Showing 15001 words to 18000 words out of 105783 words
sakowa downstairs fuskarnan tamau dinning area ya wuce, lokacin kowa ya halara za'a fara breakfast gaishe da iyayan nasa yayi tare da yi masu peck a goshi sannan ya samu waje ya zauna.
Anuty bilki ce tayi serving d'in kowa suka fara cin abincin, Mom na lura da sadiq dan ba wani cin abincin yake ba ga fuskar shi d'aure haka shima Abban nashi yake lura, Inda sabo ya kamata su saba da irin wannan halin nashi yau da fara'a gobe babu, a hankali ya ke cin abinci loma uku zuwa hudu ya miqe Mom ta ce, "Son..!
"yes Mom"
"Har ka qoshi?
"Eh na qoshi"
"Amma kasan ba zamu shirya ba ko wannan ai ba abinci ka cin ba" Abba ya amshe zancan da cewa, "shiyasa Jidda bata san cin abinci shiya ke koya mata hakan" Shagwabe fuska yayi ya ce, "Abba na sha fresh milk a d'aki da yawa shiya bana jin yunwa"
"uhm lallai dama fresh milk abinci ne? inji Anuty bilki 6ata fuska ya kuma yi ya ce, "to ni ina sha na ko shi" Langwabe kai yayi ya ce, "Angel wai daddy ne ya koya maki rashin cin abinci?
"no daddy kai da kake cin plate biyu" kowa na dining sai da yayi dariya har da sadiq din wanda tun tashin shi baiyi dariya ba Mom ta ce, "Ohni Jidda wato kare daddy ki zakiyi ko? Mom ta ida zancan tana lakace mata hanci.
******
Ba ita ta gama wankin ba sai yamma likis ta wanke su tas suka fita, inna washe da baki ta ce, "ko ke fa d'iyar Baffan ta" turo baki tayi gaba tare da zubar da ruwan d'aurayar a maguji Inna ta ce, "Oh fushi ake dani dan nace ayi tsaf ta? sallamar Baffa ce ta katse mata zancan washe da baki ya shigo had'e da sallama.
Ledar dake hannu Baffa fatuha ta amsa ya ce, "yar albarka yau wanki akayi kenan? inna ta amshe zancan da cewa, "kasan ko faman dana sha da ita sannan tayi wanki?
"ki ce min dai matsa mata kikayi"
"ai dama kai baka ganin laifin ta"
"hmm fatuha dama Ledan nan tsarabar yallo ce na makin" washe hakora tayi ta ce, "Toh Baffa na gode.!
"Yauwa yar albarka" inna ta shige qurya ta kwaso ma Baffa abincin sa.
Cikin jin dadi ta gama wanke yallon da zubo masu inna na su, sannan ta d'au nata dana fatsima ta fice.
*****
After sun gama breakfast kaitsaye family house suka wuce.
karku so kuga soyayya dangi ba tsangwama ba tsana sai tsantsar soyayya, wadda uwar mazajan na su ke gwada masu ba tare data banbanta wani ba.
Wani katafarin parlou ne wanda ya amsa suna shi yasha red carpet mai laushi sai manyan kujeru red n black, sosai tsarin parlou ya had'u Alhaji kabiru ne ya fara magana cikin muryar shi ta manya da natsuwa yana fadin irin kadarurin da suka samu a kasuwancin su, inda Baban nasu ya yanke hukunci za'a raba kudin kashi biyar, kashi 5 nasu kashi biyar na taimakon Al'umma, Kashi 2 za'a kai gidan marayu kashi 1 asibiti kashi 2 taimakawa marasa karfi, sosai sunji dad'in yarda Baban nasu ya tsara abin bayan sun gama tattaunawa akayi addu'a aka tashi kowa ya koma harkar gaban sa.
"Big man wai lafiya yau sai wani cin magani kake? inji majid sadiq ya ce, "to wazan ci ma magani kai wallahi ka bani sai shegyan surutu" ya ida zancan ya furzar da iskar bakin shi, "Naje nayi surutun in fitsari arhane wani yayi mu gani, wani saboda tsabar rashin yin maganarsa bakinsa wari ya ke" ya ida maganar yana dariya "oh dani kake ko? da gudu majid ya ruga part d'in Ammi sadiq ya bisa Ammi da ke hira da surukanta.
majid ya zo ya boye bayan ta Ammi ta ce, " Lafiya kai kuma?
"wallahi Hajiya.! bai ida zancan ba sadiq ya shigo fuska d'aure Ammi ta ce, "Ayo ai sai ka ce min wannan mai bakin ran ka tsokano" kowa na d'akin sai da ya murmusa, langwabe kai sadiq yayi ya ce, "Ammi yanzu nine mai bakin rai, kin san mai yamin kuwa?
Alhaji ya ce, "rabu da su aikai d'an wuri nane kaji" Majid ko gwalo ya masa bai san Ammi ta gansa ba ta ce, "to ja'iri Ashe kai ka tsokane sa tashi ka ban guri" dariya kowa na parlou yayi.
Sosai jin dadi suke family inda suke hira cikin ni shadi..
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Blood sister deejah
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
21_22
Basu suka dawo daga family house ba sai 9:00pm, Anuty bilki ta wuce gidan ta.
A gajiye likis ya dawo dan haka direct toilet ya shiga yayi wanka yana fitowa ya d'au jidda ya mata wanka sai rigima take masa, sai daya gama shirya ta tsaf ya samata night dress pink wando da riga ya raba mata gashin ta gida biyu sannan ya kwatar da ita ya ce, "Oya yanzu ayi bacci"
"Bana jin bacci daddy please ka bani story"
"Ok angel bari daddy ya shirya"
"Toh daddy am waiting" Sai daya shirya sannan ya qarewa d'akin kallo ba laifi ta gyara d'akin amma dai shi gyaran bai masa ba, riqe da story book din jidda ya dawo saman bed lokacin har tayi bacci smile yayi tare da yi mata peck ya jawo laptop d'in sa ya cigaba da aiki, bashi ya gama aikin ba sai 12:00am sannan ya kwata tare da jawo Jidda jikinsa kamar za'a kwace masa ita.
****
Sosai suke kallan gad'a washe da baki kasancewar yau suka fara zuwa Fatuha ta ce, "ta6 Alqawalin Allah kallo na wuce mu"
"Sosai ma" inji fatsima
"ke ni daga yau ban qara fashi wallahi kullun sai na zo"
"nima haka Qur'an" haka suka sha kallan gad'a daga nan kuma suka fara tsokana dan wannan ya zamar masu jiki sannan suka dawo gida.
****
Tunda safe ya tashi kasancewar yau Monday cikin shirin shi na uniform ya ke shiryawa ba qaramin kyau yayi ba, gafen da Jidda ke kwance ya kalla da alama baccin ya mata dad'i dan haka sai bai tashe ta ba hakan yasa baiyi mata wanka ba, briefcase nashi ya d'auka tare da yi mata peck ya fita.
A parlou shi ya ci karo da rabi'a na shara, kallan tsana ya bita da shi har yayi gaba ya dawo ya ce, "Keeee..! cikin tsoro ta d'ago qara murtike fuska yayi ya ce, "Angel na bedroom tana bacci so kibi hankali karki tashe ta, kuma idan tatashi ki mata wanka kina jina..!
"Eh..! ya watsa mata harara ya ce,
"saura na dawo naga kin min sata" ya ja tsoki ya fice.
A main parlou ya samu Mom zaune tana karanta azkar, har qasa ya duk'a ya gaishe ta tare da yimata peck Mom ta ce, "baby..!
"na'am..!
"Ina Jidda sarkin kiriniya?
"Jidda na bacci."
"Ok shiyasa ban ji motsinta ba kenan"
"eh Mom so nake ma na samama Jidda school da malamin islamiyya ya rinqa mata a gida"
"Ai hakan na dakyau kamar kasan maganar dana ke san yimaka kenan ka rigani" smile yayi tare da wucewa dining area a tsaitsaye yayi break ya fita.
*******
Tana tashi tayi wanke-wanke sannan ta share gidan su qwal ba laifi yanzu fatuha anfara yin aiki shima din sai tasa kanta, inna ce ta fito washe da baki ganin abin arzikin da fatu tayi ta ce, "Ah'ah fatuha an fara zama yan'mata, dubi yarda gidan yayi fes gwanin birgewa" rufe fuskarta tayi ala dole kunyar inna take ji inna ta ce, "ohni fatuha kunya na ake ji to madalla Allah ya shirye ki?
"Ameen inna" tare suka shiga madafi yau dai ba laifi fatuha tayi aiki sosai dan yau ko damar zuwa gantali bata samu ba.
****
Baba jummai ce cikin d'aki sai harhad'a kayan ta take cikin ganamasgo cike da tsantsar farin ciki Mom ce ta lek'o dak'in tana cewa, "Baba sai sauri kike ki tafi harkin had'a kaya" Washe baki tayi ta ce, "wallahi na matsu na ganni a wudil d'in nan na dad'e banga d'an uwana ba jauro"
"gaskiya kam, yauwa maganar samomin yar aiki fa? dan Allah baba jummai ki samomin natsatsa wadda zata iya aikin nan kisan halin baby da shegiyar tsurfa"
"Insha Allah zan duba maki" Sannan Mom ta ciro maqudan kudi tabawa baba jummai tayi tsaraba tare da had'ata da driver ya kaita tasha, murna wajan baba jummai ba'a magana,
Ana kaita ko tasha ta samu motar zuwa wudil dama mutun d'aya ake jira tana shiga mota tatashi.
***
Baffa ne tsaye bakin kofar d'aki yana cewa, "ladingo ni zan wuce yau da wuri zan dawo karki aiko min da abinci"
"toh malam" fatuha da ke zaune bisa tabarma ta ce, "Baffa zanbi ka"
"kinga zafi ake ga rana idan muka je tare wuya zaki sha fatuha" baki ta turo gaba ta fara matsar kwalla Baffa ya ce, "toh shikenan d'ako hijabin ki muje" washe baki tayi tare da shigewa akurkin d'akin ta ta d'auko hijabinta suka fice.
Misalin karfe 2:00pm motar su baba jummai ta tsaya a tasha wani irin dad'i ne ya lullu6e ta yau ta zo mahaifarta zata ga d'an uwanta da iyalan sa mashin tatara kasancewa mota bata shiga cikin garin sai dai mashin ko amalanke.
Direct gidan Baffa aka sauke ta tare da biyan maimashin sannan ta sauke yan kayan ta da tsaraba, washe da baki ta shiga gidan tare da sallama, inna dake qoqarin fitowa daga madafi chak ta tsaya, saboda tsabar murna ta rasa ina zata tsoma kanta ta ce, "Ah'ah muta nan birni sannu da zuwa" ta qarasa zancan tare da shinfid'a mata tabarma ta d'ebo mata ruwa a kwanon sha na randa mai sanyi Baba jummai ta ce, "ah ladingo sai hidama kike kya bari mu gaisako" Washe baki tayi ta ce, "mutun ya sha tafiya ruwan sha ya gagaresa, toh ya hanya?
"Hanya lafiya lau, ina fatuha yan'mata nasan yanzu dai samari sun fara yi mata layi masha Allah, indai kyau ne fatuha akwai shi"
"Hmm..! inna ta ce ta marairaice ta ce, "sun fita da Malam zuwa gona, maganar samari kuwa fatuha babu su, fatuhar da bata ganin kowa da gashi a kauyan nan wani uba ne zai yarda d'an sa ya auri fatuha bayan ta masu rashin kunya, malam baya ganin laifinta ko kad'a ko nayi mata magana zai fara sababi"
"alallai jauro haka ya bar fatuha ta zama abinda ta zama ohni jummai.! bari shi jauron ya dawo ya same ni" Haka inna ta rinqa lalla6a ta dan bata so tayi ma Baffa magana saboda kan fatuha bai jin kunyar maida magana haka baba jummai ta gama kunfan baki.
****
koda jidda tatashi bata ga daddy din ta ba, dakyar ta yarda rabi'a ta mata wanka shima sai da Mom tasa baki, ana gama mata wanka ta sako downstair wajan Mom tana mata surutu can ta ce, "grandma Ina baba jummai yau bata min wanka ba ita da daddy" ta Ida zancan tana matsar kwalla Mom ta ce, "sorry angel" tare da goge mata kwalla sannan ta jata jikinta ta ce, "baba jummai ta je kauye lokacin da zata tafi kina bacci shiyasa angel"
"Grandma shi kuma daddy fa ya tafi ya bar little princess d'in sa at home"
"sorry angel ai zai dawo kin ji.!
"grandma please call him"
"Ok angel amma sai kinyi breakfast sannan"
"ok..!
"oya muje nayi feeding naki.
Alhaji ne yayi gyaran murya ya ce, "uhm kina shan fama babanta ya maki rigima ita ma ta maki" murmushi tayi tare da shafa sumar Jidda wadda tasha gyara, tana feeding Jidda sai da suka gama tsaf sannan shima Alhaji ya wuce office.
After sun gama cin abincin Mom ta kira sadiq, yana zaune saman kujerar sa ta office idanun sa a lumshe kamar maiyin bacci wayar sa ta fara ruri a hankali ya bude sexy eye's ball d'insa ya sauke su kan screem d'in wayar, sweet Mom ne rubuce hannu ya kai ya d'auka.
daga d'ayan bangaran Mom ta ce, "hello baby ya kake ya aiki?
"lafiya lau Mom"
"Dama wannan ja'irace ta matsamin ka tafi aiki baka tashe ta ba, sai rigima take mani" murmushi yayi daga dayan bangaran hakan sai ya qara fitowa da zallan kyan sa numfasawa yayi ya ce, "Mom bata wayar"
"ok..!
Jidda dake zaune saman cinyar Mom ta washe baki tare da amsar wayar ta ce, "daddy..!
"yes angel" 6ata fuska tayi kamar yana ganin ta ta ce "shine daddy ka tafi work baka tada little princess d'in kaba"
"sorry angel lokacin kina bacci bana so na tada little princess na bacci that is why my angel"
"ok daddy inka dawo zamuyi wasa ko?
"yes mana" washe hakora tayi sannan ta ce, "uhm daddy.! ta qara bata fuska ta ce, "daddy baba jummai tatafi kauye ban dani bayan tamin promise tare zamu tafi"
"sorry angel next time tare zamu tafi kinji"
"Yeeee love u daddy.!
"Love u more angel bye" sannan ya katse wayar tare da binta da kallo.
"Yanzu tunda kinyi wayar da daddy naki sai ki huce ko" cewar Mom dariya tayi ta cigaba da zuba ma Mom surutu..
****
Aiki Baffa yake sosai fatuha na gefe tana taya shi, tare da bashi labari tana fadin abin dariya ya dara haka har suka gama.
d'auke da sallama suka shigo inna na zaune saman kujerar tayani gulma tana dama hura saboda Baba jummai nasan hura musanman damun inna, washe da baki suka qaraso fatuha ko jikin Baba jummai ta fada tana mata oyoyo Baffa ya ce, "Ah'Ah wanake gani kamar mutanan birni sannu da zuwa" sannan Baffa ya samu guri ya zauna inna ce ta ce, "ohni fatuha yaushe zaki girma kin fada mata jiki salan ki karya ta.! baki ta turo gaba ta ce, "Kai inna har wani nauyi ke gareni tare da matse yar kwalla, baba jummai ko dariya abin ya bata...
Writte by
Salma mas'ud nadabo
Editing Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
23-24
Tashi tayi daga jikin inna tana zun6uro baki gaba, Inna ta ce "Yar nema ba'a isa ayi maki magana bane ko me?
"Haba ladingo wai me yasa kike so ki rinka takura wa yarin yan nan ne? cewar Baffa Baba jummai ce tasa baki ta ce, "Ah kuyi hakuri dai, Indai jiki nane ai ta sauka ko? Inna ta murmusa batace komai ba.
Duk wata tsaraba data kawo haka ta bajewa fatuha kayan zaqi fatuha ko baki har kunne dan dadi saboda har da bakar alawa, wato (chocolate) haka shima d'an uwan nata da matar sa ta basu nasu tsarabar, sosai sunji dad'i musanman ladingo wanda take ganin baba jummai ta d'auke ta tamkar ciki d'aya suka fito, so da yawa tana fifitata kan jauro d'in ma saboda karamci irin na baba jummai da sani darajar d'an adam, sosai suka ji dadin wannan tsarabar.
A guje fatuha ta qaraso gidan su fatsima kawo mata nata tsarabar, saboda dama ta mata alqawari duk sanda baba jummai ta zo, to zata kawo mata bakar alawa"(chocolate) .
Washe da baki ta qarasa cikin gidan nasu tana cewa, "Fatsima! Fatsima!
"ohni fatuha lafiya nagan ki haka? ko yauma tsokana kukayi? inji gwaggon fatsima washe baki tayi ta ce, "Wallahi gwoggo baba jummai ce ta zo yau shine na kawo wa fatsima tsarabar ta"
"Ayya ki ce min mutan birni sun zo, aiko fatsima na kewaye ki jira ta tafito" bata ida rufe bakin ta ba fatsima ta fito washe da baki Ta ce "Fatuha"
"na'am..! tare da qarasawa wajan fatu ta ce, "ke baba jummai fa ta zo Qur'an"
"Dan girman Allah? washe baki ta kuma yi ta ce ."Tayi tsarabar baka alawa?
"Eh Qur'an gama taki nan na kawo maki,"
"kai amma naji dadi" haka suka shige akurkin dakin fatsima suna ta hira tare da sherance muta ne inna da ke tsakar gida sai cewa ta ke Allah ya shirye su.
****
A gajiye ya dawo gida briefcase din shi da ke hannu yaronsa OLA ya amsa cikin sallama ya shigo falon, Mom na zaune a parlou tana kallo angel na kusa da ita tana bacci, A hankali ya qaraso yayi hug din Mom ta baya ya ce "Wash Mom am tied" juyowa tayi suna facing d'in juna ta amsa masa da cewa "Sorry son ka je part d'inka kayi taking shower lunch inka na jiran ka"
"Ok, face din Jidda ya dan shafa.. sannan ya haura upstairs.
Yana shiga part na shi bathroom ya wuce yayi wanka ya fito sanye da bathrobe white, A hankali ya nufi dress mirror ya fara shafa lotion mai kamshi yabi ko ina na jikinsa da shi, kai tsaye Wardrobe d'insa ya nufa ya curo three quarte black sai armless t-shirt ya sa , ba qaramin kyau yayi ba masha Allah.
Cikin natsuwa ya ke sakowa daga downstairs ya qaraso parlour inda ya bar Mom har yanzu nan take, Dining area ya nufa, ya ja kujera ya zauna rabi'a na gefe a hankali ta fara saving na shi tuwan shinkafa miyar egushi wanda taji kaji da yan ciki kamshi sai tayi yake, sai data gama serving nashi sannan ta mike, harara ya dala mata dan shi kwata-kwata yan' aikin kona masa rai suke musanman yan'mata wayanda ba abinda suka sa gaba sai halin bera, wani wawan tsoki ya kuma ja wanda yasa rabi'a kyarma, dagowa yayi da sexy eye's ball's din shi ya ce... "Keeee!Tunda kin gama zubamin abincin ai sai ki tafi ko? ko sai kin gama qaremin kallo eeye."
Mom dake parlour sai data ji tsawar da Sadiq ya daka ma rabi'a juyowa tayi ta ce, "Why son? Wai me yasa kai kullun sai an jika da masu aiki ne baby? gashi nan yanzu garin fad'an ka ka tada angel daga bacci" Bata fuska yayi kamar qaramin yaro ya ce, "Mom ni wallahi bana san yan'aikin nan yawancin su duk barayi ne Mom kuma qazamai" ya ida zancan yana tsame hannu sa