Showing 69001 words to 72000 words out of 105783 words

Chapter 24 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

728

d'auke, laptop din ta dake saman bed take qoqarin sadiq ta hango kwance yana bacci, mai cike da birgewa da jan hankali murmushi ta saki tana qare ma kyakyawar face nashi kallo hannu ta kai kan screen din laptop din tana shafawa can kuma ta janye hannuta, daukar laptop din tayi ta aje saman sofa yadda zata dinga hangosa duk abinda take, toilet ta shige ta watsa ruwa tare da dauro alwala daure da towel ta fito ko da ta fito lokacin sadiq shima ya tashi dan ba alamarsa ta cikin laptop din baya saman bed, cikin sauri ta shirya tare da gabatar da sallah sket din makarantar ta ta jawo tasa tana gama sawa ta zura rigata tana 6ale ma6alin riga ta, ta hango sadiq tsaye shima yana 6ale nashi dariya suka saki a tare ta ce, "morning uncle.!
"morning too dear, kin rigani tashi na riga ki shiryawa baki da sauri" dan turo baki fatuha tayi ta ce, "dama can ka tashi idan ba" yar dariya sadiq yayi ya ce, "kwarankwatsi ban tashi ba" fashe wa da dariya fatuha tayi saboda tasan tsokanarta sadiq yake da kalamanta na da kashe laptop din yayi domin ta qarasa shirya wa.

Kusan a tare suka fito lokacin angel har ta shirya cikin uniform din ta tana dining area ita da Mom da Abba cikn nutsuwa suka qaraso, gaishe da su Mom su kayi suka amsa a tare sannan suka ja kujera suka zauna saving din su fatuha tayi sannan suka fara break cikin jin dadi bayan sun kamala peck sukayi ma Mom, Abba ne ya ce, "lallai gidan nan ana gwada min banbanci jiya ina kallo Mom dinku kukayi ma peck, ni kuma ko oho ba komai zan rama" dariya sukayi su duka tare da ba Abba hakuri kusan a tare suka fito Mom ta rako su har bakin kofa yaran sadiq sai qamewa suke, shigewa motoci sukayi Abba ya shige nashi suka bar harabar gidan.

Sosai yau sun sha karatu har da test sai da sukayi na history sosai fatuha ke maida hankalin ita da kawayan ta, Nana da Zara sune kawayan ta na makaranta kuma yan'yan masu kudi ne masu ji da wayewa da yan matanci, fatuha ko tun tana jss2 ta zana JSSCE saboda qoqarin da hazaqa yanzu haka SS2 take Hanan na SS3 Basma kuma ta gama, Nana ce ta kalle ta bayan uncle ya fita daga class ta ce, "Niko fatuha ina wannan uncle din nan naki mai kyau?" kallon ta fatuha tayi tare da aika mata harara lokaci daya ta canza fuska kamar ba ita ba ta ce, "ina ruwan ki da uncle dina?
"laaa fatuha yaushe kika zama haka? inji Nana, Zara dake gafe ta ce, "Karki ga laifin ta wallahi ai dani ce fatuha da tuni na samawa kaina mafita wallahi"
"hmmm wai me kuke nufi ban fa gane wannan hausar taku ba? fatuha ta fada yar shewa Zara da Nana sukayi lokaci daya suka ce, "wallahi rainin hankalin nan namin dadi serious, to bari kiji ki zauna nan kwado ya maki kafa, wallahi dani na samu damar ki da tuni na dama wallahi" inji Nana.
"ku dai baku da aikin yi ni ina da, uncle matsayin yayana na d'aukesa ba komai ba"
"Allahu Akbar" su Zara suka hada baki wajan fada duka fatuha ta kaima Nana da Zara da littafin dake hannu ta.

***
Basma ce zaune ita da Umma tana taya ta kwalema a d'akin ta, pictures din sadiq ne ya fado hannuta kai ta dauka ta kurawa hotan ido tana kallon tana shafawa sam ta manta da Umma na wajan ta lula duniyar tunanin sadiq.
Umma ce ta ta6a ta firgigit ta dawo daga duniyar tunani duk ta daburce tana qoqarin aje hotan, dan murmushi Umma ta saki na su na manya ta ce, "yar auta me ke damun kine kwana biyu naga duk kin rame kin zabge kamar mara lafiya" hawayan dake maqale a idanuwan tane suka zubu tare da riqe hannu umma, tac e " Umma na rasa me ke damuna tun zuwan da yaya sadiq yayi kwanaki na rasa meke damuna wallahi umma,😭 ina son yaya sadiq tun ba yanzu ba" ta ida zancan tare da rushewa da kuka ta ce, "ko kallo na bayayi..! lallashin ta Umma ta shigayi da cewa, "haba auta me abin kuka? share mata hawaye Umma tayi ta ce, "duk wata mace mai lafiya dole taso sadiq saboda ya tare duk abinda mata ke so Basma ban ga laifin ki ba, insha Allah zan taya ki da addu'a, idan sadiq alheri ne a gare ki Allah ya baki shi, idan ko haka ta faru sai nafi kowa farin ciki, kinga sai a hada da naki dana majeed tunda shima jiya yake fada min ya samu wadda yake so suna dai-dai tawa da ita" murmushi Basma ta saki tare da fita daga dakin da gudu cike da farin ciki Umma ta bita da kallo tayi murmushi irin nasu na manya.

*****
Misalin karfe 12:30pm suka tashi daga makaranta kasancewa yau friday angel na gefan ta suna jiran drive, hadadiyar motace baka ta faka gaban su fatuha kauda kai fatuha tayi kamar motar ba gaban su ta tsaya ba, saboda glass din motar tinted ne ko na ciki ba'a gani zuge glass din akayi hakan yasa angel washe baki tare da cewa "Second daddy?" majeed ne sanye cikin uniform din shi na aiki murmushi ya saki bale murfin motar angel tayi kamar tana jira ta shige gaishe shi fatuha tayi a taqaice tare da cewa, "angel fito kin san driver ne zai zo daukar mu" ta fada, murmushi majeed yayi ya ce "To ni zan d'auki kyankyawa yau na kai ta har gida dan tun dazu na kori driven, ni zan zama driver yau" dan zaro ido waje fatuha tayi ta ce "Sokake uncle ya mani fada ko?
"ah uncle ba zai maki fada ba ai yasan ni zan dauke ku, ni da shi ai duk daya ne ko baki sani ba? dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi la66an ta ta bude murfin motar ta shiga cikin nutsuwa ya ja motar, yana driven yana kallon fatuha ta cikin mirror sai da ya zo dai-dai bakin geta yayi horn bala mai gadi ya bude masa geta parking yayi su fatuha suka fito tare da masa godiya sai da suka shige cikin gida yayi ribas ya fita.

Shiga office din majeed sadiq yayi amma wayam ba majeed dan ta6e baki yayi tare da fitowa daga office din, da khaleed ya ci karo wanda shigowarsa yanzu kenan cikin fara'a sadiq ya tarbesa khaleed ya ce, "Ah wai har yanzu majeed bai dawo ba?
"oh kama san da fita kenan"
"eh munyi waya nace masa zanzo shine yace min yaje daukar baby shin daga school..!
"baby.! sadiq ya maimaita ya ce, "bansan sanda majeed zaiyi hankali ba wallahi mtww" yaja Khaleed suka wuce office din shin.

Bayan sunyi lunch fatuha ta shirya tsaf cikin lace din ta yellow anmata dinkin bubu da lace din sosai kayan sun fidota da ita abunka da fara fata, dan kwalin ta ta daurasa hawan-hawan daurin ya zauna kamar gwagwaro janbaki ta shafa maroon da yar hoda kwalliya sosai ta zauna ta tsantsara veil din ta ta dauk'o white ta yafa masha Allah fatuha ba qaramin kyau ta zuba ba,

Tana fitowa parlour ta samu Mom da majeed sunata zuba hira yana sanye da blue shada tasha aiki, cikin zazakar muryata fatuha ta ce "Mom zan je gidan mami"
"to, shikenan ki gaishe min da su"
"zasu ji, "majeed ne yayi karaf ya ce, " Tunda tafiya nima zanyi bari na aje ki a can"
"to! fatuha tace tare da yin gaba majeed yabi bayan ta shida kansa ya 6ale mata murfin mota ta zauna sannan ya bude ma kansa ya shiga,

Ko 20 minutes basu dauka ba suka Isa gidan Aunty bilki, inda majeed keta janta da surutu har ta dan saki jiki da shi yana yin horn mai gadi ya bude ya shigo da motarsa yayi parking, qoqarin fita daga motar take majeed ya ce "Baki ji ba,.! waigowa tayi sannan ya ce, "karfe nawa zaki koma gida?
"da yama" ta fada a taqaice.
"toh! shikenan zanzo daukar ki" Godiya ta masa tare da shigewa cikin gidan.

Da gudu Hanan ta rugo ta rungume ta tana cewa, "kai amma naji dad'i wallahi kin cika alqawari" gaishe da Mami tayi dake zaune parlour tana kallo sannan Hanan ta ja ta bedroom suka baje suna ta zuba hira cikin jin dadi kai ka ce yan'uwane yadda suke nuna ma juna so sai kusan yama likis majeed ya zo gidan Aunty bilki, inda ta dingq zuba masa shaqiyanci shida sadiq sun raina ta basu san zuwa gidan ta sai da dalili shi dai sosa keya kawai yake sannan suka bar gidan suka nufo gidan.

motar sadiq ce ta kunno kai cikin unguwarsu driver na ja, shi kuma yana baya, motar majeed ta wuce su gyaran murya sadiq yayi ya ce, "Wancan motar kamar ta majeed?
"yallabai ita ce ai dazu dana zo daukar fatuha, Hajiya tace min ai majeed ya kaita to qila sun dawo ne? Ras-ras kirjin sadiq ya bada wani qulolin bakin ciki ya tsayawa sadiq har yana jin ya qasa hadiye miyau.
kusan a tare suka shigo gidan sai da fatuha ta fito majeed shima ya fito murmushi fatuha ta saki tana ma majeed godiya, qoqarin bude kofar motar driver ya ke sadiq yayi magana cikin daka tsawa "karka bude.! ya fadi, shi kan shi driver sakatarere yayi da mamakin canji sadiq lokaci d'aya zaunawa sukayi a mota sadiq na hango fatuha da majeed, har tayi gaba ta dawo ta ce, "oh na manta wayana a mota" smile majeed yayi tare da bude motar ya curo wayar ya bata, tare da cewa, "gaskiya yadda na dako wayar nan ya kamata ki bani number ki" dan murmushi tayi ta ce, "uncle number ta?
"eh mana ko baza'a bani ba?
"zan baka mana" curo wayarsa yayi dake gaban aljihu ya bama fatuha ta rubuta maaa number ta sannan ya shige mota ya bar harabar gidan.

Yana fita sadiq ya bude murfin motarsa cikin zafi rai idanusa rufe da wani irin kishi mai tsanani wanda bai san yana da shi ba sai yau, shigar fatuha bedroom ke da wuya taji an banko kofar d'akinta cikin zafin rai waigowa tayi a dan tsorace tana kallon sadiq take bakin kofa idanusa sun rine da ja, gaban fatu ne ya yanke ya fadi da ganin yanayin sadiq ba tayi aune ba ya fisgota ya fizge wayar da dake hannu ta yayi wurgi da ita ta bigi bango ta dawo kasa a tarwatse ware ido fatuha tayi jikinta na rawa rike da bakin ta ban da rawa ba abinda jikinta yake tana ja da baya cike da tsoran yanayin sadiq tare da sakin kuka, manna ta sadiq yayi da bango ya koma mata kamar zaki idanuwashi sunyi jawur kamar garwashi cikin kakausar murya ya ce, "Waya baki izini fita gidan nan bada driver ba?" kuka fatuha ta kuma saki ko bakin magana ta rasa saboda tsawar da sadiq ya daka mata ganin bata da niyar bashi amsa yasa sadiq sakinta tare nufar kofar fita ya banka ta da karfi ya fita hata Mom dake part din ta sai da taji bugun kofar da sadiq yayi, zame wa fatuha tayi awurin tare da sakin kuka, koda sadiq ya shiga part nashi cili yayi da briefcase din shi saman three sitar ya zauna tare da lumshe ido yana maida numfashi sama-sama, ware idanuwan shi yayi saboda d'aya rintse fatuha da majeed ya yake gani shafa ganshin kansa yayi ya ce, "noooooo.!! Cikin d'aga murya........

Vote

Comment
Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.co m/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_ speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

                     75_76

      Sai da fatuha taci kuka ta gaji sannan taja jiki ta hau saman bed, tarasa dalilin da yasa mai kyau yake yin irin haka, kuka ta kuma rushewa da shi data tuna a irin yanayin data gansa, haka ta dinga raira kuka kiran sallah magrib yasata tashi jiki ba qwari, ta dauro alwala tare da gabatar da sallah zaune tayi bisa daduma abin tausayi ganin tunanin bai fishe ta yasa ta jawo AlQur'ani tana karantawa har aka kira sallah isha.
          bayan ta idar da sallah ta ja jiki ta koma bed ta cigaba da raira kukanta abin tausayi turo kofar da akayi ne yasata miqewa tana kallon kofar, angel ce tsaye bakin kofar qarasowa tayi d'akin tare da hawa saman bed din ta ce ,"Aunty waya saki kuka? murmushi fatuha ta qaqaro wanda iya karshi la66an ta ta ce "Ido nane ke ciwo"
     "sorry Aunty, ki fito parlour kuyi dinner naji shuru ne baki fito ba ke da daddy, shiyasa na biyo ki daddy dai yace ya koshi, ko kema kin koshi ne? ta fadi zancan tana kallon fatuha dan smile tayi ta ce, "ban qoshi ba ina nan zuwa naci komin dare" fita jidda tayi daga daki'n fatuha ta cigaba da raira kukanta har sai da kanta ya fara ciwo, ganin bame lallashin ta yasa tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya bacci barawo ya sace ta.

     Bangaran sadiq  ban da juyi saman bed ba abinda yake yana tunanin  abinda  idonsa  ya  gane  masa, dakyar ya samu ya rintsa.

          ASUBA TA GARI

  Ko da fatuha ta tashi jiki ba qwari tayi sallah sannan ta qara komawa ta kwanta saboda kanta dake  mata ciwo, kuma taci sa'a yau weekend ba ita ta tashi ba sai karfe 11:30pm ware ido tayi tare da kallon agogan dake makale a bangon d'aki, cikin sauri ta mike ta shiga toilet ta watsa ruwa.
         ko da ta fito mai kawai ta murza sai after dress data zura parlour ta fito ba kowa, dining area ta wuce ta bud'e kulolin dake jere wanjan, chpis ne da farfesun yan'ciki zubawa tayi a plate ta had'a ruwan tea sannan ta zauna, cike  da  kewar sadiq loma biyu zuwa uku tayi ta ture plate din dan kwata-kwata bata jin dad'in abincin.
       Babban abinda ke daure mata kai ta rasa laifin da tayi, yanke shawarar zuwa bama sadiq hakuri tayi, duk da bata san laifin data masa ba dan bata iya jurewa wannan horan na  rashin  ganin  sa  da  saurara dad'ad'an kalamansa  masu  sa  nutsuwa  da  kwanciyar  hankali,  tashi tayi tare da kwashe kwanika ta kai kitchen sai da suka dan ta6a hira da su baba jummai sannan ta fito.

        Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta murda handle din kofar tare da shigowa cikin sallama zaune sadiq yake saman two sitar da laptop gabansa kallo d'aya zaka masa kasan baya  cikin  dad'in rai zaka  gane  akwai  abin da ke  damunsa fuskar nan  nasa babu annuri ya  koma  captain sadiq  na  da  sak bakin  fatu  na  rawa  ta  ce, "Uncle..!  dogo kai yayi ya kalli fatuha tare da lumshe ido ya kauda kai ya ce, "Just leave me alone" sadiq ya fada a tsiwace tare da tatara takadunsa dake gabansa da laptop dinsa ya shige bedroom tare da buga kofar da karfi, har  saida  fatu  ta  razana  da  yarda  ya  buga  kofar kafarta  kasa  daukar  gangar jikinta  yayi  saboda  tashin  hankali  na sauyawar  sadiq  lokaci  daya kuka fatuha ta saki tare da fita daga part din da gudu jin ta fita yasa sadiq jingina da kofar bedroom ya lumshe ido har  cikin  ransa  yake jin  sautin  kukanta, amma  kishi  ya  hana sa  saurara mata.

      Da gudu ta wuce Mom a parlour ta shige daki saman bed ta fada tare da sakin kuka maicinrai har  da  shesheqa, kuka taci ta gaji.
         Mom dake parlour bin fatuha tayi da kallo tana mamakin mai ya hada su da  sadiq  haka, koma dai menene ai sun saba zasu shirya ne amma abin mamaki basa kai haka, kauda zancan Mom tayi tare da cigaba da kallon ta.
          Duk yinin yau babu wanda yaci abinci cikin su, ban da kuka ba abinda fatu take, shi ko sadiq sai bak'in rai dayake fama da shi.

    Iskace mai sanyi da ke ta kad'awa da alama ruwa za'ayi saboda damuna data fara shigowa, qara cida ce kawai ke tashi bakin window sadiq ya tsaya a hankali ruwa ke saukowa kallon ruwan yake yanda yake saukowa da karfi, a wannan karan lumshe ido yayi tare da ware su, ya koma saman bed ya kwanta jikinsa  ba  dadi.
       bangaran fatuha tunda aka fara ruwa ta lullu6e cikin blanket jikinta  yayi  rau  da  fever.

      Gabaki daya yini yau ba wanda yayi ma wani magana, cikin fatuha da sadiq, horan d'aki sukayi wa kansu ba tare da sun nemi abin sama bakin sallatin su ba, ba wai  kuma  basu  jin  yunwar  bane  a'a  abinci  ne  ba  zai  samu  mahali  ba, har bacci ya kwashe su.

           Washe  gari
      Shiryawa yake cikin manyan kayansa kasancewar yau zasu je family meeting, fatuha ce ta fado masa a rai kawar da tunanin yayi dan har yanzu bai huce ba ko yana hucewa sai ya dawo daga meeting.
                cikin Isa yake saukowa daga upstairs, lokacin har su Mom sun shirya suna parlour zaune suna jiran fitowar sadiq da fatuha ganin sadiq ya sako yasa Mom cewa, "angel kira Aunty mu wuce.!  ko da angel ta shiga d'akin kwance ta samu fatuha qudindine cikin blanket, fitowa tayi da sauri daga bedroom din ta ce, "Grandma Aunty bacci take"
      "toh fa! amma ai fatuha bata kai haka tana bacci" shiga d'akin Mom tayi tare da qarasawa wajan bed din fatuha ta ce a hankali, a hankali fatuha ware idanuwan ta da suka yi nauyi saboda tsabar kuka, kallonta Mom tayi ta ce "Mike damun kin fatuha? dafe kai tayi ta  ce,  "Mom kai nane ke ciwo"
    "eyya sorry dama meeting zamu tunda baki jin dad'i ki zauna kawai a gida" to kawai tace tare da shigewa blanket,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login