Showing 105001 words to 105783 words out of 105783 words
amsawa tayi atakaice ta shige kitchen Aslam zama yayi saman cinyar ta yana zuba mata surutu, cakulkuli ta shiga yi masa yana dariya tsagaitawa tayi ta ce "Ina yaya?, daga kai yayi cikin tsamin murya ya ce, "yaya na bacci" ok fatuha tace tare da tashi ta shige bedroom bata zame ko ina ba sai toilet ta sheqa wanka ta fito ta gabatar da salolin da ake bin ta, turo kofar da akayi ne ya sata smile angel ce tsaye bakin kofar sanye da jean n t-shirt ta ce, "mom sannu da zuwa,"
"yauwa" fatuha tace qarasowa tayi ta ce, "Mom ki zo muyi lunch tun dazu na dawo daga school naqi cin komai sai kin dawo," murmushi fatuha tayi ta ce " Karki qara barin kanki da yunwa kinji angel? d'aga kai tayi ta ce, "ai nasha fresh milk"
"ok muje" dining area suka wuce lafiyayan doya ce da miya tasha kaji da naman rago sai kamshi ke tashi sosai fatuha taci abincin dan wani irin san doya take kwanan kusan kullun sai ta ci ga wani iri ci da take yanzu kamar runbu da san bacci har mamaki kanta take, bayan su kamala cin abinci suka dawo parlour suna kallo Aslam sai wasa yake da kayan parlour komai ya gani abin wasa ne da an hanasa sai kuka yace zai fada ma daddy, yanzu ma haka 6ana yake fatuha jawo hannuwansa ta hada biyu tana masa fada kuka ya sa mata kamar ta daura masa wuka sadiq da shigowarsa yanzu kenan harara ya aika ma fatuha ya qaraso ya dauki Aslam ya wuce da shi bedroom nasa, ta6e baki fatuha tayi tare da bin bayansa ko kallon ta baiyi ba sai ma wasa da yake ma Aslam yana dariya miqa hannu tayi ya bata Aslam ya wurga mata harara ya ce, "Baki shi zanyi ki ida kasheshi ko me? ya ida zancan yana qara rungume Aslam dariya fatuha tayi ta ce "Dama ka bani shi saboda yanzu zai fara daura ma headache, yaron nan baya ji sam"
"hmm zakiyi bayani na kama ki kina dukar min d'a" jawo ta Sadiq yayi ta fada saman bed yana kai mata naushin wasa shi da Aslam dariya take sosai rungume sadiq tayi a hankali yake shafa bayan ta ya ce, "I miss you love" zame jikin ta tayi tare da kashe masa ido ta dauki Aslam ta maida shi parlour kana ta dawo taimaka ma sadiq ya rage kayansa suka shige toilet maqale da juna suka fito suna shan soyayya.
4 Years letter
Wata kyayakwar yarinya ce wadda baza ta wuce 4 years ba ta shigo parlour tana kuka ta fada jikin sadiq dake zaune saman three siter yana karanta newspaper idanusa manne da farin glass yana sanye cikin English wears ya qara kyau ya murje hutu ya zauna masa ya qara girma, cikin shasheqar kuka ta ce, "Daddy ka ga yaya Aslam ya amshe min baby wasa na ko" daukar ta sadiq yayi yana lallashita ya ce, "sorry little Mom, rabu da shi zan siya maki sabi okey" fatuha da fitowar daga kitchen kenan jin kukan little Mom, tana sanye cikin green lace tasha kyau har ta gaji ta ce, "Wai me yasa Aslam baya jin magana ne, duk wani neman fita ya iya? zai shigo gidan ya same ni ai sorry dear" yar yarinyar dake jiki sadiq sunan ta kausar amma suna kiran ta da little Mom saboda sunan margayiya kausar aka saka mata sosai fatuha ke ji da ita saboda ita da kanta tasa sadiq yasa sunan, yanzu haka sun koma abuja da zama fatuha ta gama karatun ta aiki take angel kuma na university.
Kasancewar lokacin lunch yayi kowa ya halara dining area suna lunch suna dariya, sadiq ne ya curo wayarsa dake cikin aljihu yace selfy su duka suka matso tare da saki murmushi happy family life.
Tamatubihamdulillah
A nan na kawo karshan wannan littafi nawa mai suna captain sadiq, ina mai miqa godiya ga dinbin masoyan wannan littafi.
Abinda muka fada dai-dai da wanda bamu fada dai-dai ba Allah ya yafe mana.
Ina godiya irin sosai din nan ga Aunty Raheenat da ta bani goyan baya wajan rubuta wannan labarin tare damin good editing dan ya qayatar da masoya wannan novel, ina miqa godiya ta irin sosai din nan muna mugun tare.
Gamai buqatar littafi na ga number ta kamar haka 07063683025
Gargadi: Ni Salma Mas'ud Nadabo ban amince kowa yayi anfani da littafina Captain Sadiq tako wacce Siga ba, duk wadda tayi\Kayi na bar mutum da rabill izati dan haka a kiyaye.
Taku har kullun salma mas'ud nadabo