.! harara ya kuma aika mata ganin bai da niyar hakura yasa ta ta6e baki ta shige mota tana yima fatuha bye bye su duka suka shige motar Aunty bilki ta ce "Idan anyi hutu this time around jidda gida na zatazo" toh ya ce mata ai sun kusa fara exam "I think this Monday zasu fara" eh Anuty bilki tace masa tare da jan motarta suka bar harabar gidan sannan su fatuha suka jiyo riqe take da hannu jidda.
Direct bedroom suka wuce sadiq kuma ya wuce dining area, ko da suka shiga bedroom fatuha ta dire jidda tayi mata wanka sannan itama tayi kusan tare suka shirya saboda itama yau ta gaji tasha surutu har da godema Allah, night dress suka sa sannan ta dau jidda tana mata surutu suna haurawa upstairs a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq, a parlour suka iske shi zaune yana kallon news da gudu jidda ta fada jikinsa ta ce, "daddy...!
"yes my angel"
"uhm daddy ina ice cream din Anuty da chocolate din ta? laqace mata hanci yayi ya ce "yana bedroom" da gudu jidda ta shige bedroom fatuha kuma na qoqarin fita har ta bude kofar, jidda ta qaraso riqe da ledar shopping ta ce, "Anuty ga naki"
"angel har dani a tsarabar" washe baki jidda tayi ta ce, "eh.!
"toh na gode" ta amsa ta fita.
Direct bedroom din ta ta shige tare da kunna haske, saman bed ta zauna tare da bude ledar shopping din tun kan ta fara shan ice cream din miyan ta ya tsinke, tana sha tana kada kai tana cewa, "Amma fa wannan abu akwai dadi sosai gaskiya mai kyau yasan kan kwad'ai.! sai da ta cika cikin ta da ice cream sannan ta kwanta bacci yayi awan gaba da ita.
****
Akwana a tashi ba wuya wajan Allah sadiq ne janye da trolley din Mom dana Abba sai da ya zo bakin kofa ya ba ola da Sunday yayi musu umarnin da su sa kayan boot, ok boss ola ya ce fatuha ko na parlour zaune sai tsoro take yanzu idan su Mom suka tafi Allah kad'ai yasan muguntar da sadiq zai mata ranan unguwa ka dai suka je amma sai da ta d'and'ana kud'ar ta, bale kuma kwanaki duka wannan zancan a zuci take tare da kukan zuci dan tasan watan cin uban tane ya tsaya, su Mom ne suka qaraso parlour tana riqe da hannu jidda sai lisafa mata tsaraba da zata mata take washe da baki fatuha ta tashi tana yi masu Allah ya kiyaye hanya, Mom har ta kai bakin kofa ta juyo da kalli sadiq ta ce, "toh ga amanar fatuha sauran kuma idan na dawo naji ka mata wani abu dan nasan hali" 6ata fuska yayi kamar qaramin yaro yana bin fatuha da harara tuni yan hanjin ta suka fara kadawa dan tasan kashin ta ya bushe, daurewa kawai take amma ji take kamar ta daura hannu aka ta sa ihu gashi baba jummai taje biki kauye daga ita sai rabi'a kuma rabi'a data gama aikin ta take tafiya, jidda ce ta katse mata tunanin datake tare da janta har suka qarasa farfajiyar gidan, sadiq ne ya shiga wajan zaman driver da alama shi zai kaisu airport tuni jidda itama ta shige motar mom ce ta juyo ta ce, "fatuha duk abinda kike buqata kiyiwa baby magana kinji" toh tace mata tana raraba ido tana daga masu hannu har motar su ta fita daga harabar gidan.
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼♂
*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*
*Edit by*
*Raheenat*
📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★
http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com
49_50
Su sadiq na fita harabar gidan, fatuha ta juyo gida cike da tsoro raurau tayi da ido kamar tayi kuka saboda tuntuni rabi'a ta tafi sai ita kadai kwal a gidan sai su ola, parlour ta zauna tayi tagumi kamar munafuka tana ta raraba ido kamar wadda tayima sarki qarya, ganin tsoran ba zai fishe ta da komai ba yasa ta kuna kallo washe da baki ta dau remote control tana canza tashoshi Bollywood ta kai tayi shiru tana kallan film gaba ki daya imanin ta naga TV jin cikin ta ya fara kukan yunwa yasa ta tashi, dining area taje ta zubo macaroni da miya yaji kifi sosai kasancewa fatuha ba mai san macaroni ba ce yasa ta zuba kadan, ta dawo parlour saman three sitar ta zauna ta fara ci bayan ta kamala ta kai plate din kitchen tare da wanke wa bedroom ta koma tare da rage kayan jikin ta ta shiga wanka bata wani dad'e ba ta fito ko da ta fito lotion ta shafa tare da feshe jikin ta da turare white t-shirt din ta na aiki tasa kasancewa rigar ta kawo mata gwiwa sai taji bata sha'awar sa skirt din gashin ta ta baza ta sharce, masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba qarewa kanta kallo tayi a dressing mirror dariya tayi ta ce "Kai dan Allah dubi yadda nayi kamar ta cikin film din dana gama kalla hhhh lol" ta kumayin dariya tana godema Allah da yawadata ta da gashi a haka tasa kafa tafita daga bedroom din.
Bangaran su sadiq yana kai su mom airport , ya wuce da jidda family house dan shi yama manta da wata fatuha part din ammi ya shiga riqe da hannu jidda, Ammi dake zaune ta ce, "a'a wana ke gani," murmushi sadiq yayi tare da zama saman kujera yana gaisheta sannan ya ce, "Matar yanaga kin qara kyau?" washe baki Ammi tayi tana gyara daurin dankwalin ta tare da amsa masa ta qaraso parlour itama ta zauna, "ohni mai gida ace min jiki yayi sauki da har na fara dakan gunba ance min kana can rai hannu Allah ka zama dan gurgu" ta ida zancan tana dariya ,turo baki sadiq yayi ya ce "Haba ammi har so kike na bingire kenan? dariya ammi tayi tare da jawo jidda jikinta ta ce, "yar nema yau ba'a amin gwalangwatsin ba" smile jidda tayi kawai tare da cewa "Ammi ina gorubar da kika ce zaki siyo min ni da jamal?
"yar nema ashe baki manta ba ai tuntuni na siya tana daki na cikin drawer" da gudu jidda ta shige dakin ammi ta dan juyowa Ammi tayi tana facing din sadiq gyara murya ammi tayi ta ce "Ni ko Sadiq ya kamata kayi aure yanzu fisabilillahi dubi yadda jidda tayi wayau sosai yarinya na shirin zaman yan'mata, amma kai baka ko maganar aure bale nuna sha'awar ka ko dai baka lafiya ne Abubakar sadiq?" sadiq dake zaune saman three sitar ya hada gira sama data qasa kamar bai taba dariya ba, Ammi ta cigaba da cewa, "kai kullun baka so a fada ma gaskiya sai ka hau gunguni shi kuma Ibrahim ya zuba ma ido ko maganar aure bai ma," sadiq ko tunda ammi ta fara magana ya kai wuya dan shi bai da sharin yin wani aure yanzu, Alhaji ne ya qaraso parlour da alama yanzu ya dawo daga kasuwa ganin Ammi nata fada yasa Alhaji qaraso dan yaji ba'a sin zancan, ganin sadiq tasa gaba ya san maganar gizo bata wuce qoqi ya ce, "haba ladingo ya za ai ki tasa yaro gaba kina masa maganar aure? koma me ake samu a auran nan ai ya taba yi inya gaji da zama haka ai dole yayi aure tunda shi ba qarfe bane", ammi tabe baki tayi ta ce "Malam kenan da yaranan na da wannan tunanin ta tuni yayi amma kwata-kwata banga alamar yin hakan ba,
"koma dai menene bakin sasa gaba ba kina masa fada ba, ko abin motsa baki ba ki basa ba amma sai fada kike masa," shiko sadiq dadine ya mamaye masa zuciya sai murmushi yake Ammi tayi yake ta ce "Wallahi malam abin ya tsayamin araine?" Alhaji zama yayi kusa da sadiq tare da shafa gashin kansa ya ce,"yi hakuri kaji Abubakar sadiq," qaqaro murmushi sadiq yayi wanda iya qarshi lips din shi alhaji ya ce, "yauwa ko kai fa," ammi asiya ta kwalawa kira ta kawowa Alhaji abinci da sadiq, sadiq sai fama daurewa ammi yake bayan asiya ta kawo komai ammi tace ya sauko ya ci, "na koshi ya fadi a taqaice," bude baki ammi tayi ta fara fada "yanzu ni sadiq ban isa nama magana ba ko na baka shawara sai ka nunamin ban isa ba, ko Ibrahim ai bai isa yamin haka ba" matsar kwalla ta fara Alhaji da ke gefe takaici ma ya hana shi magana sadiq ganin abun ammi da gaske ne ya sashi cin abincin tare da sakin rai sannan ammi ta ji dadi ba laifi ya dan saki jiki amma sai wani bangare na zuciyar shi ya ke ji kamar ta fama masa inda ke masa qaiqayi tabbas yasan yayi rashin kausar har abada bazai kuma samun wada zata maye gurbinta ba, amma wani bari na zuciyar shi yaqi yadda ya cusa son wata diya mace har ta samu gurbi a zuciyar shi numfashi ya sauke tare da miqewa tsaye yana kiran angel Ammi ta ce, "mai gida kardai ka ce min tafiya za kayi? ko har yanzu baka huce ba? murmushi sadiq yayi ya ce, "haba matar ni na isa nayi fushi dake nayi fushi dake gobe ina zan fake" washe baki ammi tayi ta ce, "yauwa dan albarka, Allah yasa ma Albarka"
"ameen ammi"
" bari na kirama yar neman