Showing 78001 words to 81000 words out of 105783 words

Chapter 27 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

725

baba jummai tayi tana kallon ta baki sake tana  cewa, "ke  lafiyar  ki  'yan nan  wani  abune ya  faru? zaunar da ita saman kujera Baba  jummai  tayi tana qara tanbayar ta lafiya kuka take sosai, cikin shasheqar kuka ta ce, "Wallahi baba bana son majeed bana jin zan iya zaman aure da shi..! ta ida zancan tana rushewa da kuka, sallati baba jummai ta hauyi tare da tafi tana  cewa, "na shiga uku ni jummai , me nake ji haka fatuha sokike ki ja mana abin fade? kowa  yana  mana addu'a Allah  ya  rufa  mana  asirri ya  kai  ki  gidan  sutura, yanzu  kuma  ki  ce  ba  haka  ba, toh idan ba majeed ba wakike so? kuka ta kuma saki cikin shasheqar kuka bakin ta na rawa ta ce, "CAPTAIN SADIQ nake so Baba..! Baba idan na rasa sadiq mutuwa zanyi, ni  shi  nake  so" ta ida zancan tana kuka mai tsuma zuciya, zaro ido waje baba jummai tayi  ta  ce, "na shiga uku ni jummai..! rungume fatuha tayi tana lallashi dan ita kanta ta tausayama fatuha ita kanta taso ace da sadiq din za'ayi, amma ya zasuyi tunda shi bai ce yana so ba? d'ago da fatuha tayi tana share mata hawayan ta ta  ce, "kiyi hakuri fatuha kinji ki cigaba da addu'a Allah yana tare dake Allah zai dubi zuciyar ki ya baki mafi alheri fatuha, ki sama zuciyar ki sallama kinji" ajiyar zuciya kawai take saki tayi lamo a jikin baba jummai.

       ban da tari ba abinda yake har wani jiri yake gani, majeed dake gefansa sai sannu yake jera  masa, toilet ya shige da sauri yana cigaba da tarin gaban zing, yana  sauke  ajiyar  zuciya  saboda  galabaita kallon mirror dake manne jikin zing  yayi  jini da ya ganine gefan bakinsa  ya sashi zaro ido waje hannu ya kai ya ta6a ganin kamar jinine yasa gabansa ya yanke ya fadi, hawayan dake maqale a idanuwasa ne suka sulalo.
           zamewa yayi a qasan toilet din yana mai da numfashi sama-sama kirjinsa  na  tsananta harbawa, miqewa yayi da sauri ya fito duk da yana jin jiri, majeed dake zaman jiran fitowarsa ne ya ta shi yana masa sannu ko amsa masa sadiq ya kasa, wardrobe ya bud'e ya jawo trolley ya fara zuba kayansa yana zubawa jiri na dibarsa ga tarin sai zuwa yake tare da jini amma duk wannan abun yaki yadda majeed ya gane sai da ya gama had'a kayan shi tsaf majeed na gefe tsaye riqesa yayi ya ce "Baby wai me ke faruwa ne? naga muna lafiya lau lokaci daya ka rude, me  ke  damun ka  ne? murmushi yayi ya ce "Karka damu tunawa nayi da flight dina na zuwa Lagos yau zai tashi kuma gashi saura 10 minutes ya tashi"
         "ok muje nayi dropping naka"
"ka barshi kawai nayi ma driver magana ka ji" ok ya ce masa tare da yi masa peck  ya  ce, "safe trip..! sannan ya sa kai ya fita dakyar ya iya jan trolley ya fita waje yana tafiya yana tari tunkan ya qaraso ashuru driver ya bude masa murfin mota amsar trolley yayi yasa a boot sadiq yana shiga mota ya fara bale button din rigarsa saboda wani  irin zafi yake  ji  numfashinsa sai daukewa yake  yana dawowa, idanusa  sun  firfito  waje  sunyi  jawur  har  lokacin  yana  tarin  jini sai  dai yasa handkerchief yana toshe  bakinsa ko da ashuru driver ya shigo mota ja yayi suka bar harabar gidan.
                Ta cikin mirror ya fara ganin halin da sadiq yake ciki a  firgice  ya  ce, "yallabai.! cikin galabaita sadiq ya iya furta, "kaini wajan Dr yakub.! da gudu ashuru ya fisgi mota sai asibitin doctor  yakub yana  driving  yana  waigen  sadiq.
             Suna Isa asibiti driver  ya  faka mota sadiq ya 6ale murfin motar ya  fito duk da yana ganin jiri, numfashinsa na  barazanar  daukewa bibiyu  yake  ganin  mutane da  hanyar  ita  kanta office din Dr yakub ya nufa yana had'a  hanya.
      bude kofar office  din  Dr  yakub  ke  da  wuya sadiq ya sulale sumame a wajan...🙆‍😰

  Muje zuwa fan's
      
            Vote
     Comment Written by
      salma mas'ud nadabo

Edit by
    Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We  are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                    81_82

            Mikewa Dr yakub yayi dan kawowa sadiq taimakon gaggawa. gabaki d'aya shima ya rud'e kwalawa nurses kira ya shiga yi da sauran ma aikatan asibitin, saboda  gabaki  daya ya  rikice, kafin kace me har an daura sadiq a gadon asibiti.
              Ashuru driver da shigowar shi yanzu ya ga za'a  wuce  da  sadiq  emergency bin gadon yayi yana matsar kwalla, ba'a zame da sadiq ko ina ba sai emergency, ashura na ganin haka ya ci birki bakin kofar emergency yana zarya, yar wayar da ke aljihunsa ya zaro dan ya kira gida amma sai dai wayar ba chaji kuma bai iya tafiya ya bar sadiq a yanzu dan ana iya buqatar wani abu, haka ya dinga zarya bakin kofar gabaki daya ya rude hankali  sa a tashe.

          Haka baba jummai ta dinga lallashin fatuha sannan tayi shuru Baba jummai  ta  ce, "fatuha  tashi kiga mu koma tunda dai kin san aiki na can na jira na.! matsar kwalla ta fara cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah Baba ki barni a nan wallahi bana san zuwa, bana son jin hayaniyar mutane, mudin na cigaba da ganin abinda ake a gida ina iya shiga wani hali" duk yadda baba jummai taso ta tafi da fatuha firtaqi ba yarda ta iya shiya ta barta ta tafi ko da baba jummai ta fita kuka fatuha ta dasa.

     Shewace ke tashi yadda kasan yaune daurin auran wajan  su  Basma, zuhura ce ta shigo da sauri ta fada jikin Basma tare da cewa "Ansa biki wata d'aya..! washe baki Basma tayi tare da jawo wayarta ta fara kiran sadiq duk wannan kira da take ba'a dauka ba, ta6e baki tayi tana  zancan zuci, "duk kayi ka gama aure dai sai munyi duk wulaqancin da kake zubamin bashi zai sa na daina son ka ba..! ta ida zancan zuci da jan d'an guntun tsaki, Hanan ce tashigo jiki a sanyaye Basma ce ta ce "Ke kuma lafiyar ki kuwa? Naga  duk  yau  baki  walwala..!
      "wallahi tun d'azu nake neman fatuha a gidan nan narasa  inda ta shiga, shi  ne abun  duk  ya  dame  ni  ta  barni  ni  kadai, na kira wayarta yafi aqirga kashe"
      "toh fa.! dazu dai tanan cikinmu har tace min kanta na ciwo na bata magani, namayi tunanin bacci tayi"
       "ok qila ta koma gida, amma bari idan mun gama abinda muke sai muje ko?
     "eh gaskiya" sannan Hanan tasa kai ta fita.

       Bangaran iyaye angama komai inda Mom ta yanke shawarar Basma ta koma can gidanta yadda za'a ji dadin kula da amaran, waje daya kuma kowa ya amince da shawara.

 
        doctors ne kan sadiq dan ceto rayuwarsa, inda suka ci sa'a ciwo zuciyar bai dad'e da kamashi ba, daya sha magunguna yadda ya kamata zai warke sai da yamma likis aka fito da shi, Ashiru yabi bayan su aka ba sadiq d'aki, har lokacin sadiq na kwance yana bacci sai qarin jini dake masa wanda doctor yakub ya bada nashi, ashiru zama yayi d'aya daga cikin kujerin dakin sai da ya dan jima sannan ya wuce office din Dr, ko da ya shiga lokacin yakub ya fita ganin wasu marasa lafiyar hakan yasa wuce gida dan sanar masu  halin da sadiq yake ciki.

           A hankali yake ware sexy eye's ball's dinsa da suka masa nauyi, bude kofa akayi a ka shigo ba kowa bane sai Dr yakub qarasowa yayi bakin gadan ya  zauna  gefen gado a hankali ya kai hannu goshin sadiq har yanzu da zafi rau cikin sanyi murya Dr ya fara magana "Captain me yasa  kake wahalar da zuciyar ka da tunani tuntuni? nayi tunanin ka daina tunani amma yanzu ka dawo da shi sadiq, har kaja ma kanka ciwo zuciya" lumshe ido sadiq yayi kawai yana saurara Dr ya  cigaba  da  cewa, "na rasa wani irin tunani kake wannan sadiq? ciwo nan da kake gani yana iya jama ka rasa aikin ka sadiq, har ma  rayuwarka, da ace asibitin mu ka je ai da yanzu an farama shirin sallama ka wajan  aiki..! rike hannu sadiq yakub yayi  da sake cewa "Please ka fada min damuwar ka please sadiq? hawaye ne masu zafi daya ke bin daya a fuskar sadiq shi kan shi yakub ya firgita da yanayin da sadiq ya koma yanzu, cikin sanyin murya Dr ya ce "Tunda baka iya fada min ya kamata a gida a san damuwar ka..! ya fadi hakan yana qoqarin fita riqe hannunsa sadiq yayi tare da ware idanuwashi da suka zama ja ya ce, "Please karkamin haka Dr bana fata kowa yasan abinda ke damuna a yanzu, please kamin alqawarin baza ka fada ma kowa ba? zame hannunsa Dr yayi dan baya jin wannan karan zaiyi shuru, har ya kai bakin kofa sadiq ya ce "Dan Allah karka fadi please" ya ida zancan yana kuka mai cinrai  chak Dr yakub ya tsaya dan gabaki daya tausayin sadiq ya lullu6e sa  damuwar  sadiq  ta  zarce  na  da  a  yanzu dawowa yayi da sauri saboda tarin da sadiq  yake dan  basa taimako, allura samun hutu ya  masa, ya fita ko da ya shiga office ya kasa zaune ya kasa tsaye yana tunanin inda matsala sadiq take dan yanzu ya lura ko yasha maganin indai zai cigaba da tunanin da yake zai zama anyi ba ayi ba.

     Ko da  ashiru driver ya koma gida har yanzu basu dawo ba, suna family house juyawa zaiyi da motarsa ya wuce family house kenan, sai ga fatuha mai  keke napep ya ajeta ta fito suku-suku ba alamar walwala dan itama a tunanin ta sun dawo, Ashuru ne yayi  parking tare da qarasowa ida take gaishe shi tayi a taqaice tana qoqarin shigewa gida ya  ce, "fatuha.!
       "Na'am" tace tare da waigowa ya ce, dama.. dama..!  gaban tane ya yanke ya fadi saboda yadda Ashurun ke magana kamar wanda yayi ma sarki qarya "me ya faru? ta fada a taqaice
    "dama yallabai ne ba lafiya yanzu haka yana asibiti na zo fada maku ne kuma har yanzu basu dawo ba" zaro ido fatuha tayi da dafe da qirji tuni hawaye suka 6ale mata ta  ce, "me ya same shi? ta fada bakin ta na rawa, "muje ka kaini asibitin idan ka ajeni sai ka biya family house ka fada masu" da sauri ta shiga motar Ashuru ya ja sai asibiti.
        suna Isa ta bale murfin motar Ashuru na gaba tana biye tana kuka suna Isa dakin ashuru ya juya fatuha ta shige ganin halin da sadiq yake ciki yasa fatuha sakin sabon kuka tare da qarasowa bakin gadon, a hankali ta kai hannuta saman kan sadiq hawayan na sulalo mata ruwan hawayan ta ne ya d'iga a saman idon sadiq, tana rasgar  kuka mara sauti a hankali ya fara ware idanuwasa sauke su kan fatuha data ci kuka har ta gaji ta  koma  tamkar sabuwar  mahaukaciya riqe hannu sadiq tayi ta ce "Uncle meke damun ka?" murmushi ya qaqaro wanda iya karshi la66ansa ya kai hannu saman fuskarta yana gogewa fatuha hawayanta lumshe ido  fatu  tayi tana  jin yarda  hannu  sadiq  ke  yawo da  hannusa saman  fuskarta  tana  sauke  numfashi  a  hankali, lumshe ido yayi tare da ware su ya ce, "My dear bana so ina ganin ki kina kuka kinji? ba wani abu bane ke damuna ba kawai fever ne saboda na daina ganin smile din ki" ya fadi zancan yana ja mata hanci smile fatuha ta saki mai had'e da kuka-kuka ta kai ma sadiq peck a goshi tana  bin  shi  da  idanuta.
                Dr yakub da yanzu ya turo kofa ya shigo, ko sanin ya shigo basuyi ba, suna  ta  kallon  juna hannuwan su  sarke dana juna tsayawa yayi yana kallon su yana tunani, musanman yadda ya ga lokaci d'aya sadiq ya sauya, hannusa sadiq ya kai gashin kan fatu ya ta6a wanda ya leko waje ya ce, "fatuha.!
      "Na'am" ta ce tana kallonsa cike da so da kauna ya  ce, "me yasa kika daina kulla da gashin kan ki? hawaye ne suka sulalo mata ta bud'e baki za tayi magana sadiq ya daura d'an yatsansa sama lips dinta ya  ce, "shhh.! a hankali ya kwance dankwalin kanta gashin ya baje a gadon bayanta ba wai wanke kan ne batayi ba a'a duk wasu mayuka masu sa gashin sheqi ta daina shafawa saboda ko lokacin hakan bata da shi, sadiq  ya  katse  mata  tunani da cewa, "har yanzu baki son majeed ko? kuka ta saki mai cin rai har da shesheqa, rintse ido sadiq yayi tare da shafa gefan face nata ya  ce, "kukan ya Isa haka mana bana so naga kina kuka kinji? d'aga masa kai kawai fatuha tayi tare da daura hannuta saman nashi bakin ta na  rawa ta ce, "Shikenan uncle yanzu Basma zaka aura? ta zama matar ka? angel ta zama diyarta ko? kuka ta kuma saki mai cin rai, lumshe ido sadiq yayi bakin ciki na cin sa smile yayi ya ce, "Nace fa ki daina kuka kuma angel diyarki ce ai" daga kai tayi ya ce, "good.! haka kuma nima naki ne? Jinjina  kai  fatu  tayi  wasu  hawayan  na  kora wasu  sadiq  ya  ce, "ko baki so na auri basma? idan baki so sai na fasa" ya fada yana smile.
      "ba wai bana so bane uhm..! bata ida zancan ba Dr yakub yayi sallama dan ya lura sai su kwana suna hira gashi fira da ya ji suna yi kamar cike take da matsala da rudani idan ya fahimta kenan, da sauri ta daura dankwallin ta tare da gaishe da Dr alura ya ma sadiq tare da cewa, "wanake gani kamar fatuha? murmushi ta saki ta ce "Ni ce"
      "gaskiya naga kin canza, ko duk amarcin ne? ya fada yana kallon face din sadiq take annurin sadiq ya fara daukewa haka fatuha dake zaune kusa da shi kawar da zancan yayi dama face nasu yake so ya karanta idan har ya gane suna son junan su, amma sai dai kowane wani da ban zai aura, insha Allah zai taya su da addu'ar cikar burin su idan  har  Alheri.

     Ko da Ashuru ya je gida ya fada kusan mota biyu sukayi ko 10 minutes basuyi ba suka iso asibiti, a lokaci fatuha na feeding sadiq abinci yana ci suna dariya dan ji yake gabaki daya kamar ya warke, turo qofar da akayi ne yasa su waigowa majeed ne ya fara shigowa turus yaja ya tsaya yana mamaki yaushe fatuha ta zo? haka Basma dake bayan shi da Umma da Mom, ashuru ne da shigowar su yanzu shi da su Abban ya fada masu yadda a kayi har ta zo dan sakin jikin majeed yayi amma har yanzu ya kasa kauda ido daga abinda ya gani, kishi ne ya lullu6e sa, fatu  kuwa duk kunya ce ta kamata aje plate din tayi tana qoqarin tashi, sadiq ya riqe hannuta yadda baza ta iya matsawa daga kusa da shi ba, dan bai iya hakuri da rashin ta kusa da shi yanzu kallonsa take tana masa alama daya sake ta amma yaqi sakinta, sai ma wasa dayake  da yatsun hannuta ganin ba yadda za tayi yasa ta hakura, tana sakar  masa  murmushi mai  cike  da  ma'anoni daban-daban Basma ko ta cika fam dan ita taso ace take kusa da shi ba fatuha ba.
         shima majeed ba laifi ya dan shaka amma yaki yadda zuciyarsa ta fadi abinda take tunani sai ma watsar da zancan da yayi, shi ko sadiq yaqi sankin hannuta da sunyi ido biyu sai ya sakar mata lallausan murmushi, Mom da ke lura da yanayin su sai suka bata tausayi dan dai kar tayi magana ace gashi, da ba abinda zai sa tace a basa auran amma da tayi magana tasan abinda zai biyo baya.
              ko da su Abba suka tanbayi Dr yakub me ke damun sadiq fever ya ce masu a taqaice .

     Kiran sallah magrib ne yasa Sadiq ya saki hannu fatuha dan ta dauro alwala lokacin har su Mom sun tafi, daga ita sai Basma sai majeed da shima yanzu ya wuce masallaci  tana Shiga toilet Basma ta matso ta zauna kusa da sadiq kasancewar ita hutu take ta  ce, "ya jikin?  cikin yauki da kisisina lumshi ido yayi ya  ce, "Da sauki"
     "Allah ya baka lafiya sweetheart" miqewa tayi tana  kwarkwasa daniyar ta masa peck lokacin yayi dai-dai da fitowar fatuha daga toilet, bin gadon tayi da kallo ganin yarda Basma ta  wani  rankwafu  kamar  zata  sunbaci  sadiq a baki, wani irin kishi ne  ya  rufe  fatu wanda ita kanta bata san tana da shi ba.
      juya mata baya sadiq yayi tare da cewa cikin cool voice, "Basma kai na na ciwo koya naji an tsayamin a kai nauyi yake min" ya fada yana kallon fatuha da saura qiris ta fashe tana  kallon su fita tayi daga d'akin da sauri ko da ta fita kuka ta saki mai ban tausayi, ta dade tana kuka sannan ta samu guri a wajen tayi sallah...
Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
      Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM


                    83_84

             Bayan ta idar da sallah tana qoqarin nade daduma majeed ya shigo lallausan murmushi ya sakarmata tare da qarasowa kusa da ita, duqar da kai tayi qasa tana wasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login