Showing 48001 words to 51000 words out of 105783 words

Chapter 17 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

717

colour ne yana da saje daya kara bayanar da kyawunsa, yana da manyan ido murmushi ya saki ganin sadiq ya qara so fararan haqoran shi suka bayana cikin jin dadi sadiq ya qaraso tare da miqa masa hannu suka gaisa ya  ce,  "Ashe dama zan kara  ganinka a duniyar nan? murmushi  Sadiq yayi  ya  ce, "bagashi ba ai kai ma baka zama shiyasa"
     "haka kuma dan last week ma na dawo daga London har muka hade da yaya jawad wajan shopping shi da matar shi har ya ke ce min sun kusa zuwa gida, jira kawai yake Aunty shukara da haihu su zo" murmushi Sadiq yayi ya ce, "haka ya fada min"  suna tattaunawa har suka qaraso kofar parlour cikin parlour suka shigo har yanzu su fatuha na nan inda ya bar su ,Sadiq ya ce  "Fatuha.! dagowa tayi ita da jidda tare da gaishe da Khaleed murmushi Khaleed yayi tare da amsawa yana bin fatuha da kallo Sadiq ya katse masa tunani da cewa "Fatuha ki kawo mana glass cup" ta ce masa toh tare da shigewa kitchen sadiq ya  ce, "jidda ga uncle.! Khaleed smile jidda tayi Khaleed murmushi yayi ya ce, "karka ce min angel ce ta girma haka"
      "ita ce mana" zaro ido waje Khaleed yayi ya ce, "kai.! amma gaskiya mun yadda zuminci, come here angel" kusa da shi jidda ta matso kallon ta yayi tare da daukar ta suka haura upstairs sai tanbayar ta ya ke tana zuba masa surutu suna shi ga part din Sadiq saman two sitar Khaleed ya zauna tare da daura jidda a cinyar shi, sadiq kuma fridge din bedroom ya bude ya curo lemu ka masu sanyi ya kawo ma Khaleed lokacin yayi dai-dai da shigowar fatuha dauke da tray da cup's amsa tray din Sadiq yayi tare da yi mata nuni da ta dau jidda, Khaleed sai bin fatuha da kallo ya ke kiran jidda tayi suka fita a tare tana fita Khaleed ya sauke ajiyar zuciya, yana kallon  Sadiq, Sadiq din ma kallon shi yake ya  ce, "big man ina kuka samo beautifully girl,"
     "wake nan ya? fadi a taqaice
"wadda ta dau angel yanzu" murmushi Sadiq yayi ya ce "Fatuha she is my sister baka ga muna kama ba" ya fadi zancan yana cigaba da zuba ma Khaleed juice khaleed ya  ce, "amma ai nasan kai ne dan auta baka da wata sister" bashi glass cup yayi na lemo yana qara saki wani murmushin wanda iya karshi lips din shi ya  ce, "she is my consin sister yanzu ka gane ko" murmushi Khaleed yayi ya ce, "amma fa tana da kyau karka ce min Basma ce ta zama mai kyau haka" tanbayar Khaleed ta kusa fara kai Sadiq wuya amma sai ya maze ya ce, "ba ita ba ce wannan diyar sister mom ce"
     "eyya.! shi kansa Sadiq yana mamaki karyar da ya zauna yana shunfuda ma Khaleed me  ke  damun  sa  haka toh me idan ya ce masa yar aiki ce, dan guntun saki ya ja a zuciyar shi  khaleed ya  katse  sa  da  cewa, "Sadiq mom fa?
      "Mom ba ta nan sun tafi uk da Abba" OK hira suke sha sosai suna kallo.


Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
   Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANI WRITERS FORUM.com

          
                    55_56

       Hira suka sha sosai Sadiq da Khaleed, basu suka tashi ba saida suka fara jin kiran sallar magrib,    alwala suka dauro a tare suka fito domin tafiya masallaci, ko da suka iso parlour ba kowa Khaleed sai kalle-kalle yake ko zai ga fatuha, hakan yasa Sadiq ya masa nisa juyawar da Sadiq yayi yasa Khaleed daga kafa bayan an gabatar da sallah suka fito daga masallaci direct gida suka dawo, basu zame ko ina ba sai dining area Sadiq ne ya shiga saving nasu lafiyayan tuwan shinkafa miyar egushi taji kaji da naman rago kamshi sai tashi yake, turawa Khaleed na shi yayi sannan ya zuba na shi tare da zuba masu juice a cup's, suna ci suna ta6a hira dan yau an hadu har basa gajiya da hira, bayan sun kamala suka dawo parlour da zama basu koma part din Sadiq ba wayar Sadiq dake aljihu ce ta shiga ruri hannu yasa cikin aljihu ya zaro ta sunnan da ya ganine manne a screen din ya sasa sakin smile, juyowa yayi ya kalli Khaleed ya ce, "gafa mutumin ka fa yake kira ni," murmushi Khaleed yayi ya ce, "kamar yasan ina nan" daukar wayar yayi tare da karawa a kunne ta daya bangaran majid ya ce "Hello big man"
   "Na'am.!
  "kana gida?
      "eh ina gida gani nan  tare da Khaleed,"
     "eyya kace ma0sa ina gaishe shi"
  "toh.!
   "yauwa dama so nake ka raka ni wata dinner please,"
    "dinner kuma? Sadiq ya maimai yana kwabe fuska  majid ya  ce, "ni dai ka rakani dan Allah nasan halin ka, yanzu ka fara min tsirfa"
     "au tsirfa ma zan ma ko? toh ban zuwa,"
    "haba kar muyi haka da kai mana please ka shirya kuma manya kaya zaka sa,"
     "bazan saba zafi ya isheni"
     "please kasa haba Sadiq nine fa"
     "toh  naji.!  naji.! ya ce masa tare da katse wayar yana kallkn Khaleed ya  ce, "ka ji ni da majid wata kuma dinner zai kwashe ni muje taso muje mu shirye muje,"
       "ni fa bana zuwa" harara Sadiq ya wurga ma Khaleed "lafiya.! Khaleed yace ya daure fuskar wasa "toh ai ji nayi ka ce baka zuwa"
    "wallahi ko aiki na can na jira na shiyasa yanzu haka fa gudo ma aikin nayi"
    "toh shikenan" part din Sadiq suka koma Sadiq ya shige bedroom tare da rage kayan jikin shi sannan ya shige toilet wanka ya sheqa ya fito daure da towel a jikin shi sai qaramin towel yana goge sumar shi lotion ya janyo ya shafa sannan ya bude wardrobe ya ciro dakakiyar shada shi brown tasha dinki da dark brown zare anmai irin dinkin nan na sarauta takalmin coffee colour yasa tuni ya fito yayi wani irin kyau, abinka da farar  fata  turare ya fesa mai kamshi da sanyin dadi tare da  manne agogwan shi silver sannan ya dawo parlour, khaleed dake saman two sitar  ya ce, "kai aboki na wannan sai kafi uban gayar kyau ai" smile Sadiq yayi ya ce "A hakan?
   "eh mana"
      "Cha6.!
   "so kake yan'mata suyi rushing kenan dama har yanzu kaqi yima angel Mom," smile Sadiq ya kuma yi ya ce "Nine Mom din jidda kuma nine daddy ta, so bata buqatar wata new Mom"
      "haka dai kake cewa lokaci nanan zuwa da zaka watsar da  wannan tunanin haka, ni ko ina sis naka har yanzu ban qara sata a ido na ba? dago ido sadiq yayi yana nazari wace sis can kuma sai ya tuna qaqaro murmushi yayi ya ce, "wai me sister na ta tsare maka tunda kazo kake zancan ta"
     "ah wallahi kawai yarinyar ta burge nine har na dan ji wani abu" kallon shi sadiq ya shiga yi kamar me neman wani abu a jikin shi can kuma sai yaja dan guntun saki ya  ce, "amma dai Khaleed wani abu ya shige ma kai ko? me za kayi da wa can yarinyar? yarinyar da ko 14 years bana tunanin ta kai, toh ka aure ta ka ji me? dariya Khaleed yayi  ya  ce, "wallahi aboki na baka kallon yarinyar nan wallahi irin sune idan suka ji kiwo kai kanka sai kayi mamakin abin da zaka gani"
     "mtsss har ka fara samin headache wallahi" wayar sadiq da tayi rurice ta katse ma Khaleed zance daukar wayar yayi ta daya bangaran majid ya ce, "Gani nan cikin filin gida ka fito mu tafi" to yace masa tare da miqewa  Sadiq ya kalli Khaleed  ya  ce, "tashi mu tafi dan zumudin har yazo," fita su kayi daga part din har sun kai bakin kofar fita sadiq ya ce "Ina zuwa"  parlour ya dawo tare da nufar dakin fatuha a hankali ya murda handle din kofar a zaune ya hango su fatuha saman daduma da alama yanzu suka idar da sallah, suna karatun AlQur'ani sallamar da yayi ne yasa fatuha aje Al Qur'anin tare da amsawa qarewa sadiq kallo fatuha tayi wani irin kyau ya mata kullun mai kyau qara kyau yake kauda idanuwan ta tayi, qarasowa dakin yayi jidda ta ruga ta fada jikinsa ta ce, "Daddy!
Na'am my angel.!
        "daddy ina zaka? zan bika"
     "angel ai yara basu zuwa" bata fuska jidda tayi tana shirin yin kuka tana dire-dire tana  cewa,  ni kam gaskiya daddy binka zanyi ban zama" langwabe kai sadiq yayi ya ce "Fatuha zo ki dauke ta" fatuha qarasowa tayi tana ma jidda murmushi ta ce, "yi hakuri kin ji jidda daddy nasan zuwa dake amma baya san dodo ya cinye ki  dodon yara yake ci" jidda ware idanuwa tayi tana kallon fatuha irin da gaske kike, sadiq ko wani irin dadi yaji yadda fatuha ke lalla6a jidda dan yasan idan ta kafa masa kuka har dinner fasa zuwa zai yi dan farin cikin jidda shine nashi, shafa kan jidda yayi ya ce, "kinji ko? ko mu tafin," maqe qafa tayi ta fada jikin fatuha dariyar da ke san zuwa ma fatuha ta guntse shima haka Sadiq peck yama jidda sannan ya fice ya fito lokaci Khaleed da majid suna ta hira yana qarasowa majid ya aika masa harara tare da cewa "Tunda nace ka raka ni sai ka shanya ni mtss"
     "oh haka nan zan bika banyi ma angel sallama ba ko? saima na fasa zuwa wallahi" hakuri majid ya bashi Khaleed dake gefe dariya yayi ya ce, "baku Gajiya da dirama wallahi har yanzu" murmushi su kayi tare da bude motocin su suka shige a tare da Khaleed suka bar unguwar.

    Sadiq na fita fatuha ta ja jidda toilet ta mata wanka itama tayi night dress suka sa tare da fitowa parlour, gidan yayi tsit ba alamar motsin mutane tsoro suka fara ji amma fatuha  daurewa take jidda kuka tasa mata ta ce  "Aunty"
      "na'am jidda"
  "Aunty ki zo muje part din daddy tsoro nake ji" shafa kanta fatuha tayi ta ce "Kiyi hakuri mu zauna anan" kuka jidda  ta fara rarewa fatuha hakan yasa fatuha daukar ta suka koma part din sadiq a parlour suka zauna fatuha ta kunna masu kayan kallo MBC 3 ta kai masu suka rashe suna kallon carton.

       suna isa wajan dinner  ke  da  wuya  kallo ya  koma  kan  su, wajen ya hadu   iyakar haduwa sun hadu duk wata mace dake wajan sai da ta yaba kyan su mata masu wayau a sace suka rinqa yaba kyan su marasa wayau ko har bin su sadiq suke, sadiq ko hade rai yayi kamar bai ta6a dariya  ba majid ko sai washe baki yake dama shi dan ina da yan'mata ne sunyi ciye-ciye da lashe-lashe majid sai da yayi kusan yan'mata biyar takaici ya hana sadiq magana  sai fuska da ya qara tsukewa kamar anmasa mutuwa, duk wadda ta zo tura kanta idan taga ba wasa a tare da sadiq sai ta ci birki ba su  suka bar wajan dinner ba sai 11:30pm lokaci sadiq har wajan ya fara hawa masa kai, ko da suka taho ba wanda yace ma wani qalla musanman majid ya san yana tankawa sadiq zai fara masa masifa dan yasan halinshi har harabar  gida majid ya saka hancin motar shi bala mai gadi sai daga masu hannu yake, tun kan majid ya ida parking sadiq yayi qoqarin fita dariya abin ya so ya ba majid amma baice komai ba yayi ribas ya fita yana shiga parlour ba kowa dama yayi tunanin haka saboda goma nayi jidda tayi nisan bacci bale kuma 11:30pm bedroom din fatuha ya bude a tunanin  shi suna ciki ganin ba kowa yayi tunanin suna part din shi haurawa yayi upstairs a hankali ya murda handle din kofar, TV ya iske nayi su tuni sunyi bacci, jidda ta dora kanta bisa cinyar fatuha, fatuha kuma ta jingina da kujera murmushi sadiq yayi tare da qarasawa ya kashe kayan kallon bedroom ya shige ya rage kayan jikinsa ya shige bathroom wanka ya sheqa ya fito sanye da bathrobe tsane jikin shi yayi da qaramin towel sannan ya zura night dress din shi parlour ya dawo har yanzu su fatuha bacci suke a hankali ya qaraso saman three sitar a hankali yasa hannu ya dau jidda bedroom ya kaita ya shinfideta parlour ya kuma dawowa, har yanzu fatuha bacci take a hankali sadiq ya kai hannu zai tashe ta sai kuma ya fasa gashin ta daya rufe mata fuska ya matsar tare da tsare  ta  da  ido yana qare mata kallo ya ga dai bacci take lumshe ido yayi tare da ware su, a hankali ya kai hannusa ya dauke ta aiko fatuha ta qara lafewa jikinsa tana sharar bacci yayi tunanin zai jita da nauyi amma sai yaji kamar ya dauki jidda a hankali ya sauke ta saman bed din shi ya ja masu blanket ita da jidda tare da qara masu gudun AC, sannan ya bude wardrobe ya ciro wani blanket din ya koma parlour ya kwanta saman three sitar ya dade kafin bacci ya dauke shi, zuwa can   bacci yayi awan gaba dashi.

   Yau su fatuha bacci har da munshari ansamu lafiyayan bed, duk da na dakin ta bana wasa bane amma duk haduwar shi bai kai na sadiq ba dan haka bacci tasha sosai ko da aka kira sallah asuba tana bacci, sadiq ne kadai ya tashi ya dauro alwala ya tafi masallaci, yana dawowa saman three sitar ya koma ya zauna tare da kunna kallo yana kallon new din safe cikin miqa fatuha ta tashi agogwa  dake manne jikin daki ta kalla kusan bakwai na safe ware ido tayi tana qoqarin tashi daga gadon da take, idanuwata ta ware sosai  tana bin dakin da kallo kwalla ta fara matsar wa tana fadin nashiga uku na lalace yau sangami zai kashe ni, wayo inna mu na bani qasan gadon ta zame tana rera kuka jira kawai take taji saukar aradu bayan ya gama kallon news din blanket din daya lullu6a da shi ya nade a hankali ya murda handle din kofar bedroom tsugunne ya hango fatuha bakin gado jin an bude kofa yasa fatuha zabura ta miqe, tana zarar ido yarfe hannu ta shiga yi dariya abin ya so bama sadiq daure fuska yayi ya bude wardrobe yasa  blanket din ciki, jikinfatuha ko sai rawa  yake  tana matsar kwalla tana yarfe hannu, ganin zai fita bai tanka mata ba ta ce , "tsakanina da Allah  ban san na shigo dakin nan ba Qur'an" ta fadi zancan tana matsar kwalla ta  cigaba  da  cewa, "wallahi iya kata parlour ban san ya na zo nan ba, dan girman Allah mai kyau kayi hakuri wallahi aljanune ke san jamin masifa," sadiq da ya tsaya bakin kofa cak yana jin fatuha wata dariya ya gutse ya juyo fuska daure harara ya aika mata ya ce, "Kin ji na maki magana ne? kin min laifi kuma kin zo kina min kuka dukanki nayi  ko me? dama ai so kike ki kwata saman bed din saboda kina jin na zama sa'anki  toh kin kwanta kinji abinda nake ji ko, to saiki zo ki fita mtss" fatuha ko rantse-rantse ta shiga yi masa shiko yayi fuska kamar gaske ganin bai tanka mata ba yasa ta fita daga daki da gudu tana fita saman bed ya fada ya saki dariyar har mamakin tsoran fatuha yake ta iya rashin ji amma intaga an kamata yanzu ta fara kuka  gyara kwanciya yayi dama da kyar yayi bacci saboda bai saba bacci kujera ba.

Bangaran fatuha ko tana shiga daki ajiyar zuciya ta saki tare da shigewa toilet ta yi alwala.

    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau  dadi gobe akasin haka, amma fadan da sukeyi da  sadiq ya ragu harkar shi  yake tayi nata, ta dage sosai jidda na koya mata karatun boko duk da itama din ba wani nisa tayi ba bangaran karatun ta na adini ba'a magana dan maida hankali take sosai, ga wani girma data qara dakyau yanzu haka su Jidda sun gama exam Aunty bilki sai matsama sadiq take ya  kawo jidda hutu tunda  su  Mom  basu  nan.

    Su Mom ko sun gama abin da ya kai su uk, amma Alhaji ya dage baza su dawo yanzu ba sai sun gama soyewar su sannan, aiko Mom bata masa gardama ba dan ita ba wanda take san faran ta ma rai kamar Alhaji.

     Sanye yake da blue shirt mai dogwan hannu, sai jeans sumar shi tasha gyara waya ce manne a kunnan shi da alama da Mom yake waya, sai shagwaba yake zuba mata sai da yazo  parlour sannan ya katse wayar tare da kwallawa fatuha kira, fatuha da yanzu ta fito daga wanka wata yar ficiciyar riga ta zura ta fito da gudu kallon ta yayi tare da kauda kai ya ce, "Kije ki hada ma jidda kayanta  a trolley" shagwabe fuska tayi tana kallon sadiq kamar zatayi kuka, kallon ta ya kuma yi sannan ya kauda kai yaga alamar idan ya biye mata ba inda zai kai jidda kuma shi gaskiya ba zasu tafi tare ba, idan suka tafi wazai gyara masa part din shi, bedroom fatuha shiga  sai da tayi kukan ta son ranta sannan ta cigaba da hada ma jidda kayan ta, jidda ko sai murna take zataje taga Jamal,  bayan ta gama hada mata kayan ta fito da trolley din  parlour sadiq na saman two sitar jidda na riqe da hannun fatuha daukar  trolley din yayi ya fida waje su fatuha na biye dashi a baya, cikin boot ya sa trolley din tare da kama hannu jidda, fatuha ko ji take kamar ta daura hannu a kai ta saki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login