Showing 30001 words to 33000 words out of 105783 words
dai-dai cin ta tasa hannu ta fara ci hankalin ta kwance tana ci tana lumshe ido saboda tana son chips sadiq bala mata harara ya ke tayi wata loma da tayi sai da abin ya kusa bashi dariya da haushi duk suka had'e masa ita ko ko a jikin ta su Mom ma harkarsu suke.
Bayan angama breakfast har bakin mota sadiq ya raka jidda, fatuha na riqe da lunch box din jidda sai da ta tafi sannan suka juyo zasu koma gida, da gudu fatuha ta wuce sadiq sai da taje bakin kofa sannan ta juyo ta masa gwalo tare da kwaikwayar yarda yake tafiya ta fashe da dariya ta shige da gudu, cije lips din shi yayi tare da tura hannu shi cikin sumar sa ya ce, "oh Allah ka bani ikon cima yarinyar nan sannan shima ya qarasa parlour ko da ya shigo ba kowa sai baba jummai da ke kwashe kayan breakfast, gaishe ta yayi ta amsa washe da baki, part din shi ya wuce ya murda handle din kofar ya ji rufe mamaki ne ya rufe shi fatuha da ke jingine jikin kofar ta ce, "mai kyau kwarankwatsi ban bud'e ma kofar nan sai na gama aiki na dan nasan halin ka kai mugune wallahi, ka na shigowa zaka bigeni" sadiq da ke wajan kofa yayi sororo yana mamakin raini da fatuha ta masa cige lips yayi tare da barin gurin saboda ya san idan ya cigaba da tsayawa har kashe ta sai yayi dan bacin rai, fatuha jin ya tafi yasa ta cigaba da aikin ta tanayi tana yan'wake-wakyan ta har ta gama tuni daki yayi kyau sosai sannan tabi part din da turaran wuta tuni part din ya dau kamshi da kyau sannan ta qara gudun AC dakin ita kanta sai da taji kamar tayi bacci dan Kyan da part din ya mata.
A hankali taje bakin kofa ta murda handle ta leqa taga ba kowa, sannan ta fito da sauri ta wuce sadiq da ke kwance saman three star idanuwan shi lumshe kamar me bacci yana kallon fatuha ta ruga daki da gudu ta kule, tsoki ya ja tare da tashi duk kiyi ki gaba zan kamaki ne tare da wucewa part nashi dan bacci yake ji ko da ya shiga part din shi da kanshi sai da yayaba kyan da part din yayi, ga kamshi sai tashi yake da sanyi irin yadda yake so lumshe ido yayi ya ja jiki ya hau bed ya kwanta.
Tana shiga bedroom kayan jikin ta ta rage ta shiga toilet, tayi wanka sosai dan yanzu ba qaramin jin dadi take ba idan tana wanka amma da a kauye sai anyi da gaske, yanzu ko fatuha ansan muhinmancin wanka, daure da towel ta fito ta goge jikin ta tare da shafe jikinta da lotion mai kamshi ta feshe jikin ta da turare yar hoda da murza duk ba wata kwalliya tayi ba masha Allah fatuha tayi kyau, uniform din ta ta zura sannan tataro gashin ta wanda ya cure gudaya tana qoqari kamashi amma ta kasa saboda yawan shi da tsaho 6ata fuska tayi tace, "Allah sarki inna da kina kusa da kin gyara min" magana da su kayi da Mom ce ta fado mata daure kan tayi da sauri ta haura upstairs dakin Mom ta shiga ba ta nan neman ta ta shiga yi, kitchen ta shiga tare da tanbayar su rabi'a ina Mom, ta ce mata tana part din Abba ,toh tace tare da komawa parlour ta samu wuri ta zauna tana kallkn film din India tana washe hakora.
Mom ce zaune da Abba a bedroom din shi tana zaune saman kujera a hankali ya qaraso ya rungume ta ta baya, murmushi tayi ya ce, "madam kullun qara kyau kike baki tsufa gashi har da jikoki," dariya tayi ta ce "Ya za'ayi na tsufa bayan mijin nawa kullun yaro yake komawa" hancinta ya ja cikin tsokana ya ce, "uhm next week zan koma uk kan magana nan gaskiya this time around ban tafiya ni kad'ai, tare nake so mu tafi" murmushi Mom tayi ta ce "Kamar kasan abinda ke raina kenan" smile yayi ya ce, "uhm kuma sai gashi na rigaki fada ba," ya ida zancan tare da yi mata kiss a kumatu ta ce, "ni ko Abban sadiq kunyi waya da jawad kuwa? dan murmusawa yayi ya ce, "Eh jiya munyi waya ya ce min yanzu shukura tsohhon ciki gare ta, so yake in ta haihu sai su zo ganin gida" murmushi Mom tayi ta ce, "Allah ya sauke ta lafiya kamar kasan nayi missing nashi wallahi ya kamata jawad ya dawo Nigeria da aiki, amma nasan ba lallai bane ya so ba saboda na lura yafi sin London sosai,"
"uhm ke dai ki ce d'anki kike san gani, yauwa gobe ki shirya ina so muje wajan Ammi muyi masu sallama kafun mu tafi" to tace masa tare da tashi zata fita jawo ta yayi jikinsa ya ce, "please idan kinje karfa ki dad'e ki bar tsohon mijin ki da jira kinji" murmushi tayi tare da kashe masa ido.. lol ah tsofafi na konewa hehe.
( shawara ga mata please mata ya kamata musani tsufa baya hana soyayya karki ce dan kina da manyan ya'ya ki ce ke kin girma ita soyayya bata girma, kuma gyara da tatalin miji shi ke qara dankwan soyayya, so da yawa wasu matan suke jawa maza jansu bin mata saboda kina ganin kin girma komai sai ki daina, idan mijin ki mai so ne daga nan zai fara bin ya'ya cikinsa a waje suna masa yana jin dadi please mata mu kiyaye) .
Fatuha da ke zaune saman kujera tana kallo, Mom ce ta sauko daga upstairs, cikin ladabi fatuha ta gaishe ta tare da tuna mata maganar gyaran kan, toh shikenan Mom ta ce, "je ki shirya mu tafi,"
"Mom bada wannan kayan zani ba?
"eh kisa kayan gida" toh tace mata ta shige bedroom, Mom ko part din Abba ta koma ta tanbaye shi zata fita ya bata izini, sannan ta dawo dakin ta ta shirya cikin atamfa black mai ratsin red n yellow bubuce mai kyau tuni Mom ta fito sosai bedroom d'in fatuha ta wuce tsaye, ta same ta ta rasa kayan da zata sa washe da baki momt ta qaraso ta ce, "fatuha har yanzu baki shirya ba? shagwabe fuska tayi ta ce, "Wallahi Mom na rasa kayan da zansa ne, zabamin dan Allah" to tace mata wata hadadiyar gown Mom ta janyo brown colour mai ratsin milk da Stone's a jikin rigar mai dogwan hannu ce sai veil milk, masha Allah fatuha ba qaramin kyau kayan suka mata ba cib suka mata qirjin ko kamar tasa bara saboda yadda kayan suka mata rolling veil din tayi da gashin ta data daure sai abin ya bada kala ta fito fes, takalmi tasa black mai kyau suka fito, direct parking space suka wuce Mom ta jasu suka fita sai fatima salon da ke gandu.
Basu wani dad'e ba a Solon din ba sosai aka gyara gashin fatuha dan ko mai ba'a sa mata ba saboda laushin gashin ta dan idan aka sa masa mai, zai iya konewa gyara shi kawai akayi masha Allah ita kanta fatuha sai da ta tsorata da gashin ta saboda har qugunta ya kai, da yaji gyara amma sai ya rage yawa su kansu yan wajan yaba gashin su kayi ana gamawa suka dawo gida, a parking space moym tayi parking suka fito har zasu shiga gida sai ga driven jidda ya kunno kai yayi parking da gudu jidda ta qaraso tare da rungume fatuha ta ce "Anuty kinyi kyau,waya maki kwalliya?" dariya fatuha tayi dan ita ba wanda ya mata kwalliya d'aukar jidda tayi suka qaraso parlour sadiq na zaune saman two star yana shan coffee gefensa kuma baba jummai ce suna d'an taba hira da shi da alama tafiya zatayi.
Cikin sallama suka qaraso, sadiq ya amsa sallamar, fatuha ke dauke da jidda, jidda ta zame daga jikin ta ta ruga wajan sadiq ta rungume sa wasa ya shiga yi mata tana dariya qarasowa Mom tayi ta zauna saman three star ta ce "Oya a wuce aje a cire uniform, kin bar Anuty na jiran ki " sadiq ne ya dago ya kalli fatuha ya wani tabe baki tare wurga mata harara ya miqa mata jidda, baba jummai ko sai yaba kyan da fatuha tayi take tare da yima su Mom sai da safe fatuha kuma ta ja jidda zuwa bedroom.
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com
*fan's ana mugun tare dinnan sosai*🤝🏽
39_40
Bayan ta gama ma jidda wanka ta shafe ta da mai tare da saka mata kaya jeans n t-shirt riga pink wando bleu sannan ta gyara mata gashin ta, tuni jidda ta fito tayi kyau masha Allah, toilet ta koma ta d'auro alwala kasancewa 4:00pm tayi ita da jidda suka gabatar da sallah suna idarwa fatuha ta cire veil din kanta tana kallon gashin ta a mirror tana washe baki, jidda ce ta ce, "Anuty gashin kine haka? jiyowa fatuha tayi washe da baki ta ce, "kema kin gani ko? Ai Allah daga yau na gama yawo da d'ankwalli wallahi wannan gashi kamar ba nawa ba"
"gaskiya Anuty kina da gashi dama ki qaramin.! Jidda ta ida zancan tare da washe hakora murmushi Fatuha tayi tare da maida dankwallin ta jawo hijabinta dana jidda suka wuce wajan malam.
Sosai suke karatun, damma karutun ya zo ma fatuha da sauki dan duk wani qari da malam ya mata jiya ta juye masa shi, shi kansa yana yabawa da qoqarinta, qara musu yayi, dan haka basu suka shiga gida ba sai 6:00pm
Sadiq dake tsaye gaban dress mirror yana gyara sumar shi a hankali ya ji an bud'e kofar dakinsa, cikin zafi rai ya juyo a tunaninsa fatuha ce ta zo masa da wani sabon rainin sai kuma idanuwansa ya gane masa majid.😀
6ata fuska yayi tare da juya masa baya yana mai cigaba da shirinsa cikin nutsuwa, smile majid yayi ya qaraso with full confidence nasa ya ce, "big man fushi kake dani ko?
kauda kai sadiq yayi ya nufi wajan drawer yana ciro kayansa murmushi majid yayi tare da zama saman sofa, tsaf sadiq ya gama shiryawa fuskarsa daure ya dau phone nashi da ke bedside drawer, zai fita majid ya riqe masa hannu tare da shagwabe fuska ya ce, "sorry bros.! juyowa sadiq yayi ya wurga masa harara ya ce, "leave me alone..! tare da fisge hannusa zai murda handle na kofa kenan majid ya ce, "haba sadiq am sorry nine fa majid" juyowa sadiq yayi yana kallonsa ya qara bala masa harara ya ce, "kasan da haka shine ka manta dani ko?
"sorry kasan bana zama sosai shiyasa amma ai na kusa dawowa nan da aiki, ka ga dawo ka zauna muyi magana" Jin hakan yasa sadeeq sakin handle d'in kofa ya dawo ya zauna majid ya ce, "baby me ya samu qafar ka naga kamar kana d'ingishi?
jan tsaki sadiq yayi ya ce "tsautsayi ne kawai"
"eyya sorry " sadiq ya ce, "Tashi muje parlour na gaji da zama a bedroom"
"OK.. Majid yace
parlour suka koma suka dasa sabuwar hira basu suka daina hira ba sai magrib, dauro alwala sukayi tare da wuce wa masallaci
"Aunty..!
"na'am.!
"dan Allah ki koyamin qarin d'azu ban iya ba sosai,"
"to shikenan nima zaki koya min na boko ko?
"eh zan koya maki mana Aunty"
"To bari mu fara yin sallah" Tashi sukayi tare da dauro alwala suka gabatar da sallah bayan sun idar fatuha ta qara biyawa jidda karatun sannan jidda ta fara koyawa fatuha ABCD karku so ku ga kwamacala dakyar-dakyar ta dan iya shima ba sosai ba amma tasa ma ranta sai ta iya ko dan ta dinga jin abinda sangami ke cewa wani lokacin.
Bayan sun dawo masallaci majid ya fad'a two sitar ya ce, "wash am tied..!
Guntun tsaki sadiq ya ja ya ce "kai dai kam ka bani daga zuwa masallaci har ka gaji sai ka ce ba namiji ba mtss..! fruit ya curo a fridge ya fara ci majid ya zuro hannu suna ci suna hira majid ya ce, "ni fa na fara gajiya da wannan gwarancin aura zan zo nayi wallahi.! smile sadiq yayi ya ce, "aiya kamata kam dan gaskiya ka dade ba aure"
"aikai ma ya kamata kayi wani auran sadiq, duba da yau kusan shekara kausar 5 da rasuwa sadiq, ya kamata kayi aure haka ko saboda angel..! 6ata fuska sadiq yayi ya ce, "majid bana tunanin zanyi wani abu wai shi aure yanxu, tunda na rasa kausar na rasa wani 6ari na rayuwata, majid kafin a samu mata kamar kausar sai antona, kausar tatara komai dana ke so agun mace, bana tunanin akwai wata ya'mace da zata iya maida gurbinta" ya ida zancan cikin sanyin murya hawaye masu zafi na zubomasa kallon tausayi majid ya masa cike da lallashi ya ce, "sorry baby na famama inda kema ciwo ko? girgiza kai yayi tare da goge hawayan idanusa da bayan hannu yayi smile ya ce, "majid baka famamin komai ba, indai tunanin kausar ne ba yau na fara ba, yau kusan 5 year da ita nake kwana da ita nake tashi majid.! murmusawa majid yayi tare da qoqarin canza topic dan a duniya ba abinda ya tsana irin damuwar sadiq haka shima sadiq ba abinda ya tsana irin damuwar majid, kallon ball suka shiga yi tare da yin musu dama sun saba ba yau suka fara ba danma yanzu sun girma ne, da da ne har kuka sai Sadiq ya sa majid cikin nishad'i suke kallon.
"Kinga zo muje mu ci abinci muyi sallah na maki wanka kafin baban ki ya biyo mu" washe baki jidda tayi fatu na rike da ita suka koma parlour dining area suka wuce fatuha ta fara saving nasu tuwon shinkafa miyar taushe taji Alayahu da kaji cikin nutsuwa suke ci a plate daya.
bayan sun kamala fatuha ta kwashe kwanikan ta kai kitchen jidda kuma ta haura upstairs, dan tayi missing daddy tun da ta dawo daga school bata qara ganin sa ba, bata iya jira har sai an mata wani wanka, a hankali ta murda handle din kofa a zaune ta gansu a parlour rugawa tayi jikin majid tana cewa, "small daddy I miss you.! smile majid yayi, "miss you my angel how are you?
"fine uncle" sadiq ne ya murmusa ya ce "ni fa yanzu fushi nake da angel tunda tayi new Anuty take mantawa da daddy" 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka take ce, "uncle ba haka bane new Anuty na da kirki kuma tana min wasa kuma kasan wani abu daddy" sai ta zamo daga jikin majid taje ga Sadeeq tahau yimasa rad'a akunne, jin abinda take gayamasa yasashi yin wani killing smile... {Wanda koni Salma ban san me jidda take cemasa ba,} majid ya ce, "Na zo maki da ice cream amma tunda dadynki kawai kika fad'amawa bana baki ice cream dina" Jin abinda majid yace shiyasata jidda tsalle tana kuka sai ya bata ganin da gaske kukan ta ke sanyi na gaske sai ya ce, mata ta bari sai zai tafi ya dauko mata.. washe hakori tayi ta ce "thank u small daddy" tare da yi masa peck tanamaici gaba da cewa, "Aunty bata san na gudoba dan wanka zata min fa😀" murmushi majid yayi ya ce "to d'iyar Anuty kice ina gaida Anuty.!
Kallon sa sadiq yayi a zuciyarsa yace da kasan wacece fatuha da ko hanya daya baza ka so ta hada ku ba balle kuma wata gaisuwa ta6e baki yayi tare da jan tsaki ciki-ciki
Tana fitowa daga kitchen ta fara neman jidda ba ita ba alamar ta upstairs ta haura saboda tasan bata wuce part din sadiq, tana last stairs kenan sai ga jidda ta fito daga part din washe da baki murmushi fatuha tayi ta ce.. "shine baki jira na maki wanka ba sokike daddy yamin fada ne?girgiza kai jidda tayi fatuha ta dauke ta direct bathroom ta dire ta ta fara yi mata wanka sai da ta wanke ta tas sannan suka fito ta aje ta saman bed ta janyo lotion da night dress din jidda sai da ta shafe ta dashi, sannan ta zura mata kaya.
"Big man bari na zo na wuce dare nayi"
"tun yanzu dare bai wani yi ba na d'auka fa kwana ka zo min wallahi kaga mun dade bamu hadu ba" murmushi majid yayi ya ce, "next time zankwana"
"To shikenan.
har bakin mota ya raka sa ya ciro ice cream din jidda ya bashi ya ce, "gashi aba angel nasan Anuty ta maqale ta shiyasa bata fito ba ka shafa min kanta"
"ok ka gaishe min da Umma da Ammi"
"to zasu ji Alhaji da baba fa me suka tsarema da baza ka ce a gaishe su ba? dariya sadiq yayi tare da kai masa duka "wallahi majid ka rainani tunda na ce a gaida mutan gida ai suma sun shiga" harara majid ya bala masa ba "wani nan Ammi da Umma kawai ka ce kuma da yaushe ma ka girmeni har kake fadi na raina ka" harara sadiq ya qara wurga masa ya ce, "ai dai na baka 4 hours ko qarya nayi" ya qarashe tare da hade ran wasa, dariya majid ya fashe da ita tare da ba mota wuta ya ce, "sai da safe ace ma Mom na zo tana part din Abba" Toh sadiq yace masa da daga masa hannu