Showing 72001 words to 75000 words out of 105783 words

Chapter 25 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

711

sannan Mom ta fita ko da ta fita sadiq ta aika ma harara tare da ayana ma ranta idan sun dawo zatayima  tufkar hanci.

       Katafarin parlour su da aka ware danyi meeting suke zaune, tunda sadiq ya shigo gabansa ke yankewa yana fad'uwa yarasa dalilin hakan addu'a da ke  bakinsa ya furta dan samun nutsuwa, duk  kuma  ya damu  da  yanayin  daya  bar  fatu yafi  tunanin  harda  hakan  ya  hanasa  nutsuwa, majeed ne ya shigo tare da zama gefen sadiq ya  miqa masa hannu suka gaisa dakyar sadiq ke danne zuciyarsa kan majeed  da bata hakuri.
        Alhaji Babba ne ya shigo sanye da babba riga tasha aiki sai sheqi kayan suke, da sallama ya shigo tare da zama a kujerarsa ta musanman wato kakan su sadiq, Ammi na gefansa na dama sauran jikoki da iyaye na gefe da yan uwa.
            Taro ya fara budewa da addu'a sannan ya fara jawabin cikin nutsuwa ya  ce, " ina  maku  barka  da  zuwa Allah yasa yarda  ku  ka zo  taron  nan  lafiya  mu  koma  gida lafiya, kuma  na  ji  dadin  yarda  kuke  zuwa  wannan taro na  qara dankon  zuminci kamar yarda kuka sani ko  wani  lokaci  muna  samun  alherai  da  yawa  bangaran  kasuwancin mu  ina  ma albishir da abubuwa da yawa na farin cikin a wannan shekara mun samu kimanin billioths of naire cikin ribar kasuwancin mu, mun talafawa gidan marayu da asibitoci  mun biyawa mutun 30 kujerun maka..! kabara wajan ya dauka tare da hamdallah.
      Gyaran murya Alhaji yayi  ya ce,  "Kuma ga muhimiyar sanawar Majeed ya  samu matar da zai aura..! sadiq dake zaune saman kujera gabansa ya qara yankewa ya fadi ras-ras muryar Alhaji babba ce ta dawo masa dodan kunne, "Alhamdulillah  mun  nema an bamu saboda  karamci, ba kowa bace sai yar gidan ibrahim wanda yake ruqo fatuha..! har gidan iyayan ta muje munyi bincike ashe ma akwai sanaya a tsakanin mu kuma sun aminci sun bada haka ya  mana  dadi matuqa..!  wani irin gumi ne ya karyo ma sadiq maitsananin zafi take nan ya fara ji wutarsa na d'aukewa jikinsa  rawa  ya  d'auka  jin  kalaman  Alhaji  yake  tamkar  saukar  aradu, wani  irin  amo  kalaman  suke  masa  cikin brain, ba sadiq ba hata Mom sai da ta girgiza da wannan furucin, ita  dake qoqarin  furta  abinda  ke  ranta sai  gashi an masu shigar  sauri  da  karfi  kirjinta  ke  bugawa  tana  tunanin  halin  da  d'an  autanta  dilo  zai  shiga, wata kalmar ya qara jefowa a karo na biyu "sadiq kuma mun yanke shawarar bashi kanwarsa Basma amma da sharadi idan har ya kawo wadda yake so nan da sati daya kamin asa biki to za'a basa dama ya auri wadda yake so, Basma ma kuma ta hakura wannan shine hukuncin dana yanke.! sannan ya kalli baban Basma ya  ce, "Alhaji khabiru cika mana taro da addu'a..!

      Gabaki d'aya parlour juyawa sadiq yake dakyar ya samu ya miqe, jiri  na  neman  kadasa majeed ban da murna  ba  abin da yake  finally  yanzu  zai  samu  fatu  shawo  kanta  kawai  ya  rage masa, ko ta kan sadiq bai bi ba haka Basma baki har kunne tana  ganin shawo  kan  sadiq  ya  so ta  abu ne  mai  sauki  kamar  yarda  Umma ta  sheda  mata.
           sadiq ne kadai da Mom basu farin ciki, sai Hanan da tashin  hankali  ya hanata  motsi  sanin  matsayin da  fatu  ta  aje  sadiq.
               yana fitowa daga parlour parking space ya nufa cikin sauri ya bale murfin mota ya shiga, da gudu ya fisgi motar ya harba kan titi gudu yake tsulawa kamar zai tashi sama, ko  ganin  gabansa ba  yayi  saboda  tsanin  tashin  hankali  mara  musaltuwa,  fatu  da  majeed  abun  kamar  a  mafarki, yana isowa gida ya danna horn da  karfi  dan  sam  bai  san  mai  yake  ba, bala mai gadi na bude masa geta ya ce "Subhanilillah..! Saboda yadda sadiq ya shigo da motar da  mugun  gudu  kamar  zai  tashi  da  bala  mai  gadi.
      ko daidaita parking ya kasa ya bale murfin motar ya fito, cikin sauri ya wuce part dinsa yana shiga ya zame bakin kofa tare da dafe kansa, jijiyar  kansa  duk  ta  taso  saboda  tsabar  tashin  hankali maganar Alhaji babba na dawo masa, cikin  dodan  kunne miqewa yayi ya shige bedroom saboda har yanzu bai dai na ganin jiri ba, gani  yake kamar  kunnasa  bai  ji  dai-dai ba  wani irin kuka sadiq ya saki mai tsuma zuciyar mai saurare kneeldown yayi a wurin bakinsa na  rawa  yana  furta, no..! No..! I cant believe abinda  kunne  na  ya  ji  noo..! fatali da kayan d'akin sadiq  yake kamar sabon kamu, duk  abinda  ya  dauka  ya  wurga sai  ya watse  ya  dawo  kasa sai da yayima d'akin fata-fata ya shiga toilet da kayan jikinsa sakar ma kansa shower yayi, maganganun Alhaji babba har yanzu  ke masa yawo a brain wata zuciyar ta ce "Wato jiya fatuha tabama majeed izinin turawa gidan su? Dama  fatu  ba  so  na  take  ba? Jikin  sadiq  na  rawa ya  furta  Kalaman bakinsa hadeye  kukan da yake yayi ba shiri ya fito sharkaf ya zauna kasan carpet bai damu da kayan dake jikinsa ba ya  takure  waje  daya.

      Bangaran fatuhu ko tunda su Mom suka fita gabanta ke faduwa, ta rasa dalilin haka ta rasa sukunin ta jin an bude kofar d'akin ya sata waigowa Mom ce tsaye bakin kofa murmushi fatuha ta saki wanda iya karshi la66anta ta  ce, "Mom har kun dawo da wuri haka? eh tace tana qoqarin danne damuwarta, ta  qarasa shigowa zama tayi kusa da fatuha cikin sanyi murya ta ce "Fatuha gobe da safe ki shirya zaki je wudil Baffa nasan ganin ki?" sannan ta tashi ta fita kallo fatuha tabi Mom da shi take nan jikinta ya haubari da tsoro-tsoro ko dai uncle ya kai qarata kauda zancan tayi tasan ma ba zanyi haka ba, amma zuciyarta na cike da tanbayoyi, ganin bata da amsa ta hakura.

      Ola sadiq ya kira a waya bugu d'aya zuwa biyu ya dauka, "ina san ganin ka" sadiq ya fada a taqaice.
           ko da ola ya zo ganin watsin da akayima dakin sadiq ya tsorata kallon sadiq yayi da magana a bakinsa, ganin fuskar sadiq ba annuri yaja baki ya tsuke, nuni ya masa daya gyara d'akin shi kuma ya shingida saman sofa, yana  jin  wani  quna  da  suya  da  zuciyarsa  ke  masa hawaye daya na bin daya saman fuskarsa kamar ba soja ba,

      Gabaki d'aya gidan Alhaji Ibrahim ba wanda ya rintsa, daga angel sai Abba ne kawai suka samu bacci,
        bangaran sadiq ban da kukan zuci ba abinda yake, fatuha kuwa tunanin me yasa Baffa ke neman take?  ko dai inna ce ta rasu? ba'a son fada mata girgiza kai kawai  tayi.

      Tunda safe fatuha ta tashi ta shirya cikin riga da sket dinta na atamfa yellow mai ratsin white a jiki masha Allah kayan sun hauta sai dai fuskarta tayi fayau, bayan ta kamala ta fito parlour cikin nutsuwa ta gaida Mom da Abba dake ta break angel na gefe itama ganin bata ga sadiq ba yasa gaban ta ya qara faduwa a karo na biyar jiki ba qwari ta zo ta hada tea kurba biyu zuwa uku ta aje Mom ce ta ce, "Fatuha har kin koshi?
  "eh Mom dama idan zan yi tafiya bana wani cin abinci" to Mom tace, sannan ta qara da cewa, "ga driver nan zan had'a ku da shi idan ya kai ki yau zai maido ki, ki gaida mutun gida sannan idan kin isa ki kira ni ki fada min" lagwabe kai fatuha tayi ta ce, "Mom ai jiya wayar ta lallace"
       "garin yaya?
"fadowa tayi daga saman dressing mirror ta dauke"
     "eyya to bari na baki baby Nokia idan kin dawo a sake wata" to fatuha tace tare da shi ga daki ta dauko sim dinta, miqa mata wayar Mom tayi ta zura sim dinta ciki har ta kai bakin kofa ta dawo ta haurawa sama part din sadiq ta nufa a hankali ta murda handle din kofar taji kule gam tsoro ne ya kamata amma ba yadda ta iya haka ta dawo, tare da yima mom sallama angel ko sai rigama take sai tabi fatuha Mom ta hana.

     Shigewa mota tayi driver ya harba da su kan titi cikin dan qanqanin lokaci suka isa wudil, cikin kwatancan fatuha har driver ya kawo ta gida fitowa tayi a hankali tana qare ma gidan su kallo gabaki daya gidan ya canza a yadda ta san sa, mamaki ne ya bayana a fuskarta qarasa shiga tayi ciki da sallamah Inna dake  parlour ce ta fito da  murna tana yima fatuha maraba da zuwa duk da fatuha ba'a cikin jin dadi take ba bata yadda inna ta gane ba, parlour ta jata suka shiga har yanzu mamaki ne shinfide a fuskarta  tana  qarewa  gidan  na su  kallo  yarda  yayi  kyau ko  abirni  sai  haka ta ce cikin sanyin murya "inna waya gyara gidan nan? murmushi inna ta saki ta  ce, "yaron arziki sadiq wallahi shi ya mana abin arzikin nan, ya  canza  mana  gida ya  koma  kamar  aljanna  duniya" murmushi fatuha ta saki mai cike da jin dadi Baffa ne ya yaye labilan dakin ya shigo har qasa fatuha ta tsugunna ta gaisheshi amsa mata yayi a taqaice  sannan ya samu wuri ya zauna, itama fatuha qasa tayima kanta mazauni tana jiran jawabin Baffa gyaran murya Baffa yayi  da cewa, "Fatuha.!
    Na'am Baffa.!
"Fatu nasan cewa na maki laifi amma kiyi hakuri ina fatan bazaki watsamin qasa a ido ba? ina fata bazaki bani kunya ba? duk wannan jawabin da Baffa keyi kan fatuha na qasa d'ago kai tayi ta ce, "insha Allah Baffa bazan baka kunya ba"
      "yauwa diyar albarka, dama  nasan  baza  ki  watsamin  kasa  a  ido  ba, dama d'an uwan sadiq ne ya zo neman auran ki tare da iyayansa jiya daddare, mukanmu munyi mamaki da wannan zuwa fatuha ganin halacin da zura'a suka mana gashi nasan baban yaron hakan yasa na amince dan na lura yaron mai nutsuwa ne, Kuma dama neman auran budurwan anso iyayanta su za6a mata miji na gari da wannan nayi la'akari na za6a maki majeed a matsayin miji..! dagowa fatuha tayi a razane dan sai yanzu ta fahimci inda aka dosa   idanuwan ta taf da kwalla suka ciko  nan take hawaye suka fara anbaliya a fuskarta me yasa mai kyau zai mata irin wannan horan me yasa zai  mata  haka  dama  hukuncin  daya  dauka  kenan  dama  majeed  ne dalilin  fushin da mai  kyau  yake  da  ita  mai  yasa  bai  ji  ta  bakinta ba, fita tayi daga parlour da gudu ta fada dakin inna ta saki wani  irin kuka mai tsananin ban tausayi, inna ce ta dafa bayanta tana lallashinta cikin  tattausar murya, "haba fatuha bai kamata ki watsawa muta nan qasa a ido ba duk  halacin  da  suka  maki  banyi tunanin  haka  daga  gare  ki  ba, kuma  yaron  nan  kin  san  sa, kuma kowani mutun da qadarar dake zuwa masa fatuha idan dai majeed alkhairi ne a gare ki Allah ya tabatar ke  dai  na ki  addu'a  ne" haka inna ta dinga bitana tausar fatuha har ta samu tayi shuru tana sakin ajiyar zuciya, ko ruwa kasa sha fatuha tayi sai bayan sallah la'asar suka dau hanyar kano wayar tace dake cikin jaka taji qara message ya  shigo sai a lokacin ta tuna da Mom tace ta kira ta curo wayar tayi ta karanta message din kamar haka,

     Sister ina matukar farin cikin sanar dake yau buri na ya cika, mafarki na  ya  kusa zama  gaske, tun jiya nake qoqarin kiran ki wayar taki shiga ba wani albishir bane ila yaya sadiq ya kusa zama miji a gare ni, sannan ina taya ki murnar zama in-law a gidan mu cikin family din mu daga Basma your sister..

         Wani irin kuka fatuha ta saki mai cinrai ko qarasa karanta sakon ba tayi ba wayar ta fadi jikinta ban da bari ba abin da yake, ashuru driver ya juyo ya  ce, "haba fatuha komai yayi zafi maganin shi Allah bai kamata kina kuka irin haka ba , addu'a  ce  makamin  mumini..!  duk wannan magana da ashuru yake fatuha ba jin shi take ba kalmar sadiq yazama miji na kawai ke yawo cikin qwaqwalwarta har suka iso garin kano fatuha na sheka kuka kamar ranta zaifi ta, ko da ashuru yayi horn aka bude geta kafin ya tsaida motar ta bale murfin motar ta fita da gudu sadiq da yanzu ya ji qarar shigowar mota daga labila yayi tare da koma ya cigaba da zarya a bedroom.

           Da gudu fatuha ta haura sama ko kallon mutanan parlour batayi ba part din sadiq ta wuce Allah ya bata sa'a tana bude kofar ya bude, ganin bata gashin a parlour ba yasa ta shigewa bedroom da gudu.
           fadawa tayi jikin sadiq dake  tsaye tare da sakin kuka mai cinrai, rintse ido sadiq yayi yana jin yadda fatuha ke sheqa kuka, sai  yanzu  ya  gane  ba  sa hannu  fatu  cikin  abinda  ya  faru cikin sarkewar harshe ta ce, "Uncle dan Allah karkamin haka wannan horan yamin nauyi wallahi bazan  iya dauka ba, kaji  mai  kyau..! my  uncle..! my  happiness..! dama ace mafarki nake abin da nake ji ba gaske bane..!  ta ida zancan   tare da sakin sabon kuka ta zame kasa.......



Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
    Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn= H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERS FORUM.COM

             
                        77_78

Kuka fatuha ke rairawa kamar ranta zai fita,  gabaki d'aya jikinta rawa yake qafafuwan sadiq ta riqe cikin shashekar kuka ta ce, "Please uncle I beg you in the name of God a janye maganar auran nan, wallahi ban shirya yin aure ba yanzu ba, babu  abinda  ke  tsakanina  da  majeed i  swear.! taqara rushewa da wani sabon kuka har yanzu jikin fatuha 6ari yake bakinta na  rawa  ta  ce, "uncle ya zanyi da karatu na? bayan duk duniya ba abinda nake so sama da shi, wallahi uncle ba abinda ke tsakanina da majeed kaji..! ta qara sakin kuka mai cin rai ( ko ni salma sai da na matse kwalla😥) da kyar sadiq ya sai ta kansa ya  hade hawayan dake maqale a kwayar idanuwansa, juyawa yayi, ya d'ago fatuha tsaye dake durqushe tana kuka ya zaunar da ita zaman bed amma duk da haka ba daina kukan tayi ba jikinta  sai  rawa  yake  tana  faman  sauke  ajiyar  zuciya, fridge ya bude ya curo robar ruwa ya tsiyaya a cup ya miqa mata, kuka kawai take baji ba gani, aje cup din sadiq yayi saman bedside drawer ciki cool voice sadiq ya ce "Fatuha..! tsagaita kukanta mai  sauti tayi tana kallon sadiq hawaye  na  sulalo  mata, lallashin ta sadiq ya shigayi cikin sanyi murya ya ce, "Fatuha ina so ki sani ko kadan bani na maki haka ba dan me  zan  maki  haka  ba  tare  dana ji  ta  bakin ki  ba" daura hannusa yayi a fuskarta, haka itama fatuha ta daura nata saman hannusa tana sauke ajiyar zuciya, ya cigaba da cewa "Bayan na dau alqawarin samamaki farin ciki har qarshan rayuwar ki fatuha? dan meyasa zan rusa maki mafarkin ki da  alkwarin  dana  dauka? ina so ki kasance mai daukar qadara mai kyau da mara kyau, da anyi shawara dani fatuha ba abinda zai sa na amince a katse maki karatun ki, ko  a  baki  abinda  baki  so, ko yanzu nasan majeed zai barki kiyi karatu kinji, ki kasance me yima iyayan ki biyaya zaki ga ribar haka, kuma insha Allah zaki so majeed saboda majeed nada kyawawan hali kuma yana son ki zai baki duk wata kulawa, ba zai bari ki taba zubar da hawayan ki a kansa ba, na  tabbata yana  sonki  so  haqiqa ki daure ko so d'aya ne ki sama ranki son majeed ko dan yana dan uwa na..! wasu zafafan hawaye ne suka gangarowa fatuha tana bin sadiq da kallo, dan ko bakin magana ta rasa, dama  mai  kyau  bai  ta6a jin  sonta  ba  dama  ita  ke  haukarta, tunda  gashi  shawara  yake  bata  ta  so  wanin  sa.
        sadiq ko ban da daurewa ba abinda yake dan numfashinsa neman yankewa yake, sai ya numfasa yake cigaba da maganar saboda zafi da quna da qirjinsa ke masa ganin  fatu  zatayi  nisa  da  shi, glass cup sadiq ya miqa ma fatuha da  ruwa  ciki amsa  tayi  jiki  mace ta kafa kai ta shanye ruwan a hankali taji sanyin ruwan na ratsata, shiru suka dauka na mintina ba wanda ya tanka, can sadiq ya ce, "Fatuha kimin promise baza ki tada hankalin ki ba" dakyar fatuha ta iya furta  to wasu hawayan suka sulalo, jiki ba qwari ta tashi tana qoqarin fita sadiq ya bita da kallo dan bai jin zai iya tsaida ta saboda ganin tama qara famamasa ciwo ne a ransa.

                Tana fita sadiq ya kafa rubar ruwan ya shanye yana maida numfashi tare da ganin wasu taurari namasa yawo.

      Tsayawa tayi bakin steps ta share hawayan ta dan bata san Mom ta gane cikin nutsuwa ta sako, tana  wasa  da  yatsun  hannuta Mom da fitowar daga kitchen kenan ita da baba jummai murmushi ta saki ta  ce, "ah fatuha har kin dawo? eh tace tana qoqarin hadiye hawayan idanuwan ta Mom ta  ce, "Ahamdulillah ya su inna?
      "lafiya lau" ta ce, sannan Mom ta ce, "ina fata Baffa bai maki dole ba" d'aga kai fatu tayi  alamar a'a idanu  ta  taf da  hawaye tana  wasa  da  yatsun  hannuta baba jummai ce ta shafa fuskarta ta ce, "Alhamdulillah hajiya ni dai bani da abin cewa kun gama min komai a rayuwata" ta ida zancan tana matsar kwalla ta  cigaba  da  cewa, "daga kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login