Showing 99001 words to 102000 words out of 105783 words

Chapter 34 - Captain Sadiq Book 1 Hausa Novel Complete

18 Jan 2025

719

daukar su  direct gida ya dire su.

         Wanka suka yi sannan fatuha ta shirya cikin 3 quarter pink da t-shirt  milk  ba qaramin kyau fatuha tayi ba, sai gashin kanta da ta sharce ya kwanto har gadon bayan ta fitowa tayi daga bedroom ta shiga kitchen, tuwon shinkafa ta daura miyar Egushi taji naman rago kamshi sai tashi yake sannan ta ahada juice din mangworo dan ba qaramin dadi yake mata ba, kwana biyu nan bayan ta kamala ta dawo dining ta jera sannan ta koma bed ta qara sheqa wanka ta fita ta shirya cikin gown din ta maroon mai stone's dikin ya hauta sosai parking din gashi kanta tayi jin a shigone ya sata waigowa angel ce tsaye bakin kofa, murmushi tayi ta ce, "Mom kinyi kyau" murmushi fatuha tayi ta ce, "thank you my angel" langwabe kai angel tayi ta ce,  "Mom ina so naje gidan Mami yau ne birthday Jamal" smile fatuha tayi ta ce, "To shikenan amma sai kin fara lunch" dan shagwabe fuska tayi ta ce, "Please Mom kin san fa nice best friend tare zamuyi komai"
         "ok naji ina zuwa" wata hadadiyar gown ta curo daga wardrobe tare da gift ta ce, "gashi wannan gown din taki ce ita zaki sa ki tafi" wani irin tsale angel tayi ta rungume fatuha tana mata peck ta ce, "thanks Mom.! Sannan ta zame jikin ta dariya fatuha tayi tare da lakace mata hanci ta ce, "Wannan  gift din kuma na Jamal ne" Godiya ta mata tare da rugawa daki ta shirya girgiza kai fatuha tayi ta cigaba da abinda take, rungumeta ta bayan da akayi yasa fatu lumshe ido  ta ce, "Habibi na" ajiyar zuciya sadiq ya saki ya ce, "My love gabaki daya make up din nan ta gigitani kinyi kyau" smile tayi tare da juyowa suna facing juna a hankali ya kai hannu ya warware parking din....


Written by
        Salma mas'ud nadabo

     Edit by
          Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

                           99_100

1 Month letter

   Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi, inda sadiq ya samu qarin girma dan yanzu haka abuja ya koma da aiki sai weekend yake dawowa kano, fatuha kuwa  shirye-shiryan SSCE suke angel kuma JSSCE, sosai suke samu kulawa wajan sadiq inda yake fifita son su dana kowa, ya ware masu guri na musanman a zuciyarsa haka itama fatuha sosai take bashi kulawa da nuna masa tsantsar soyayya.

    Bangaran su fatima majeed ya sama mata makaranta su fatuha ta fara tun daga jss1, sosai take maida hankali dan ganin taci ma burin ta.

        Basma kuwa Khaleed ya sama mata admission a BUK tana karanta english, sosai take samun kulawa wajan  Khaleed. 

    Dr yakub kuwa soyayya suke zubawa tsakaninsa da  Hanan har manya sun shiga maganar.

      Yauma kamar kullun wainar flower take soyawa wadda kwana biyun nan ta zamar mata jiki, dan ko yini bata iyayi bata ci ba,  har wata yar kiba tayi da haske komai na jikin ta ya ciciko da ka ganta kasan tana jin dadi, hutu ya qara ratsata  rungume ta da akayi ne yasata sakin murmushi kasanewar ta san ba mai yin hakan sai sadiq, waigowa tayi tana kallon sadiq cike da so da kauna sadiq na sanye da kakinsa hannu sa na riqe da qugunta, kallonsa take cike da so ta ce, "Habibi na yaushe ka dawo? Light kiss sadiq ya sakar mata a lips ya ce, "Yanzu nan ji nayi bana iya hakuri rashin ganin ki har sati, gaskayi sweetheart daukarki zanyi mu koma tare, na fara gajiya da zama ni kadai ba mata kamar wani gauro" smile fatuha tayi ta ce, "Bari na kashe gas din nan to" kallon wainar yayi tare da cewa "Me kike da wannan abun? ci tace ataqaice tana qoqarin tura wani cikin bakin ta dan bata iya hakuri, bin ta da kallo sadiq yayi da cewa, "Yaushe kika fara cin wannan dear? d'aga kai sama tayi ta ce, "uhm na dan kwana biyu" ok yace tare da daukar ta suka haura upstairs cakulkuli ya shiga yi mata sai dariya take zubawa dan tsagaitawa yayi yana kallon face nata ya dire ta saman bed ya ce, "Ina Angel? shafa gefan face nashi Fatuha tayi ta ce, "Tana gida wajan  grandma dazu da baba jummai ta zo shine ta bita suka tafi" ok yace yana yawo da hannusa cikin rigarta yana qanqace ido mai cike da sakonni ya fara kiss nata ko ta ko ina kiss juna suke with immense feeling da dukan su suke da shi, yana aika mata da sakonin shi masu zafi haka ita fatuha ganin zasu lola duniyar ma aurata naja masu kofa na fice.

            A  tare suka shige toilet  sukayi wanka, dauke da ita sadiq ya fito yana mata cakulkuli tana dariya ta ce, "Habibina sokake ciki na ya qule ko? ta ida zancan tana mai da numfashi lakace mata hanci sadiq yayi ya dire ta saman sofa ya janyo lotion yana shafa mata itama tana shafa masa sannan suka shirya cikin jeans n t-shirts iri daya jeans blue rigar red da ratsin dark blue n white  wani irin kyau suka zuba masha Allah.

    Parlour suka fito a tare, suka wuce dining area lafiyayan chicken and vegetable stew tayi  da cuscus da miyar kwai , tun kafi sadiq ya fara ci ya lumshe ido saboda kamshi dadi dama gashi fatuha ba baya ba wajan iya abinci, saving nashi ta gama yi sannan ta  fara feeding nasa yana ci yana jin dadi gefe ga natural lemun kankana amsar cokalin yayi ya kai abinci baki fatu ta amsa tana ci zuciyar ta na tashi da gudu ta haura sama tana kakarin amai, binta sadiq yayi a baya toilet ta shige tana kwarara amai kamar zata amayo yan cikin ta gabaki d'aya sadiq ya rude sai tanbayar ta yake lafiya, wanke mata fuska yayi da kuskure mata baki ya d'auke lamo tayi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya ba abinda ke mata dadi kamar turaran dake jikinsa kamar karya sauke ta, saman bed ya dire ta ya koma toilet ya wanke inda tayi aman, ya wanke toilet din ya fito gefan bed ya dawo ya zauna yana ta6a goshin ta ya ce, "sweetheart sannu" yauwa fatu tace cike da kasala, mirginowa tayi ta lafe jikinsa tana shinshinar kamshin turaransa tayi lamo, haka sadiq ya dinga jera mata sannu  wayarsa ya dauka dake saman bedside drawer ya kira Dr yakub ko mintin 10 ba'ayi ba yazo, sadiq ya masa iso har bedroom har lokacin fatu na kwance tana rawar dari tana qudindine cikin blanket, sannu Dr yakub ya mata kana ya mata yan gwaje-gwaje tanbayar ta yayi ya ce, "me dame ke damun ki kamar mai dame kike ji? cikin sanyin murya Fatuha ta ce, "Zazzabi ciwo kai da yawan tashin zuciya, tun ba yau ba" rubuce-rubuce Dr yakub yayi ya bata wata yar kwalba ya ce, Ta shiga toilet tayi fitsari a cikinta  ta kawo masa a hankali ta tashi ta shiga toilet sadiq dai na gefe sai sannu yake mata, ko 5 minutes batayi ba ta fito  amsar kwalbar yayi yasa cikin jakar aikin shi ita kuma Fatuha ta koma ta kwanta smile yayi yana kallon sadiq ya ce, "Insha Allah zata samu sauki indai abinda nake tunani ne sai dai muce Allah ya raba lafiya, amma for now sai mun fara yin test tukun" murmushi ne ya subuce ma sadiq  da fatan Allah yasa abinda shima yake tunanine .

         Har bakin mota ya raka Dr yakub sannan ya juyo gida, ko da ya dawo kwance ya same ta yadda ya barta, saman bed din shima ya hau tare da taba goshin ta cikin shagwaba ta ce, "Habibina"
        "na'am sweetheart" lumshe ido tayi ta ce, "Zanci irin wannan abincin dana fara ci randa na zo birni" kallon ta sadiq ya shiga yi yau kusan shekara nawa shi yanzu aka tare shi da bindiga bai iya tuna me akayi ranar, cikin sanyin murya sadiq ya ce, "Sweetheart kiyi hakuri ki fadi wani abun, amma wannan bana iya tuna ko me akayi, ko kina iya tunawa sai a maki?  d'aga kai tayi ya ce "To fadi min"
     "shinkafa da miya da kosulo da farfesun yan'ciki" to sadiq ya ce mata tare da yi mata peck ya fita,

      Kitchen ya shiga ya samu baba asabe na goge-goge gaishe ta yayi a taqaice ta amsa ya fada mata abinda zata ma fatuha to tace masa, jiki na bari ta fara aikin, shi kuma ya koma bedroom sai zuba masa rigima fatu take, ko da baba asabe ta gama ta kai dining area ta jera, dauko Fatuha sadiq yayi ya kawota dining ya daurata saman cinyarsa  ya fara saving nata a hankali ya nufo da cokalin bakin ta tunkan ya kai bakin ta zuciyarta ta fara tashi da  sauri ta miqe riqe ta sadiq yayi yana kuma tanbayar ta kafin ya ida magana ta wanke shi da amai  langwabe kai sadiq yayi ya ce, "Sorry my wife" kuka ta saka masa lallashita ya shiga yi  ya dauke ta suka koma bedroom bai dire ta ko ina ba sai cikin toilet, wanka su kayi a tare sannan yasa bathrobe ya nado Fatuha cikin towel sai kuka take masa yana lallashinta kwantar da ita yayi yana qoqari dauko lotion wayarsa ta hau ruri a hankali ya kai hannu ya dauka suna Dr yakub ne ya baiyana a jikin scream din cikin sauri ya dauka tare da karawa a kunne, "hello Dr yakub" daga dayan bangaran Dr yakub ya ce, "albishirin ka" dan tsaki sadiq yaja ya ce, "me kuma hakan ina fama da mara lafiya kana kirana ka min irin wannan kidding din"
         "toh shikenan tunda baka son sanin maganin" dan smile sadiq yayi ya ce, "Goro.!
        "yauwa ko kai fa amma fa sai ka bani Goran albishir"  to sadiq yace yana mai qaguwa yaji mai Dr yakub zaice dariyar shaqiyanci Dr yayi ya ce, "angon qauri kasha kamshi" Dr ya fada yana dariyar shaqiyanci ya ce, "congratulation madam na da juna biyu na wata 1," wani irin lallausan murmushi sadiq ya saki ya ce "Wai da gaske kake?" ya ce, "eh mana,!
        "gaskiya naji dadin wannan albishir,"
        "toh nima a bani goran albishir dina" dariya sadiq ya saki tare da cewa, "na dau nauyin tafiyar ku zuwa honeymoon kowace qasa kuke so a duniya zan  baku kudin kashe wa" wata irin dariya Dr yakub ya fashe da ita ya ce, "Wai da gaske kake? ya ce, "eh mana ana daura maku aure da Hanan zaka ji alat"
   "Aiko mun gode sosai anjima ka shigo ka amshi magungunata" to sadiq yace a takaice sukayi sallama ya kashe wayar juyowa sadiq yayi ya sakar wa fatuha da lallausan murmushi itama smile tayi lotion ya shafa mata tare da  samata kaya sannan shima ya shirya kallon ta yake cike da so ya daura hannusa saman cikin ta ya ce, "My love yanzu nan akwai baby na ko" kallon sa Fatuha take tace "Wani baby kuma? ya ce, "babyn mu mana da zaki haifa mana soon ni da angle" ganin yarda fatu tayi kicin-kicin da rai yasa sadiq cewa, "ko baki so ki haihune uhm" ya fada yana kallonta kuka ta saki ta tashi daga jikin sadiq ta ce, "Allah bana so yanzu ya zanyi da exam da ciki tun yanzu yana bani wahala bale kuma idan na fara exam ya zanyi da shi" kuka ta saki tana cewa, "Allah bana so  a cire min shi a kai kasuwa" jawo ta sadiq yayi jikinsa ya ce, "Fatuha yanzu jinina ne baki so? ya fada yana kallon ta "ni ban ce bana son jinin ka ba, amma ai matsamin zaiyi shikenan haka zan dinga  shiga cikin su Nana da ciki" ta ida zancan tana kuka ta cigaba da cewa, "kalli ka gani ko fa yau cikin ya hanani cin abinci, ya hanani duk wata walwala"
        "yi hakuri Fatuha ai duk wannan abun na dan lokaci ne, zai daina" tsale tayi ta dire ita bata so sai dai a zubar har  ta kai ga ran sadiq ya fara baci qoqarin fita yake daga dakin ya ce, "ki shirya gobe a zubar da cikin, ni kuma na  auro wadda zata iya zama da ciki na koma a inane" kuka fatuha ta saki tana cewa, "Allah ba mai shigo min gida ni kadai ke da kai wallahi," ta ida zancan tana qara sakin kuka, abinma dariya yaso ya ba ma sadiq ganin duk tabi ta rude yasa sadiq ya ce mata ya fasa amma sai idan zata zauna da cikin sa amincewa tayi ba shiri tare da juya masa baya tana qara sautin kukan ta.

       Jawo ta sadiq yayi yana lallashin ta ya ce, "ai na ce na fasa tunda kina so yanzu" lamo tayi a jikinsa cikin cool voice ya ce, "My love me zaki ci? cikin shagwaba ta ce, "Dan wake" bata fuska sadiq yayi ya ce, "gaskiya babyna ba zaici mai da yaji ba," kuka ta fara shirin samasa ganin ba yadda zaiyi  haka ya fada ma baba asabe tayi mata dan wake ba laifi taci dan wakyan sosai da akayi har da side plate.

        Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda fatuha ke samun kulawa sai dai cikin tana mai laulayi ne sosai, kusan a tare suke laulayi da su fatima amma sai dai duk ta fiso wahala ga wani shegyan kwadayi da ya samata angel ko da taji Mom na da ciki murna ba'a magana Mom za tayi mata qani ko qanwa ta samu abokiyar fira.

      Shirye-shirye ake sosai na bikin Hanan dan yau duk kusan sun halara family house saboda yau ne za'ayi kamu, bayan sun gama exam din mathematics a school driver ya zo daukar fatuha bai zame da ita ko ina ba sai family house, a gajiye likis ta dawo yana sauke ta tashigo gida umma ce ta tare ta, ta  hada mata ruwan wanka ta shiga toilet ta fito kasancewar ansan yadda cikin ta yake farfesun kifi Mom ta mata mai dadi tana fitowa ta iske kayanta saman bed after dress ce ta zura sannan ta fito parlour tana fitowa ta samu su fatima suna ta kwasar  nasu farfesun, kwabe fuska fatu tayi tana kallon Mom da itama kallon ta take dariya daki'n ya dauka Mom ta jawo ta jikinta tare da bude mata kola ta fara feeding nata tana amsa sai janta suke ta fiye raki harara da dinga aika masu Mom ta ce, "taje tayi din kuma din ai kawai shuru kukeyi da baku rakin kuma raki ba'a sani sai ranar juyewa" ammi dariya tayi ta ce, "kai hauwa kina fama da surukan nan naki, kina shan drama" ya zanyi ammi, komai cikin walwala da jin dadi da soyayya suke dan sun samu gidan maza jan nasu ya zama kamar gidan iyayan su dan yanzu sunfi mazan ma samun qugun zama har qorafi mazan keyi saboda banbanci da ake masu anfifita matan a kansu musanman yanzu da suke da juna biyu..
Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

    
                      101_102

     Godiya ta musanman gare ku REAL-HAUSA-FULANI-WRITERS-FORUM wannan shafin naku ne, ana mugun tare irin   sosai din nan Allah ya bar zuminci Allah ya qara hada kanmu

          Qoqarin sa rigar ashobenta  take da mami ta dinka masu, amma sket din ya kasa shiga saboda hips dinta daya qaru, lagwabe kai tayi tana qara tura skirt din tana jin kamar tayi kuka jin an bude kofa ya sata waigowa sadiq ne ya shigo dakin, kuka ta fara rera masa tunkan ya qaraso gareta, qarasowa sadiq yayi da sauri ya dago da fuskar fatu da tayi shafe-shafe da hawaye ya ce, "My wife me ya saki kuka uhm? wani kukan ta qara saki ta ce, "Habibina ashobe na ya kasa shiga ta tun dazu nake jan sket din yaki shiga" ta ida zancan tana sa masa kuka jawo ta jikinsa yayi ya zaunar da ita saman bed ya ce, "Wannan ne matsalar?" d'aga kai tayi alama eh, "toh shikenan bani kayan na gani" amsar kayan sadiq yayi ya duba Allah ya taimakesa akwai space,  zaunawa yayi ya warware skirt din da rigar sannan ya miqa mata tasa maqale qafa tayi ita bata iya sa kayan hannu ta nauyi yake mata, lakace mata hanci sadiq yayi ya ce, "My love yau baby  na rigima ya saki ko? turo baki tayi gaba cike da shagwaba kiss nata sadiq ya fara ko ta ko ina ganin zai zarce yasa fatu samasa kuka, smile yayi ya ce, "sorry.! sannan yasa mata kayan shima shirya cikin manyan kaya sannan ya jata suka fito ko da suka fito lokacin su fatima sun shirya ita kadai suke jira ta fito, tana fitowa fatima ta ce, "Sai muje ko?  ta ida zancan tana aika mata harara wasa murguda mata baki fatu tayi sannan suka fice sadiq kuma ya wuce wajan angwayan saboda kamun ba maza.

          Suna shigewa mota fatima ta ce, "Ke haka ake? daga shiga sa kaya saiki maqale da miji"
      "kam me kika daukan to nayi din" ta fada tana aika ma fatima hararar wasa Fatima ta ce, "abin da kike tunani" dariya suka kwashe da ita a tare Fatima ta ce, "wannan cikin kamar ya dawo maki da halin ki na baya" dariya fatu ta saki ta ce, "har kin sa na tuna san da muke zuwa gonar mai gari.! dariya suka kuma saki suna tuno yarintar su mai cike da drama  kallon juna suka yi tare da cewa, "Allah mun gode maka bamu ta6a tunanin ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login