Showing 60001 words to 63000 words out of 105783 words

Chapter 21 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

716

wajan Hanan kuma ta d'an kirme mata sosai fatuha ta saki jikin ta amma sai dai tana dan d'ari-d'ari da Basma, kiran sallah magrib ne ya tashe su daga fira alwala suka dauro suka gabatar da sallah bayan sun idar angel ta shigo da gudu d'akin ta ce "Aunty fatuha daddy yace ki fito mu tafi?" to tace tare da yafa mayafin ta a tare suka fito da su Hanan parlour a tsaye suka tada sadiq Aunty bilki ce ta 6ata rai ta ce, "haba baby kabari kuyi dinner mana sai ku tafi"
"a'a gaskiya yau girkin baba jummai zanci I miss her food"
"oh ni ba kayi missing din nawa ba ko?
"ba haka bane sis so kike muyi barnan na gida ko?
"toh shikenan a gaida gida dan ko rakiyar banyi" langwabe kai sadiq yayi ya ce, "please kar muyi haka mana" harara wasa ta kaimasa sannan ta ja veil din ta dake saman kujera suka fito a tare hira suke sosai kamar karsu bari, bude murfin mota sadiq yayi angel ta shige gaba fatuha na baya sannan ya ja motar bai zame dasu ko ina ba sai shoprite shiga su kayi yayi masu siyaya sosai ice cream teddy's duk ya kwaso kayan wasa kamar bai jin kudin ya cika boot da su sannan suka juyo gidan a gajiye likis.

Yana horn bala mai gadi ya bude masa geta yayi parking sannan yayi masu ola nuni da su kwaso kayan boot lokaci ma jidda tayi bacci, fatuha ce ta dauko ta suka shige gida upstairs sadiq ya haye fatuha ta shige bedroom kaya kawai ta cire ma jidda tasa mata na bacci, tana qoqarin cire nata akayi knocking din kofar zura hijabi tayi ta bude ola ne riqe da trolley din jidda da kayan wasanta, duk ya aje sannan ya mata sai da safe rufe kofar tayi ta rage kayan jikin ta, ta wuce toilet tayi wanka ta fito daure da towel tsane jikin ta ta yi ta shafa mai sannan tasa rigar baccin ta gown dai-dai gwiwa white n brown mai zanan cartoons, sannan ta saki gashin kanta tare da daukar jidda part din sadiq ta wuce da ita a parlour ta same shi yana kallon news kamar kullun, sanye da kayan baccinsa maroon riga da wando mai dogon hannu bedroom ta shige ta shinfidar da jidda sannan ta fito har ta fito yana nan yarda ta barshi a parlour har yanzu haka yake, qoqarin fita take ya ce, "fatuha ki kawo min dinner na nan" to ta ce masa sannan ta fita.

Direct dining area ta wuce ta zubo masa tuwan shinkafa miryar taushe tasha naman rago sai kamshi ke tashi, sannan ta wuce part nashi saman stool ta aje masa plate din zata fice riqo hannu ta Sadiq yayi tare da cewa "Fatuha waya bata makin rai tunda muka dawo na gabaki daya baki farin ciki? ko bros ya maki laifine?"
"laa Allah ba abinda kamin kawai na gajine yau munsha hira da su Hanan"
"toh naji amma ai ba kiyi dinner ba"
"bana jin yunwa ice cream din dana sha ya cika min ciki wallahi"
"ok tunda hakane na fasa kai ki school din" zaro ido waje fatuha tayi ta ce, "dan Allah kayi hakuri Allah zanci"
"tam oya zo zauna muci" zame hannu ta tayi daga ruqwan da sadiq ya mata ta zauna a qasa tare da jawo plate din gaban ta shima sadiq din zama qasa yayi cikin nutsuwa ta fara kai loma daya sannan ta debo ta kaima sadiq amsa yayi wata lomar ta debo ta kai masa baki hadawa yayi da yatsanta ya ciza yar qarasa ta saki tana yar fe hannu ta dariya sadiq ya saki, kuka ta fara masa tana kai masa bugun wasa riqe hannu yayi yana dariya ya rungumeta ya furta "sorry sis"can qasan maqoshi yana magana yana shafa bayan ta lamo tayi a fafad'an qirjinsa tana maida numfashi dago da fuskar ta yayi ya ce, "sis yau baki surutu kamar ankule maki baki, gashi kin bata min night dress da miya gaskiya ba zan yadda ba" ya fadi a dan shagwabe, kallansa fatuha tayi ta lumshe ido tare da cewa, "yi hakuri mai kyau bazan sake ba"
"good girl to fada min Fushin nan name to?
"uhm uhm dama ina so naje kauye ne kwana biyu wajan inna kafin na fara zuwa makaranta"
"wannan shine damuwar?
"eh.!
"ok karki damu insha Allah zan kai ki" zame jikin ta fatuha tayi daga na sadiq riqe habar ta Sadiq yayi ya ce, "fatuha ki dauke ni kamar yayan ki duk abinda ke damun ki ki fada mani na maki alqawarin samamaki farin ciki, kamar yadda kika samamin fatuha" murmushi ta saki wanda ya bayana fararan haqoran ta daukar plate din abinci tayi zata fita sadiq ya rako ta har kitchen ta aje plate din ta wanke hannu ta.

sai da ta zo bakin kofar shiga bedroom sadiq ya mata peck a goshi itama ta mashi a kumatu sannan ta shige bedroom shima ya haura upstairs.

***
Bayan kwana biyu haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda sadiq ke bawa fatuha da jidda kulawa sosai haka suma suna faran ta masa rai, wani bangare na daban yake jin fatu a ransa wanda baya iya fassara hakan, duk wanda yaga sadiq a yanzu yasan baya fama da wata matsala, sai wani kyau da yake ta qarawa.
bangaran karatun adini kuwa fatuha tayi nisa sosai tana mai da hankali, yadda ya kamata kuma a yanzu duk duniya bata da aboki ko qawa sama da captain shine uwar ta shine uban, ya riga ya zama wani 6angare a rayuwar bata bari yayi fushi da ita ko kad'an domin a duniya ba abinda ta tsana sama da fushin captain a kanta.
baba jummai ko duk yadda ta bigi cikin fatuha ta fada mata wani abu na daban, akan abinda take zargi bata samu ba, sai da kanta ta gane abinda take tunanin ba haka bane, zalla shaquwace kawai tsakanin sadiq da fatuha.

Dr yakub yafi kowa farinciki da canji sadiq har mamaki yake da hamdallah da sadiq yaji shawararsa ya canza lokaci daya.

Kwana biyu ko daya je wajan Ammi ma taji d'adi ganin canjinsa haka majid da kwana shi biyu da dawowa daga Lego's anmasa transfer ya dawo kano da aikin, sosai sadiq yaji dad'in haka ko ba komai dan uwan shi ya dawo kusa da shi.

Kasancewa yau ta kama friday shirye-shiryan ake sosai na tarbar su Mom, yau zasu dawo Nigeria tare da yaya jawad haka Aunty bilki ta kwaso duka yaranta tazo dasu anata aiki.
fatuha na hango sanye da uniform din ta na yan'aiki wanda ta dade raban data sasu sun mata kyau sosai part din sadiq ta wuce riqe da cup na coffee ganin baya parlour yasa ta tura qofar d'akin yana tsaye gaban dressing mirror sanye da shada blue ta sha aiki da dark blue zare yana combing din gashi kansa, murmushi ya saki tare da qarasowa wajan fatuha amshe cup din yayi ya aje saman stool kallo tabi shi da shi dan yau ba qaramin kyau ya mata ba har mamakin kanta take da har yau ta kasa ganin wanda yafi sadiq kyau da komai har ma da kwarjini gashi kullun qara kyau yake, hura mata iskar da akayi ya sata ware manyan idanuwan ta tana kallon sadiq har cikin ranta take jinsa, smile yayi ya ce "Tunanin fa? kin hanani tunani amma ke gashi kinayi yanzu" far da ido fatu tayi ta ce, "bafa tunani nake ba"
"to mikikeyi bayan gashi na gani?
"uhm kayi kyau ne kawai" lallausan murmushi captain ya saki ya ce, "thanks ke ma kinyi kyau"
"a haka din?
"eh mana" cup ya dauka ya kai bakinsa ya wani lumshe ido ya ce, "hmmm lallai fatuha ta iya hada coffee gaskiya zani da ke" dariya tayi ta ce "Allah idan na biye ma sai mu kwana anan muna surutu"
"ko? tam shikenan tafi tunda tafiya zakiyi ni bana so kiyi aikin shiyasa nace akiramin ke, amma tunda kin fi so ki wahala shikenan tafi munma 6ata" langwabe kai fatuha tayi ta ce, "Kayi hakuri ka ga su Mom ne zasu dawo kaji"
"ok amma sai kin min peck ko kina tafiya" to tace tare da yi d'age ta masa peck a goshi sannan ta fice daga d'akin murmushi sadiq ya saki yana shafa goshinsa ya bita da kallo.

Written by
Salma mas'ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best ★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

67_68

Da misalin karfe 1:00pm flight din su Mom ya sauka Nigeria lokacin har Sadiq ya Isa airport da yaransa kusan mota uku akayi ta tarbar su Mom da Abba a hankali suke saukowa daga matatakalar jirgin Mom na sanye da lace ash mai ratsin pink blue, Abba na sanye da shada brown tasha aiki da dark brown zare yaya jawad da Aunty shukura na baya suma sunsha shigar alfarma tana riqe da babyta, jawahir yana riqe da hannu babansa cikin fara'a suka qaraso gaban motocin.

Cikin sassarfa sadiq ya qarasa ya kai ma Mom hug, dan murmushi ta saki tare da rungume Abba ya murmusa ya ce, "baby wai yaushe zaka girma ne? dake gefe Mom yar dariya tayi 6ata fuska sadiq yayi irin na shagwaba tare da cewa "Danma banyi kuka ba kun tafi kun barni" yar dariya jawad yayi sannan yaran sadiq suka bude masu motocin suka shige.

A tare motocin suka kunno kai gida bala mai gadi ya wangale masu geta washe da baki yana daga masu hannu, dai-dai parking space motocin suka faka suka fara fitowa tun kafin su shigo gida yan gida suka fito kowa ka kalla kasan cike yake da farin ciki, haka jikokin a tare suka shige parlour su ola suka shige da kayan su ciki.

Murna wajan sadiq ba'a magana saboda dama yayi missing din Mom din shi dakuna suka shige matafiyan suka sheqa wanka, sai misalin karfe 3:00pm aka halara a dining area duk wanda ka kalla cikin farin ciki yake, cikin nutsuwa suke lunch din inda jawad da sadiq suke ta zuba hira Aunty bilki da shukura matar jawad, amma duk wannan hira ake hankalin sadiq na Kansas fatu kalle-kalle yake ya ga ta inda fatuha zata fito, abinci ne gabansa amma ya qasa ci saboda yanzu ya saba tare suke ci da fatuha ko tayi feeding din shi loma biyu zuwa uku yayi ya ture abincin.

Bangaran fatuha ko tunda ta kamala aiki cikin ta ke nukurkusa duke take a daki sai kuka take rairawa , qoqarin miqewa take ta kasa saboda cikin ba qaramin kullewa yayi ba bud'e kofar da a kayi yasa fatuha d'ago jajayan idanuwanta Hanan ce ta shigo cikin sauri ta qaraso wajan fatu ganin halin da take ciki ta ce, "fatuha meke damunki? ta fadi a dan tsorace kuka ta kuma saki tana riqe da marata, ganin ba abinda fatuha take cewa yasa Hanan fita lokacin kowa na parlour ana zuba hira Momi tace cikin rawar murya kowa ya waigo "Momi fatuha ba lafiya gata can kwance tana kuka wai cikin ta.! mikewa tsaye sadiq yayi har suna yar rige-rige da Aunty bilki haka Mom ta biyu bayan su suna shiga suma a durkushe suka same ta, sai kuka da take ta fama rairawa Aunty bilki ta matso kusa da ita tare da cewa "Fatuha menene ? cikin kuka-kuka ta ce "Ciki na Momi "
"sorry tashi a kaiki asibiti kinji"
"bana iya tashi" ta fadi tana qara sakin saban kuka Aunty bilki ce ta taimaka mata ta tashi gabaki daya sket din ta ya baci da jini ashe aladace ta fara, "sannu kin ji Aunty bilki ta ce kallon Mom Aunty bilki tayi ta mata nuni da ta kori su sadiq waje aiko haka akayi aka tasa keyar su waje.

"Sannu kinji fatuha girmane ya zo kinji ba wani abu bane, yanzu shiga toilet ki wanke jikin ki sai kin fito na gwada maki yadda ake" d'aga kai fatuha tayi ta shige toilet a duduke Aunty bilki ta fita taba sadiq kudi ya siyo pad ya dawo kallo ya bita da shi tare da cewa, "ki bar kudin bari naje na siyo," murmushi tayi ta maida kudin ta cikin handbag sannan sadiq ya fita ko minti 10 bai yi ba ya dawo ya miqa mata pad din, ta qara komawa lokacin fatuha ta fito duk yadda ake anfani da pad haka Aunty bilki ta gwada ma fatuha tare da bata yan shawarwari na gyara jikinta saboda yanzu ita ba yarinya bace, sosai ta ji dadin jikinta sannan ta bata magani tasha saman bed ta koma ta kwanta bacci ya sure ta Aunty bilki ta fita.

Basu suka bar parlour ba sai da akayi kiran sallah magrib yasa suka wuce masallaci, su kuma matan suka wuce part din Mom basu suka dawo ba sai bayan isha'i jawad ya wuce part din su sadiq ya shige gida, parlour ba kowa bedroom din fatuha ya wuce a hankali ya bud'e kofar kwance ya hango ta saman bed ta dunqule waje daya rife kofar yayi tare da qarasa shigowa, gaban bed din yayi kneeldown a hankali ya kai hannu yana shafa gashin kanta cike da begenta da tausayinta, a hankali ta ware idanuwan ta kan sadiq, kuka ta saka masa mai cike da shagwaba da yarinta, "shhh..! kukan ya Isa haka mana uhm" har lokacin sadiq na sakin tattausan murmushinsa yana shafa gashin kanta kamo hannusa fatu tayi tana qoqarin kai masa marata inda ke mata ciwo sauri kauda hannusa sadiq yayi tare da wayancewa dan ya lura har yanzu fatuha yarinyace shiyasa take haka a hankali ta furta, "mai kyau"
"na'am Sister" cikin wata kasalaliyar murya fatu ta ce, "Zai daina ciwo"
"eh mana gobe da kin tashi zaki ji kin warke kin ji sis" to ta ce masa tare da riqe hannusa tana wasa da su kamar an tsunkunesa ya tashi ya fita fatuha ta bishi da kallo.

Kitchen ya shige ya d'auko mata fresh milk mai sanyi ya dawo bedroom, har yanzu tana yadda ya bar ta tana bin sadiq da ido bata fresh milk din yayi ta kafa kai ta shaye sannan ya mata peck a lunatic tare da yi mata good night ya fice.

Kun san kwanan fatuha 4 tana period tayi wanka Mom ta gwada mata duk yadda ake.
haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi inda yanzu duk gidan ba wanda bai san shaquwar fatuha da sadiq ba, Mom ko in ban da dadi ba abinda take ji dan gani take fatuha alheri ce a rayuwar su, sannan sadiq ya sheda mata zai kai fatuha school kuma tayi na'am da zancan.

Harhad'a kayan ta dana jidda take a trolley saboda yau zasu je wudil, bakin fatu har kunne bayan ta gama had'a kayan tsaf a trolley ta wuce part din sadiq zaune a parlour ta samesa harara ya aika mata tare da kauda kai, dan 6ata fuska fatuha tayi tare da matsawa kusa da sadiq har yana jin saukar numfashinta mai fitar da sayayan kamshi ta ce, "mai kyau.! qara kauda kai yayi langwabe kai fatu tayi cikin siririyar muryarta ta ce, "yi hakuri idan nama laifi" ta miqe zata fita ruqo ta yayi tare da cewa, "shine dan zaki tafi gida shine ko ki leqo da safe? Lumshe ido fatu tayi ta ware su kan sadiq cike da kulawa ta ce, "yi hakuri, ka hada kayan naka?
"nope..!
"to na hada ma"
eh yace a taqaice d'akin ta shige ta hada masa nashi kayan cikin trolley ta fito da su dama shima ya shirya saboda tsabar zumudi ko break fatu ta kasayi haka Mom ta mata shatara na arziki har bakin mota ta rako su, acewarsu kwana biyu zasuyi su dawo saboda ankusa komawa school da sun dawo fatuha zata fara zuwa.

Sannan sadiq ya ja mota suka bar harabar gidan angel sai murna take tare da zuba masu surutu har bacci ya kwashe.

Ko 2 hours basuyi ba suka Isa wudil tunda suka iso fatuha ke bin kauyan da kallo, rayuwar ta da fatsima ta dawo mata sabuwa dai-dai kofar gidan su fatuha sadiq yayi parking har yanzu gidan nan yadda yake sai dai dan tsufa da ya fara sai yar kofar da akasa 6ale murfin mota fatu tayi cikin sauri ta shige gidan.

Inna na zaune saman kujera tayani gulma tana tankad'e, fatuha ta shigo da gudu tana cewa, "Inna..! Inna.! ta fada jikin ta cike zakuwa dagowa da ita inna tayi a dan tsorace washe baki tayi ganin fatuha binta inna tayi da ido dan dai fatuha na diyar ta da tace ba diyar ta bace, saboda girma da haske da ta qara bakin inna bud'e sallamar sadiq ce ta katse mata tunani ta ce, "kinga inna na bar mai kyau waje shida jidda" fita tayi tare da ba sadiq hakuri ta ruqo jidda suka shigo har qasa sadiq ya gaishe da inna, fatuha tayi ma inna bayani aiko inna hannu biyu-biyu ta amshe su dan ta yaba da hankalin sadiq jidda na gani inna ta samu kaka ta maqalewa inna, ta saki jikinta.
Da gudu fatuha ta fita daga gidan sadiq ya fita da ido bata zame ko ina ba sai gidan su fatsima, tana shiga ta shiga kwalla mata kira ba fatsima ba har Gwaggo a rude suka fito saboda jin muryar da suka dad'e suna kewa, da gudu fatsima ta fada cikin fatuha tare da sakin kukan farin ciki, murna wajan fatsima da fatu ba'a magana d'akin ta ja fatuha sai dai yanzu fatsima duk tayi sanyi nan take taba fatuha labari ranar daurin auranta mijin ya rasu, fatuha sai da ta tausaya mata sannan suka koma gida a tare lokacin inna har ta bama Sadiq masauki tare da kayan motsa baki jidda kuma na maqale da ita.

Kun san a tare suka wani da fatsima inda sadiq ke ta fushi fatuha ta barshi shi d'aya, basu suka rabu da fatsima ba sai gab da magrib lokacin Baffa ya dawo shima cike da farin cikin, inda ya dinga jan sadiq a jiki suna taba hira sama-sama, inna ta cika gabansa dafura da nono da tuwan dawa miyar kuka tasha manshanu, sosai sadiq ya saki jiki yaci abincin.

Misalin karfe 8:30pm bayan sun dawo daga masallaci sadiq ya wuce masaukinsa, bayan fatuha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login