Showing 90001 words to 93000 words out of 105783 words
daki aka bashi tare da sa masa life sport machine sai qarin jini da ake masa, a hankali Dr yakub ya qaraso gaban gadon yayi kneeldown, hawaye ne ke masa zarya a hankali ya kai hannusa ya shafa sumar kan Sadiq ya ce, "Friend why me yasa kake bama kanka punishment haka? why sadiq.! ya ida zancan hawaye masu zafi na gangaro masa wayara ce dake ringing ciki aljihu ya curo tare da kallon suna dake maqale a screen din majeed, kashe wayar yayi gabaki daya tare da jawo wayar sadiq ya kashe sannan ya dau kayan sadiq da aka cire masa yaba daya daga cikin ma'aikatan asubitin su wanke.
Bayan ankamala dinner kowa ya dau hanyar zuwa masaukinsa majeed sai kiran layin sadiq yake, baya shiga dana Dr yakub, yana mamakin abun ya faru yau ya rasa mai ke damun sadiq hakura yayi da kiran tare da maida wayar aljihu.
Bangaran Basma ko kuka take sosai tare da taqaicin amincewa da auran sadiq, Khaleed sai bata hakuri yake tare da ganin rashin kyautawar sadiq ya rasa dalilin da zai mata irin wannan cin fuskar bayan tana qanwarsa kuma matar da zai aura, shi a ganinsa duk wanda ya samu Basma a matsayin mata ya mure, ya rasa me yasa sadiq ke nuna rashin ko in kulla a kanta, kuma majeed na gani ko ba komai yasan dole zai ji haushin sadiq da wannan tunanin suka qaraso gida ko Godiya bata masa ba ta shige gida da sauri tare da tsananta kukanta.
Motar su fatuha na fakawa majeed ya fara jero mata kalaman soyayya tare da jan ta jikinsa, ganin zai wuce gona da iri yasa fatuha sakin kuka, lallashin ta majeed ya shiga dan kukan fatu na d'aga masa hankali yayi mata peck, ko saurara shi ba tayi ba ta bale murfin motar ta fita da sauri.
Bangaran sadiq ko bashi ya tashi ba sai wajan 2:00am na dare a hankali yake ware sexy eye's ball's dinsa da wani irin ishin ruwa ya tashi, Dr yakub da ko rintsawa baiyi ba ya miqe da sauri ya qaraso wajan shi cikin cool voice sadiq ya ce, "Ruwa..! da sauri Dr yakub ya bude fridge ya dauko rubar ruwa ya bashi ko da ya sha ruwan miqewa yayi yana qoqarin cire jini da ake qara masa riqe hannusa Dr yakub yayi ya ce, "Captain me kake shirin aikatawa? ya fada bakin shi na rawa kallonsa Sadiq yayi ya ce, "so nake na tafi gida bana so majeed ya gane bani da lafiya, na san yanzu haka Basma name fushi dani, na ruguza mata farin cikinta saboda rashin hakuri na" ya ida zancan yana cire qarin jinin wasu hawaye ne masu zafi suka zubu ma Dr yakub ya ce, "Sadiq wai me yasa kake so ka raya rayuwar wani ka bata taka? why sadiq? Dr yakub ya fada yana jijiga sadiq kuka sadiq ya saki tare da cewa "ka dai kiran majeed da wani d'an uwa nane kuma na jini, bazan ta6a bari majeed ya mutu saboda bakin ciki na ba, nafi son farin cikin majeed a kan na kowa a duniya, bani da d'an uwa sama da majeed, kasan ko ya majeed ya ke waje na yana so na yana son farin cikina, tunda da nake da majeed bai ta6a nuna min abinda yake so ba kamar fatu ba, ina iya ce ma kan fatu majeed ya san me so saboda haka ban taba bari saboda ni ya rasa rayuwarsa..! sadiq ya ida zancan yana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare a hankali ya ida cire kayan asibiti dake jikinsa yasa kayansa wayarsa ya dauka tare da kunna ta Dr yakub mutuwar tsaye yayi yana bin sadiq da kallo cikin bacin rai ya ce, "kai taka rayuwar yaya za'ayi da ita, kai taka zuciyar ayi yaya da ita? Sadiq ka fahimce ni kafi majeed buqatar fatu, kafi majeed son ta, ka duba halin da kake jefa kanka, ka falasa abinda ke ranka tun kafin gobe fatu ta zama malakin majeed..! tabbas yanzu yasan me sadiq yake nufi so yake ya rasa rayuwarsa ya zamar masa dole ya kawo karshan abunan ko saurarashi sadiq bai yi ba saima car key daya dauka tare da fita yana ingisawa.....
Vote
Comment
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R
*Email* [email protected]
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
91_92
A hankali yayi parking motarsa ya mata key, harabar gidan tsit ba motsin kowa sai motoci birjik kamar wajan saida mota, a hankali ya cigaba da takawa duk da yana jin jikinsa kuka-kuka ya fara ji sama-sama hakan ne ya sasa tsayawa tare da kallon agogo hannusa mamaki ne ya lullu6e sadiq a hankali ya fara bin inda kukan ke fita, fatuha ce zaune sama resting chair tana raira kuka, qarasowa yayi gabanta firgigit ta dago a tsorace ganin sadiq ne yasa fatu mikewa tsaye ta ruga da gudu ta fada jikinsa ta qanqamesa tare da sakin wani irin kukan, rungume ta sosai sadiq yayi yana jin kukanta har cikin ransa tamkar shima ya fashe da kukan ko ya samu sauki cikin zuciyarsa daurewa kawai yake, d'ago fatu yayi suna kallon juna jawo hannuta yayi suka zauna a hankali yake shafa bayanta ba wanda yace ma dan uwansa ko da kalma daya, sun dau kusan 5 minutes a haka fatuha ce ta dako tana kallon sadiq kamar yarda yake kallonta cikin sanyin murya ta ce "Uncle.! ya naji jikin ka da zafi? dan smile sadiq yayi ya ce "Nima haka naji jikin nawa" kallonsa take cike da kallon tuhuma da tanbayoyi fal a zuciyarta ganin yarda ya rame ya zabge amma sai ta kasa magana komawa tayi saman fafadan qirjinsa tayi lamo tana sauke numfashi a hankali, kunsan a haka suka zauna har bacci ya dauke fatuha idanuwan sadiq biyu yana kallon fatuha har sai da ya fara jin kiran sallah asuba sannan ya tashe ta ya ce, "Dear tashi asuba tayi?" qarayin lamo fatu tayi jikin sadiq ta qanqamesa shafa gashin kanta yayi a hankali ya furta, "Fatuha..! a hankali ta ware eye's ball's din ta, ta ce, "Na'am.!
"tashi mu shiga gida asuba tayi" jiki ba qwari ta tashi har tayi gaba ta tsaya chak idanuta taf da kwalla da sauri ta waigo kusan lokaci daya suka waigo da sadiq suna kallon juna cikin murya mai matukar taushi fatu ta ce, "Yau ne zan rasa farin ciki na.! yaune mafarki na zai rushe, ina ma ace dogon bacci nake na farka ahalin yanzu" wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata ta ce, "Yanzu duk wata rayuwa da mukayi zata zama tarihi mai kyau? Numfasawa tayi saboda muryarta dake sarkewa ta furta, "ina ma fatan alheri Allah ya baku zaman lafiya da Basma.! tana ida zancan ta fashe da kuka mai ban tausayi ta juwa sadiq baya rungume ta sadiq yayi ta baya tamkar karamin yaro hawaye na masa anbaliya cikin sarkewar harshe sadiq ya ce "Fatuha ki kasance mai biyaya a daki'n mijin ki kin ji, majeed na sonki please karki bari majeed yayi kuka dake dai-dai da rana daya, duk wanda yayi hakuri a rayuwa zai ga ribar haka..! ya ida zancan yana share hawayansa ya waigo da fatu suna facing juna yana sakar ma fatuha lallausan murmushi dayafi kuka ciwo, suna kallon juna da sauri fatu ta shige cikin gida.
Duk inda ka wuce hada-hada ake da shagali abinci ke ta yawo da kayan motsa baki, kaji ko har ture su ake da naman rago yan'matan amarya na zaune a daki, shirya fatuha ake saboda wudil za'a wuce da ita sai an daura aure aje dauko ta, tunda ake mata make up take kallon agogo tana irga mintinan da suka rage ta zama malakin majeed, hawaye ne taf a idanuwanta bayan angama make up din ta zura kayan ta atamfa mai ratsin green, pink, brown masha Allah kayan sun mata kyau tasha danqareriyar sarqa ta gold da yan hannu sai sheqi take, Aunty bilki ce ta leqo ta ce, "Fatuha ku fito ga motocin da zasu kai mu wudil?" gaban tane ya yanke ya fadi dan har wani jiri take gani a haka su fatsima suka sata tsakiya aka lullu6eta aka kaita wajan su Mom sukayi sallama, anata guda har suka fito harabar gida, mota suka shige driver ya ja suka har ba kan titi.
Wanka angwayan kawai suke suna shiryawa Khaleed ne ya kalli sadiq ya aika masa harara tare da cewa, "Wai ina kaje jiya? bala masa harara sadiq yayi ya ce, "Ina ruwan ka da inda naje? ka fiye sa ido, irin kune ana ruwa kuna irgawa" dariya majeed yayi ya ce, "Kai dai tashi kayi wanka kaji baby ko ni ban tanbaye ka ba sai shi, ga kayan ka can tun dazu na aje ma ina so yau ka kasance cikin farin ciki kamar kowani ango.! majeed ya ida zancan yana zura kayansa a hankali sadiq ya miqe ya shiga toilet majeed ya bishi da kallo tare da ida shiryawa, tunda sadiq ya shiga toilet yake kuka kamar qaramin yaro sai da yayi son ransa sannan yayi wanka ya fito.
ko daya fito Dr yakub ne kadai daki'n kallosa sadiq yayi tare da kauda kai ya cigaba goge jikinsa da qaramin towel, sai da ya gama shafe jikinsa da lotion mai kamshi da sanyi dadi sannan Dr yakub ya balo magani ya miqawa sadiq dan bata fuska sadiq yayi yace "Wannan fa? daure fuska Dr yakub yayi ya ce, "Magani mana" bai ida rufe bakinsa ba aka turo kofa aka shigo, murmushi sadiq ya saki ganin ya jawad qarasawa yayi ya rungume jawad zame jikisa yayi tare da bata fuska ya ce, "Sai yauma zaka zo? smile jawad yayi yana bin sadiq da kallo yarda ya zabge ya rame ya ce "Sorry baby tun jiya na zo kuma na zo nemanka aka ce baka nan, ya naga ka wani rame ka zabge kamar ana dibar ka ana miya ko duk hidimarce"dan lagwabe kai yayi yana murmushi ya furta, "Toh shikenan, bayan makara harda sheri, ina su Aunty shukura?
"tana wajan su Mom"
"ok.! Dakakiyar fara shada ya jawo white getzner tasha aiki ta gaji malin-malin su jawad ne suka taimaka masa ya shirya tuni ya fito yayi kyau masha Allah duk da ya rame idanusa sunyi ciki, bayan sun gama shiryawa suka fita
Zaunawa sadiq yayi tare da kallon agogo dake manne a bangon daki, karfe 1:30pm saura minti talatin a daura auran su, haka ya dinga dane zuciyarsa yana bata hakuri.
Suna isa wudil gida ya dau gud'a baba jummai ta fito da sauri tana cewa "Ladingo amaryar fa ta iso" inna washe da baki ta bude masauki da su fatuha zasu sauka kusan tare suka shigo, Aunty bilki na riqe da ita masauki suka sauka nan aka fara jera masu kayan motsa baki, kama daga waina alkubus sinasir tuwan shinkafa da lafiyayin kaji da lemuka, yan'matan amaryar ko alwala suka fara daurawa suna sallah kasancewa azahar tayi haka itama fatuha ta gabatar da sallah sannan suka zauna aka fara gudanar da biki.
gwaggo ce ta aiko a kira fatsima tashi tayi ta fita har Nana zata bita sai kuma ta dawo ta zauna, ko da fatsima ta isa gidan su shima cike yake da baqi, mamaki ne ya lullu6e fatsima babban abinda yafi daura mata kai har da dangin babanta, to ko suma bikin fatuha suka zo? watsar da zancan tayi tare da shigewa daki inda gwaggo take washe da baki gwaggo ta tarbi fatsima ta fara mata magana. (duk yarda naso naji me ake cewa na kasa ji, hakan yasa ni da Aunty Rahenat muka bar gun jiki a sabule lol.)
Duk inda ka waiga a cikin masallaci Sheikh Isyaka Rabi'u mosque ya cika da manyan mutune yan daurin auren, sadiq ne cikin din bin jama'a, a nata masa Allah ya sanya alheri duk wannan abu Dr yakub na lura da yanayin shi majeed ma sai murmushi yake saki daka ganshi kasan yana cikin farin ciki, haka shima Khaleed dan yasha kyau har ya gaji tamkar ango, gyara lasfika da kayine yasa gaban sadiq ya yanke ya fadi, kirjinsa ya bada dam zuciyarsa ta tsinke bugun zuciyarsa ya qaru rawa jikinsa ya dauka gudun jinin jikinsa ya qaru take wata irin zufa ta fara karyo masa bugun zuciyarsa na harbawa fat-fat dam-dam tamkar ana lugude cikin zuciyarsa, tabbas yasan ana daurawa ya zama gawa dishi-dishi ya fara gani yana ganin jiri maganar mutane na lunkuwa cikin dodan kunnasa da kwakwalwarsa, a hankali ya fara kutsawa cikin taron jama'a yana tafiya, yana tari mai dauke da gudan ji tamkar kaki zufa ta jika shi sharkaf a hankali yake takawa dan yanzu ya fara yin nisa da masallacin.
Cikin masallaci ko MALAM JAURO YA BADA DIYARSA KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI GA DAN ALHAJI IBRAHIM WATO SADIQ IBRAHIM, MALAM ALIYU YA MIQA DIYARSA KAN NAIRA DUBU DARI WATO FATSIMA ALIYU GA DAN ALHAJI KHABIR WATO ABDULMAJEED KHABIR, TARE DIYARSA BASMA YA MIQA TA GA DAN ALHAJI SANI WATO KHALEED KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI kowa na masallaci kallon-kallo aka koma mamaki ne ya lullu6e kowa.
sadiq wanda fitowarsa kenan majeed ya biyosa ya kwalla masa kira da cewa "Baby..! waigowa yayi idanusa jawur ya galabaita sosai ya fita hayacinsa yana sauke numfashi a hankali tafe da zuciyarsa hawayan wahala na bin kumatunsa ya jike sharkaf da zufa zaro ido majeed yayi da karfi ya murfa, "sadiq..! dim sadiq ya durkushe a kasa duniyar na juya masa yana sauke numfashin wahala dakyar-dakyar ya sulale baya numfashi, da gudu majeed ya qaraso tare da sakin kuka yana cewa "No..! no..! Baby karka min haka ka tashi ka ji baby.! Majeed na maganar yana dan dukan fuskar sadiq da ko motsi bayayi cikin matsanan cin kuka ya ce, " in dai fatu ce na bar maka sadiq bana son ta Allah, duk laifi nane na kashe baby da kai na tashi ka ji baby kasan bama haka sadiqqq..! majeed ya koma tamkar zarare yana magana hawaye na masa zarya Dr yakub da kusan tare suka iso wurin daskarewa yayi tsaye ganin halin da sadiq yake cikin jikinsa rawa ya dauka kaf-kaf dan baya tunanin akwai sauran wani abu rai jikin sadiq su Baba da Abba dake cikin masallaci da alhaji babba jin yarda majeed yake kururuwar kiran sadiq suka fito da gudu liman ya rufa masu baya da yan daurin aure.
Dakyar Dr yakub ya samu damar bud'e baki yana tsiyayar hawaye ya ce "Ba kuka zamuyi ba, muyi sauri mu kai shi asibiti" jikin majeed na rawa ya dauki sadiq chak ya bud'e murfin mota yana kuka ganin ba zai iya tuqin ba yasa doctor yakub ya amshi car key din suka bar harabar masallaci da gudu su Abba suka rufa masu baya.
kuka majeed yake yana cewa "Ban taba tunanin abin ya kai haka ba? am so sorry sadiq ka yafemin, duk nine sila" sanbatu yake sosai a haka suka iso asibitin sai da aka wuce dashi emergency sannan majeed ya zame jikin bango tare da sakin kuka, wayarsa ya curo cikin aljihu ya danna number Umma bugu daya zuwa biyu ta dauka kuka majeed ya saki yana cewa "Umma saboda ni ina ji ina gani baby zai rasa ransa? Ya fadi hakan tare da sakin kuka ita kanta Umma kuka take dan labarin tuni ya cin masu ta tausayawa sadiq.
Kafin ka ce me, asibitin ya cika da yan'uwa, majeed na ganin Abba ya mike da sasarfa ya qarasa garesa ya fada jikinsa yana kuka kamar qaramin yaro ya ce, "Shikenan Abba bakin ciki na zai kashe baby, bazan ta6a yafewa kai na ba har sai sadiq ya tashi lafiya Abba ka ce su ceto rayuwar baby duk nine sila komai, na tafka babban kuskure nayi anfani da son da baby ke min na cutar da shi..! a hankali Abba ke shafa bayan shi tare da zaunar da shi d'aya d'aga ciki'n kujerin dake gurin, ajiyar zuciya kawai majeed ke saki cikin sanyin murya Abba ya ce, "Ba laifin ka bane majeed ka ji.! har da laifin sadiq da yayi nauyin baki ya kasa fad'a, da kansa yayi wasa da damar daya samu, hasali yarinyar nan kullun suna tare gida daya kusan komai nasa ita ce amma yayi zurfin ciki da nauyin baki? ko yanzu da kukayi magana aka sauya daurin auran? indai fatuha tace bata son sa dole ya sake ta" kuka majeed ya saki tare da cewa, "Abba da kunne na naji irin son da suke ma juna su, kamar yarda basu rintsa ba jiya, nima ban rintsa ba ina jin irin kalaman da suke fadawa juna, kuma dama na dade ina zargin akwai so tsakanin su amma baby yaki furtawa, tun ranar da aka sa bikin mu, sannan Dr yakub ya karamin bayani daran jiya, Abba dan Allah a taimaki rayuwar baby? ya ida zancan yana qara sakin kuka, haka abba ya dinga lallashinsa har yayi shuru, Ammi ko sai kuka take tana share majina saboda tausayin sadiq,