Showing 33001 words to 36000 words out of 105783 words

Chapter 12 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

707

har sai da motar shi ta fita sannan sadiq ya koma cikin gidan.

      dauke da jidda fatuha ta fito, lokacin  yayi  dai-dai  da shigowar  sadiq  parlour ballama fatuha harara tare da kauda kai, itako tayi kamar bata gani ba, yana gaba suna bayan shi jidda na zuba surutu suna shiga part din a parlour fatuha ta aje jidda tana qoqari fita, kamar  daga  sama  ta ji  zazakar  muryarsa ta doki dodan kunna  ta "keee.. Yace da ita birki ta ja ta tsaya zuciyar ta na dukan uku-uku dan bata manta rashin kunyar da ta masa ba da safe  maganar sa  ce ta  kara  dawowa  da  ita  daga  duniyar  tunani "ba dake nake magana? ya fada cikin daka tsawa, juyowa tayi tana zare ido  ya ce, "kije kitchen ki hada min coffee ki kawo min" zaro ido fatuha tayi waje take ce, "uhm kwarankwatsi ban san me hakan ba" tsoki yaja mtss "yar kauyan banza toh  bunu nake nufi tea mara madara zaki had'a ki kawo min  karki sa sugar a ciki" ya ida zancan tare da balla mata harara abin ma dariya ya so ya ba fatuha wani lokacin sadiq idan yana harara kamar qaramin yaro a zuciyar ta ta ce, "bai ma san idan yana fada wani qara kyau yake ba..! ta dan ja tsaki ta fita, saida ta gama hada masa ta kai masa yana zaune parlour yadda ta barshi jidda na saman cinyar shi da alama bacci ya dauke ta hannu ya miqa zai amshi coffee tana bashi ya saki cup din ya fadi gaba daya ruwan tea din ya zube mata a kafa wani irin ihu fatuha ta bude baki zatayi wata  irin  fisgowa  sadiq  yama  fatu  ta  fado jikinsa tare da toshe mata baki yana kallon ta damn sanyayin  idanusa ido cikin ido, idanuwan fatu t cicikowa sukayi da kwalla hawaye daya nabin daya saboda  azabar  ruwan  tea  din  daya  konata.
   murmushi mugunta  yayi na  gefan baki komin banza ya sata kuka, gashi matsar da yayi ma bakin bana wasa bane dan bakin sai radadi yake mata, sai da tayi kuka san ranta sannan ya sake ta tare da hankada ta ta fadi kasa sannan ya tashi ya kashe kayan kallo ya matso gaf da ita har tana jin saukar numfashinsa tana  sauke  ajiyar  zuciya  sama-sama tuni  idanu  ta  sun  rine  zuwa  ja  sadiq ya ce cikin cool voice nasa "wannan kad'an na maki akwai saura nan tafe..! ya ja saki tare da daukar jidda sai da ya kai bakin kofar bedroom ya juyo tare da yin killing smile din shi ya cigaba da cewa, "kuma ki tabata kin gyara gurin kafin ki bar wajan? Yana fad'in hakan ya shige bedroom ya barta tana matsar kwalla tare da jera masa Allah ya isa ta  ce, kuma indai gyara gurine wallahi banyi mugu kawai sannan taja kafar ta wadda ta kone wajan har yayi ja bakin tama haka saboda ya ji matsar manya.

      Direct bedroom dinta ta wuce  tare da rage kayan jikinta, bathroom ta shige tayi wanka ta fito daure da towel tana shafa mai tana mai cigaba da jera masa Allah ya isan, a haka har ta gama shirin tafada saman bed se bacci...

Written by
        Salma mas'ud nadabo

Edit by
      Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn_=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANI WRITERSFORUM.com


                         41_42

Kiran sallah asuba ne ya tada fatuha, alwala ta d'auro tare da yin wanka bayan ta idar da sallah ta shafe jikin ta da mai kamar kullun tare da fesa turare  uniform ta zure sannan ta d'aure gashin kanta wanda dakyar ta kama sa, ganin bai kamuwa yasa ta sake shi haka kawai ta fita direct part din sadiq ta shiga tana karema parlour  kallo, har yanzu glass din jiya nan zube a parlour baki ta ta6e ta shige bedroom sadiq na kwance jidda na maqale a jkinsa da alama daga masallaci ya dawo bacci ya kwashe shi dan jalabiya ce a jikin sa ba night dress ba sajan nan nashi yayi luf-luf kwance, qare masa kallo fatuha tayi sannan ta bala masa harara  ta  ce, "kamar idanuwan shi biyu..!  a hankali ta sa hannu ta fara janye jidda daga jikinsa jawo jidda ya qara yi ya maqale ta, abin ma dariya ya ba fatuha qara jan jidda tayi shima ya qara jan jidda haka suka riqa ja inja  qara leqa fuskar sa tayi taga dai bacci yake a hankali ta qara miqa hannu zata janye jidda cikin dubara  ta janye jidda direct bathroom ta dire ta, kamar kullun ta shirya jidda murmushi tayi  washe da baki  ta ce, "Anuty I like you" murmushi fatuha tayi tare da langwabe kai ta shafa kan jidda tare da cewa, "jidda kisan ban iya wannan yaran ba" murmushi jidda tayi take ce, "ina nufi kina birge ni Anuty" murmushi fatuha tayi wadda ya baya kyawawan hakoran ta ta ce, "nima haka Jidda" peck jidda tayi mata itama fatuha peck tama jidda.

     Jawo hannun jidda  tayi cikin nishadi suka qaraso dining area tea ta shiga hada ma jidda mai kauri, wanda yaji ovaltine da madara  tare da bread n egg a hankali ta shiga feeding din jidda tana amsa itama idan taji dadi sai ta gutsuro bread din taba fatuha, Mom da Abba ne suka qaraso cikin fara'a dining area cikin ladabi fatuha ta gaishe su, cikin  fara'a suka  amsa hada masu breakfast fatu ta shigayi, jidda ce ta washe baki tare da cewa, "morning grandma n grandpa"
      "morning too angel" suka amsa a tare  bayan fatu  ta gama hada masu ta aje masu cikin nishadi suke breakfast.

    Tsaye yake gaban dress mirror sanye da bathrobe hannu shi riqe da qaramin towel yana goge sumar kanshi da alama daga wanka ya fito, cikin nutsuwa yake shirinsa lotion ya shafa tare da saka uniform din sa sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi, booth din shi ya curo ya saka black sai sheqi yake tsaf ya fito sojan shi hula shi ya dauko ya sa sai agogo silver na azurfa wanda  ya  dace  da  tsintsiyar  hannusa wani irin kyau yayi ba d'an kad'an ba  sai dai fuskar nan d'aure ba  wani  walwala  kamar  kullun briefcase nasa ya dauko tare da d'aukar wayarsa da ke bedside drawer a hankali ya bud'e kofar bedroom kallo daya yayi ma parlour tare da jan dogwan tsaki ya  furta, "fatuha kin rainani wallahi..! sannan yasa qafa ya fito daga part din a hankali yake saukowa daga upstairs tuni kamshi turaran shi ya mamaye parlour fatuha da ke feeding din jidda ta dago idanuwa tana qaremasa kallo sosai  take  ganin  kyan  sadiq har ta  manta  kanta  wajan  kallonsa, cikin isa ya qaraso wayar shi ya cure ya kara a kunne cikin nutsuwa yake wayar.
      "holle ole.! daga daya bangaran ola ya ce, "hello boss"
        "ka zo ka amshi briefcase dina" to ya ce masa tare da kashe wayar ya qaraso dinning area smile yayi wanda  iyakar  le66ansa tare da gaishe da su Mom jidda washe da baki ta gaishesa haka fatuha banza yayi da ita kamar bai ji ba tare da qare mata kallo  ganin  yarda  gashin  ta  ya  kwata  har  gadon  baya,  tsintar  kansa  yayi da  maganar zuci, "yau kuma wani sabon iskancin yima mutane yawo a gida ba dankwali  ya  kamata yana yin maganar ne  duk cikin zuciyarsa.
           a hankali ta jawo cup da niyar hada masa breakfast hannu ta ya rike ya wurga mata wani irin kallo ya aje hannu tare janye cup din Mom ce ta aika masa harara sai yayi kamar bai gani ba ya cigaba da aikin da ya ke ole ne ya shigo cikin sallama suka amsa sannan ya amshe briefcase din sadiq ya fice da ita Abba ne ya katse shurun da cewa,  "Alhamdulillah ka ce min qafa ta warke? murmushi sadiq yayi tare da cewa, "eh Abba.!
           "toh masha Allah"
   "Abba ya maganar kwangilar ku kunko samu?
         "a'a munan dai muna fama amma insha Allah this time around zamu samu abinda muke so insha Allah" murmushi sadiq yayi tare da cewa, "Allah yasa" Mom ta amsa da ameen tashi yayi tsaye tare da cewa, "oya angel mu tafi" Mom  ta  katse  sadiq  da  cewa "baby karka ce min ruwan tea din har ya isheka ba bread ba komai"
         "eh Mom na koshi"
      "toh shikenan, ka  dai  kula  da  kanka" hannu jidda ya kama har sun kai baki ko Abba ya ce, "yauwa baby ina san fadama ranar Sunday tare da Mom din ku zamu tafi uk"
        OK sadiq ya ce tare da sa kai ya fita fatuha na biye da su da lunch box din jidda har gaban mota sannan ta miqa wa jidda lunch box din tare yi mata peck sadiq kallon su yayi tare da ta6e baki har  mamakin  shakuwar  jidda  da  fatu  yake  bai  ta6a ganin  mai  aikin  da  angel ta  shaku  da  ita  ba  kamar  fatu  ba  kawar da  tunanin  yayi sannan ya shige mota.

     A hankali ta juyo ta shige gida, kwashe kayan breakfast din tayi Mom na zaune a parlour tana kallo fatuha ta zo ta wuce kitchen, washe da baki ta gaida baba jummai itama baba jummai washe da baki ta amsa, rabi'a na gefe tana gyara kayan miya tayata fatuha ta shiga yi suka gyara tare sosai ta taya su  baba jummai, saboda aikin kitchen na burge ta kusan tare da ita aka dafa lunch baba jummai ko dadi take ji har qosawa take suje kauye jauro yaga yadda fatuha ta koma kamar balarabiya, ta  wani  siko  ta  zama  yan  mata bayan sun gama aikin fatuha ta wanke duk wani kwano da akayi anfani da shi rabi'a ko sai hanata take amma taqi bari sai da suka gama komai sannan fatuha ta dawo parlour, ko da ta dawo Mom ta bar parlour  bedroom ta shige tare da rage kayan jikinta bathroom ta shige ta watsa ruwa d'aure da towel tafito bayan ta gama komai sannan ta tuna ashe bata gyara part din sangamin ba,  ko mai bata shafa ba ta zura kayan ta direct part din sadiq taje ta fara gyara sai da ta gyara shi tas, sannan ta zauna a parlour saman three sitar tana maida numfashi  lumshe idanunta tayi tare da ware su, fita tayi daga part din ta koma bedroom ta kuma watsa ruwa sannan ta shefe jikita da mai tare da fesa turare da maida uniform din ta.


   Misalin karfe 2:00pm su jidda suka dawo, kasancewar yau sadiq bai da wani aiki tare suka dawo, part dinsa ya nufa masha Allah gyaran part din ya masa yana jin dad'in ganin part din shi a gyare, duk rashin jin fatuha tasan aikin ta shiyasa wata rana yake d'aga mata kafa, bathroom ya shige ya watsa ruwa ya fito cikin wando da riga ya shirya, kayan sun masa kyau sosai, bangaran su fatuha kuwa jidda na dawowa yadda ta saba yi mata haka ta mata sannan tace taje parlour ko da ta fito parlour  daddyn ta gani jikinsa ta fad'a tana zuba masa surutu shikuma yana sauraranta yana jin dad'i, Mom da Abba ne ke saukowa daga upstairs Abba sanye da shada malin-malin  brown Mom na sanye da atamfa pink mai ratsin green n bleu sanye da mayafinta ba qaramin kyau sukayi ba, parlour suka qaraso washe da baki jidda ta sauka daga jikin sadiq ta riqe hannun grandpa murmushi Abba yayi ya ce "Sadiq yau da wuri ka dawo daga wajen aiki  kenan?" smile yayi tare da cewa, "eh..!
      "to mu zamu wuce gidan Ammi mu masu sallama"
           "to Allah ya tsare"
"ameen.! jidda ce ta ce, "grandpa zan biku"
    "toh shikenan yima fatuha magana" cewar Mom, "sai muje tare ko" rugawa tayi bedroom fatuha kuwa tunda jidda ta fita wani irin bacci ne ya sure ta ko da jidda ta shigo ta samu fatuha na bacci veil din ta ta d'auka tare da fita tana  cewa, "grandma Anuty na bacci"
     "toh shikenan tunda bacci take mu tafi kawai ta samu hutu ne" washe da baki jidda ta bi su Abba, sadiq ya rako su har parking space sannan ya koma gida ko da ya koma wani irin killing smile yayi upstairs ya haura sannan ya fito kitchen ya shiga ya dako ruwa a fridge mai sanyi wanda har qanqara ya fara saboda tsabar sanyi a hankali ya murda handle din kofar dak'in fatuha ya shiga.
        hangota yayi saman bed kwance tana sharar bacci gashin ta ya baje saman gadon,  da  alama  tana  jin  dadin  baccin cije lips yayi sannan ya qaraso sai da yazo dai-dai face nata ya bud'e murfin rubar ruwan ya juye mata shi, fatuha da ke bacci wani irin razana tayi ta tashi cikin  gigicewa ta yunkura zata fita saboda tsoro, sadiq ya jawo gashin kanta tare da dauke ta da lafiyayan mari,wani irin kuka fatuha ta saki tare da zama saman bed jajayan eye's din ta ta dago tana kallon sadiq wani irin murmushi yayi ya ce "Fatuha yau zan koya maki hankali, bani kika so ki nakasa ba? toni yau kona maki gashi zanyi" ya ida zancan tare ya matse mata fuskarta, idanuwan fatuha sunyi jawur sai kuka take tana bama sadiq hakuri ganin  ya  koma  mata  bakin  kumurci  dama  ya  lafiyar  giwa  bare  tayi  hauka sosai  tsoron  sadiq  ya  d'arsu a zuciyarta  ganin  abinda  yake  kokarin  yi  ta  zaro  manya-manya  idanuta  waje, ashana ya ciro a aljihun shi ya kunna tare da fusgo gashin ta wani irin kuka fatuha tasa tana  cewa, "dan Allah mai kyau kayi hakuri wallahi bazan sake ba" ta ida zancan tana qara rushewa da sabon kuka "shhhh.! yimin shiru fitsarariyar banza..! nufo gashin ta yayi da wutar dake  hannusa take fatuha ta fashe da wani sabon kukan tare da tafiya luuuu ta sume, murmushi sadiq yayi ganin suma tayi ya ce, "marar kunyar qarya" kitchen ya koma ya d'ako wani sabon ruwan sanyi ya dawo bedroom ya qara juye mata shi wata irin ajiyar zuciya ta saki tare da fashewa da kuka tana bama sadiq hakuri sam  ta  kasa  kwatar  kanta  saboda  yarda  sadiq  ya  matse  ta  can  karshan  bed  har  suna  jin  saukar  numfashin  juna  su, da  sauri-sauri  numfashin su  ke  harbawa  harda  sadiq  din  daya  matse  ta, cije lips yayi yana qare mata kallo yarinya ce sosai amma sai rashin kunya duk a zuci yake wannan zancan, bindiga ya ciro ya daura mata akai tuni fatuha ta saki fitsari ta sauke numfashi agwagwame cikin sarkewar murya ta ce, "dan Allah mai kyau kayi hakuri bazan sake ba" tsaki yaja tare da cewa, "fitsari ma kikayi ko? ya  fada  cikin  daka  tsawa  bakin  fatu  na  rawa  ta  ce, "a'a wallahi ruwa ne haka wallahi" murmushi gefan  baki  yayi ya  kara  hada  rai dan yasan qarya take yana  kallon  gashin  kanta  daya  hargitse sannan ya ce, "daga yau sai yau kika qara min rashin kunya sai na 6ula maki kai da wannan abar kina  jina ? girgiza kai tayi alamar baza ta sake ba, sannan ya  hankada ta kanta ya bigi gado ta qara sakin wani sabon kukan sannan sadiq ya sa kai ya fita.

Written by
         Salma mas'ud nadabo

Edit by
      Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_dial_&_yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                       43_44

Sai da fatuha ta ci kuka sosai tare da jerawa sadiq Allah ya isa, sannan ta tashi jiki ba qwari ta nad'e zanin bed din  Allah ya taimake ta katifar akwai leda dan haka ruwan da fitsarin bai shige cikin katifar ba, iya karshi saman bedsheet tatare shi tayi ta aje ta shiga toilet ta watsa ruwa, tana gamawa ta fito ta d'auki bedsheet din ta wanke shi tas sannan ta fito da bokitin ta aje agefe sai da ta shirya tsaf sannan ta dau bokitin ta fita ko da tafi dasu ola taci karo da Sunday yaran sadiq suna ta shawagi a tsakar farfajiyar gidan, kai tsaye wajan shanya ta nufa ta shanya bedsheet din sannan ta dawo ta zauna saman wata resting chair da ke a farfajiyar gidan, lumshe ido tayi tana jin wani tsoro sadiq na ratsa ta, wasu hawaye masu zafi na zubo mata, dan yau ba qaramar wahala tasha a hannun shi ba take nan wani zazza6i mai zafi ya lullu6e ta sakamakon ruwan sanyin da sadiq ya sheqa mata, ganin masasarar taci qarfin ta yasa ta ja jiki ta koma parlour saman three sitar ta zauna ta qudindine waje daya  tana kyarma abin gwanin ban tausayi😰.

    Bangaran sadiq ko zuciyar shi fes bathroom ma ya shige ya sheqa wanka bai jima sosai ba ya fito daure da towel da dan karami yana tsane gashin kansa,  gaban dress mirror ya tsaya yana gyara kanshi da ya tuno da yanda fatuha tayi sai ya saki murmushi jin dadi bayan ya gama shiryawa cikin 3quarte  da armless t-shirt din shi cikin shirin shi na zuwa gym, sannan ya feshe jikinsa da turare masu sanyi kamshi a hankali ya bude handle din kofar tare da barin part din cikin isa yake sakowa daga upstairs, fatuha ya hango saman three sitar qudindine kauda kansa yayi yana qoqarin fita har yayi gaba sai kuma ya dawo saboda rawar  sanyi  da yaga jikinta nayi har ana  jiyo  had'ewar  hakoranta yasa yaji tausayinta kadan azuciyarsa, a hankali ya qaraso gaban three sitar  ya leqa fuskar ta wadda tayi jawur ga shatin hannu shi kwace a fuskar ta lumshe ido yayi tare da waresu a kanta, a hankali ya kai hannu ya ta6a goshin ta ji yayi goshi da zafi rau  kamar wuta, a hankali fatuha ta ware idanuwan ta ta fara rera masa kuka a tunanin ta wani muguntar ya zo ya mata, daurewa yayi tare da cewa, "yima muta ne shuru kafi na kife ki da wani sabon marin..!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login