Showing 81001 words to 84000 words out of 105783 words
da carpet din hannu ta, a hankali majeed yasa hannu ya d'ago da fuskarta, kallon fuskar majeed yake cikin so da kauna, cikin sanyin murya ya ce, "My love me ya saki kuka?" kamar jira take ya tanbayeta ta fashe masa da saban kuka, rungume ta majeed yayi yana lallashinta ya samun daya daga cikin kujerin wajan suka zauna, daura kanta yayi a kafadarsa yana shafa mata bayanta a hankali cikin sanyi murya ya ce "My love bana so naga kina kuka, idan kina kuka sai naji nima kamar nayi, meke damun ki? ki fada min koma menene zan samamaki indai zai saki farin ciki..! dagowa fatuha tayi ta kallesa, a cikin azuciyar ta ta ce "Ba komai zakamin ba, ila ka ce ka fasa aure na! ka barni da muradin raina da zabin zuciyata, abinda nake son gani safe rana dare wanda bana gajiya da ganinsa, wanda bana gajiya da saurarasa, wanda na tsunduma kogin son sa tun kafin na san menene so..! rushewa da sabon kuka fatu tayi gabaki daya majeed rudewa yayi da yanayi fatuha, sai aikin lallashin ta yake dakyar ya samu ta daina kuka sai faman ajiyar zuciya da take, daura kanta yayi saman kafadarshi yana wasa da yan yatsun ta masu laushi sun dau mintina suna a haka sannan fatuha ta zame kanta daga kafadarsa tana qoqarin tashi, d'ago fuskarta yayi yasa lallausan hannusa yana goge mata hawayan ta tare da yi mata peck a goshi runtse ido fatuha tayi tana jin wani irin suya da zuciyarta kema ta mai cike da tsanar majeed, hannunta ya riqe suka miqe a tare sannan ya amshi dadumar hannuta a hankali suka bude kofar d'akin suka shigo, har yanzu sadiq na kwance amma ba bacci yake ba, Basma na gefansa tana zuba masa iyayi yana saurara, shigowar su fatuha ce tasa shi d'an dagowa ya jingina idanuwasa ne suka sauka kan hannun fatuha cikin na majeed, wani irin b'akin ciki ne ya taso masa tabbas wannan ba jinya aka zo ba zuwa akayi a qarasa shi, lumshe ido yayi dan baya iya jurewa ganin baki'n cikin, zame hannunta fatuha tayi tare da zama tana facing sadiq.
Majeed qarasawa yayi wajan sadiq tare da shafa sumar kansa ya ce, "Baby.! bude idanu sadiq yayi tare da sakin murmushi riqe hannunsa majeed yayi ya zauna, ya aika ma sadiq harara wasa yayi tare da cewa, "Shine baka da lafiya kakasa fada min baby? wai me yasa kakemin haka? abu na damun ka baka fada min saboda ban kai matsayin ba ko? ya fada yana lagwabe kai dan shagwabe, fuska sadiq yayi ya ce "Sorry banyi tunanin fever ya kai haka ba, nayi tunanin har sai naje Lagos nasha magani"
"uhm please next time karka sake haka,"
"tam.! yace tare da tsinkulin majeed ganin yarda ya shiga damuwa murmushi ya saki ya ce, "kaci abinci?
"no.!
"me yasa baka jin yunwa ne? so kake ciwo ya cigaba da riqe min kai ko? plate majeed ya jawo ya zuba abinci shinkafa da miya tasha naman rago a hankali ya shiga feeding sadiq yana amsa cike da son dan uwa na shi yana ci yana jan shi da hira mai cike da nishadi, dariya sadiq yake can kuma yayi shuru yana bin majeed da kallo, sosai jikinsa yayi sanyi, murmushi majeed yayi tare da aje plate ya ce "Kallan fa?" smile Sadiq yayi ya ce "Ba komai" juyawa majeed yayi ya kalli fatuha ya ce "Sweetheart ku tashi muje na saukeku gida" ok fatuha tace tare da tamiqewa, Basma ko peck ta ma sadiq tare da masa sai da safe ta fita, hadiyar zuciya ne kadai fatuha ba tayi ba sannan suka fice har sun kai bakin kofar mota, fatuha ta ce "Tayi mantuwa" da sauri ta koma dakin lokacin idanuwasa sadiq na lumshe.
A hankali fatuha ta qaraso ta shafa sumar kansa, bude ido yayi yana kallon ta ya ce "Fatuha kin dawo ne ki kulla da uncle?" murmushi ta saki ta ce "Mantuwa nayi uhm"
"mekika manta? peck ta masa a goshi sannan ta ce "Kaga abinda na manta" smile sadiq ya saki tare da jawo ta ta fado saman qirjinsa har tana jin bugun zuciyar shi, sasanyar ajiyar zuciya suka saki a tare suka lumshe ido suka ware su kan juna su, lips din ta sadiq yabi da kallo a hankali ya daura finger dinsa saman lips din fatuha, kallon shi take me cike da kauna haka shima tafiyar tsutsa sadiq ya dingayi mata a lips lumshe ido fatu tayi jikinta ya mutu mudus lokaci daya tana sauke numfashi a hankali wanda ya hadasa ma sadiq mutuwar jiki, yana mai cigaba da yawo da finger dinsa a lips dinta zuwa dokin wuyanta riqe hannusa fatu tayi tare da d'an cizan shi dariya fatuha ta saki tana masa gwalo tana wani juya ido, dan shagwabe fuska yayi ya koma kamar baby face yana bin fatu da kallonsa mai qara tsundumata duniyar son sa cikin sanyi murya fatu ta furta, "sorry..! ta riqe kunnanta, ja mata hanci sadiq yayi tare da yi mata peck a kumatu, fatu na jin yarda karan hancinsa ke gogar kumatunta mai cike da wani salo mai tafiya da nutsuwa, dakyar ta iya jawo nutsuwar ta furta, "uhm uncle bari na tafi nabar mutane na jirana a waje" da sauri ta mike daga saman bed din zata fice riqe hannun ta sadiq yayi lumshe ido fatu tayi tana sauke ajiyar zuciya da sauri-sauri wasu hawaye na sulalo mata, ta waigo ba shiri tana kallon sadiq dake binta da kallo itama shi take kallo ya kankance ido mai cike da ma'anoni daban-daban zame hannuta tayi sannan tasa kai ta fita.
Tana fita taci qaro da majeed gabanta ne ya yanke ya fadi lokaci daya, ta dan da burce kallon ta kawai majeed yake ya kasa kau da idon sa bai ce komai ba suka shige mota suka bar asibitin.
Kwanan sadiq uku asibiti aka sallame shi, sosai ya samu kulawa wajan yan'uwan shi tare da soyayyar su, ya murmure Alhamdulillah.
Zaune suke a dining area suna lunch har da Basma saboda yanzu ta dawo gidan da zama angel na gefe tana zubama sadiq shagwaba sai ya kai ta shan ice cream, Mom sai tsiya take mata, Basma ce ta kalli sadiq tare da jefa masa kallan so murmushi ya mata wanda iyakar shi la66an shi fatuha na zaune tana lura da hakan gabaki daya annurin ta ya dauke dan ji take ma abincin ya isheta, ture plate din tayi tare da tashi ta barwurin kallo sadiq ya bita da shi tana shiga bedroom ta fada saman bed tare da sakin kuka, sai da taci kuka ta gaji sannan ta bude bedside drawer wani album ta curo tana kallo pictures din tane ita da angel da sadiq tana kallo tana dariya da murmushi mai kuka. haka ta dinga kallan pictures din har bacci ya dauke ta.
Bayan sun gama lunch suka koma parlour suna kallo Basma sai jan sadiq take da labari tun bai biya mata har ya dan fara sakar mata, amma duk bayan mintina sai ya kalli bedroom din fatuha sallamar majeed ce ta katse masa tunani, da sauri Basma ta qarasa wajan shi ta ce, "bros I miss you?
"miss u more sis"
"ya su Umma" ta fada
"suna nan lafiya lau," dan bata fuska majeed yayi ya ce, "matsala ta dake shegyan surutu ko bari bakiyi na huta kin fara tanbayata, haka zaki dinga yima sadiq? murmushi ta saki tare da rufe fuskarta ta6e baki sadiq yayi tare da kauda kai, qarasowa majeed yayi ya zauna kusa da sadiq suka gaisa, sannan ya ce, "ina my love? wani irin kishi ne ya rufe sadiq shuru yayi bai tanka ba Basma cikin zakuwa ta ce, "tana bedroom.! zunbur ya miqe ya shige a hankali ya bude kofar kwance ya hango ta saman bed smile yayi tare da qarasowa, bacci take rungume da album a hankali yasa hannu ya zare album din ya bude album din yana kallon picture dinta da sadiq ya fara gani, kanta na bisa kafadar sadiq suna dariya ya dade yana kallon picture din, sannan ya bude d'aya shafin ya gansu su uku cikin picture din suna shan ice cream haka majeed ya dinga bin pictures din yana kallo musanman in da yaga wanda fatuha da sadiq sukayi picture din har mamakin irin shaquwar da sukayi yake bai taba tunanin shaquwar su har ta kai haka ba, aje album din yayi yana qoqarin yaga sadiq bakin kofa fuskarsa a ha...
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R
*Email* [email protected]
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
85_86
Murmushi sadiq yayi tare da qarasowa ya dauki album din da majeed ya aje, ya bud'e sannan shima ya aje tare da kallon bed fatuha na kwance gashin kanta ya baje a bed, take kishi ya lullu6e sadiq qoqarin fita yake majeed shima ya miqe suka fita a tare, ko da suka fito Mom na zaune tana kallo Basma na gefe angel na assignment gaishe ta majeed yayi tare da yi mata peck cikin fara'a ta amsa tana tanbayarsa ya su Umma ya ce "Suna lafiya lau" sannan suka fita da sadiq.
Basu zame ko ina ba sai family house, bangaran Ammi suka fara shiga da sallama suka shiga Ammi na zaune tana kallo washe da baki ta amsa tana cewa, "A'a wanake gani?" ta fada tana gyara dankwalin kanta ta ce, "dan tselankwa na dauk'a baka zuwa ai" zama su sadiq su kayi saman two sitar suna murmushi ta ce, "mai gida ai na dauka baka zuwa godiya? mu d'au zunkudediyar budurwa mu baka amma ko leqe? yar dariya sadiq yayi wanda iya karta la66ansa dan shi a gaskiya har mantawa yake da Basma a matsayin matar da zai aure ya ke, Ammi ce ta katse masu zance da cewa, "bari na kawo maku fura,"
"to Ammi amma dai taji nono?
"ina ruwan ka da abinda zata ji? nifa dan mai gida nake badan kai ba, kai har gajiya nake da ganin ka wallahi" dariya majeed ya saki ya ce "naji ba komai ai danayi aure kin bar ganina wallahi," wani miyau mai daci sadiq ya hadeye tare da kallon majeed ta qasan ido Ammi ta katse masa tunani da cewa, "kai dai ka sani" sannan Ammi ta shige kitchen ta dauko masu fura a fridge tasha nono ta aje masu, sun sha sosai sannan suka dinga zuba fira suna cikin hira Alhaji babba ya shigo shima aka dasa da shi, sai kusan yama likis sannan suka wuce part din Umma inda umma ta dinga nan da sadiq dama can dan gaban goshin tane bale kuma yanzu da zai auri auta sai da suka sha fira sosai kiran sallah magrib ne ya tashe su dauro alwala su kayi suka wuce masallaci.
Bangaran su fatuha ko tana tashi wanka tayi, sannan ta shafa lotion mai kamshi ta zura after dress black ta mata kyau sosai sai dai tayi yar rama kad'an saboda tunani, parlour ta fito ta iske Basma na kallo cikin fara'a ta qaraso ta zauna kusa da ita, yar hira suka ta6a sama-sama sannan suka shige kitchen kusan a tare suke aikin, inda baba jummai ke ta bin fatuha da kallo saboda gabaki daya yanzu fatuha bata walwala ga wata yar rama da tayi, haka dai suka dinga aikin bayan sun kamala Basma da rabi'a suka kwashe kulolin suka kai dining area, a lokacin ne baba jummai ta ja fatuha gefe tana mata yar na siha kan tayi hakuri kar ta jama kanta ciwo ta rage tunani, dan ta lura kwana biyu nan ko abinci bata ci, kuka tasa mata lallashin ta baba ta dinga yi har ta samu tayi shuru tana qoqarin goge hawayanta Basma ta shigo kallon ta tayi ta ce, "Fatuha me ya saki kuka?" murmushi fatuha ta qakaro wanda iya karshi la66an ta ta ce, "Albasa ce ta shigar min ido"
"eyya sorry ke je ki wanke fuskar" to tace tare da fita daga kitchen din, ko da ta shiga toilet sana'ar ta cigaba wato kuka sai da tayi san ranta ta fito kaya ta canza tasa riga da skirt na atamfa ash mai ratsin pink masha Allah kayan sun mata kyau, sai dauri da tayi kasancewa hutu take ko sallah ba tayi ba.
fitowarta daga daki yayi dai-dai da shigowar su majeed mutuwar tsaye majeed yayi yana binta da kallo dan ba qaramin kyau ta masa ba, son ta da kaunarta ne ya qara lullu6e majeed, haka shima sadiq ji yake kamar yaje yayi hug nata saboda ba qaramin kyau ta masa ba cikin sauri-sauri majeed ya qarasa wajanta yana sakin smile ya ce, "My love kinyi kyau" murmushi fatuha tayi wanda iya karshi la66an ta sadiq na tsaye bakin kofa dan ko qarasowa ya kasa, kamar zai rungume ta majeed yayi yana magana can qasan maqoshi yarda futu kad'ai zata iya ji "My love kullun qara kyau kike, ji nake kamar na jawo lokacin auran nan namu" sadiq dake gefe sai hadiyar bakin ciki yake dan har ya fara ganin jiri a hankali yake jefa kafarsa da bai san inda zai wurga ta ba, har ya samu ya haura upstairs tun kan ya Isa bedroom ya fara tari da bin bango ya isa toilet, tari kawai yake tare da jini zamewa yayi a qasan toilet yana mai da numfashi yana cire buttom din rigarsa dan ya samu iska ya dau mintina goma yana a haka, a hankali ya ja jiki ya koma bedroom kayan jikinsa ya rage yasa jallabiya ya bude bedside drowe ya ciro magani ya sha tare da shigewa blanket saboda fever dake damun shi a yanzu, lumshe ido yayi wasu hawaye masu zafi daya na bin daya.
Sakin ta majeed yayi tare da yi mata peck a goshi kallon kofa tayi wayam ba sadiq ba alama, haka shima majeed, "oh sweetheart kin ga kin rudani da yawa ko sadiq na manta da shi" ya fada yana dan langwabe kai, fatuha da ta cika taf dan qiris take jira ta fashe daurewa kawai take ta ce, "Ai sai ka bishi..! ta fada tana qaqorin shigewa bedroom hannun ta ya riqe yana sakin murmushi ya dawo ya rungume ta ta baya rintse ido tayi tana jin wata tsanar shi cikin rawar muryar ta ce "Majeed please ka bari? so kake su Mom su fito su ganmu haka? ta fada tana qoqarin kwace kanta majeed ya ce, "uhm to me dan sun ganmu how many day's ya rage ki zama tawa"
"naji duk da haka ai da kunya" fada tana sa masa kuka sakin ta yayi yana bata hakuri ko sauraran shi ba tayi ba ta shige daki tare da fadawa saman bed ta saki kuka.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu na farin ciki wasu na bakin ciki, inda ciwo keta cin sadiq dan yanzu sosai yake zubar da jini duk da yana shan magani da zai sa yaji sauki, amma abun sai gaba yake dan har ya fara fida rai da duniya.
Cikin kayan ta na uniform take shiri duk da jikin ta ba kwari, bayan ta kamala ta fito su Mom na zaune suna break cikin nutsuwa ta gaishe su ta zauna ta jawo cup zata hada tea, kamshi turaran da ya doki hanci tane ya sata waigowa, sadiq ne sanye cikin uniform dinsa masha Allah yayi kyau sai yar rama da yayi gaishe da Mom yayi tare da yi mata peck ya ja kujera ya zauna, cup fatuha ta jawo zata hada masa tea, da murmushi Basma ta mika hannuta amshi cup din dake hannu fatu ta ce "Fatuha barshi kawai na hada masa da kai na, tunda ke kinga school zaku tafi karku makara" miqa mata cup din fatu tayi jiki ba kwari ta zauna tana juya nata tea din idanuwan ta taf da kwalla, taki yarda ta dago idanuwanta? kuma taki shan tea din, tana gama had'a tea din ta miqo wa sadiq yana miqa hannu zai amsa ya saki cup din ya fadi tea din ya bare a dining area dagowa fatuha tayi saboda tea din ya zuba, kallon sadiq take shima ita yake kallo lallausan murmushi ya sakar mata Basma da duk ta rud'a ta ce, "yaya sadiq tea din bai bata maka kaya ba ko?
"Eh Basma"
"ok bari na hada ma wani"
"barshi kawai nama koshi" dan 6ata fuska tayi, tana kallonsa ta ce "Yanzu baza ka ci komai ba? mom ce ta ce, "Kyale shi indai wannan ne ya saba da haka" to kawai Basma tace tare da fara tatare inda tea din ya zube.
Kasancewar yau majeed be zo daukar fatuha ba yasa sadiq ne ya sauke su a makaranta, duk da ba wata magana sukayi ma juna ba amma hakan ba qaramin dadi ya masu ba, basuki su dawa ma a haka ba.
2weeks letter
Biki ya matso gadan-gadan yasa Mom ta samama amaran mai gyaran jiki, gyara suke sha sosai dan har sun fara murjewa da kyau da sheki dan yanzu Mom ko bari batayi su sadiq su ga amaran.
Tunda bikin ya matso kullun sadiq da fever yake kwana yana tashi duk ya wani fige ya koma Kala tausayi kamar ana dibarsa ana miya, gashi yaqi zuwa Dr yakub ya duba shi har yayi mita ya gaji, majeed yayi tanbayar duniyar nan sadiq ya fada masa damuwarsa amma fir yaki sai dai ya ce, ba komai.
Majeed ne ya shigo bedroom din sadiq, sadiq na zaune saman sofa ya jingina ban da tunani ba abinda yake, dafa