Showing 18001 words to 21000 words out of 105783 words

Chapter 7 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

704

daga cikin plate d'in abincin  tare da dalla wa rabi'a harara y'all ce, "ai saiki zo ki kwashe ragowar abinci ki cinye mara mutunci kawai..! ya qara jan tsoki mtssss..! ya dawo  parlour ya zauna tare da d'aura Jidda a cinyar sa ta  ce, "Daddy please muje shan ice cream"
            "Ok angel bari na d'ako car key sai mu fita" aje Jidda yayi saman three star sannan ya haura sama.

                            *****
             Sai da suka kusan cinye rabi alawar, sannan suka saurara mata sai dai muce Allah ya  tsare kar ayi zawo.
                   Sai yamma likis fatuha  ta waiwayi gida shima d'in ma dan zata canza kaya dan ta je gad'a Washe da baki fatuha ta qaraso gida, Inna da baba jummai sai labari suke saman tabarma ta zo ta wuce su, baba jummai washe da baki ta ce, "Fatuha yan'mata" murmushi tayi tare da shigewa uwar d'aka, baba jummai ce ta qare mata kallo tsab ta ce "Masha Allah fatuha kyakyawa ce sai dai  rashin jita baya bari a gani" tana da d'an tsawo dai-dai gwargwado ita ba gajera ba kuma baza'a kirata doguwa ba, tana da karan hanci kamar biro, bakin ta d'an qararami ne pink, ba laifi tana da hips sai dai yanzu ne ta fara kirgan dangi , wannan kenan, baba jummai ce ta numfasa ta ce..."Ni ko ladingo ina so inzan koma zan tafi da fatuha, dama  hajiya tace na nema mata wanda zata dinga taimakama yar jikarta saboda yarinya ce, shine da na yanke shawara idan jauro ya dawo daga gona sai mu tattauna kan zancan"
         " Ta6 baba jummai bana jin malam zai yarda da batun ki, saboda  baya bari taje ko ina iyakar ta cikin kauyan nan, baba jummai da malam zai yarda da haka nima da zan so hakan, ko dan fatuha ta gyaru tunda nasan birni da kauye ba d'aya bane dole inta je can ta nutsu suma  yan  kauyan  su  huta" nisawa baba jummai tayi ta ce, "Bari jauron ya dawo ni na masa magana"
            "toh Allah yasa ya amince..

  Fatuha ce ta fito washe da baki daga uwar d'aka, tasha jan baki a dole yau itama gad'a zata ta ce "Inna nayi kyau? murmushi inna tayi ita da baba jummai suka hada baki suka ce, "Kinyi kyau fatuha" qara washe baki tayi sannan ta sa kai ta fice.

                         *****
  Riqe da car key ya dawo main parlour tare da d'aukar Jidda ya ce, "Mom zamu fita shan ice cream may be mu biya gidan Anuty bilkisu"
        "OK a dawo lafiya, angel amin tsaraba fa"
            "toh grandma" sannan suka fita.

    Ko da suka fita anwanke masa motarsa CRB black, Kaitsaye wanja motar suka wuce  ola ya bud'e masa murfin motar dana Jidda tare dayi ma Jidda wasa sannan suka sa kai suka fita, sosai yayi yawo da Jidda, daga nan suka wuce gidan Anuty bilki.
                       Cikin jin dadi ta tarbe su inda ta cika Sadiq da kayan fruit Jidda ko sai wasan su suke ita da jamal, da murmushi Aunty bilki ta ce..."Ohni baby yanzu an fara zuminci" tana fadin hakan ne cikin zollaya, harara ya wurga mata ya  ce,  "oh you mean da bana zuminci ko tunda haka kika ce bari na tashi na tafi" hararar wasa ita ma ta masa ta  ce, "tab naga yarda zaka fita daga gidan kuwa" hira suka sha sosai daga nan suka wuce family house.

     Part din ammi ya fara zuwa  tana zaune saman one star tana kallon film din India wanda ko za'a kashe ta bata san me suke cewa ba, washe da baki ta juyo tana cewa "Ah'ah yau mai gidana da kansa? ya  Hauwa'u ita da  Ibrahim d'in?"
         "lafiya lau" ya ce tare da zama
    "Ka ce min da sarkin surutu ka zomin yanzu ta fara min wannan yaran nasu na yahudawa" Murmushi Sadiq yayi ya ce, "Kisha kurimin ki Ammi ai koya maki take"
            "Ah ni ina zan iya wannan gwalangwatsin wannan sai ku" Asiya ta kwallawa kira, cikin sauri ta qaraso  tare da gaishe da sadiq Ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana Ammi ta  ce, "Yauwa yan'nan kawo ma mai gida furar dana dama d'azu tana cikin fridge"
            "toh Ammi" ta mike ta wuce kicin.
    Haka akayi ta kawo masa fura ya sha sosai, saboda shi Sadiq mutun ne mai son fura sai da ya sha ya koshi sannan suka wuce part d'in Umma,

  Suna shiga part d'in da Basma suka ci karo, sanye take da riga da wando riga mai dan gajeran hannu pink mai manya flowers tayi kyau sosai duk da yarinya ce hakan yasa shape din ta fitowa, Kallo d'aya Sadiq ya mata ya watsar Gaishe sa tayi tare da jan hannun Jidda tana mata wasa  sadiq ya ce "Basma ina umma?
       "Umma na bedroom"
"OK ki  ce  mata  na  zo" Sannan ya samu  guri ya zauna.
        Umma  da murmushi ta fito sun dad'e suna hira, Inda tasa talatu ta cika masa tray da kayan motsa baki ,suna cikin hira majid ya dawo suka dasa sabuwar hira.

                        *******
  Sosai suke jin dad'i gadar inda yau sai da su fatuha suka taka, duk da ba wani abu suka iya ba, Sosai sun burge mutane ita da fatsima saboda cikin tsari suke rawar su kamar manyan yan'mata....!
Writing by
         Salma mas'ud nadabo

Edit by
       Raheenat

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★ we are the best★

https://mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&_tn_=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                    25_26

         Basu suka dawo gida ba sai bayan isha lokacin har jidda tayi bacci,  d'auke yake da ita har suka qaraso  parlour, lokacin rabi'a tana qoqari fitowa daga kitchen, wani irin kallo ya wurga mata jiki ba qwari  ta gaishe shi har tayi gaba ya ce, "Keeee.! Tsayawa tayi cikin tsoro da fargaba, Harara ya qara wurga mata cikin tsawa ya ce mata "Sai ki zo ki amshe ta ko?" Jiki a sa6ule ta amshi jidda, ya  ce,  "Kiyi mata wanka sannan ki samata night dress ki kawo min ita d'aki na dan ban yarda ta rinqa kwana da ke ba ki koya mata halin bera" tsaki yaja  Mtsss, sannan ya wuce part din Abba.

            Abba na  zaune  saman two star fuskar shi manne da glass, sanye yake da fara jalabiya blue remote ne a hannusa yana kallon news, Mom na gefen sa tana yanka fruit.
         D'au da  sallama ya shigo tare da gaishe da Abba,  cikin fara'a Abba ya amsa ya ce "Ah har kun dawo daga zuminci?
           "Eh Abba"
"toh masha Allah ina jidda?
          "jidda tayi bacci"
     "madallah" sun dad'e suna hira sama-sama daga nan Sadiq ya wuce part nashi, ko da ya shiga d'akinsa ya iske ankwantar da jidda shima bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito sai da ya gama shirin shi na bacci sannan ya had'a coffee yana sha yana dana laptop din shi ,ya dad'e a haka sannan ya ture laptop d'in tare da janyo jidda jikin shi bacci ya d'aukesa.
 
                     *****
       Bayan an gama gad'a kowace ta wuce gidan su, da sallama fatuha ta shigo gida lokaci Baffa ya dawo gida yana zaune bisa tabarma inna na kusa da shi baba jummai na gefe su, gefan baba jummai ta je ta zauna washe da baki itama baba jummai murmusawa tayi sun danyi hira sama-sama da fatuha daga nan bacci ya sureta.

      Baba jummai ce tayi gyaran murya ta ce "Dama jauro ina so muyi wata magana da kai" inna da ke kusa da Baffa tayi qoqari tashi baba jummai ta ce "Kema  zauna" haka ko akayi inna ta samu guri ta zauna.
   Gwoggo  ta  cigaba  da  cewa, "Dama so nake nama ka magana kan fatuha ina so idan zan koma birni sai mu koma tare," Zaro ido Baffa yayi waje yana kallon yar uwar tasa a zuciyarsa ya ce "Anya ko baba jummai tasan me take fada kuwa?"qara murmusawa tayi ta ce, "jauro ina fatan ba za ka watsamin qasa ido ba, a ganina fatuha nima d'iya tace  jauro," Baffa ne  yayi tsale  ya dare ya ce bai san zancan ba babu inda fatuha zata tanan kauyen nan tare da shi baze lamunci hakan ba, baba jummai ce ta fara matsar kwalla tana cewa "Ba komai jauro dan ka ga Allah bai bani haihuwa ba shine zaka wulaqanta ni kan diyar ka, jauro da Allah ya bani haihuwa da yau ba zanji zafin abinda kayi min ba," tana maganar tana kuka inna sai lallashinta take, ganin kukan da take yasa jikin Baffa yayi sanyi dan shi a ganinsa babu abinda baba jummai zata nema a rayuwar shi ya hana ta, sai  gashi  kan  fatuha suna  neman  samun  Matsala da  yar  uwarsa.
              Bayan da ya iya haka ya hakura ya amince  tatafi da fatuha, aiko washe da baki ta masa godiya tare da yi masa alqawarin zata riqe amanar fatuha sosai daga nan kowa ya wuce dakinsa.
                      
                          ******
     Ko da ya tashi ya gama shirin sa ciki uniform masha Allah yayi kyau sosai,  zai d'au briefcase d'in sa kenan jidda ta tashi washe da baki ta ce, "Daddy morning"
          "morning too angel"
"uhm yau ma daddy guduwa zakayi ka bar little princess din ka a gida? langwabe kai yayi ya ce "Sorry angel daddy work zai tafi kinji kuma yara basa zuwa, kema very soon zaki fara zuwa school ai kinaso ko angel? washe baki tayi ta ce "Yes daddy zan fara zuwa school kamar yarda su yaya Hanan ke zuwa da Anuty Basma ko?
       "Eh mana angel" tsale tayi ta kai masa hug "thanks my daddy" smile yayi tare da yimata peck ya  ce,  "please angel ki tsaya rabi'a ta maki wanka kin ji, naji grandma na cewa kullun sai kin yi rigima" 6ata fuska tayi ta ce, "Daddy...!
         "shhhh.! tare da yi mata peck a kumatu ya fice.

      A dining area ya had'u da Abba shima yana breakfast, Mom na  gefen shi a hankali ya qarasa yayi masu peck sannan ya samu waje ya zauna ya fara breakfast, lafiyayan chips ne da plantain and egg sai tea mai kauri wanda ya sha ovaltine, cikin natsuwa suka gama break d'in su, Abba da Sadiq tare suka fito inda yaran Sadiq ke ta kwasar gaisuwa wajan Abba   tare da qamema Sadiq d'in cikin natsuwa motocinsu suka fita daga harabar gidan.

                         ****
    Ko da fatuha ta tashi wanke-wanke tayi, sannan ta d'au tulun ta gidan su fatsima ta biya tare suka fito suna tafe suna hirar su, kandala suka hango d'auke da farantin gyadarta qarasowa su kayi wajan ta, Kallon su take jiki ba kwari  harara suka wurga mata tare da cewa "Bamu gyad'a ta murtala" jikinta baqwari ta fara zuba masu gyad'ar tasan ko zata mutu baza su bata kudin gyad'ar ba, kuma ta matsa masu  su tona mata asiri sai da ta gama zuba masu sannan fatuha ta amsa ta ce  "Cikin Murtala da d'an mai gari ya mana alqawari ne muka amshi gyadar, sannan kice masa ko ya bamu murtalar mu ko kuma murtala ta rinqa haihuwa" sannan suka wuce suka barta tsaye tana matsar kwalla.

            Suna isa rafi suka aje tulu nan su gefen rafi suka wuce gonar mai gari suka fara tsinkar mangwaro da gwaba, sai da suka d'iba son ransu sannan suka zo zasu fita mai gadi ya kama su.
          "kai-kai uban wa ya baku ikon shigowa gonar mai gari? har ku tsinke  masa mangwaro.! Fatuha ce ta turo baki gaba ta ce, "bala ne ya bani izinin shigowa"
     "shegiya mai kama da mayu, shi balan sa'an kine? Koko  sabo  da  raini  irin  naki  dama  kin  rai  uban  kowa, inama kika san balan? harara fatsima ta wurga masa ta  ce, "idan baka yarda ba sai ka kai mu wajan shi ka ji da kunnan ka" ta ida zancan tana gyara d'aurin zaninta.
            "Ai  dama  ba  kunya  ta  ishe  ki ba mindin   naji  akasin  haka  na  lahira  sai  ya  fiki  jin  dad'i "
      Aiko haka akayi mai gadi jan su fatuha yayi har gaban bala, sai yan harare-harare suke koda ya  suma bala ya  masa  bayani sai ya ce, "shi ya ce su d'inba dan yasan in bai ce ba tuna masa asari zasuyi, na  sun  ta6a kamasa  da  kandala gari  kowa  ya  sani  ana  ganin sa  da  mutunci sannan yasa mai gadi ya sake su wani irin dad'i suka ji suna ta shewa suka isa rafi suka debo ruwa.
         
                        *****
Bai zame ko ina ba sai Yandutse college dan samoma jidda admission, bai sha wani wahalla ba ya samama ta inda duk angama abinda za'ayi, ranar Monday sai ta fara zuwa school sannan ya wuce office, a cewar shi inya dawo gida da yamma zai samamata malamin adini.
                 
                       ****
       Kwanci tashi asarar mai rai yau satin baba jummai d'aya a wudil inda take ta had'a kayanta dana fatuha, Fatuha sai kuka take har da  majina dan ita a ganinta baba jummai bata mata adalci ba ita tace mata tana son birni da zata kwashe ta su tafi, toh Wallahi sai nayi rashin mutunci idan sunje  kenan, cewar  fatu  a zuciyarta baba jummai ce ta juyo ta  ce, "haba fatuha sai ka ce za'a cinye ki sai kuka kike haba fatuha kinsan muna tare kuma zan kula da ke kamar yarda inna zata kula da ke, dan Allah kiyi hakuri kiyi shuru kinji" Inna da ke gefe duk da tana jin wani irin amma tasan baba jummai ba zata tayi abinda zai cutar da fatuha ba amma ko yaya tana jin zafin rabuwa da fatuha saboda fatuha yarinya ce mai shiga rai, ta  wani  fanni  kuma  gara  fatun  ta  tafi  ko  muta  nan  kauyan  sun  huta  da  jarabar  fatuha, a hankali inna ke lallashin fatuha har tayi shuru haka shima Baffa da ke gefe haka baba jummai ta gama had'a kayan fatuha cikin yar leda gari yayi zafi ta miqa mata ta rungume.
       Baffa kuma yaje taro masu mashin,  Sallama fatsima tayi ta shigo falon kallo d'aya zaka mata kasan itama ta ci kuka har ta gaji, wani saban kuka suka dasa ita da fatsima dakyar aka lallashe su sannan baffa ya shigo ya sheda masu gamai mashi din.
       Suna kallon su har suka 6ace maganin su Baffa ya goge yar kwallar shi, dan shi kad'ai yasan yarda yake ji, suna isa tasha suka samu motar Kano basu wani dad'e ba motar ta tashi.
      
                    *******
      Idanuwansa lumshe kamar wanda ke bacci,  zaune yake saman resting chair yayi crossing leg's nashi ta6a shin da akayi ne ya sasa ware sexy eye's ball's d'in sa ba kowa bane sai majid murmushi yayi ya ce "Yaushe ka zo ban sani ba?
        "yanzu na shigo Mom ta ce min kana nan" sannan ya zauna daya daga cikin chairs din sadiq  ya  ce, "OK ya aiki? 
     "Alhamdulillah soma nake na dawo nan da aiki, kai Allah ya taimake ka har yau basu ma transfer ba"
          "Aiko dai ai bana fatan hakan wallahi" murmushi sukayi su duka suka cigaba da magana a matsayin su na abokai kuma yan'uwa...

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
       Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

     https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
           
                             27_28

         Misalin karfe 5:00pm motar su fatuha ta tsaya a tasha lokacin har bacci ya d'auke ta tana kafadar baba jummai rungume da jakarta gari yayi zafi, ahankali baba jummai ta shiga tashin ta, aiko nan tatashi tana wani wiqi-wiqi da idanu da qarewa tashar kallo, mutanene birjik haka suka zuro kafafun su suka fito daga motar, Baba jummai ce ta zaro wayar ta cikin zani y'ar baby nokia ce ta  fara  kiran  Mom  ta  sheda  mata  isowarsu bugu d'aya zuwa biyu Mom ta d'auka washe da baki baba jummai ta  ce, "hello hajiya gani na iso ina tasha.! daga d'ayan bangaran Mom ta  murmusa  ta ce.. "masha Allah yanzu zan aiko driver ya d'auke ku"
          "Toh hajiya" sannan ta datse kiran tana Murmushi ta kalli fatuha ta  ce, "Yanzu za'a zo d'aukar mu kin ji yan'nan" kad'a kai fatuha tayi dan ita a wannan lokacin haushin kowa take ji.
      Ba'a fi  30 minutes ba driver ya qaraso tare da kwashe kayan su ya zuba cikin mota, inda yayi-yayi da fatuha ta bashi Jakarta ta qi ba yanda ya iya haka ko suka tafi.

          Kai tsaye sultan road suka wuce nan fa fatuha ta fara zare ido tana qarewa unguwar kallo kamar wadda ta zo aljana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login