Showing 75001 words to 78000 words out of 105783 words
fatuha aiki sai gashi ta zama yar gida har zaku aura da ita hajiya na gode na gode, Allah ya bar zuminci" baba jummai ta fada tana share kwalla idanuwanta Mom ta ce, "haba baba ai duk mun zama d'aya ai fatuha ta cancanci abinda yafi haka, kamar 'ya take waje na" Mom ta fada cikin sanyin murya tana mai taya sadiq bakin cikin rashin fatu duk halin da yake ciki tana sane sarai, haka baba jummai ta dinga zuba Godiya sannan tasa kai ta fita, fatuha kuma ta shige bedroom ko da shiga d'aki sana'ar ta fara wato kuka dan ya zamar mata jiki daga shekaran jiya zuwa yau, bedside drawer ta bude ta ciro sarqar da sadiq ya bata tana kuka tana zancan zuci, dama duk abin da sadiq yake mata ba so bane mai yasa captain zai mata haka, bayan ta jima tana fama da sonsa tun kan tasan me so tunda tasa kafarta gidan ta kamu da son sa amma sai gashi wani sabon kuka ne ya kwacewa fatu kuka ta ci sosai har ta gaji sannan bacci ya dauke ta.
Bangaran Basma ban da murna ba abinda take daga ta kama wannan pillow sai ta saki ta Kama wannan, tana jujuyawa cikin dakinta cike da annushuwa, duk wasu qawayanta ta fesa masu zata auri handsome, har wani jin ta take a sama yanzu, zata auri captain.
majeed ko ya kira layin fatuha har ya gaji yanke shawarar zuwa gidan gobe yayi yaga sanyin idaniyansa, duk da cewa yasan ya mata katsalandan a ganin sa komai zai wuce, sannan ya juya ya gyara kwanciyarsa cike da kewarta.
Washe gari
Kiran sallah ne ya tashi fatuha jiki ba qwari ta shiga toilet ta sheqa waka ta dauro alwala wani irin jiri ke dibar ta, saboda kukan da tasha jiya dakyar ta iya gabatar da sallah ta zura uniform dinta ta dauki school bag din ta ta fito,
Ko da ta qaraso dining area Mom ce da Abba sai angel dake gefe cikin nutsuwa ta gaishe su kamar kullun taja kujera ta zauna, ruwan tea kawai ta iya hadawa tana sha kamar tana shan magani kamshin turaran daya doki hancinta ne yasata dagowa sadiq ne cikin uniform dinsa yana riqe da briefcase dinsa, yasha kyau har ya gaji sai dai fuskarsa ba walwala angel ce ta gaishesa ya amsa tare da yi mata peck, kallon shi fatuha take har ta kasa kauda idanuwanta haka shima sadiq ita yake kallo tuni idanuwan ta suka ciko da kwalla girgiza mata kai sadiq yayi alamar kar tayi kuka, yana murmushin dayafi kuka ciwo lumshe ido tayi tare da qoqarin hadiye kukan da ke niyar kuboce mata, sallamar majeed ce ta doki dodon kunanta, ware ido tayi tana kallon kofar sanye yake da uniform dinsa shima sai sheqi yake yayi kyau har ya gaji, qarasowa yayi tare da gaishe da su Mom amsawa tayi cikin fara'a, tare da cewa, "ya su Umma?
"su Umma lafiya lau Mom" sadiq dake tsaye take fara'asa ta dauke daurewa yayi ya tataro nutsuwarsa ya saki murmushin karfin hali ya ce, "my man yau kai ne da sasafe nan? Sosa keya majeed yayi tare da kallon fatuha kauda kai tayi ta cigaba da juya tea din dake gabanta dan ba sha take ba.
Haka sadiq ya dinga danne zuciyarsa, fatuha kuma haka ta gama juya tea din ta tashi tare da daukar school bag dinta, ta ja hannu jidda suka fice tare da yima Mom sai sun dawo, tana fita majeed yabi bayan ta haka shima sadiq kasancewar office zasu.
Zata shiga mota majeed ya ce, "baki ji ba..! daure fuska fatuha tayi dan wata tsanar majeed take ji juyowa tayi a fusace dan ta gayamasa mara dadi hango sadiq tayi bakin mota da alama su yake kallo, kauda kai sadiq yayi yana wani jin suya a zuciyarsa da rad'ad'i bale murfin mota yayi ya shige, murmushi fatuha ta saki wanda iyakar shi la66an ta ta ce, "uncle majeed ina kwana" cikin zaquwa ya ce, "lafiya lau my love," cikin sanyi murya ya ce "Fatuha!"
"na'am.! tace a taqaice dan dakyar take masa magana saboda tsanarsa da ke bin zuciyarta ya ce, "nasan na maki laifi my love naje nayi abu bada sanin ki ba amma please kiyi hakuri" wasu sabin hawaye fatuha ta hade ta ce "Ba komai.! tana qoqarin bale murfin mota ta tsinkayo muryar majeed "idan dai kin hakura please ki bini nayi dropping na ki? daure fuska fatuha tayi dan bata jin zata iya bin majeed a yanzu, lagwabe kai majeed yayi ya ce, "please ki bani dama duk da nasan bani da mazauni a zuciyar ki, musanman dana maki karantsaye, amma dan Allah kiyi hakuri ki so ni koda kad'ane, tunda nataso ban ta6a samun yarinyar da ta kwanta min a rai ba kamarki ba, fatuha please ki bani dama na gwada maki soyayyar da nake maki" haka majeed ya dinga magiya dakyar ya samu fatuha ta shiga motar shima sai da jidda suka shige ya ja motar.
Sadiq dake zaune cikin mota yana kallo su duk yadda suke, dakyar ya iya saita nutsuwarsa tabbas yasan duk ranar da fatuha ta zama malakin majeed ba abin da zai hana shi zama gawa, dakyar ya iya bude baki ya ce ma driver "ja mu tafi.! ba musu yabi umarnin ogansa suka bar haraban gidan.
suna zuwa wajen aikin Sadiq ya 6ale murfin mota ya fito tare da daukar jakarsa, ahankali yake tafiya kamar kazar da kwai ya fashema aciki, duk inda ya wuce ma'aikata nata gaisheshi hannu kawai yake d'aga masu, domin jiyake bakinsa yayi masa nauyi, yana zuwa office dinsa yabude yashiga, yayi jifa da Briefcase dinsa ya zauna bisa kujera wani kuka ne ya ku6uce masa mai radadi da ciwo, jiyake duniyar nayi masa zafi, bai ta6a sanin yana kaunar fautuha ba sai yanzu da yake shirin rasata, na har abada Why majeed ! me yasa zakamin haka? me yasa kake neman rushemin farin ciki na? me yasa zakace kana son Fatuha alhalin nafika bukatarta a yanzu, na fika son ta why majeed..! da karfin tsiya ya daki teburin dake gabansa ya ce, "nooooo Fatuha tawace insha Allah, danni aka halice ta" wani murmushin karfin hali sadiq yayi (da ni Salma nakasa gane ma'anar hakan)
Majeed nayin parking a harabar makarantarsu Fatuha ta kama murfin motar zata bude, da sauri ya dana wani remote ya rufe koffofin motar, cike da tsiwa ta dubeshi suna hada ido dashi ta sunkuyar da kai kasa, batasan meyasa majeed yake mata kwarjini ba duk yanda taso yimasa rashin kunya suna hada ido zata nemi nutsuwarta ta rasa, murmushi majeed yayi ya ce, "Haba My love, ya za'ayi kifita kibar mijinki da tsananin tunanin ki? ya kamata ki fada min wata kalma da zai sani tunanin ki koda ina office ne please matata kada kice min a'a" takaicine ya lullu6e Fatuha, ban da iskanci gidan uban wa aka d'aura mana aure dashi da har zai kirani matarsa taja tsaki a ranta mtsss, a fili kuma ta ce "Please uncle kabarni natafi dan Allah" ta karasa maganar kamar zata masa kuka "Sorry my lovely zaki tafi amma dan Allah kiyi min murmushi ko zan samu nutsuwar zuciyata?" Fatuha ta ce a ranta "Dan iska shege mugu kawai Allah yasa zuciyar ka ya dawama da bakin ciki kamar yarda kake qoqarin sani, A fili kuma tayi murmushi da iyakarshi le6enta, majeed ya bud'e masu kofar da sauri ta fita tayi gaba, jidda na qoqarin binta majeed yaciro kudi masu yawa yaba jidda shi kansa baisan ko nawane ba tayi masa godiya tare da masa peck a kumatu ta tafi da gudu domin har Fatuha tayi mata nisa, shima majeed cike da farinciki ya bar harabar makarantar.
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R
*Email* [email protected]
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
79_80
Ko da fatuha ta shiga class ba wani walwala, haka su Nana suka dinga tanbayar ta mai ke damunta ta fada masu meke damun ta, amma firtaqi gaya masu damuwar ta, Nana ce ta ce, "fatuha kenan baki daukemu a matsayin qawayan ki ba ko wayanda zamu kashe tare mu birne tare ba? Shiyasa zaki boye mana abin da ke damun ki" Zara ce ta budi baki ta ce, "Kyale ta Nana ai dai mun san matsayin mu yanzu, bai zama dole ta fada mana damuwarta ba" Zara na qoqarin jan Nana subar seat, fatuha ta riqe Zara ta ce, "please kuyi hakuri, zan fada maku damuwa ta.! ta ida zancan hawaye na sulalo mata, duk abin ya faru haka fatuha ta kwashe ta fada masu ta karashe zancan da cewa, "ina son captain so mai tsanani wanda ke tafiya tare da bugun numfashina amma sai gashi lokaci daya" kuka fatu ta saki mai cin rai ta fada jikin Nana tana gunjin kuka, Zara taji haushi ba kadan ba haka suka dinga bama fatuha hakuri tana raira kuka dakyar suka shawo kanta.
Bangaran majeed ban da dad'i ba abinda yake ji, zuciyar shi fes take daya lumshe ido kyakyawar fuskar fatuha yake hagowa sai ya qara sakin smile, matsala sa daya da fatu ta kasa sakewa da shi.
Jingine yake saman kujera office ya rasa sukuninsa, idanuwan shi na lumshe saboda nauyin da suka masa har wata masasara ke rufe shi ga wani irin zafi da qirjinsa ke masa, tamkar an daura masa dutse mai nauyi a hankali ya ware sexy eye's ball's dinsa da suka rine sukayi jaa wayarsa dak'e ruri cikin aljinhunsa ya curo sabuwar number ce baro-baro a screen din, da kamar ba zai dauka ba sai ya daure ya dauka tare da karawa a kunne, daga dayan bangaran cikin zazakar muryata cikin yauki Basma ta masa sallama, amsawa yayi a taqaice tare da tanbayar, "wake magana? gyara kwanciyar tayi daga inda take tare da kankame wayar dan wani irin sanyi ke ratsata, dan gyaran murya tayi cike da shagwaba ta ce, "Yaya sadiq ni ce fa Basma..! ko number ta ashe baka da ita? ta ida zancan cikin shagwaba Sadiq dake kishingide saman kujera, ranshine ya qara suya dan shi duduniya ba macan dake birge shi ko bashi sha'awa kamar fatuha, ko wannan magana ma da take yi jiyake kamar tana watsa masa ruwan zafi, tsuke fuska sadiq yayi kamar tana ganinsa ya ce, "Yanzu ina wani aiki ne letter mayi magana idan na dawo gida" bai jira cewarta ba ya katse wayar tare da yin wurgi da ita ta daki bango ta dawo watse ko ta kanta bai bi ba ya sa kai ya fice daga office din, domin idan ya cigaba da zama tabbas kwakwalwar shi da zuciyarsa suna iya bugawa.
bin wayar tayi da kallo tare da dan bata fuska, ta aje wayar ta kwanta.
Ko da aka tashi su fatuha majeed ne ya zo daukar su, ganin shine yasa ta had'a gira sama data kasa dan ba abinda ta tsana kamar ganinsa, ba yadda ta so haka ta bale murfin motar ta shiga tare da gaishe shi, kallon ta yake mai cike da so da kauna, sannan ya ce "My love daga gani yau kin sha wuya da yawa? ina fata dai kina kulla min da kanki?" dan guntun tsaki fatuha ta ja ciki-ciki sannan ta ce a cikin zuciyar ta "Har wani kira kake na kulla ma da kaina mtww dan iska kawai" muryar majeed ce ta doki dodan kunnan ta a karo na biyu ya ce, "My love! ko duk gajiyar ce tasa ko magana ba'a san yimin?" dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi la66an ta ta ce "A'a" murmushi majeed yayi tare da cigaba da driven, haka ya dinga janta da surutu tana amsa masa sama-sama sannan ya wuce da su shoprite yayi masu siyaya ice cream da cake, jidda ko sai dadi take ji dan har yanzu bata san inda aka dosaba.
Suna kunna hancin motar su, suka ci karo da sadiq wanda shima dawowarsa kenan wani irin dogon numfashi sadiq yaja a duk lokacin da yaga majeed da fatuha, numfashinsa sai ya nemi ya dauke ko qirjinsa ya dinga masa zafi, dakyar ya iya d'aga kafarsa dan baya so ko fuskar su ya gani sun fito a tare, amma sai dai kash majeed ya riga ya kira sunan sa. lumshe ido yayi ya tsaya chak! sai da ya kwashe yan mintina sannan ya waigo tare da sakin smile din karfin hali, ta gabansa fatuha ta raba ta wuce jidda nata zuba masa surutu sannan itama ta shige, miqa mashi hannu majeed yayi suka gaisa ya ce, "big man duk yau ban ganka a office ba"
"oh ina cikin office ina wani aiki ne gobe ma nake so na wuce Lagos"
"Lagos kuma? me zaka je yi lagos? cewar majeed
"zan je nayi 2week ne cikin ruwa na dawo"
"Eyya to Allah ya taimaka"
"Amin..! yana qoqarin shigewa majeed ya ce, "Baby..!
"yes..! ya ce a taqaice
"dama ina so muyi wata magana"
"ok mu shiga ciki" ok majeed yace tare da bin bayan sadiq suka shiga part din sadiq briefcase dinsa sadiq ya aje tare da rage kayan jikinsa ya shiga toilet, ya dade a toilet din baiyi wankan ba yana kukan bakin ciki sannan ya tashi yayi wanka, sanye da bathrobe ya fito da qaramin towel a hannusa yana goge jikinsa, majeed na zaune saman sofa shima tashi yayi ya shige toilet ya sheqa wanka ya fito ko da ya fito lokacin sadiq ya shirya cikin black 3 quarter da white shirt mai gajeran hannu, yana zaune saman sofa idanuwansa lumshe, shiryawa majeed yayi a tsanake sannan ya bude wardrobe din sadiq ya ciro riga da wando riga blue sai dark blue jeans sannan ya bude fridge ya curo fresh milk ya tsiyaya a cups ya miqama sadiq ya amsa.
zama yayi kusa da sadiq ya ce, "Please ina so kamin taimako guda daya please?
"ok inajin ka indai baifi karfina..! murmushi majeed ya saki ya ce "Bai fi karfin ka ba" gyara zama sadiq yayi yana sauraran majeed riqe hannusa majeed yayi cikin lagwabe kai ya ce, "please baby kamin hanya fatuha ta so ni..! tsura masa ido sadiq yayi da idanuwansa da suka ciciko da kwala hadiye su yayi yana saurara majeed ya cigaba da cewa, "baby ina son fatu wallahi ina sonta i love her more than how you think, ban ta6a jin son wata d'iya mace ba kamarta ba, baby karkayi tunanin irin son da nake ma sauran yan'mata nake mata a'a son ta nake da gaske ba da wasa ba, idan har na rasata zan iya rasa rai na ina jin sonta mai yawa sadiq na kamu da sonta mara musaltuwa ina manta kai a gabanta ita ce bugun zuciyata sadiq...! majeed ya fada, da sauri-sauri numfashin sadiq ke gudu zaune yake tamkar an dasa akwai yana bin majeed da ido kamar sakarai gabaki daya jikin shi ya mutu sai zuciyarsa dake tsinkewa kamar zata fito waje dan tashin hankali, dan matse hannusa da majeed yayi ya sasa dawowa daga duniyar tunanin, smile ya saki yana kallon majeed ya ce, "my man karka damu kaji d'an jama aji take amma nasan zata so ka kaji, kasan yadda mata suke amma nasan zata so ka har ku dai-daita babu macan da zata same ka ta fasa kai kasan da haka, kana da abinda kowace 'ya mace zata so ka" murmushi majeed ya saki tare da kaima sadiq hug ya ce, da gaske Bros..!
"Eh mana.!
"Ka tabbata fatu zata so ni?
"Sosai ma..! hawaye dake maqale idon sadiq ne suka cigaba da anbaliya dan ko yasan ya rasa fatuha, dan baya fatan abinda zai samu majeed dan uwan shi abokinsa mai son farin cikinsa bashi da aboki dan uwa saman da majeed, mai yasa ma tun farko yake kishin d'an uwan nasa, lokaci yayi da ya kamata ya ba zuciyarsa hakuri jin majeed zai zame jikinsa yasa sadiq saurin share hawayansa tare da sai ta kansa murmushi suka sakar ma junan su, fira suka fara sama-sama kiran sallah magrib ne ya tashe su.
1week letter
Shirye-shiryan aketayi a family house, kasancewa yau za'a sa rana biki duk wanda ka kalla cikin farin ciki yake musanman Basma da majeed.
zaune suke cikin d'akin yan'mata sunata zuba hira muryar Basma kadai ke tashi fatuha na gefe tana matsar kwalla dan har yanzu gani take kamar wasa, kamar kuma a mafarki tashi tayi ta fita daga d'akin ganin kayan da ake ta wucewa da sune yasa jikin fatuha qara sanyi.
fitowa tayi daga parlour hango qanan Baffa tayi su baba Barau kasancewa komai Abban sadiq ya ce zaiyi tunda fatu hannusa take, wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata yanzu ta tabbatar za'a samata rana da wanda bata so a matsayin miji kuka ne ya ci karfin ta, fita tayi daga gidan gabaki daya dan ko sanin inda zata ba tayi ba jefa kafar kawai take kan titi, can baba jummai ta fado mata a rai keke napep ta tara ta shige ta ce, a kaita gadan qaya" kasanwcewar gidan baba jummai kan titi yake bata wani sha wahala kwatantawa mai napep gidan ba kukan da take yasa mai keke napap din bar mata kudin saboda ya tausaya mata.
ko sallama bata cika ba ta shige gidan, baba jummai dake qoqari fita, fatuha ce ta fada jikinta tare da sakin kuka kamar ranta zai fita, rud'ewa