Showing 45001 words to 48000 words out of 105783 words

Chapter 16 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

710

ta nufa tare da haye masa cinya tana masa surutu ta ce, "daddy.!
"yes angel.!
"daddy please muje shan ice cream please" ta fadi tana lagwabe kai ja mata hanci sadiq yayi ya ce "Wannan bakin naki kullun san zaqi yake" dariya tayi mai nuni tana cikin farinciki, ture plate din gaban shi yayi tare da aje jidda qasa qafa ta shiga bubuga masa ita aladule sai sun je shan ice cream yau yace mata "Ok Angel is ok daina kukan kije Aunty ta shirya ki ko" sannan ya haura sama yana last stairs jidda ta ce, "amma har da Aunty zamu tafi dan kar dodo ya ji mata ciwo" toh yace tare da bude kofar part din shi.

Shirya jidda tayi tsaf amma ita ta rasa kayan da zatasa, duk gwon din data janyo sai ta maida jidda rugawa ta yi parlour zaune ta sami sadiq cikin shirin shi na qananan kaya yasa red riga mai ratsin black mai dogwon hannu shirt sai wando black da takalmi yasha kyau har ya gaji sajan shi ya kwanta luf sai sheki yake sumar kansa tasha gyara jidda ta fada jikinsa ta ce, "daddy..! a dan shagwabe sadiq ya juyo alamar gajiya ya ce, "menene angel? lagwabe kai tayi ta ce, "daddy zo ka za6a ma Aunty dress ta rasa wanda zatasa" dan guntun tsaki sadiq ya ja ya ce "Angel me yasa kika fiye rigima?" um bata fuska tayi tana shirin yin kuka tana qoqarin sauka daga jikin sadiq hakan yasa sadiq tashi ba dan ya so ba bedroom din fatuha ya shiga tsaye ya ganta gaban drawer ta riqe qugu ga kaya baje a saman bed bakin kofa ya tsaya yana qarewa bayan ta kallo juyowa fatuha ta yi jin kamar ana binta da kallo ta bayanta su kayi 4 eye's da sadiq dake binda da sexy eyes ball d'insa kauda kai tayi ta cigaba da abinda take a hankali ya qaraso wata gwon ya gani kawai ya jawo ba wai da ya lura da ita ba miqa mata yayi ya ce, "kisa wannan mu tafi" sannan yasa kai ya fice cikin 5 minute fatuha ta shirya cikin red gwon mai stones sai black veil tasa tare da murza hoda ta shafa lipstick wani irin kyau fatuha tayi komai na shape din ta ya bayana duk da ba wasu shekaru gare ta ba amma ita kanta tana mamakin girman jikinta kallo daya zaka mata kasan ta hadu tayi tamkar ba yar aiki ba takalmi tasa tare da feshe jikin ta da turare masu kamshi sannan ta yafa veil din ta, a hankali ta bude handle din kofar bedroom din parlour ta fito sadiq dake zaune saman two sitar ya lumshe ido, jidda na zaune gefe shi kamshin turaren fatuha ne yasa sa ware sexy eye's ball din shi ya sauke su kanta wani irin kyau ta masa na ban mamaki sosai ya zage yana binda da idanusa ta6e baki yayi yace ashe wannan yarinyar nada kyau duk yana wannan zancan ne a zuci miqewa yayi tare da daukar car key suka fita, gaba jidda ta shiga fatuha na baya jidda sai zuba mata surutu take.

Sun sha yawo kamar me ice cream ko har sai da suka ture, fatuha ko baki har kunne dan dadi duk inda suka wuce sai an kalle su saboda sun sha kyau sun gaji munjibir park sadiq ya kai su zama yayi a resting chair yana kallon su, su fatuha wasa ko ba wanda basuyi ba, basu suka bar munjibir park ba sai yamma likis a gajiye suka dawo gida, fatuha ko dadi fal a zuciyar ta jidda ko saboda tsabar gajiya tayi bacci cikin mota.
hancin motarsa yasa cikin gida bayan mai gadi ya wangale get parking space yayi parking bala mai gadi sai washe hakkra yake daga masa hannu sadiq yayi tare da dai-daita parking din motar sannan ya kashe motar, kamar jira fatu take ta fito murfin motar gaba ta bude tana qoqarin d'aukar jidda shima sadiq ya turo kai da hannu yana qoqarin daukar jidda ji kake gwab sun qume kai "wash..! sadiq yace fatuha ma haka yadda sadiq yayi da fuska shi yaba fatuha dariya sai kace baby boy, dariya ta saki har ana ganin fararan haqoranta sosai take dariyar mai cike da birgewa, dariya da fatuha take sai ta qara mata kyau hakan yasa sadiq mutuwar tsaye yana kallon fatu yana qara ganin kyanta 6oyaye na bayana na ban mamaki, kallo da yake mata ne yasa ta tsagaita dariyar tare da daga masa gira hakan maido da sadiq saiti harara ya aika mata ya wani had'e rai ya ce, idan kin gama dariyar ki dauko ta mu shiga gida" dariyar da yake shirin zo mata ta guntse tare da daukar jidda.

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Salma mas'ud nadabo

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄

★we are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=,52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSFULANIWRITERSFORUM.com


         
                53_54

          Sadiq na gaba tana biye dashi a baya, bakin bedroom din ta taci birki tana qoqarin bude kofar sadiq  ya juyo fuskarsa ba yabo ba falasa ya ce, "ina kuma zaki da ita bayan tayi bacci?
     "uhm dama wanka zan mata" shafa sumar jidda yayi tare da cewa, "Ki samata night dress kawai saboda tayi nisan bacci" Allah ya taimake ta jidda ta ta6a fadin Kalmar shiyasa ta gane mai yake nufi, haurawa sama yayi ita kuma ta shige daki tare da kunna haskyan dakin shinfide jidda tayi sannan ta soma rage kaya jikinta, sai da ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito daure da qaramin towel cikin nutsuwa ta shafe jikin ta da mai tare da zura night dress din ta riga ce pink mai zanan cartons jikin rigar, rigar dai-dai gwiwa ta tsaya sai dan siririn hannun kamar na vest gashin ta ta sharce ya baje a gadon bayan ta, bayan ta gama shirya kanta ta shirya jidda cikin kayan bacci, sannan ta dauke ta a hankali take taka upstairs din saboda yau jidda ta qara nauyi cikin nutsuwa ta murda handle din kofar part din sadiq, parlour ba kowa sai sanyi AC dake tashi da kamshi direct kofar bedroom ta bude tsaye ta hango sadiq gaban dressing mirror yana goge sumar shi da qaramin towel sanye yake da bathrobe white hakan yasa ana ganin lallausan gashinshi na qafa kauda kai fatuha tayi, tare da yin sallama juyowa yayi ya qare mata kallo, mamaki gashin fatuha ke ba shi gashin har yaso ya mata yawa juyowa yayi ya cigaba da abin da yake shinfide jidda tayi tana qoqarin fita, lumshe ido sadiq yayi tare da ware su ya ce, "Fatuha..! juyowa tayi tana kallon shi can sai tayi qasa da eye's ball's din ta, ki hada min coffee toh tace tare da fita downstairs ta dawo tare da shiga kitchen ta hada masa coffee ta dawo, ko da ta dawo yana zaune a parlour yana kallon news aje masa tayi saman stool tare da ficewa, cikin nutsuwa ya shiga shan coffee yana kallon news amma sai dai ku san kallon news din kawai yake ba wai dan yana fahimta ba, kashe kayan kallOn yayi ya koma bedroom saman bed ya kwanta tare da janyo jidda jikin shi lumshe ido yayi ba wai dan yana jin baccin ba, saboda gaba ki daya kwanakin nan da tunanin kausar yake kwana.


   Tana shiga bedroom ta fada saman bed tare da yin addu'a bacci ko   minut 10 ba tayi ba bacci ya kwashe ta.

        Kiran sallah asuba ne ya tashe ta wanka tayi tare da dauro alwala tana fitowa uniform tasa tare da gabatar da sallah, sannan ta shafa mai ta fesa turare  parlour ta fito ko ina share kwal hakan ya tabatar mata da rabi'a ta zo, kitchen ta shiga washe da baki ta gaishe ta cikin fara'a ta amsa kasancewar yau Saturday shiyasa fatuha bata je part din sadiq da wuri ba, rabi'a ta shiga tayawa aiki doya suka fere suka dafa sannan suka yanka fatuha ta gyara albasa rabi'a ta fasa kwai  ta kade tare dasa albasa da percil da tonka sante da tafarnuwa da sauransu, fatuha  na kallo soya doyar da take,  rabi'a da taga fatuha ta iya suyar sai ta sakar mata ta shiga gyara fruit saboda za'ayi ma sadiq juices da su bayan ta gyara ta markada  ta juyo a  jug ta saka qanqara ta kai dining area kafin ta dawo fatuha ta kamala soya doyar ta juye a kula rabi'a shigowa tayi da murmushi ta ce,"Ah sannu da qoqari" murmushi fatuha tayi Rabi'a ta  ce, "ki kai kula dining ni bara na soya kwai" to fatuha tace tare da wanke hannu ta a zing ta dau kula ta wuce dining area, bayan ta aje kula ta dawo parlour ta kunna kallo arewa24  tana kallon gari ya waye washe da baki take kallon dan tana jin dadin shirin ganin goma ta gota yasa ta haura upstairs tana bude parlour zaune taga sadiq saman three sitar, idanuwan shi lumshe abin ya so ya dan bata mamaki saboda bai saba bacci a parlour ba sallama tayi sadiq da ke jingine kamar me bacci ya ware sexy eye's ball's din shi kan fatuha tare da amsawa kallonsa tayi ta ta6e baki tare da gaishe shi amsawa yayi kamar bai san magana fatuha ko shiga daki tayi amma sai dai yau tana ganin suku-suku da sadiq yayi, yayi yawa sai taga yayi kamar wadda bai samu bacci ba tabe baki ta yi ta ce, "ke Fatuha ina ruwan ki?" duk wannan zancan a zuci takeyin shi tada jidda tayi washe da baki jidda ta tashe tana cewa, "Aunty good morning? murmushi fatuha tayi tare da daukar ta ta kaita toilet ta mata wanka suka fito suna dariya tsane mata jiki tayi sannan ta shafa mata lotion kasancewar akwai wasu kayan ta a dakin shiyasa anan fatuha ta shirya ta, jeans n  t-shirt tasa mata rigar white sai jeans blue masha Allah tayi kyau sosai  fita tayi daga dakin tabar fatuha na gyara daki.

  Washe da baki ta fada jikin sadiq ta  ce, "daddy morning"
          "morning too angel, how was ur night angel,"
     "cool daddy n Ur's daddy"
"The same" ya ida zancan yana mata peck jidda  ta  ce, "daddy..!
   "yes sweet..!
"uhm me ya sami eye's din ka sunyi ja," lumshe ido yayi ya ce, "angel daddy ciwo ido yake,"
     "sorry daddy, a kira uncle yakub ya duba ka please daddy,"
        "na warke ai har ma nasa ma gani"
   "sure daddy?
     "yes  my  angle" peck ta masa cheeks tare da cewa, "daddy am Hungary,"
      "ok ina Aunty ?
Aunty na busy now, OK muje nayi feeding naki ko sweetheart," OK daddy daukar jidda yayi yana mata wasa tana dariya sai da suka qaraso dining area ya ja kujera ya zauna sannan ya d'aura jidda saman cinyarsa ya shiga saving din su sai da ya kamala ya fara feeding din jidda yana bata tana bashi cikin jin dadi.

       Bayan ta gama share bedroom din tas ta dawo parlour ta kwalwale shi tas, ta kunna Burne  a socket tare da sa turaran wuta tuni part din ya dau kamshi mai sanyi, gudun AC ta qara lumshe ido tayi tare da zama saman three sitar tana qarema dakin kallo, ita kanta part din ya mata kyau yadda ta gyara shi ji tayi kamar tayi bacci tashi tayi ta fita daga part din.

    A hankali take sakowa daga upstairs jidda dake saman cinyar daddy ta kwalawa fatuha kira, cikin jin dadi "Aunty..! wata irin juyowa fatuha tayi har sai da gashin kanta iska ta kad'a shi fari tayi da ido ta ce "A..!  Sadiq  dake  zaune  yana  kallon  fatu  tamkar  an  dasasa kashe  ma  jidda  ido  tayi  tana  sakowa ta  dage  mata  gira kujera  sadiq  ya  bi  ya  lafe  yana  bin  fatu  da  ido yarda  takeyi tamkar  da  shi  take, dariya jidda tayi ta ce, "Daddy ka ga yadda gashin Aunty yayi" lumshe ido yayi ya ware su kan fatuha yana qare mata kallo gani yake kamar idannuwan shi ke mai gizo kwanan kullun qara canza masa take kawar da zancan yayi ya cigaba da abinda yake,  saukowa jidda  tayi daga cinyar shi riqe da doya a hannun ta fad'a jikin fatuha ta  ce, "Aunty..!
   "na'am.!
  "bude bakin ki na baki yam" toh fatuha tace tare da bude dan qaramin bakinta ji tayi jidda ta bata ragowar doyar hannunta sadiq da ke zaune saman kujera dining yana kallon su ta qasan ido har mamakin yadda jidda ta saba da fatuha haka yake, ta6e baki yayi ya shanye ragowar tea din da yake sha ya miqe  ya wuce su ya haura upstairs fatuha ko dining tazo ta cika tunbin ta sannan taja jidda suka koma parlour suna cikin kallo rabi'a ta fito tare da yi masu sallama, har bakin gate suka rakata bala mai gadi sai tsiya yake ma jidda ita kuma sai turo baki take fatuha ko dariya abin ya bata janyo jidda tayi suka dawo cikin gida suka cigaba da kallo.

    Wani irin sanyi da kamshi ya doki hancin shi part din kwal kamar ba'a kwana ciki, wani irin sanyayan ajiyar zuciya ya saki tare da sakin handle din kofar, bedroom ya shiga nan ma wani irin lallausan smile ya saki komai ya mai yadda yake so take ya ji wani irin bacci na fizgarsa saman bed ya fada tare da sauke ajiyar zuciya bacci da baiyi jiya ba shi ya kwasheshi.

    Sun sha kallo har sun gaji  ba su suka bar parlour ba sai 1:30pm shima kiran sallah ne ya tashe su, alwala suka dauro sannan suka gabatar da sallah suna idarwa suka dawo parlour, ola ne yayi knocking din kofa fatuha ta tashi ta bude masa washe da baki ya kalle ta, cikin hausarsa mara fita ya ce, "madam sannu"
  "yauwa.! fatuha tace "dama wannan malam min ne da ke koya maku karatu ne ya zo yanzu," murmushi fatuha tayi ta ce, "malam ai ba da rana yake zuwa ba" ta fadi tana leqa waje ta  ce, "bari ina zuwa" daki ta shiga ta janyo  hijabin ta tare da daura zani saboda mini skrt ne jikin ta  sannan ta fito lokacin har ola ya koma bakin aikin shi malam na zaune saman tabirin mai gadi suna dan taba hira cikin nutsuwa fatuha ta qaraso tare da gaishe shi, murmushi yayi ya amsa ya  ce, "ah malama fatuha" murmushi kawai tayi  ya  ce, "kinga yau na zo tun 2:00pm wallahi ina da wata safga  anjima shine nace da naki zuwa gara na zo yanzu tunda kwana biyo ba muyi karatun ba" murmushi fatuha ta yi ta ce, "aiko dai malam mun gode bari na kira jidda" toh yace mata tare da tashi daga tebirin bala mai gadi ya koma inda suke gabatar da darasin, fatuha na shiga gida tasa mata hijabin ta suka fita.

    Cikin jin dadi suka gabarta da darasin su inda malam yayi masu qari tare da yi masu yan tanbayoyi suka bashi amsa sai da ya tabatar sun gane misalin karfe hudu ya sallame su, ya wuce akan cewa gobe karfe hudu zai zo insha Allah littafan su suka kwashe suka shiga gid, dama daure da alwala  fatuha take  sallah ta gabatar sannan ta cire zanin ta shiga wanka tana fitowa daure da towel ta tsane jikin ta tare da shafa jikin ta da lotion har ta dauko uniform din ta zata maida ta tabe baki, tunda na gama aiki ai sai na sa na gida dan ni na fara gajiya da su.! ta fadi tana turo baki wardrobe ta bude ta curo wata pink gwon mai dogwan hannu rigar  simple ce mai kyau tayi shape sosai tayi mata kyau rigar ita kanta sai da ta yaba rigar parlour ta dawo ta zauna, jidda na zaune tana kallon carton itama ta zauna tana kallon.

    Ring din wayar shi dake bedside drawer ne ya tasheshi dan guntun tsaki yaja tare da kai hannu ya dau wayar, ba tare da ya duba suna ba ya  ce, "hello.!  cikin alamar gajia ta daya bangaran a kayi dariya, sadiq tashi yayi zaune tare da saki guntun murmushi, ta  daya  bangaran  aka ce, "wallahi sadiq baka da kirki Allah yasa ma ka gane mai magana? yar dariya yayi tare da shafa sajan sa ya  ce, "ba Khaleed bane? dariya Khaleed yayi ya ce, "ashe dai kana gane mutane" dan guntun tsaki sadiq ya ja ya  ce, "ya za'ai na kasa gane muryar childhood friend dina,"
     "ai ka kyauta ina majid ai ya fika zuminci,"
    "haka dai kace"
     "toh yau na leko Kano insha Allah zan shigo"
     "toh shikenan sai ka zo idan ka zo ka kira ni" toh yace tare da yanke wayar agogwan dake manne a bangwan daki ya kalla ware sexy eye's ball's din shi yayi "ohno na kwanta ina ta bacci har 4 ya gota.! tashi yayi tare da yaye blanket din jikin shi toilet ya shige ya sheqa wanka yafito daure da qaramin towel a qugunsa, hannun shi riqe da qaramin towel yana tsane sumar kan shi yana cikin shafa lotion wayar shi ta fara ruri hannu ya sa ya dauka tare da karawa a kunne ta  daya  bangaran  aka  ce, "hello big man ganin a filin gidan ku" smile sadiq yayi ya ce, "are u serious,?
   "yeah angayama kowa irin kane mara zuminci" dariya sadiq yayi  ya  ce, "kai friend nine fa"
  "koma yane.!
"toh shikenan ganin zuwa" katse wayar yayi tare da zura jallabiya white ya fito daga part din shi ya wuce su fatuha a parlour suna ta karatun dan fatuha ta dake sai jidda ta koya mata karatun boko yanzu haka har ta iya ABCD.

      Yana fita farfajiyar gida ya hango Khaleed jingine jikin motarsa mai tsada kallo daya zaka masa kasan shima dan hutu ne, kuma gaye ne sanye yake da shada  tasha diki mai kyau Khaleed chocolate

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login