Showing 87001 words to 90000 words out of 105783 words
san abinda zai sa ta matsa kusa dashi, shafa gashin kanta ya shiga yi a hankali hakan ba qaramin dad'i yake ma fatuha ba, tana jin yarda hannu sadiq ke mata tafiyar tsutsa a dokin wuyanta can kamar an tsinkuli sadiq ya miqe yana tari da sauri ya shige toilet fatuha ta biyo bayan shi tun kafi ta iso ya kule toilet din da key, dan baya so taga halin da yake ciki, aman jini yake sosai ya dade a toilet din yana abu d'aya fatuha ko duk ta rude sai faman kiran suna sa take tana yan hawaye yana bude toilet ta fada jikinsa a rud'e tana created "Mai kyau me ke damun ka please ka fada min?" ta fada ta shafa masa gefen fuskarsa saman bed ya hau tare da jawo fatu ya ce, "Ba komai kawai na kware ne" haka fatuha ta dinga masa sannu sannan tasa kai ta fita.
Washe gari
Bayan fatuha tayi wanka ta shirya cikin lace dinta maroon mai kyau masha Allah tayi kyau har ta gaji, fatar jikinta sai sheqi take ko da ta fito parlour ba kowa bedroom din angel ta shiga kwance ta hango ta, d'an girgiza kai fatuha tayi tare da bud'e wardrobe ta tafido trolley jidda ta fara zuba mata kayan ta sai da ta gama zuba kayan tsaf ta aje trolley din tana qoqarin fita angel ta tashi ta ce, "Aunty.! cikin sanyin murya juyowa fatuha tayi tana kallon jidda idanuwan ta taf da kwalla da gudu jidda ta rugu ta rungume fatuha tare sakin kuka itama fatuha kamar jira take ta fara nata kukan ba mai lallashin wani sai da suka ci kuka son ransu sannan suka yi shuru suna sauke ajiyar zuciya a tare angel ce ta dago ta ce "Aunty shikenan yanzu bazaki auri daddy na ba? dan smile fatuha tayi tana goge hawayan idonta ta ce, "Angel bai kamata kina damun kanki ba kinji? idan kina son bina sai ki bini mu zauna tare" 6ata fuska angel tayi ta ce, "Aini nafi so na ganki da daddy bada kowa ba"
"Na sani angel, amma shima uncle majeed ai daddy kin ne, da shi da Abban ki duk daya ne, ko kin manta irin son da second daddy yake maki ne My angel Uhm" haka dai fatuha ta dinga lallashin angel sannan ta tafi.
Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta bude kofar part din ta shiga, parlour ba kowa sai kamshi dake tashi bedroom ta shiga kwance ta hango shi qudidine cikin blanket, a hankali ta qarasa zama tayi gefen bed din, a hankali ta fara janye blanket din tana kallon face din sadiq a hankali ta kai masa peck a goshisa, ware sexy eye's ball's dinsa yayi ya sauke su kan fatuha smile ya saki tare da juyawa ya gyara kwanciya dai-dai saitin kunan shi ta ce cikin cool voice din ta "Uncle ka tashi kowa ya gama shiryawa kai kadai ake jira" ware idanuwa yayi yana kallon ta jawo ta yayi ta fad'a saman fafadan qirjinsa ya ce, "Fatuha me yasa kike so ki katse min bacci, ko kun tafi zan iya biyo ku okey.! lamo tayi a qirjinsa ta ce, "Saboda na dinga kallon ka kafin muyi nisa da juna, shiyasa na tashe ka" ta fada idanuwan ta taf da kwalla tashi zaune sadiq yayi yana facing nata shima ji yake kamar yasa kuka, kawai daurewa yake shiyasa yake nuna mata rashin damuwarsa langwabe kai fatuha tayi ta ce, "Ka hada kayan ka ne?
"nope.!
"ok bari na hada ma"
Haka fatuha ta shiga hada ma sadiq kayansa yana kallkn ta saida ta gama hada kayan tsaf tabi daki'n da kallo, kuka ya kubuce mata saboda tunowa da rayuwa da sukayi a baya shikenan yanzu rayuwar ta zama tarihi kuka take sosai, har da durkushe shikenan son da takewa sadiq ya sha ruwa, dagota sadiq yayi ya jawota jikinsa yana lallashi a hankali ta fara magana, "Mai kyau me yasa mutum baya samun abinda ya ke so a lokaci da yake so? ta fada tana qara rushewa da kuka a hankali sadiq ya lallu6o lips din ta ya fara mata hot kiss wanda shi kanshi bai san yana hakan ba, har suka zube kasan carpet bai kyale ta ba har sai da ta tsaigaita kukan, tana sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya sake ta yana maida numfashi, hada face nasu yayi guri guda yana magana can qasan makoshi mai kama da rad'a ya ce "Fatuha please ki dai kuka, dama shi rayuwa bai zama dole mu samu duk abin da muke so ba, muyi hakuri jarabawa ce daga Allah, insha Allah zai bamu sakamako mai kyau, dan haka muyi addu'a Allah yasa hakan shine mafi alheri a gare mu, kuma ki daina kukan haka saboda yana tadamin da hankali a duk sanda naji.! d'aga kai tayi tare da kauda kanta dan gabaki daya kunya ta lullu6e ta, tashi tayi ta fita da sauri daga bedroom din, ko da ta fita jingina tayi da kofar tana maida numfashi a hankali ta daura hannuta saman lips din ta, ji tayi kamar an yaye mata bakin cikin dake damun ta sannan ta fito da gudu d'aga part din haka shima bangaran sadiq haka yaji.
Bayan kowa ya gama hada kayan shi su ola suka wuce da su boot gabaki d'aya, jikinta fatuha susuku yayi, haka sukayi mota 5 fatuha ta dade tana kallon gidan sannan suka bar harabar gidan suka harbawa kan titi,
***
Bayan sun Isa family house dangi har sun fara cika, take jikin fatuha yayi sanyi dan tasan tabbas ta rabu da sadiq har abada, haka shima bangaran sadiq hakan yake ji a ransa.
Bayan sun dan huta kowa ya aje kayan shi inda ake ajewa, aka kira mai lale ta fara yima amaran lale kafin ka ce me qawayan amaran sun fara halara, Zara da Nana har sun zo sai rawar kai suke zubawa, sallamar da akayi ne yasa fatuha juyowa cikin fara'a, waza ta gani inba fatsima ba, da gudu ta ruga ta rungumeta cike da murna haka itama tuni dakin ya dau shewa duk da fatuha ba jin dad'i take ba, amma ganin fatsima ba qaramin dadi ya mata ba, hakan yasa ta fara walwala.
Bangaran Basma ma haka qawayan ta duk sun hadu yan gayu masu ji da kan su, sai shewa suke suna taya Basma murnar samun handsome kamar captain sadiq, sai pictures suke kamar ba gobe kowa ce ka duba face nata kasan cikin farin ciki take.
Angwayan ma friends nasu da suke qasashan waje har sun fara sauka, haka part din nasu ya cika taf da bakin gida dana ketare, duk wannan abun da ake sadiq na gefe ya zuba masu na mujiya kamar ba abinda ke damonsa, sun san halin miskilancin sa shiyasa ba kowa ya damu da hakan ba sai Dr yakub dake ta faman lura da shi dan yasan sarai ciwo ne ke cin sa kowani lokaci zai iya faduwa...
fan's kuyi hakuri da wannan page din ba yawa, saboda ina school shiyasa, abubuwan sunyin yawa ga shirye-shiryan fara exam amma insha Allah gobe zan maku page mai yawa idan na samu dama
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=yn=H-R
*Email* [email protected]
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
89_90
Shirye-shirye suke sosai kasancewar yau ake kamu, da misalin karfe 4:00pm kowace ka gani shiryawa take cikin ashobe, Fatuha da ke zaune cikin toilet tana sana'ar kuka knocking din kofar da akayi ne ya sata miqewa tana share hawayanta, Hanan dake bakin kofar ta ce, "Fatuha ki fito me make up ta zo har an gama ma Basma ke kadai ake jira" to tace tare da yin sauri ta watsa ruwa ta fito.
Ko da ta fito shaharariyar me make up fandi ta zo fatuha kawai take zaman jira, tana daure da towel ta fito ta zauna tana shafe jikinta da mai, Aunty bilki ce ta shigo da kayan da zasu sa washe da baki ta aje kayan ta ce, "a'a fatuha dama ba'a gama make up din ba" daga kai fatuha tayi Aunty bilki ta cigaba da cewa, "ya kamata kuyi sauri ku shirya kar ku 6ata lokaci saboda da kun dawo zaku dinner" to tace sannan Aunty bilki tasa kai fa fice, a hankali fandi ta fara tsantsara mata make up kafin ka ce me fatuha ta fito wasu peak materials tasa gown mai stone's masha Allah tasha kyau har ta gaji, kanta na daure da head silver, ita kanta me make up ta yaba da irin kyan da fatuha tayi, su fatsima ne suka shigo sanye da ashoben su ash atamfa mai ratsin peak suma sun sha head kun san a tare suka fito da Basma kusan kaya colours daya suka sa har yan mata amaryar anko daya su kayi, motoci ne masu numfashi da tsada suka faka amaran suka shige ba a zame ko ina ba sai meenah event hadadan hall na party iyakar haduwa hall din ya hadu, kuma ya qayatar kasancewar kamun na mata zala ne shiyasa ba ango ko daya sai yan'mata da iyaye, yan asharale ne suka fara buga ganga tuni hall ya dau sauti amaran zama su kayi ma zaunin su aka fara gudanar da shagulgula, su fatsina da Nana da Zara fili suka shiga suna ta kwaso shoki haka suma qawayan Basma biki yayi biki sai dai muce Alhamdulillah .
Fatuha ko duk wannan bidirin da ake zuciyar ta naga muradin ranta, ji take kamar ta rushe da kuka kallon kowa take da ke farin ciki da walwala angel ta hango itama ba laifi ta saki jikin ta tana warwasawa.
Anci ansha inda aka raba turaru kan wuta da atamfofi masu tsada sosai, aka raba kaya kamar ba'a so, sai kunsan yamma liqis taro ya watse suka dawo gida.
Ko da suka dawo wanka amaran suka qara tare da dauro alwala suka gabarta da sallah magrib da isha, sannan amaran aka fara shirya su cikin wani wanka ni kai na har mamaki nake irin shirin da akayi ma bikin, lace suka sa blue mai ratsin dark blue mai shegen tsada ga make up da aka qara zuba masu sai kamshi suke, yan matan amaraya ko pink lace suka sa mai ratsin white kowa ce tasha make up, fatuha ko saboda tsabar kyau kasa gane ta kake, dan ba qaramin kyau tayi ba kuma ga annuri da ya sauko mata na amarci, Basma ma ba'a barta a baya ba tayi kyau b sosai.
Shiryawa angwayan suke cikin getzner shada blue tasha aiki da dark blue zare malin-malin, duk wannan shirin da sadiq keyi jinsa yayi suku-suku dan kwata-kwata baya tare da walwalarsa links yasa ma hannun rigarsa sannan ya daura agogo a tsintsiyar hannusa hublot ya zura takalminsa black mesarath tuni ya fito yana sheqi da wani irin kyau, sajan fuskarsa ya kwanta luf-luf ya daura hula wadda ta dace da kayan gashin kansa ya leqo ta gefe-gefan hular feshe jikinsa yayi da turare masu kamshi da sanyi dadi kusan shigar su iri d'aya da majeed shima ba'a barshi baya ba dan yasha kyau har ya gaji, sai murmushi yake saki fararan haqoransa na bayana, aboka nan angwayan ma ba'a bar su a baya ba dan suma sunsha kyau ko wana su sai sheqi yake, Khaleed sai rawar kai yake zuba wa haka shima Dr yakub ba'a bar shi a baya gayu su kayi na sosai abun ka da bikin manya.
Cikin natsuwa suka fito suka shige motocin su Benz black, haka motocin masu zafi suka harba kan titi dan dauko amaran kasancewar a hotel suka shirya, ko da suka iso amaran sun shirya tsaf motoci aka fara shiga kowace amarya ta shige motar angonta,
Da murmushi majeed ya dubi fatuha da wani irin kallo mai cike da so da kauna, ba qaramin kyau ta masa ba ga wani fitinan kamshinta daya mamaye hancinsa mai kashe jiki, a hankali daura hannusa saman na fatu yana kallon lalan dake hannuta ja da baki yayi wani irin kyau ya ce, "My love lalan nan yayi kyau, bama shi kadai ba harda ke din ma" smile tayi wanda iya karshi la66anta ta janye hannuta daga cikin na majeed ta qara manewa karshan kofar tana tuna abin sonta.
Da kallo Sadiq yabi Basma ba laifi ta masa kyau, yau ce rana ta farko daya fara ganin kyanta ayanawa yayi a ransa, tunda ya ga Basma haka to ya fatuha zata kasance? wani irin kishi ne ya lullu6esa da qunar zuciya juyowar da yayi ne su kayi ido hudu da Basma smile ya sakar mata da kauda kai.
A dai-dai affcent center motocin suka faka lokacin har wasu sun halara tun daga bakin hall din kana jiyo irin sautin dake tashi, wajen ya hadu ba karya, kallo daya zaka masa kasan naira tayi kuka wasu kujeru ne na alfarma a hall d'in wanda ko ba'a fada ba zaka gane hall din na d'an wane da wance ne, jerawa yan'matan amaran sukayi masu ashobe, haka suma abokan angwayan suka jera reras masha Allah shigar ta su yayi kyau, amaran suka shiga tsakiya da angwayan Sadiq sai bin fatuha yake da kallo bugun zuciyarsa na daduwa, ta masa wani irin kyau ita kanta fatuha ta qasan ido take kallon sadiq tana jin wani irin kishinsa dan ba qaramin kyau ya mata ba.
A natse suka shigo hall din, wajen ya gwarare da shewa da ihu, tuni aka canza salan kida da sauti majeed hannusa na maqale dana fatuha yadda ya shige mata kamar zai maida ta ciki, sadiq ya cika taf dan har ya fara jin kirjinsa na masa zafi duk sanyi AC dake ratsa hall baya ji sai zafi da yake ji zufa na karyo masa, kidin da aka saki sai ya qara dagula masa lusafi ya fara hanging jiri riqe hannu Basma yayi dan ba yadda zaiyi dan baya so ya bata ma qansa rai, ko bai so Basma so na aure ba yana sonta a matsayin ta na kanwar sa, sosai ya damke hannuta yana sauke numfashi a hankali dake neman kwace masa, ko da suka shiga gurin zama suka yi aka fara gudanar da shakali, can na hango su Aunty Rahenat anata kai kawo anzu shagali😜 ashe abin ba ita kadai ba ce har da yan Real Hausa fulani writers, can na hango Fulani da Aunty Rahama Nalele suna rabawa mutane kayan motsa baki, nima dai ba'a barni a baya ba dan na shiga a dama dani shoki kawai ake kwasowa.
A hankali majeed ya matso daf da kunan fatuha ya ce, "My love yanzu fa gobe kamar yanzu kin zama tawa ko? yana magana yana wasa da yan yatsunta Sadiq dake gefe yana kallon su bakin ciki na qara qumesa, dafe kirjinsa yayi domin yafara yi masa nauyi, zufa sai karyo masa take tamkar wanda ke bakin wuta a hankali ya miqe ya saci jiki ya bar guri tunda ya fito daga hall din jiri ke di barshi yana had'a hanya yana sauke wani irin numfashi mai baraza na da rayuwarsa, ko gabansa baya gani dakyar ya iya isa inda akayi parking motarsa ya daura hannusa kenan ya ji an riqe hannunsa, waigowa yayi su kayi 4 eye's da Dr yakub girgiza kai Dr yakub yayi ya ce, sa...!! bai furta abinda yayi niya ba ida sadiq ya fado jikisa sumame, rudewa Dr yakub yayi ya cewa, sadiq..! captain..! ka ga sadiq tashi ka ji kalle ni ka bud'e ido karka mana haka, ka gani ko abinda zurfin cikin ka zai ja mana karka barni aboki na ka ji captain.! kuka yakub yake sosai ya rude ya rasa abunyi daukar sadiq yayi cak yasa a mota ya bar harabar gurin da gudu..
Duk wannan bidirin da ake ba wanda yasan halin da sadiq ke ciki sai Dr yakub, MC ne ya fara cewa, "amarya da ango su fito su yanka cake ango ya ba amaryarsa itama ta basa" saukowa sukayi a hankali suka tsaya majeed ya yanka cake d'in yaba fatuha a baki itama ta basa hall din ya dau ihu, sadiq aka kira da Basma amma ba ango ba alama haka MC ya dinga kira ango ganin abin kunyar dake shirin faruwa yasa Khaleed hawa a matsayin ango yaba Basma cake a matsayin sadiq tuni hall ya dau tafi, Basma iyakar cika ta cika bata taba jin bacin rai ba irin na yau, yaune ta tabbatar da sadiq bai sonta kuma ba zai taba sonta ba tunda har ya iya wulaqantata gaban bainar jama'a, idanuwan ta taf da qwalla, tana tausayawa kantada irin rayuwar da zatayi a gidan Sadiq, haka akayi taro kusan duk abinda ango zaiyi ma amarya Khaleed ne yayi ma Basma.
Ko da fatuha ta juya bata ga sadiq ba tuni idanuwan ta suka kawo ruwa, dama shi take gani tana jin sanyi a ranta.
Ko da Dr yakub yaja mota basu zame ko ina ba sai asibitinsa, suna shiga aka turo gadon daukar marasa lafiya sadiq da yanzu idanuwansa sun fara budewa saboda oxygen d'in dake manne a hancinsa haka yake ganin asibitin na juya masa numfashinsa na sama-sama, Dr yakub kuwa kuka yake sosai, emergency aka wuce da shi doctorsa sun dade a kansa Dr yakub ma kasa shiga yayi sai zarya da yake a bakin kofar kusan 1 hour suka dauka sannan aka fito da sadiq manne da oxygen a hancinsa