Showing 63001 words to 66000 words out of 105783 words

Chapter 22 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

721

ta gama sa kayan bacci ta shirya jidda itama cikin nata sannan ta hada ma sadiq coffee kamar yadda ta saba a gida ta ja hannu angel suka wuce masaukinsa, da sallama ta d'aga labilan d'akin suka shigo, amsawa yayi a taqaice ta aje masa coffee ya amsa tare da aika mata harara wasa hannuwanta biyu tasa a kunne alamar bada hakuri tana rausaya kai d'an murmushi sadiq ya saki yana binta da kallo.
hira sukayi sama-sama inda angel ke ta zuba qiriniya har bacci ya kwashe ta, daukar ta fatuha tayi tana qoqarin fita sadiq ya mike ya masu peck tare da shafa kan angel dake kwance saman kafadar fatu, suka wuce d'akin fatuha.

*Washe gari*

Tunda safe fatuha ta tashi ta share tsakar gida tas, ta hura icce ta dora koko tare da dumama tuwan jiya, ta juye a kwanan samira tana qoqarin fitowa daga kitchen inna ta fito d'aga uwar d'aka washe da baki tana bin tsakar gida da kallo tana zancan zuci, alallai fatuha anyi hankali.! har qasa ta gaida inna ta amsa cikin fara'a sannan ta shige qurya ta fido jidda ta wanke ta tas ta shirya ta cikin jean n t-shirts masu kyau, sannan itama ta shige kewaye tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga da sket na lace red mai kyau sai yar hoda data murza da lipstick ba qaramin kyau tayi ba sannan ta dau kwanonin da tasama sadiq abinci ta nufi d'akin inna da ke surfa gero ta ce "Aiko dazu da sasafe tare suka fita da Baffan ki gona" murmushi fatuha ta saki ta ce, "shine baffa bai je dani ba ko? ta zun6oro baki tare da shigewa ciki ta aje masa abincin tana fitowa ta ci qaro da fatsima, washe da baki ta tarbeta kusan a tare su kayi kallaci sannan suka fita yawo ganin gari, duk inda fatuha ta wuce sai antanka da irin kyanda tayi da nutsuwar da ta qara haka aka rinqa layin zuwa ganin fatu ta zama balarabiya, haka ta dinga baje tsaraba tana rabawa fatsima ko tasha tsaraba kamar ba gobe.

Kwana su biyu a kauye inda yan kauye ke cewa fatuha ta zo da larabawa, itama ta zama balarabiya sun sha yawo da sadiq har rafi sai da ta kai shi, da gona mai gari inda suke satar mangwaro a da, sosai ya ji dad'in kauyan ba dan kad'an ba.

Fatuha ce riqe da trolley tana rusa kuka ita bata komawa, sai da inna tayi da gaske sannan ta shige mota sadiq yasa trolleys a boot tare da yima Baffa shatara na arziqi, duk yadda Baffa yaqi amsa haka sadiq ya matsa masa ya amsa, haka Baffa ya dinga samasa albarka fatsima har da yar kwallata sannan suka dau hanyar kano cike da kewa.

********** ********** ******

Akwana atashi ba wuya wajan sallah fatuha dai ta fara zuwa makaranta inda aka sata jss1 sosai take maida hankali kuma tana gane karatun gashi Alhamdulillah Allah ya zuba mata qoqari na ban mamaki, dan har tafi masu qoqarin ajin a yanzu a tare suke zuwa da jidda a yanzu jidda na primary 2 kusan duk makarantar su d'aya da su Hanan da Basma hakan ya qarasa suka shaqu duk inda kaga Hanan to zakaga Fatuha ko Basma sosai suke maida hankali akan karatunsu.

Kamar yadda aka saba tashin su misalin karfe 3:30pm driven yayi parking suka bale murfi motar suka fito a tare, sanye fatuha take da uniform din ta riga mai dagon hannu milk sai sket dark green dai-dai gwiwa sai dan qaramin hijab milk, jidda kuma biri da wando ne sai milk riga a ciki green a sama kallo d'aya zaka masu kasan sun gaji likis tun a parlour jidda ta fara wurgi da jakarta fatu ta ce, "oh no why this angel bari dai grandma ta fito ta zane ki.! sama nayi da ido ina tunanin wake wurgo wannan turancin kamar a mafarki ashe fatuha ce ohni salma😧, daukar bag din jidda tayi tana zun6oro baki ta kai bedroom dinta,

Har fatuha ta shiga bedroom ta fara cire mabalin rigar ta, ta tuna da ice cream din ta dake bedroom din sadiq cikin fridge da sauri ta fito ta haura upstairs, a hankali ta bude part din ta shige parlour ba kowa sai kamshi dake tashi, bedroom ta shige tare da nufar fridge, ganin Sadiq tsaye yana qoqarin cire rigar uniform dinsa ya sata cewa, "uncle..! waigowa yayi cikin smile ya qara kyau da kwarjini ya ce, "yes dear.!
"uhm ya naga ka dawo yau da wuri haka uncle?
"na gama aiki ne gobe da safe flight dina na zuwa london zai tashi zani wani course ne ba zata ya zo min, hada kayana na dawo yi" dan bata fuska tayi tare nufar fridge ta dau ice cream tana ta kunbure-kunbure ta fice Sadiq ya bita da kallo.

Vote
comment Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM

                      69_70

👏🏽Godiya gare ku mosayan ❤wannan novel, ina jin dad'in yarda kuke comments😍 ana mugun tare irin sosai din nan.🤸🏽‍♀🤸🏽‍♀

    wannan shafin naki ne Maimuna Lawal Allah ya bar zuminci har ya'ya da jikoki Ameen🤝

         Fatuha na shiga bedroom ta aje ice cream din saman bedside drawer dan gabaki d'aya ice cream din yafita ran ta, a duniya ba abinda ta tsana kamar mai kyau yayi nisa da ita, ita kanta har mamakin hakan take jiki ba qwari ta ida cire school uniform tare da shigewa bathroom ta sheqa wanka ta fito, bayan ta tsane jikin ta tabi da lotion mai kamshi tare da sanya black after dress din ta mai stone's d'aure gashin kanta tayi kamar ganmo tare da murza yar hoda  da lipstick masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba, fitowa tayi daga bedroom din ta wuce na Mom cikin sallama ta shiga mom Na tsaye gaban dress mirror tana shiri da alama fita za tayi cikin fara'a ta amsa fatu ta ce, "Mom fita zakiyi ne?"
        "eh wallahi zani gidan Ammi ne, dama yanzu nake cewa ko zaki raka ni? dan murmushi fatuha tayi itama tana san zuwa wajan Ammi din nan amma tunda ta zo sau biyu ta ta6a zuwa gashi tana san ganin Basma, amma Assignment ba zai bari ba gashi malam anjima zaizo ta  ce, "Mom kin manta yau wednesday,"
       "oh haka fa na manta fa shaf next time munje"
       "kuma wallahi Mom ina san zuwa Basma har ce min take bani da kirki bana zuwa,"
       "ai ta fada duk zaryar da suke maki baki zuwa masu kema kin fara koyan halin uncle din naki," dan smile fatuha ta saki mai cike da jin dad'i ita dai duk abinda za'a ce daga mai kyau yake so take ta  ce, "Mom ai baya san yawo uncle shiyasa"
      "ke kuma sai  biye masa kike ko, zuminci fa abin wasa bane" Mom ta ida zancan tana daukar handbag din ta kusan a tare suka fito, angel na zaune a parlour tana kallon cartoon ganin grandma zata fita yasa ta tashi tana cewa, "grandma zan biki please"
        "nope yau malam zaizo" zu6uro baki Angel  tayi gaba tana sanyin kuka ta  ce, "please grandma ki je dani," fatu  ta  ce, "angel kiyi hakuri grandma ta je kin ji, muma ranar Friday mun tafi kinji.! d'aga kai jidda tayi ba dan taso ba,  har bakin mota suka raka ta suka juyo.

    A dai-dai bakin kofa suka ci qaro da sadiq yana sanye da 3 quarter black da white t-shirt da alama gym zashi, kauda kai fatuha ta yi ala dole fushi take da sadiq, smile yayi tare da d'aga angel sama yana mata wasa tana dariya ko kallon inda fatuha take bai yi ba saboda ya lura yau rigima take ji, ra6awa tayi ta gefansa zata wuce ta cika taf qiris take jira ta fashe, ruqo hannu ta yayi hakan yasa ta tsaya chak a wajan, ta kasa kwace hannu ta sai binsa da take da kallo, aje jidda yayi qasa yana aje ta kamar jira take tayi cikin gida da gudu, fisgo da fatuha yayi ta fado saman fafadan qirjinsa har tana jin bugun zuciyarsa lamo tayi a qirjin nasa idanu ta  lumshe, a hankali ya d'ago da habar ta yana kallon ta lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha cikin cool voice dinsa ya ce "Fushin na menene uhm? dan 6ata rai tayi tana qoqarin zamewa daga jikinsa tunda bai san fushin me take ba, dan matse ta yayi da karfi ta saki yar qara, ta fara matsar kwalla kamar  jira  take  tana  binsa  da  idanu  ta cikin  tattausar  murya  sadiq  ya  ce, "daga nace zanyi tafiya sai fushi fatuha 3 days fa kawai zanyi kin ji dear," turo baki gaba tayi  ta  ce, "ni ba fushi nake ba"
      "to me kike?
"ba komai"
   "ok tunda ba fushi kike ba please ki had'a min kayana, na rasa kayan da zansaka kin riga kin shagwaba uncle da yawa," d'an zunburo baki ta kuma yi maicike da shagwaba sadiq  ya  ce, "please karki ce bakiyi"
      "zanyi mana"
"promise.!
    "promise..!
"good girl"ya sakar  mata  peck  a  goshi ya fita.

    Bayan ta kamala hada masa kaya sannan ta kalli agogon dake manne a d'akin kusan karfe 4:30 sauri fitowa tayi daga part din ta wuce bedroom, d'auro alwala tayi tare da gabatar da sallah tana gamawa ta d'auko alQur'anin ta, saboda yau laraba, alqur'ani kawai suke yi tare da jawo hijab din jidda tun a parlour ta zura mata suka fita a tare, lokacin har malam ya zo karatu suka yi sosai inda malam ya masu qarin bayani akan hadisi, sai  gab da magrib suka shigo cikin gida, alwala kawai suka gabatar tare da yin sallah.
        bayan ta idar ta tsaya yin lazumi sannan tayima jidda assignment tayi nata kiran sallah isha ne ya tashe su bayan sun gabatar suka fito parlour sukayi dinner sannan kowa ya wuce bedroom din shi saboda sun gaji likis.

        Asuba ta gari

      Sallah asuba fatuha tayi tare da yin wanka, mai kawai ta shafa tare da sa yar gown iya karta gwiwa sannan ta fito bedroom din jidda ta shiga tayi mata wanka tare da shirya ta cikin uniform sannan ta bar d'akin, kitchen ta shiga cikin sallama baba jummai nata jefa bafanke gaishe ta fatuha tayi cikin fara'a ta amsa sannan suka gaisa da rabi'a, bude fridge tayi ta fido yan cikin rago ta gyara ta d'aura kan wuta tare da zama tana taya su baba jummai aiki, sai hanata suke amma taqi sai da farfesun yayi ta juye a kola tare da hada coffee tasa a tray direct part din sadiq ta wuce.
         a hankali ta murda kofar parlour ba kowa aje tray din tayi saman stool ta nufi bedroom, tsaye ta hango sadiq yana qoqarin saka necktie  sallama tayi tare da gaisheshi cikin fara'a ya amsa sannan ta qaraso ta amshi  necktie din tana samasa bayanta samasa ta kallesa da  murmushi  kwance  a fuskarta  ta  ce, "uncle you look so handsome" tare da masa peck shima peck ya mata tare da daukar suit dinsa black ya riqe a hannu, fatu  ta jawo trolley dinsa  suka fito parlour lokacin angel ta turo kofar tare da cewa "Daddy..! ta fada jikin sadiq hug nata yayi d'an shagwabe fuska angel tayi ta  ce, "daddy am going to miss you"
    "me to angel.!
"amma daddy zaka min tsaraba teddys"
    "yes angel.! washe baki tayi ta ce, "Aunty fatuha kema ki fadama daddy tsarabar da zaimaki" smile tayi tana  kallon  sadiq  kamar  yarda  yake  kallonta ta ce, "Duk abinda daddy yake so shi nake so yamin tsaraba" kallon ta sadiq yake mai cike da so da kauna sannan ya zauna saman one sitar tray ta jawo ta zuba masa farfesun a boll saboda sadiq mutun ne mai son farfesu shiyasa fatuha kullun sai ta masa dan ta faran ta masa, feeding din shi farfesun ta fara yana sha angel itama tana bashi haka suka dinga feeding din juna su cikin jin dadi happy family sannan suka fito tray din fatuha ta kai kitchen ta wuce bedroom tasa uniform tare da d'auko school bag dinta.

  Fitowar ta parlour yayi dai-dai da fitowar su Mom da Abba cikin nutsuwa ta gaishe su peck sadiq ya masu shida angel itama fatuha peck tayi ma Mom suka fice a tare mota d'aya suka shiga da sadiq driver na ja sai da aka zo school din su yayi parking, gaba ki daya idanunta sukayi rau-rau alamun zatayi kuka, suka bama sadiq hug suka fice yana kallon su har suka shige classes sannan driver ya ja mota sai airport.

   
      Tunda sadiq ya tafi su angel suke missing nashi Mom har mamaki suke, bata ko yar rahanan sun daina idan kaga suna raha to sadiq ne ya kira waya, haka shima can cike yake da kewar su inda yake jin kamar wata yayi ba kwana uku ba.

    Akwana a tashi ba wuya wajan Allah yau kwana sadiq biyar kuma yaune ranar dawowar shi, zo ku ga murna wajan su fatuha sai zuba rawar kai ake Mom sai janta take dan yanzu fatuha ta tashi d'aga yar aiki dan tuni sadiq ya yan'tata duk wani abinci da sadiq ke so fatuha ita da kanta ta masa sannan ta jera a dining area.

     Bedroom ta shige tare da yin wanka, kaya ta fido  ta rasa wanda zata sa duk wanda ta fido sai ta maida can ta hango wata red gown me stone's, aje ta tayi a gefe ta tsantsara kawalliya ba qaramin kyau tayi ba, sannan ta zura riga masha Allah indai maganar kyau ake fatuha ta kai, angel ce ta shigo da gudu itama sanye da gown pink ta ce "Aunty daddy ya dawo?" waigowa tayi tare da yin fari da ido cike  da  zakuwa suka fito a tare  shigowar sadiq parlour kenan su fatuha suka fito, kallo sadiq ya bisu da shi mai cike da so rugawa su kayi a tare suka rungume sadiq dariya ya saki kamar  yarda  suma suke  cike  da  farin  ciki  ya  ce, "zaku kadani.! Mom dake saukowa daga upstairs dariya ta saki ta ce "Sadiq kai da yaran ka kuna dirama wallahi" smile yayi tare da hug din Mom in taqaice maku duk wani girki da fatuha tayi sai da sadiq ya ci inda yake ta binta da kallo, ganin ta  kara  girma.

      Bayan ya hutu ya fido tsaraba yabama fatuha I phone 6 waya dadi da murna wajan fatuha ba'a magana jidda kuma Tap Apple mai shegyan kyau tare da new Teddy's haka suka dinga zuba murna baki har kunne.

         *2years letter*

     Wata kyakyawar matashiyar budurwace da baza ta wuce 16 years ba ta rugo da gudu daga upstairs gudu take amma komai na jikin ta amsawa yake sanye take da 3 quarter pink sai riga white mai gajeran hannu tana  sakin  murmushi  mai  qara  fito  da  zalla  kyanta bangaje mutun da tayi ne ya sata tsayawa chak, cikin cool voice din ta ta ce "Sorry ..! tare da ra6awa ta gefansa ta wuce mutuwar tsaye majeed yayi yana binta da kallo jin  wani  abu  ya  harbi  zuciyarsa  lokaci  daya kafadarsa ya d'age tare da sakin killing smile yabi stair's din da kallo, yana  ayana  yarda  ya  ganta wai gowa ya kuma yi ko zai ga yarinyar amma ba alamar mutum sauke  ajiyar  zuciya  yayi.
      sama ya haura direct part din sadiq ya wuce a hankali ya murda handle din kofar ya shigo, sadiq na zaune saman three sitar yana kallon news cikin sallama ya qaraso amsa masa sallamar yayi tare da aika masa harara wasa ya  ce, "sai yau zaka nemeni dan raini senses? dariya majeed ya saki tare da cewa "Sorry" ya zauna yana  cewa, "ni dai yanzu ba wannan zancan ba wacece na gani yanzu kamar daga part din nan ta fito? gaban sadiq ne ya yanke ya fadi qaqaro murmushi karfin hali yayi ya ce "Fatuha ce" *(Ohni salma🤦‍♀ yaushe fatuha ta waye haka🙄lol)* ok majeed yace tare da cije lips dinsa  yana ayana  wasu abubuwa a ransa......hmmmm

Muje zuwa fan's😘

Vote
      Comment

Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best ★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                 71_72

Ina matukar Godiya ga masoyan wannan novel, ina jin dad'in yadda kuke bani goyan baya wannan shafin naku ne duk masoyin CAPTAIN SADIQ*

 

      Ko da fatuha ta shiga bedroom wayar tace ta hau ruri dake bedside drawer, cikin fara'a ta d'auka saboda sunan dake maqale a screen din wato Hanan, daukar wayar tayi tare da kallon screen din kasancewar video call ne saman bed ta haye ta  ce, "Hey yan'mata ya kike?
      "lafiya lau, wai yaushe zaki zo gida ne? ina so muje gidan Ammi birthday din Basma ya kusa?
          "a ina za'ayi birthday din? inji fatuha
    "kema kin san ba'a gida za'ayi ba"
    "Chab aikin san halin uncle wallahi ba zai barni naje ba"
     "nifa matsala ta dake kenan wallahi, ke komai uncle komai shi.! shi..!
    "Eh naji din.!
"yanzu dai ki masa dubara sai muje"
       "gaskiya ina tsoran fushinsa kin manta randa muka je birthday din haulat kenan?
       "wallahi ban manta ba ina sane ras,"
     "toh yayi kyau, amma fa zan shigo insha Allah"
     "to shikenan ki gaishe min da angel"
  "tam.! ta katse wayar tare da kwaciyarta tana  tuna kyakyawar  captain sadiq wadda  bata  gajiya  da  tozali  da  ita har  rana  mai  kamar  ta  yau  kankame pillow tare  da  lumshe  ido.

    Kamar yarda suka saba idan suka had'u haka suka dinga zuba hira tare da yin musu, dama sun saba baza su taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login