Showing 6001 words to 9000 words out of 105783 words

Chapter 3 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

699

da haihuwa akayi suna inda yaro yaci suna idiris wato suna Malam idi, Ana mai lak'abi da jawad sosai rana suna akayi shagali bayan shekara biyu ta k'ara samun wani cikin, lokaci Ibrahim yayi kudi sosai ya qara murjewa shi da Hauwa'u daka gansu kaga Hutu inda yake ba Hauwa'u kulawa sosai har ta haifi d'iyar ta lafiyaya rana suna taci Bilkisu, sosai suke samun kulawa wajan iyayan na su.
CAPTAIN SADIQ
👮

CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂


*written by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Blood sister deeja*
Follow me on wattpad: salmamasudnadabo

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM 🐄*


9_10

Yau kusan shekara 2 da haihuwar bilkisu inda Alhaji ke sa ran Hauwa'u zata samu wani cikin amma shuru hakan yasa hankalin shi ya tashi, musanma shi alhaji Ibrahim mutun ne mai son haihuwa ne haka suka cigaba da rayuwa cikin so da kauna inda alhaji Ibrahim yake faranta ran Hauwa'u amma cikin zuciyar shi nan maqale da san yaga ta qara haihuwa.
gidan su ko na rijiyar zaki sun rushe shi sun ginawa iyayan nasu katafarin gida mai kyau family house.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi da san juna yau shekarar Hauwa'u 3 ba ciki kuma yau ne tatashi da wani irin zazzabi da ciwo kai sosai hankalin alhaji ya tashi haka ya kai ta asibiti akai mata yangwaje-gwaje inda aka shedawa alhaji Hauwa'u na dauke da juna biyu, zo kuga murna wajan alhaji baki har kunne ya daurawa cikin san duniya haka suma ya'ya nashi saboda basu da burin da ya wuce Momin su ta haihu su sha suna, locakin itama Aunty aisha nada ciki matar kabiru zo kuga yadda surukar su ke basu kulawa da nuna masu soyayya duniya ta zamar masu sabuwa yayin da mazan nasu ke rawar kafa kan cikin .
Cikin su na da wata 7 akayi bikin rukayya da mijin ta aliyu ansha shagali anyi bidiri sosai ankai amarya kaduna GRA.


Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau safiyar lahadi Hauwa'u tatashi da naquda kaitsaye asibiti suka wuce tahaifi kyakyanwa dan ta namiji, murna wajan alhaji Ibrahim ba'a magana da Aisha ta zo barka da tsohon cikinta ita da kabiru sun dade sosai a asibtin ita ma Aisha tunda safe take jin naquda tana daurewa, kasancewa ita haihuwar farko ne saboda sun dade basu haihu ba, basu suka fara shirin barin asibitin ba sai dare a dai-dai bakin kofa ta fara naquda nurses suka bata taimakon gagawa Alhamdullilah itama ta haifi dan ta namiji zo kuga murna wajan su ba'a magana, ba a salame su ba sai washe gari da safe murna wajan family ba'a magana kamar ranar aka fara haihuwa.
Kwana 7 da haihuwa akayi gaggarimin suna a family house nasu inda dan Ibrahim yaci sunan kakan shi na wajan mahaifiyarsa wato *Abubakar sadiq* ana mai lakabi da baby shi kuma dan kabiru *Abdulmajid* sosai akayi bidiri anzubar da kudi yadda ya kamata bayan suna da kwana daya alhaji Ibrahim ya koma katafarin gidansa daya tsara a sultan road, sosai gida ya hadu inda duk wani abin morewa na rayuwa akwai agidan sosai kowa ya tayasu murna.

****
_Bayan shekara biyu_

sadiq yayi wayau sosai bashi da aboki sama da majid inda aka dau son duniya aka daura masa, yaro kullun kara kyau yake kamar dan larabawa kowa bama sha'awa yake amma sai Allah ya daura masa qiwuya kamar me gashi abu kadan bai isa yasasa dariya ba idan kaga yana dariya to yana hannu Mom ko Abba to wannan dariya har qyaqyatawa

20YEARS LETTER
******
wani kyakyanwan saurayi ne shida wani shima ba laifi ya hadu ba kowa bane sai sadiq da majid awajan shakatawa sosai suke hira cikin jin dadi lokacin sun gama karatunsu har sun fara aiki su na sojoji, sosai suke jin dadi wasu yan mata ne nesa dasu sai kallon su suke ba kowa ba ce sai kausar da kawayan ta suma sun zo shan iska Nana ce ta zuguro Kausar ta ce, "wow kawata kalli wayan can guys din sun hadu sosai" kamar bazata juyo ba sai kuma ta juyo tana juyowa sukayi ido hudu da sadiq takenan zuciyarta ta fara harbawa wani irin sonsa da kaunar sane suka kama zuciyarta lokaci daya haka suka bar gun tana cike da kaunarsa da begen sa shiku bai ma san tanayi ba gida suka koma suma tun daga ranar kausar ta rasa nutsawarta, duk wata hanya da tasan zata ga sadiq ita take bi ta sha wahala sosai kamin ta samo number shi tun tana kira bai dauka har ya fara dauka suna dan taba hira.



Haka rayuwa ta cigaba ta tafiya soyayya mai karfi ta shiga tsakanin kausar da sadiq har ta kai ga iyayan su sun sani, sosai iyayan sun ji dadin haka murna wajan kausar da sadiq ba'a magana musanma kausar da ita ta cusa kanta ga sadiq din.
shirye-shiryan biki ake sosai inda kowa ni gida ka leka abubuwa ake gudanarwa sosai ranar asabar aka daura auran *kausar Umar and sadiq Ibrahim* sosai kowa yayi murna ankai amarya gidan mijin ta dake sultan road gida mai kyau sosai wanda daga gidan su ba nisa zuwa gidan su sadiq.

sun raya wannan dare nasu da sunna manzon Allah (S A W) bayan komai ya wakana tayi kuka ranar har ta gaji saboda sadiq ba qaramin namiji bane, dan ya dirje ta yadda ya kamata shida kanshi ya taimaka mata tayi wanka sannan ya barta tayi na tsarki ranar ko yasha shagwaba har ya gaji sosai yake samata albarka kasancewa ta zo masa da budurcin ta har gidansa, sosai yake jin kaunarta wani irin so suke ma juna su kamar su cinye juna.

*****
_2years letter_
kausar ce asibiti ita da doctor kuka take masa sosai tana cewa, "wallahi doctor bazan iya jurewa rashin haihuwa ba saboda ko ban haihufa ba, wannan ciwon zai iya kashe ni kowani lokaci, ina son na haihu doctor bana so sadiq yasan cewa Ina da wannan ciwo"
"why kausar ya kamata ki sanar da mijin ki ko shine yaji haka zai tausaya maki, bai taba yadda ki zauna da wannan cikin saboda wannan cikin ajalin ki ne..! bawai nasan gaibu bane amma duk wani mai cutar ANEMIA bai iya daukar ciki ki duba ki gani ke kanki duk month sai an maki karin jini bale kuma yanzu har da baby a jikin ki" wani irin kuka mai ban tausayi ta saki ta ce, "gaskiya doctor bana iya zubar da cikina doctor, bana iya zubar da jinin sadiq no I cant doctor..! turo kofar da akayi ne yasa doctor saurin miqewa kausar kuma tayi sauri fara goge hawayanta da bayan hannuta tana girgizawa doctor kai alamar karya tona mata asiri washe bakin karfin hali yayi ya furta, "congratulation captain sadiq matar ka na da juna biyu "
"what..! ya zaro ido yana washe baki ya ce, "thank god finally am gonna be a farther" ya kai ma kausar hot kiss a lips dinta yana shafa cikinta murna yake sosai inda doctor ke ta binsu da kallon tausayi sosai sadiq yayima doctor tukwici saboda kyankyawan albirin daya masa.
kaitsaye gidan Mom suka wuce suna shiga da sallamar su kausar sai sunne kai take kafadar Mom sadiq ya daura kansa ya lunshe ido jawad da ke zaune da yake ya zo da iyalan shi Nigeria kasancewar shi ba kasa yake zaune ba yana zaune a London da matarsa da d'ansa jawahir wanda ke da shekara3 yana zaune saman three sitar ya ce, "wai yaushe zaka girma ne baby? Yar dariya sadiq yayi ya ce, "sai ranar da my wife ta haihu ka fara qirga month daga yau am going to be a father" wani irin dadi ne ya lullu6e Mom ita ko kausar sai sunne kai take da jin kunyar abinda sadiq keyi da tausayin kanta kuma, Bilkisu ce ta dungure masa kai ita ma lokacin Hanan na da 6years ta ce, "kai dai baka da kunya wallahi"
Mom ta ce, "ku kyale min yaro to me? dan ya fada mani?
"yauwa Mom that is why I love you" ya kaimata peck a cheeks Mom ko ta zage sai nan take da kausar ita da Bilkisu da matar jawad sosai suke gwada mata soyayya.
hakan yasa kausar ta shige toilet tayi kuka ta gaji tabbas tasan tayi dace da dangin miji burinta bai wuce ta haihu ba, tasan zasu riqe mata amanar babyta ko bayan ranta, shafa cikinta tayi tana share hawayanta da bayan hannu ta.


Sosai kausar ke samun kulawa da so da kauna wajan sadiq, inda yake gwada mata tsantsar soyayya har take jin dama karta mutu ta danwama dashi a gidan duniya, a duk lokacin data tuna ciwonta, kuka take sha sosai sannan ta share hawayan ta cikin ta har ya kai wata 5 bata samun wata matsala ga kuma sadiq da ke tatalin ta kamar akwai.


Sadiq ne tsaye gaban dressing mirror yana shiryawa cikin uniform nasa ba karamin kyau yayi ba kausar ta qaraso wajan shi tana sanye cikin night dress nata fara riga dai-dai gwiwa tana bin sadiq da kallo mai cike da tsantsar so ta ce, "habibina..!
"Na'am honey"
"uhm.! tana maganar tana gyara masa ma6alin rigarsa ta ce, "gaskiya kayi kyau sosai"
"ko.?
" eh mana" ta shagwabe fuska ta furta, "har na ji kishi Allah yasa kar yan'mata su kalle min kai" hancin ta ya ja ya ce, "honey bame kalle miki miji kinji"
"tam.! Sadiq ya kai hannu ya shafa cikin ta ya ce, "ya lafiyar baby na?
"lafiya shi lau habibi" smile ya saki mai sanyi yayi kissing goshin ta da cikin ta mika masa briefcase nashi tayi yana fita da gudu ta shige toilet ta fara aman jini-jini ta hanci ta baki, jiri take gani sosai har bata iya ganin gaban ta a dadafe ta rarafa ta hau gado tana numfashi sama-sama.


Har yayi nisa da gida ya tuna yayi mantuwa ribas ya ci ya dawo ko da yayi sallama bai ji motsin kausar ba, daki ya nufa a tunanin shi bacci ya dauke ta musanman yadda ya lura cikin mai sata bacci ne lullu6e take cikin blanket sai kyarma take ya shigo dakin har zai fita ya dawo yaye blanket din mai zai gani kausar ce a sume sai hancin ta da jini ke biyowa.
sosai hankalin sadiq ya tashi daukarta yayi kamar baby duk ya rode ya sakata cikin mota kai tsaye asibitin wajan aikin shi suka wuce wato na sojoji, yana isa nurses suka fito suka basu taimakon gaggawa.
Idan hankalin sadiq yayi dubu ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zarya yake.
Bangaran kausar kuwa doctors sun dukufa akanta domin ceto ranta, Mom sadiq ya kira yana kuka kamar qaramin yaro yana fada mata yadda akayi, Mom na jin haka ita da baba jummai suka taho asibitin sosai Mom ke kwantar masa da hankali da created, insha Allah kausar zata samu lafiya"
wajan laida biyar kausar tasha na jini biyu na sadiq biyu na jawad daya na majid sosai hankalin su ya tashi doctor ne ya fito daga dakin yana goge zufar fuskar shi da sauri suka karasa wajan doctor suka hada baki wajan furta, "ya jikin kausar?
"Alhamdulillah munshawo kanta dakyar yanzu tana samun hutu ne" sadiq ya kira da yayi zuru-zuru harda yar rama yini daya yayi ya ce, "ka same ni a office"
"to Dr yakub" cikin sauri ya bishi suna shiga yakub ya cire glass din dake manne idanusa yana kallon sadiq ya ce, "A gaskiya sadiq ka bani mamaki ya za'ayi ka yadda matar ka ta samu ciki bayan kasan tana da AMENIA why sadiq?
"what..! ya furta zunbur sadiq ya mike ya ce, "yakub bangane mai kake fadi ba Ina tunanin kunnena bai ji dai-dai ba ko?
"oh karka raina min hankali mana kana nufin baka san tana da shi ba ko me? ras qirjin sadiq ya bada wasu hawaye ne masu zafi zuka zubo masa ya ce, "why kausar me yasa zakin min haka" kuka yake sosai har saida Dr yakub ya tausaya mashi ya rugumesa yana shafa masa baya alamar lallashi a hankali yake magana cikin sarkewa harshe ya ce, "yakub I don't no kausar na da ANEMIA ban sani ba me yasa zata 6oye min why yakub she no I love her Allah nafi son ta akan baby serious yakub, please ka cire mata cikin please bana iya rayuwa bada kausar ba..! ya kara rushewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro sosai yakub ke lallashin sa har ya samu ya samu nutsuwa ya bashi fresh milk mai sanyi yasha ya rage kuna da zuciyarsa ke masa a hankali ya fita daga office din ya shige dakin da a kwantar da kausar tana kwance fuskar nan tata tayi fayau alamar ciwo ya cita sosai, kallo daya ya mata idanusa suka ciciko da kwalla jikin Mom ya fada cikin dashashiyar murya ya fara ba Mom labarin abin da ya faru, sosai Mom ta girgisa da batun sadiq har da yar kwalata sadiq ya cigaba da cewa, "me yasa kausar zata min haka mom? ya kara rushewa da wani saban kuka kamar karamin yaro..

Writing by
        Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Blood sister jeedah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
  
                           11_12
    
        Turo kofar da akayi ne yasa Sadiq  tsagaita kukan da yake, Abba ne tsaye bakin kofa cikin sasarfa sadiq ya qarasa wajan Abba,  ya qara sakin wani sabon kukan Abbane ya rugume shi alamar lallashi ya  ce,  "shhh!! Sorry son be are strong man sai ka ce ba soja ba, insha Allah she will be fine" Abba ya  juyo kan  jawad  ya ce,  "Jawad ka kaishi gida ya samu hutu kaji"
   "Daddy..!
  "Shhhh..! ya isa kaji jawad  ka kai shi gida kawai" Haka ko akayi.
       jawad ne ke driving nasu cikin mota ba wanda yayi ma wani magana, sadiq idanun shi a lumshe har suka iso gida bala mai gadi ne ya bud'e masu  gate tare da  jajanta masu, parking space yayi parking suka fito a tare.
     bedroom d'in sadiq suka shiga ya kwanta saman bed tare da lumshe idanun sa, zuciyarsa na wani irin suya musanman idan ya tuna da halin da abin kaunarsa ke ciki, Jawad ne ya katse masa tunani ta hanyar shafa sumar kansa, ahankali ya ware sexy eye's ball's d'insa ya  d'aura su  kan jawad riqe yake da glass cup da fresh milk a ciki ya ce,  "Sadiq please ka daure ka ci wani abu nasan tun breakfast d'in safe baka qara sa komai a cikin ka ba, please ka gama ka sha magani headachen nasan yana damun ka" numfashi ya ja ya cigaba  da cewa, "insha Allah wife naka zata samu sauki kaji baby" kamar ba zai sha fresh milk d'in ba, amma saboda bai ga wasa a idanu yayan nashi ba ya amsa, Sha biyu zuwa uku yayi ya aje saman stool ya qara lumshe ido maganin headache jawad ya 6alo tare da ruwa ya bashi ya sha, sannan ya lullu6esa da blanket ya fita.

      Bacci ne mai nauyi ya d'aukesa bashi ya tashi ba sai yamma liqis wanka yayi yasa Jean's n shirt bleu mai dogan hannu sannan yayi sallah la'asar, ba qaramin kyau yayi ba sai dai fuskan nan fayau saboda kukan da yaci sannan cike take da alamar damuwa, car key nashi da ke saman stool ya d'auka ya fita.
         kaitsaye asibiti ya wuce yana parking motarsa a harabar asibitin aka fara kiraye-kirayan sallah magrib Masallaci ya shiga yayi sallah zai futo kenan suka had'u

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login