Showing 66001 words to 69000 words out of 105783 words
rabuwa ba, ba tare da sunyi musu ba, amma duk wannan hirar da suke majeed tunanin fatuha na maqale a ransa cike da begen sake tozali da ita karo na biyu, kiran sallah magrib ne ya tashe su, d'auro alwala sukayi suka wuce masallaci.
Basu dawo gida ba sai bayan sallah isha, ko da suka dawo majeed bai shiga gidan ba daga waje ya tsaya tare da jan motarsa yana tunanin ta inda zai 6ulo domin ya kara tozali da fatu tattausan murmushi ya saki yana tuna kyawuta mai gusar da nutsuwar wucin gani, wannan lokacin sam ba zaiyi wasa da damarsa ba dan a gaskiya a shirye yake da ya aure ta kota halin kaka.......hmmm tofa..!
Ko da sadiq ya shigo gidan Mom na zaune a parlour ita da angel suna kallo, kallon parlour sadiq yayi tare da cewa "Angel ina Aunty?
"tana bedroom Dady" ok yace sannan ya haura sama ko minutes 5 bai yi ba ya dawo parlour tare da wuce wa bedroom din fatuha, zaune take saman bed tana assignment da laptop tana sanye da rigar bacci dai-dai gwiwa sai gashin kanta data nanad'e sa kamar ganmo.
Bud'e kofar da akayi ne yasa ta d'aga eye's ball's din ta saki tattausan murmushi ta ture laptop din dake gabanta tana qoqarin tashi, harara sadiq ya aika mata, tare da cewa, "Ina car Key's dina?" zuburo baki tayi gaba sadiq ya cigaba da cewa, "wato kin rai nani ko? shine zan fita kika d'auke min car key's kika boye"
"sorry uncle, bana so ka fita ne ka sha rana, kuma da ka fita ai da bakon ka bai same ka ba, am sorry.! tasa hannuwata biyu a kunne ta langwabe kai ta ce, "Allah yaba ka hakuri" matsowa sadiq yayi kusa da ita har tana jin saukar numfashinsa ja mata baki yayi har sai da ta saki yar qara, ta6e baki tayi tana shirin yin kuka cikin wata irin murya can kasan makoshi sadiq ya ce, "kul kika min kuka wallahi yau sai kin kwana kina kneeldown, kuma kin san zan iya, bani key's dina," bedside drawer ta bude tare da zaro key's din ta miqa masa tana qoqarin komawa saman bed jawo hannuta sadiq yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau ta masa ba, lumshe ido yayi tare da ware su a kanta murmushi fatuha ta saki mai cike da sakonni iri-iri wani langwabe kai sadiq yayi yana binta da kallon qasan ido ya ce, "rufe idanuwan ki kiga wani abu" cikin sauri da zakuwa fatu ta lumshe idanuwanta wani d'an kit ya fido tare da bude kit din ya ce, "oya bud'e.! wata hadadiyar sarkar gold ce sai sheki take da walwali kallo daya zaka mata kasan ba qaramar sarqa ba ce bude baki fatu tayi tana kallon sarqar wani irin ihu fatuha tasaki tare da rungume sadiq, shima rungume ta yayi tare da kai hannu saman gashin kanta ya warware daurin data masa ya kwanto gadon bayanta, cikin cool voice sadiq ya ce can kasan maqoshi yarda sai fatu zata iya jinsa cikin rad'a ya ce, "Gashin ki yafi kyau a haka..! smile tayi tare da dagowa daga fafad'an qirjinsa da murmushinta mai qara mata kyau ta juya masa baya tana facing din dressing mirror tare da matsar da gashin kanta gefe tana kallon sadiq ta cikin mirror a hankalin ya kwance sarqar lumshe ido fatu tayi tana jin yarda hannu sadiq ke yawo a dokin wuyanta, samata sarkar yayi ya tsare ta da ido ya jin farin ciki jin shuru yasa fatu ware ido ta sauke su kan sadiq daya daura kansa saman kafadarta, suna kallon juna ta cikin mirror ba qaramin kyau sarkar ta mata ba da murmushi ta juyo tare da cewa, "Uncle na gode" murmushi sadiq yayi ya ce, "nike da godiya fatuha yau kusan shekarana uku bana tunani, bana zuwa asibiti kin zamar min wani bangare na rayuwata" murmushi ta saki tare da fita daga d'akin da sauri.
tana Isowa parlour ta fad'a jikin Mom tana cewa, "Mom kin ga sarkar da uncle ya siya min? murmushi moym tayi irin nasu na manya ta ce, "amma dai gaskiya mun gode wannan kyau ta haka" lokacin yayi dai-dai da fitowar sadiq daga bedroom din fatuha, angel ce ta turo baki ta ce, "Daddy ni fa☹?" ja mata kumatu yayi tare da fido mata zube na gold ya sa mata murmushi ta saki ta fada jikin sadiq ta ce, "love you daddy" tare da yimasa peck Mom ta ce, "lallai abin ma yar haka ce kenan? yaran ka kawai ka sani ni kuma ko oho" Mom ta fada, bayan Mom sadiq yaje tare da zuro kansa a wuyanta ya ce, "sorry Mom next time siyayarki ce ke kad'ai kin ji" d'an smile Mom tayi tare da shafa sumar kan sadiq shima zagayowa yayi ya zauna sun dad'e suna hira sannan kowa ya wuce bedroom dinsa.
Bangaran majeed ko cikin farin ciki ya koma gida, ko da umyma ta tanbayesa sai ce mata yayi ya kusa cika mata burin ta, murna ko har ba'a magana ko da ya koma d'akinsa da ya rintse ido fatuha yake gani tana sakin murmushinta mai tafiya dashi haka ya dinga juyi saman bed har bacci barawo ya sace shi.
*Asuba ta gari*
Kasancewar yau weekend fatuha ta shiga kitchen tare da su baba jummai suna aikin suna zuba hira kunsan a tare suka gama komai, da misalin karfe 10:30 take tsaye gaban dining tana jera kayan abincin cikin nutsuwa sallamar da kayi ne yasata dagowa tare da kallon kofar ta amsa a taqaice majeed ne, sanye cikin shada ash tasha aiki sai kamshi yake zubawa yana fad'ad'a murmushisa dining area ya nufo tare da yin smile fararan hakoran sa suka bayana. gyara murya yayi tare da cewa, "Dama ashe kyawawa na aiki? gaskiya kamata yayi ace warhaka kina can d'aki kwance kina bacci" d'agowa fatuha ta d'anyi a tunanin ta tuntuni ya shige ciki dan tasan kowaye a gidan saboda tasha ganin pics nashi dan murmushi ta saki cikin yauki ta ce, "Suwaye kyawawa anan? naga dai ni kad'ai ce" ta ida zancan tana wai gawa murmushi ya kuma saki a qaro na biyu ya ce, "fatuha kenan duk inda wata kyakyawa take kin kai ai, idan ma baki sani ba to yau zan fad'a maki, wallahi kin hada duk wani abun da ake nema wajen wata y'a mace..! yar dariya ta saki ta ce, "yau uncle da tsoka ka zo gidan nan ko? Ko dai yau ranar tsokana ce? bata ida rufe bakin ta ba sadiq ya shigo sanye da kayan gym dinsa da alama daga gym ya dawo, tunda yaga fatuha da majeed tsaye gabaki daya annurin fuskarsa ya sauya kamar an aiko masa da mutuwa daurewa yayi ya qaqaro murmushi ya ce, "my man da yaushe ka shigo?
"yanzu na shigo bama kowa parlour sai wannan kyakyawar dake ta faman aiki, ni fa a ganina ko kallonta kake ya isa ya kosar da mutun daga yunwa" wani irin kallo sadiq ya wurga ma fatuha tare da bin kayan jikinta da kallo gown ce mai kyau sai dai ya matseta duk wata sura na jikinta ana gani, ganin kallon da sadiq ya mata yasa ta barin parlour ba shiri, majeed kuma ya bita da kallo har yana cewa, "har zaki gudu? ko tanka masa ba tayi ba ta shige bedroom, wai gowa yayi yana kallkn sadiq ko lura da irin canjin da fuskarsa sadiq tayi baiyi ba ya haura upstairs, sadiq ya biyo bayansa.
bayan sadiq yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya daya saba sawa suka fito tare da majeed dining area suka nufa, lokacin kowa ya halara gaishe da su Mom sukayi a tare, tare da jan kojera suka zauna Mom ta ce, "a'a yau wanake gani a gidan nan da fara safiya? dan murmushi majeed yayi yana sosa keya "lallai kam ka kyauta, amma dai wuni ka zo yi?
"eh mana Mom ki sha kurimin ki Mom nama kusa kwaso kayana na dawo nan da zama" ya ida zancan sa yana sunkuyar da kan sa kasa, dariya Mom da Abba sukayi sadiq ko ya cika fam kamar zai fashe, jawo plate fatuha tayi zatayi saving sadiq kamar yadda ta saba, sai da ta gama samasa nashi zatayi saving majeed ya fakaici idanuwan su ya riqe hannu fatuha alamar kar ta zuba bata dau abin komai ba a tunaninta hutar da ita yake son yi, ta zauna ta fara cin abincin ta sadiq ne yayi saving majeed da kansa sannan suka fara break duk wata loma da majeed zai kai sai ya kai kallonsa kan fatuha idan sukayi ido hudu ya aika mata killing smile dinsa duk wannan abun a qwayar idanu sadiq, yake faru sosai ransa ke 6aci ganin kamar itama fatu na maida masa da martani lokaci daya annurinsa ya d'auke abincin ya gundiresa, cikin bacin rai ya ture plate din dake gabansa cike da masifa da zafin rai ya bar dining, kallo su Mom suka bishi da shi, fatuha ce tayi qoqarin tashi Mom ta ce, "Kyale shi ki cigaba da cin abincin ki, tunda kika ga haka ba qaramin abun ke damun sa ba" d'aga kafada majeed yayi tare da cewa, "Indai sadiq ne ai ba yau ya saba haka ba, yanzu ne yayi sauki" tunda sadiq ya bar dining fatuha ta rasa nutsuwar ta, tunda safe ta lura yake d'acin rai ta rasa dalili...hmm!
Ko da ya shiga part dinsa a parlour ya zauna tare da lumshe ido wani irin bacin rai na damun shi, kuma gashi ya rasa dalilin haka dafa shin da akayi ne yasashi ware eye's ball's dinsa fatuha ce tsaye da plate a hannu ta cikin cool voice ta ce "Uncle please kayi break koma waye ya 6ata ma rai kayi hakuri" ta ida zancan tare da zama tana miqa masa plate amsa yayi ya aje gefe yana kallon fatuha kamar me neman wani abu a fuskar ta can Kuma ya kauda kai tare da cewa, "zanci kin ji tashi ki je bana san magana ne" ya fadi yana lumshe ido fita ta zo yi lokacin yayi dai-dai da shigowar majeed bigewa su kayi da junan su, "ohshh..! majeed yace haka ma fatuha ta ce tayi baya waigowa sadiq yayi yana kallon su wani miyau mai daci ya hadiya, dariya fatuha ta saki tare da cewa "Sorry uncle.! majeed ya ce, "tunda nazo gidan nan kike bige ni, har saida kika bige zuciya ta" zaro ido waje fatuha tayi tana dan kule bakinta ta ce "Kai uncle..! ba ruwana" ta fadi zancan tana ida fita duk da bata gane nufin Majeed ba, ritse ido sadiq yayi tare da dunqule hannuwansa lokaci daya jijiyar kansa ta taso yana mai da numfashi sama-sama majeed ne ya dafa shi lumshe ido yayi, a hankali yana jawo nutsuwarsa zagayowa yayi ya zauna yana cewa, "big man ina tunanin ka daina zafin rannan naka ashe har yanzu kana yi, wai ma waya bata ma rai haka big man?
"kawai am not in the mood shiyasa"
"eyya sorry ko alura ce ta motso? ya fadi yana dariyar shaqiyanci pillow kujera sadiq ya wurga wa majeed ya ce, "wallahi ka rainani kai naka bai tashi ba sai nawa," dariya majeed ya saki ya ce, "kasan me Ammi ta ce?
"a'a sai ka fadi"
"ta ce wallahi next meeting idan bamu fido mata ba wallahi auran dole zata mana, ni dai nayi mata very soon zaku santa, amma kai ban sani ba kana nan kana ruwan idon nan naka" dan ta6e baki sadiq yayi tare da cewa, "Ba wani ruwan ido har yanzu banga wadda ta dace dani bane shiyasa..!
"ko? za kayi bayani sanda Ammi zata kwasoma yar kauye,.! dariyar yake sadiq yayi tare da d'aukar remote control...
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R
*Email* [email protected]
*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM
73_74
this page is for you ummin mama
Sai bayan sallah isha majeed ya bar gidan su sadiq, bayan sadiq ya dawo party din shi ya wuce yana shiga yaci qaro da angel na kallo cartoon, murmushi ya saki tare da cewa, "my Angel? ya qaraso kusa da ita ya zauna peck ya mata a goshi angel ta ce, "daddy.!
"yes dear.!
"please gobe muje shan ice cream please daddy"
"sweetheart gobe ba time kin ga akwai work amma idan na dawo da wuri zamu je kijin angel"
"ok daddy, daddy yau a nan zan kwana" ta ida zancan ta cikin shagwaba dan ja mata hanci sadiq yayi tare da cewa, "Yanzu kin zama big girl fa? ko baki gani yanzu fa you are 9 years old ko baki sani ba? smile tayi ta ce "Haka kuma nima daddy zan zama kamar Aunty fatuha ko idan na girma?
"yes mana..! smile ta saki tare da yi masa peck a goshi ta ce, "good night daddy"
"night angel.
Fatuha ce tsaye gaban dressing mirror tana feshe jikinta da turare da alama shirin bacci take, dan kayan bacci ne a jikinta pink da ratsin green riga ce dai-dai gwiwa mai dan siririn hannu bayan ta kamala shirin ta, ta baza gashin ta har gadan bayanta. tsurawa dressing mirror ido tayi tana tuna lokaci da sadiq yasa mata sarka lumshi ido tayi tare da daura hannuta saman wuyanta tana tuna movement din da suka kasance da sadiq jiya dayake sa mata sarqar saurin ware ido tayi tare da cewa "you are very stupid fatuha..! tare da fita daga daki'n tana sakin tattausan murmushi.
bedroom din angel ta shiga lokacin har ta shirya cikin night dress din ta, tana kwace cikin blanket, a hankali fatuha qaraso kusa da ita ta zauna bakin gado tana shafa forehead din angel ware ido angel tayi kasancewa bacci bai dauke ta ba shafa gashin kanta fatuha tayi ta ce, "Angel bakiyi bacci ba?"
"uhm yanzu na dawo daga party din daddy"
"ok.! peck fatuha tayi mata tare da gyara mata blanket din ta kashe haskyan daki'n tare da rage gudun AC dakin ta fita.
Ko da fatuha ta fita kitchen ta shige ta had'a coffee ta daura cup din saman tray ta haura saman, a hankali tayi knocking din kofar, "come in.! aka ce hakan yasa fatuha bude kofar a hankali ta shigo, sanyi AC ke tashi da kamshi na musanman cikin fara'a ta qarasa shigowa sadiq na zaune saman three sitar sanye da night dress din shi blue masu taushi wando da riga, cikin nutsuwa ta samu guri ta zauna saman one sitar, miqa masa glass cup din tayi amsa yayi yana smile kurba biyu zuwa uku yayi tare da kallon fatuha ya ce, "kamar akwai magana a bakin ki" dan murmushi tayi tana wasa da yatsun hannu ta, "ina jin ki.!
"uncle dama-dama uhm gobe ina so naje family house ne ni da Hanan" wani irin miyau sadiq ya hade take nan coffee ya fita ransa, "waza taje gani family house ? ya fada cikin zuciyar sa qara hada rai yayi kamar an aiko masa da sakon mutuwa majeed ne ya fado masa a rai qara tsuke fuska yayi ya ce "Ban shirya ma zuwan ki family house ba" ya fadi a taqaice, "uncle...! d'aga mata hannu yayi ya ce "Yawon yayi yawa ina laifin kije gidan Aunty bilki, next time kin je can din" ya fadi a taqaice dan murmushi tayi wanda iya karshi la66anta, saboda bata san gardama da sadiq ko dan karya bata ransa ta ce, "Toh..! qoqarin fita ta take jiki ba qwari jawo ta sadiq yayi ta fado saman fafadan qirjinsa dariya fatuha ta saki tare da dan dukan qirjinsa cikin wasa, murmushi ya saki tare da d'ago da habarta ya ce "Na dauka kinyi fushi da uncle ne? dan 6ata fuska tayi tare da daura hannuta gefan fuskarsa tana kallon kamar yarda ya tsare ta da shanyayin idanusa ta ce, "bana fushi da uncle kuma ba zan fara ba..! Kuma dama can gidan Mami nayi niyar zuwa Hanan ce tace na tanbaye ka muje can" qarewa lips dinta kallo sadiq yake har ta kai aya yana jin wani sanyi na ratsa sa tunda daga d'an yatsan sa har zuwa kansa ya ce, "Ok.! zame jikinta daga na Sadiq tayi ta ce, "Uncle bari na tafi"
"ok har kin fara jin bacci ne na dauka hira kika zo taya ni" har lokacin hannu fatu na cikin na sadiq yana murzasu a hankali dan smile tayi wanda ya bayana fararan hakoran ta ta ce "Ba bacci nake ji ba kawai zan tafi ne saboda bana son dare yamin a nan ina jin tsora fita ni ka dai" d'aga gira sadiq yayi wanda ya kara bayana kyansa ya ce, "ok good night.! ya saki hannuta har ta kai bakin kofa ta jiyu ta ce "uncle zaka taya ni hira kafin bacci ya dauke ni?"
"yeah..!
"ok zan kira ka video call idan na je bedroom" dawowa tayi ta masa peck a goshi sannan ta fice daga part din.
Ko da ta koma bedroom laptop ta kunna, a bangaran sadiq ma haka kiran fatuha ya shigo laptop din sadiq dauk'a yayi yana kallon ta kamar tana gabansa, yana shan coffee yana kallonta suna magana surutu ta cigaba da zuba masa yana dariya, har cikinsa na kulewa haka itama sosai sukayi hira inda sadiq yake jin bacin ran dake damunsa ya tafi, har tayi bacci suna video call smile sadiq yayi ganin fatuha tayi bacci sannan shima ya kwanta, amma duk da haka ya kasa kashe laptop din kuma ya kasa kauda idanuwasa daga kanta yarasa dalilin da yasa inda yana tare da fatuha yake bata guri na musanman a zuciyarsa wasu abubuwan bai san yana yi ba idan suna tare so da yawa ya kan manta kansa idan yana tare da fatu, ita ka dai ce macan dake ganin murmushinsa fara'a shi da halinsa da wannan tunanin bacci ya dauke sadiq ba tare da ya kashe laptop ba.
*Asuba ta gari*
Addu'a cike a bakin ta tashi tana miqa