Showing 54001 words to 57000 words out of 105783 words

Chapter 19 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

718

  Misalin karfe goma na dare ya shigo gidan tsit ba motsin kowa, idan da sabo ya saba dama shi mutun ne ba mai son hayaniya ba part nashi ya wuce  tare da shigewa bathroom ya sheqa wanka, yana  fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jallabiya white ba qaramin kyau ta masa ba, fitowa yayi daga part din na shi ya wuce main parlour direct dining area ya wuce abinci ya zuba dan kad'an shinkafa da miya ce tasha kayan had'i loma biyu zuwa uku yayi ya ture plate din dan kwata-kwata baya jin dad'in jikinsa gabaki daya, yayi missing din jidda bama ya ganewa yayi missing nata sai ya je bacci  zai ji bed din wayam sai dai yayata juyi har ya samu bacci ya dauke shi, gashi baya so ya je gidan Aunty bilki yasan yana zuwa zata ce Jidda ta kawo shi shiyasa yake hakura.
         bangaran su Mom ko duk san da ya tanbayi ranar dawowar su sai Mom ta ce sai sun gama abinda suke.

         Jiki ba kwari ya koma part din shi,  wata irin fever yake ji sama-sama ga qirjin shi na masa zafi, magani ya cura daga bedside drawer  ya sha sannan ya kwata ta tare da rufe jikin shi da blanket.

         Asuba ta gari fatuha na tashi ta tsala wanka tare da gabatar da sallah, sannan ta koma bacci cike da kewar su inna, dan gabaki d'aya yanzu kauye take so ta koma, zama gidan yanzu ya fara hawar mata kai abu d'aya ke mata dadi yanzu shine idan malam ya zo koya mata karatu shima da sun gama ya tafi zata shigo gida kamar maya, gaskiya ta gaji da irin wannan rayuwar gashi kwanan ta lura mai kyau ko abinci baya ci, anya yana gidan ma kuwa ba ita kad'ai suka bari ba sannan ta ja dan guntun tsaki tare da gyara kwaciyar ta.

      Ba ita ta tashi ba sai kusan karfe 10:30 brush kawai tayi tare da gyara gashin kanta ya kwanta har gadon baya, sannan ta fito parlour sanye da gwon black mai kyau masha Allah fatuha tayi kyau ga wani haske da ta qara, gashi kullun yan matan ci bayana yake a jikinta.
       Jin bata ji kamshi bane yasa gaban ta ya fadi leqawa kitchen tayi taga wayam ba rabi'a ba alama dan bata rai tayi ta dawo parlour tare da wucewa dining area, bude kulolin jiya ta fara yi jiya ma kusan ita kadai ta ci abincin dan guntun tsaki ta kuma ja tare da kwashe kayan ta wuce kitchen, gyara kitchen d'in ta shiga yi sai da kitchen din ya fita tas sannan ta d'aura ruwan zafi kan wuta ta fita sai da ta gama gyara ko ina sannan ta dawo kitchen, ta juye ruwan zafin cikin flacks  sannan ta soya kwai ta juye a plate ta rufe yan ciki ta fido a fridge suma ta wanke ta gyara ta d'aura a tukunya tare da gyara kayan miya ta zuba da k'yan kamshi tuni kitchen din ya gwaraye da k'amshi dad'i,  parlour ta fito tare da haurawa up stair's a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq wani irin sanyi da kamshi dadi suka doki hanci ta, lumshe ido tayi tare da ware su tana qarewa parlour kallo tsit parlour ba kowa, hakan ya tabatar mata da mai kyau ya tafi wajan aiki kofar bedroom ta nufa tare da bude ta a hankali  ta shiga dakin kamar yarda ta saba, sanyi AC ne kawai ke tashi sai kamshi kayan d'akin ta fara tatarewa duk da d'akin ba wani dati yayi ba blanket ta jawo zata linke sai taji anja, ware ido tayi waje tare da fara jin tsoro ko lafiya qara jan blanket din tayi taji anja dawowa tayi gaban bed din tayi tsaya a hankali ta kai hannu duk da zuciyar na dukan uku uku saboda tasan yau tuesday sadiq na zuwa office kuma baya kaiwa wannan lokacin bai fita ba, a hankali ta sa hannu ta fara yaye blanket din dai-dai fuskar sadiq taja ta tsaya Chak, saboda ba abinda sadiq yake sai rawar dari, a rude fatuha ta ce "Mai kyau me ya same ka? ta fadi bakin ta na rawa inbada rawar dari ba abinda ya ke sai hawayan fever dake bimasa fuska dan ko magana bai iyawa sai ma rintsa ido da yayi yana qoqari jawo blanket ya rufe jikin shi, riqe blanket din fatuha tayi tana  kallonsa  cike  da  tausayinsa har da yan  hawayanta tana  cewa, "mai kyau dan Allah me ke damu ka? hannuta  na  rawa  ta  kai hannuta tata6a goshin shin wani irin zafi taji rau take nan ta hau reramai kuka duk fever da ke jikin sadiq sai da fatuha ta dan bashi dariya, da  tausayi  ganin  yarda  take  damuwa  da  shi  sosai  duk da basa  wani  shan  inuwa  d'aya, yadda  ta rude sai ka ce yau ta fara ganin ana fever amma sai ya guntse dariyar tare da qara lumshe ido dan bai san ganin wannan kukan ko mutuwa yayi ai sai haka fita tayi daga d'aki ganin zaman bai fishe ta, tana zuwa bakin k'ofar fita suka ci qaro da ola shima zai shigo ya ji ko lafiya Oga bai fito ba, ganin fatuha na kuka yasa shi tsayawa tanbayar ta lafiya kora masa bayani kawai tayi sannan, shima ya haura sama part din sadiq wayar shi dake aljihu ya ciro ya kira doctor yakub sannan ya zauna saman sofa fatuha kuma na zaune kusa da sadiq tasa ruwan a ruba da towel tana dadana masa akai saboda jikin nashi ba qaramin zafi yayi ba cikin 15 minutes doctor ya qaraso gaishe shi fatuha tayi tare da matsa masa ya zauna, shi kuma ola ya fice, duba sadiq ya shiga yi  yan rubuce-rubuce yayi tare da gwada Bp din shi ya hau sosai kallon sa doctor yakub yayi tare da gwada kai ya curo allura zai  masa fatuha dake gefe sai ka ce  ita za ayima wa ritse ido tayi  tana  ji  tamkar  ita  doctor  zai  ma  allura dan ba abinda ta tsana kamar allura, bayan ya kamala duk abinda yake Dr yakub ya juyo cikin fara'a ya ce, "insha Allah anjima zai tashi kuma insha Allah fever zata sauka karki  damu anjima zanzo" fido magunguna doctor  yayi ya  ce, "dan Allah idan ya tashi ya samu yaci abinci dan babu alamar ya ci abinci, idan zan dawo zan dawo da ledar ruwa" to fatuha ta ce masa tare da masa godiya ta rakoshi har bakin kofa ta koma ciki, Ko da ta koma ciki, kitchen ta shige ta qarawa farfesunta dake wuta ruwa sannan ta koma part din Sadiq leqa fuskar  shi tayi ganin yana bacci yasata sakin ajiyar azuciya tare da ta6a goshinsa ta  ce, "Alhamdulillah zazza6in ya sauka" sannan ta rage gudun AC d'aki ta fara gyara part din.Written by
        Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

 
  📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com-Real-Hausa-fulani-writers-forumRHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_*
realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

          
                       61_62

       Sai da ta gama gyara part din tsaf sannan ta koma kitchen, lokacin har farfesun yayi ta juye a kula tare da plate ta zuba a  tray da bread a hankali take taka upstairs saboda ta cika tray din da kayan abinci, bakin kofa ta aje tray din sannan ta bude kofar ta shiga har cikin bedroom ta aje a stool qara leka fuskar sadiq tayi a qaro na biyu murmushi ta saki tare da zama gefan shi tana kallon yadda sajansa ya kwanta luf har mamakin kyau irin na sadiq take, sai dai yayi yar rama sannna fuskarsa tayi fayau dariya tayi ta ce "Ohni sangami ciwo yayi kamu kayi bulun buqwi tunda likita ya tsulama allura kaji zafi sai bacci kake, qila ma suma kayi saboda  zafi, kai  ma ka  ji  yarda naji  ranan yadda kayi bacci kamar ba masifafe ba, amma da ka warke zaka fara cika mana gida da tsuwa, na huta da masifar ka ko ta kwana biyu ce uhm bari na lalla6a naje nayi wanka a toilet din ka tunda kai ka zama gawar shanu dan tashin ka ba yanzu.

       Tashi fatuha tayi ta bude wardrobe ta ciro qaramin towel ta rage kayan jikinta tasa towel, duk wannan abun da fatuha ke duk a kunnan sadiq dan ya dade da tashi kawai dai yayi lamo ne, toilet din ta shige ta sheqa wanka ta fito ko da fito cikin sanda take tafiyar har ta qaraso gefe bed leqa fuskar sadiq tayi tana riqe da qaramin towel tana goge gashin kanta ta  ce, Allah sarki ba wan Allah sai bacci kake baka san wainar dana ke toyawa ba wai da zaka tashi dana sha masifa, yarfe gashin kanta tayi wanda hakan yasa ruwan gashin ya watso ma sadiq a fuska dan motsa ido yayi hakan yasa fatuha zaro ido tare da yin lamo tana zare ido tana yarfe hannu ganin ya juya ya gyara kwaciyar shi ya sata sakin a jiyar zuciya, baki dressing mirror din shi ta tsaya tana kallon mayukan dake baje akan dressing mirror  tsuru-tsuru tayi tana tunanin man da zata shafa can ta kai hannu kan wani mai na gashi kasancewa fatuha ba boko yasa ta d'auka ta fara shafawa sadiq dake kallon ta ta qasan ido sai dariya yake guntsewa, in taqaice maku duk wani mai dake saman dressing mirror sai fatu ta shafa dan taji ya mai kyau ya ke ji sannan ta fita daga d'akin, tana zuwa bedroom dinta kaya tasa sadiq dake d'aki dariya yayi sosai har da riqe ciki dan guntun saki ya ja tare da cewa "Yar kauye kawai..! Sannan ya tashi a hankali duk da har yanzu baya jin karfin jikinsa wanka yayi sannan ya fito yasa jallabiya ash mai kyau sannan ya gabatar da sallolin shi, yana idarwa  ya qara koma wa ya kwanta dan karfin hali kawai yake.

    Sket da riga tasa na atamfa mai ratsin dark green da coffee brown sai gyara gashin kanta da tayi tare da yin  ture ka ga tsiya dauri, sannan ta qara fesa turare rufe bedroom din tayi ta fito sannan ta haura upstairs direct bedroom din sadiq ta shige kwance ta gan shi amma sai dai wannan lokacin idanuwan shi biyu murmushi ta saki tare da qaraso wajan shi cikin sanyin murya ta ce "Mai kyau ya jiki?" lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha jim yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau tamasa ba musanman dan qaramin lips din ta pick kauda kai yayi tare da cewa, "da sauki.! ya lumshe ido smile ta kuma yi tare da jawo tray dake saman stool ta cigaba da saving nashi cikin nutsuwa kasancewa tasan bai cin abinci bane sosai, shiyasa ta zuba masa farfesun yan cikin kad'an ciki dan boll,

    Cikin sanyi murya ta kuma cewa "Mai kyau.! ware sexy eye's ball's din yayi ya qara sauke su kan lips din ta cikin shagwaba da sanyi murya ta ce, "Mai kyau dan Allah ka ci farfesun  nan ka ga likita yace ka ci abinci"   hade rai sadiq yayi tare da lumshe ido tare da yin magana cikin cool voice nashi ya ce "Bana jin yunwa fatuha" dan bata rai tayi tare da rausaya kai ta ce "Dan Allah kaga ko akauye idan bani lafiya idan banci abinci ba inna har dure take min, dan na samu lafiya ka ga yanzu Mom bata nan bale ama dure, dan Allah ka ci" ta ida zancan tana rausaya kai tana kallon sadiq dake kallon ta kamar qaramin yaro qara hade rai yayi ya ce "ba fa naci leave me alone pls" zaro ido fatuha tayi ta ce "Kai kasan wannan"  murmushi yayi wadda bai yi niya ba ya ce "Fatuha wai yaushe zaki waye?" dariya tayi ta ce "Sai ranar dana fara zuwa boko ka ga da jidda nan ita ke koyamin yanzu kuma tana gidan Aunty bilki" ta ida zancan tare da yin raurau da ido sadiq  ya  ce, "ai ta kusa dawowa kin ji, uhm to kina san karantun ne? bai ida rufe bakin shi ba Dr yakub ya shigo, cikin sallama tare wurgawa sadiq harara dake kwance gaisheshi fatuha tayi har qasa sannan ta dau boll din farfesun ta aje a tray tana qoqarin fita doctor  yakub ya  ce, "ah wai fita zakiyi da kin tsaya ai" murmushi fatuha tayi ta ce "Ina da abinyi ne a kitchen shiyasa"
    "ok.! wannan abincin fa nawaye? kallon sadiq tayi dake ta faman aika mata harara tayi tsaye tare da sada kanta qasa, juyowa Dr yakub yayi su kayi ido hudu da sadiq "mtww haba captain me yasa kake haka ne please, wai bana sha fada ma ba ka rage damuwa ba uhm saboda tsabar damuwa  ka daurawa kanka hawan jini, me yasa kake abune kamar mara tawakali ai kowa ya sani duk me rai mamaci ne tunda kausar ta bar duniya ka daina walwala ka maida zuwa asibiti kamar zuwa kasuwa, haba captain ko dan lafiyar ka da matsayin ka ka hakura da wannan tunanin please," lumshe ido sadiq yayi kamar yakub na magana da dutse tsaki Dr yakub yaja ya ce "To wannan abincin da kaqi ci  me hakan ke nufi?" ware ido yayi yana aika ma fatuha harara dan shi kwata-kwata baya buqatar wani abinci a cikin shi amma saboda tsabar naci irin na fatuha yanzu tasa sai ya ci abinci dan guntun tsaki yaja yana kallon yakub dake ta masifa yanzu "ka daure ka ci abinci ko nama alura ai dai ba saina fadama ila da alura kema mutun ba idan ba abinci ba" duk yadda ya so ya kauce ma qincin abinci sai da yakub ya takura masa ya sha farfesun kad'an  ba tare da bread ba ba laifi farfesun ya masa dadi duk da bakinsa ba test aje boll din yayi fatuha ta dau tray din ta fita alura Dr yakub ya masa tare da daura masa ledar ruwa saboda ya lura sadiq baya san cin abinci yana lafiyar ma yaci kadan bale yanzu.

     Dawowar fatuha ce tasa Dr miqewa ya ce "To ni zan wuce dan Allah ki kulla da cin abincin shi idan bai ci ba ki kira Aunty bilki ki fada mata ai yasan halin ta"  d'aga kai fatuha tayi sannan ta taimakamasa da daukar masa  briefcase din har sai da suka zo bakin kofa ta masa sallama ta rufe gidan bedroom din sadiq ta kuma.
           Tana dawowa harara ya bita da shi sannan ya ja saki murguda masa baki itama tayi tare da zama saman sofa sanin  ba  zai  iya  tashi ba  yasa  fatu  haha sadiq  ya  ce, "keee wakike murgudawa baki? raurau da ido fatuha tayi ta ce "Bada kai nake ba"
           "Dawa kike to? ya fada cikin sigar masifa "uhm ba da kai nake ba wallahi"
        "mtww wallahi karki bari na tashi dan na tashi saina karairayaki, bama na hana ki yawo ba hijabi ba eh?
    "amma ai a waje ka ce ba'a gida ba,"  tsaki ya  ja, mtww  sannan ya juya ya lumshe ido.Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/Mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=,H-R

*_Email_* [email protected]

*_Facebook_*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                   63_64

Juya bayan da sadiq yayi yasa fatuha jan dan guntun tsaki tare da kallon agogan dake maqale a bango kusan karfe 8:30 na dare, tashi tayi ta bar part din ta koma part din su tana shiga bedroom ta rage kayan jiki ta, ta  shiga toilet ta sheqa wanka ta fito daure da towel ko shafa mai ba tayi ba, ta bude wardrobe ta ciro kayan baccin ta riga da wando pink masu mayan flowers da zanan ya'yan cartoon, d'aure gashi kanta tayi da wata yar kibiya ta d'aure kai sannan ta fesa turara har zata kwanta sadiq ya fado mata a rai ta barshi a d'aki shi kad'ai, gashi baya da lafiya tashi tayi zubur zata fita sai kuma taci birki ta ce "Ko naje tijara zai mun dan ba mutunci gare shi ba, karma ya tsinka ni.! wata zuciyar tace haba fatuha duk rashin mutuncin mutu bai da lafiya ai dole ya shafa wa mutane lafiya riqe handle din kofar tayi kamar me na zari can kuma ta bude ta wuce part din sadiq  ta shiga dakin har yanzu bacci yake parlour ta dawo ta kuna kallo dan ba wani bacci take ji ba  cikin jin dadi take kallon arewa24 suna shirin tarkon kauna  gaba ki d'aya film din ya mata d'adi sosai sai da aka kamala film din misalin karfe 10:00 na dare sannan ta leqa dakin sadiq, bakin bed din ta tsaya tana qaremasa kallo a hankali ta kai hannu zata taba goshinsa amma ta kasa dunqule hannu tayi tana nazarin jikin nasa ganin ya motsa ya sata gyara tsayuwa tana kallon yanayinsa lumshe ido tayi a hankali ta kai hannu tata6a goshin sadiq ji tayi zafi rau kamar garwashi mamaki ne ya kamata da tsoro cikin rawar murya ta ce "Mai kyau?" shuru sadiq yayi saboda shi kad'ai yasan yadda yake jin fever na damu shi kneeldown fatuha tayi gaba gadon ta qara cewa, "mai kyau.! a qaro na biyu, bude sexy eye's ball's dinsa yayi a hankali yana kallon fatuha data fara matsar kwalla smile yayi ya ce cikin cool voice nashi "Menene fatuha? kin kasa bacci ne?" girgiza kai tayi alamar a'a "to menene? kallonsa fatuha ta kumayi ta ce "har  yanzu masasaran nan bata  sauka  ba  duk  da  likita  ya  duba  ka  tana matsama baka ji jikin ka da zafi ba? da a kauye ne da inna ta dafa ma magunguna kuma da kasha zaka warke, amma nan likita sai duba ka yake amma ka qi warkewa mai kyau, dan Allah ka daina tunani kaji shiyasa kaqi warkewa" ta fadi zancan tana zubar  da 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login