Showing 33001 words to 36000 words out of 145791 words

Chapter 12 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

309

kafin nan ka tara wani abu"


" A'a Farida, idan na yi haka na ci amanar mahaifin ki. Duk cikin 'ya'ya na ba wadda ta wuce shekara ashirin na aurar da ita, Maijiddah ce ma har ta kai ishirin Win. Idan ba ?addara da ta faWa miki ba ai da tun shekaru uku da su ka wuce anyi bikin ki"

"Baffa Allah ba matsala ka bari irin watan uku na wata shekara sai ayi kafin nan komai ya dawo normal"

"A'a Farida ko da duka gonakaina zan sayar dan na samu kuWin yi miki aure zan sayar. Ai idan na bari wata shekara sai duniya ta zageni. Idan ba su iyayen yaron sun ce bai gama shiryawa ba ai da tareda Maijiddan zan haWaki"

"Baffa dai" ta faWa kaman za ta yi kuka.

"Tashi ki je ki kwanta. Allah ya kaimu watan December"

"Baffa nikam..."

"Tashi na ce" ya faWa da Wan ?arfi.

Ta tashi tana guna-guni ta bar falon.

Sai da ta fita Baffa ya ?ara godewa Allah domin halin Salihu na kyauta kam Farida ta Wauko, dan lokacin yana raye bashida rowa ko kaWan, zai iya bayar da abu shi ya rasa kuma hakan bai dame shi ba...

................


Lagos


Ranan Monday da safe ya isa Lagos, kai tsaye office ya wuce kasancewa dama shi Waya ya je ya bar su Alizah a gidan ma?ocin sa kuma abokin aikin sa Mr AbdulRaza?.
Bai Wauka Aneesa za ta zo ba tunda ya gaya ma ta zai je Kano kuma zai bar yaran a wajen ma?ota.
?arfe takwas da rabi na dare ya isa gidan Mr AbdulRaza? dan Wauko yaranshi. Sai dai da ya je ake ce ma sa Aneesa ta zo ta Wauke su.
A take a wajen ya kira Aneesa amma ba ta Wauka ba. Hankalinsa bai tashi ba sai da ya je gida mai' aikin su ta ce Aneesa ta wuce da yaran Abuja. Yai ta kiran numbar Aneesan amma ba a Wauka. ?arshe dole ya kira numbar ?aninta Nazir ya ce ya kaiwa Aneesa.

Minti biyar sai ga kiran Aneesa a wayarsa.

"Wannan wanni irin iskanci ne Aneesa za ki Wauke min yara ba tareda kin sanar da ni ba"

"Iskanci kuma AbdulWahab, Ni da 'ya'ya na. For your information, kai da su Baby sai ka janye maganar auren ka. Ko kuma su zauna tare da ni anan amaryarka ta haifa ma ka wasu"

"Anny kin san yaran nan suna Makaranta fa"

"And so, zan sa su a wani anan"

"Look Aneesa, ki maido min da yarana gobe-goben nan ko kuma..."
?iiit ta kashe kiran.

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0?? 1?? 3??



Kwana biyu Aneesa ba ta turo ma sa yaran ba dan haka dole ya kira Alhaji, mijin Maman Aneesan kenan, ya ma sa bayanin komai shi baya ma gari dan haka bai san su Alizah na gidan sa ba. Ya jima yana yiwa Aneesa faWa akan ta ajiye aiki ta je ta zauna da yaranta amma ta ?i. Kasancewa Maman ta ba ta bashi goyon baya ba shi ya sa yai shiru ya zuba mu su ido. Ya auri Hajiya Salma ne lokacin Aneesa na da shekara goma shabiyu ?aninta kuma na shekara tara. Bai taSa banbanta su da 'ya'yan sa na cikin sa ba, makaranta mai tsada su ka yi da ta gama sakandare ya turata karatu ?asar waje.

Aneesa ta haWu da AbdulWahab ne a cikin jirgi, daga Lagos za ta wuce Abuja. Sun kusan shekara biyu su na soyayya kafin su ka yi aure saboda dagewa da Aneesan ta yi akan za ta yi masters kafin ta yi aure. Bayan sun yi aure ta fara aiki da wani Kamfani a Lagos. Shekaru biyu da su ka wuce Kamfanin su ka buWe wani branch a Abuja kuma su ka nemi Aneesa ta koma wajen. ?arin matsayi da albashi su suka ruWi Aneesa ta tsallake mijinta da 'ya'yanta ta wuce Abuja. Abdulwahab ya yi faWan ya yi fishin amma duk a banza. Haka ya kira Maman Aneesan ya mata bayani akan ba da yawunsa Aneesa ta koma Abuja ba. BuWan bakin Maman sai ta ce "AbdulWahab idan ta ajiye aikin za ka iya ba ta dubu Wari shida da hamsin a wata ne (650,000)?" Wannan maganar shi ya sa AbdulWahab ya sauke makaman ya?in sa ya ha?ura ba dan ya so ba, sai dan inda ya ke ganin za a mata faWan ma goyon bayanta ake. Bai faWawa iyayen sa ba sai da ?annensa su ka je ma sa hutu bagtatan su ka tarar Aneesa ba ta nan da farko ce mu su yai ta je gida ne kawai daga baya su ka gano komai, nan Hajiya Yelwa ta ce ba ta san zance ba ta ya za'ayi yana Lagos matar sa na Abuja wai sai ?arshen wata za ta zo...

Alhaji yai waya ya ce maza Nazir ya maida yaran Lagos. Kasancewa Aneesa ta fita wajen aiki sannan Mama ma ta fita ya sa ya Wau yaran ba tareda wanni cikin su ya hanashi ba. Ya na samun tiketin jirgi sai Lagos. Baby da Alizah sai murna dan dama sun ?agu su koma school sannan su ka Dad Win su.

...................


Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro, duk da dai abubuwan sun zo a tsukekken lokaci amma hakan bai hana Baffa ko Baaba Sabuwa yin ?o?ari wajen yiwa 'yar su gata ba. Da ke AbdulWahab na da gida a Kano anan za a ma ta jeren kayan ta.
Farida kam abun ya haWu ya ma ta yawa kwana biyu su na aiki sosai a kamfani da ke akwai wani sabon contract da Kamfanin ya samu ga kuma shirye-shiryen biki. Har Wan rama ta yi saboda zirga-zirga. A cewarta Maijiddah tana da gidadanci ba kaman ?annen ta da idon su ya buWe ba, dan haka ta ke sa'ido akan komai saboda ayi komai na zamani...


Gulma kam a Najeeb constructions sai ma abinda ya ?aru musamman da aka kori Halima sannan aka ba wa Khalidah suspensio. Dayawa su na tafiya da cewa Najeeb da Farida su na soyayya ne musamman kasancewa har yanzu bai koreta ba duk da kuwa irin karya dokoki da ta ke. Sai dai duk gulman a bayan fage a keyi dan ba mai iya tunkaran Najeeb ko Farida. Irin dukan da Faridan ta yiwa Halima ma ya sa su ke tunanin ?ila Farida na da taSin hankali...

?an baccin da ba ta samu sosai cikin kwanakin nan saboda matsowar bikin Maijiddah shi ta ke yanzu a office. Sallaya ta shimfiWa a ?asa ta kwanta tana narkan bacci hankali kwance.

Ya kira telephone ba a Waga ba, ya kira wayarta still ba a Wauka ba. Computer Win sa ya jawo ya duba ko ta fita ne sai ya hangota chan ?asa tana bacci. Ya jima yana kallonta kafin ya tashi ya Wau key da wayarsa ya fita.

"Miss Salihu" ya faWa da Wan karfi lokacin ya tsugunna kusa da ita. Sai da ya kirata a na uku sannan ta tashi a firgice. Ganin shi tsugunne ya zuba ma ta ido ya sa ta Wan goge fiskarta ta ce " sannu Sir Najeeb"

"Bacci a bakin aiki Miss Salihu"

"Yanzu sai ka ce acikin albashina. To ka yi ha?uri gajiya na yi"

Yadda ta yi maganar ya bashi dariya sai dai haWa rai yai ya mi?e ya ce ta tashi za su fita.

Bin sa ta yi zuwa office ya nuna ma ta takardun da za ta Wauka. Bacci bai gama saketa ba amma haka ta tattaro takardun ta biyoshi. Tsabar mugunta sai ya ?i ya bi lifter ya bi stairs.
Suna saukowa ta fito da biro ta Wan ?ara sauri ta caka ma sa biro a bayan wuyan sa. Hannu ya sa ya shafa wajen ba tareda ya juyo ba. ?aramar tsaki ta ja ta sake kai hannu za ta sake caka ma sa sai kuwa ?iris ya juyo.
"Wayyo Allah na!....Wayyo!" Ta faWi cikin ihu, ta zubar da files Win hannunta ta koma baya da gudu.

Irin yadda ya ga ta tsorata ta fita da gudu sai abin ya sa shi dariya. Sometimes ya kan yi tunanin yarinyar nan na da taSin hankali...

Kai tsaye office Win Anas ta je. Tana magana tana haki ta ce " Ya Anas.... ka taimakeni... yau na tsokano tsuliyar dodo"

"Mi ya faru? Mi ki ka yi?"

Ba ta bashi amsa ba sai ma ta cigaba " wallahi ba zan sake ba. Ni ban ma san ya akayi na ma sa haka ba, dan Allah ka je ka bashi ha?uri"

"Me ki ka yiwa Najeeb"

Ta Wan yi ajiyar zuciya ta ce "biro na chaka ma sa a wuyan sa"

"Biro" Anas ya maimaita sannan ya kwashe da dariya.

"Ya Anas ba dariya za ka yi ba fa, ha?uri za ka je ka bashi"

"Yanzu ke Farida a wanni dalilin za ki ma sa haka?"

"Kawai haushi na ji ya tashe ni a bacci kuma ya ce wai mu sauko ta stairs"

Cikin zuciyarsa ya ce "lallai Farida na jinjina mi ki"

A fili kuwa cewa yai " yanzu dai kin amince kin yi laifi?"

"Na yi. Wallahi na yi"

"Shikenan, mu je na same shi"

"A'a kai ka fara zuwa tukunna, ni zan jira ka anan"

"Ki zo mu je ba abinda zai mi ki"

Jiki a sanyaye ta bi bayan Anas su ka wuce office Win Najeeb.

A zaune su ka sameshi yana waya. Daga bakin ?ofa Farida ta tsaya dan idan ma wani abin zai ma ta za ta samu ta gudu da wuri. Anas ya ?arasa wajen sa ya zauna yana Wan dariya ?asa-?asa.
Yana ajiye wayan Anas ya ce "YallaSai mun zo biko, ?anwar mu ta yi laifi kuma ta gane kuskurenta. Ayi ha?uri"

Shiru yai na Wan da?i?ai sannan ya ce " ta gaya ma abinda ta yi?"

"Ta gaya min, kuma na ma ta faWa sosai"

"Good, akwai psychiatrist da na kira yanzu, zai zo ya gwada min ita dan ban yarda da lafiyar ?wa?walwar ta ba"

Daga inda ta ke tsaye ta ce " haba Sir Najeeb, psychiatrist kuma. Sai kace mai taSin hankali"

Kallon Anas yai ya ce " idan aka tabbatar min da lafiyarta ?alau, then she can work with me. Idan tanada matsala kuma sai ta je ayi treating Win ta, dan ba zan iya aiki da mahaukaciya ba"

"Sir ka rama abin da na ma ka idan haka ne" ta faWi da Wan ?arfi

Shiru yai yana kallonta sai chan kuma ya Wau biro ya mi?e tsaye. Tana ganin ya nufota da biro a hannu ta tsume, wai a dole ba ta damuba irin ta surrender Win nan. Sai dai saura taku kaWan ya isota ta buWe ?ofa ta fita da sauri.

Najeeb ya ce " you see, she's crazy"

Anas yana dariya ya ce " she's just funny. Dan Allah kar ka ma ta komai"...


Fitan Aisha Farida kam ai sai gida, dan ba ta yadda ta tsaya ba. Sai da ta je ta tuna ai ko wayarta ba ta tsaya Wauka ba jakarta kawai ta Wauka. Ta yi tsaki sannan ta yi amfani da wayar Jiddah ta kira Yakubu ta ce ya je ya Wauko ma ta wayarta a office.

"Yanzu ke tafiya gida ki ka yi ba tareda an tashi ba, Sir Najeeb ya sani?"

"Ya sani mana, kai dai je ka Wauko min wayata kawai"...

Najeeb ya fito daga office Win sa zai fita ya ji wayar Farida na ringing, ganin bai ga jakarta ba yai tunanin ta tafi ne. Zuwa yai ya Wau wayar amma kafin ya Wauka kiran ya yanke, take kuma aka sake kira sai ya ga sunan mai kiran an saving da *My Ray*. Tsaki ya ja sannan ya saka wayar a Aljihu ya fita.
Yakubu da ya zo bai ga waya ba ya kira Farida ya gaya ma ta. Ita kuwa ta rantse indai aka sace ma ta waya a Najeeb constructions to za ayi ?aramin ya?i dan kuwa ba za ta yadda ba sai an fito ma ta da waya...


..................

"Yanzu kinga wannan jakar, duk kayan ciki na ki ne. Na fi awa Waya ina za?ulo waWannan kayan a wajen ma su gwanjo. Wallahi ko manya-manyan boutique ki ka je ba za ki samu kaya ma su kyaun wannan ba, ai gwanjo rufin asiri ne. Sai ki samu kayan da har ki gama yayinsa ba za ki taSa ganin irin sa ajikin wani ba"

Maijiddah ta buWe jakar ta fara fiddo kayan da ke ciki. Duk wanda ta Waga sai ta yi saurin ajiyewa saboda yanayin kayan sun bata kunya.

"Jiddah ya na ga kina wani yan?wane fiska kaman kin ga kashi?"

"Anty Farida wannan kayan ai...."

"Ai me? Na ce ai me?. Dan Uban ki ina siya mi ki mutunci kina cewa ke tsiya ki ke so. Wannan kayan da ki ke gani da su ake cin gari. Balle ke da ki ke da kishiya, kishiyar ma wayayyiya 'yar boko"

"To Anty kuma sai insa wannan kayan in fito?"

Wani kallon banza Farida ta ma ta sannan ta ce " idan kin ga dama ki sa, idan kin ga dama kuma ki ?ona su idan kin je chan. Ni dai na san watarana sai kin kirani kince Anty Farida zan iya samun irin kayan nan wallahi ko nawa zan biya ki nemo min su. Lokacin ni kuma sai na karSi kuWi mai tsoka a wajen ki kafin na nemo mi ki"

"Ki yi ha?uri Anty"

"Ba batun ha?uri ba ne Jiddah, so na ke ki waye ki shigo gari kema. Idan kin je kin mallake zuciyan maigidan gaba Waya. And Wallahi zan faWa mi ki gaskiya ba da hijabi ko manyan kaya ake sace zuciyan miji ba"


"Anty Farida wani mai ?atuwar mota yana kiran ki a waje. Maijiddah ke kuma wai inji Rashidan Bala wai za ta samu kitso?"

"Zo nan Sadi?" Farida ta faWa tana kallon molelen kan yaron da ya sha aski.
Yana zuwa ta kama shi ta ma sa dundu uku a baya.
"Ban hana ku kiran Maijiddah da sunan ta ba? Eh. Mi na ce ku dinga ce ma ta?"

Yaron cikin kuka ya ce "Anty Maijiddah"

"Good boy. Yanzu ka je ka cewa Rashida, Anty Maijiddah ta dena kitso"

Yaron ya fita yana kuka yana ?o?arin sosa bayan sa....


Ba ta gane motar wayeba amma ta san koma waye to babba ne. Ba ta tunanin kuma Alhaji Hussaini ne, wanda ta haWu da shi a wajen aiki ya zo wajen Sir Najeeb ya nace ya nemi numbarta, sai da ta sissilleshi sannan ya ha?ura ya dena kiran ta.

Tana ?arasawa jikin motar ta zagaya wajen driver ta ?wan?wasa glass Win saboda tinted ce ba ta ga wanda ke ciki ba. ?an sauke glass Win aka yi sannan aka mi?o ma ta waya, tana ganin hannun ta ce "Sir Najeeb!" sai kuma ta yi saurin rufe baki tunowa da ta yi da abinda ta yi a office yau.

?arasa sauke window Win yai sannan ya ce " Miss Salihu karSi wayan ki"

Ta yi saurin karSan wayan sannan ta ce "na gode Sir" bai ce komai ba ya ja motar sa ya tafi...



"Kaman motar Sir Najeeb na gani Wazu a ?ofar gida"

"Shine. Waya ta ya kawomin"

Da mamaki Yakubu ya ce " Sir Najeeb Win?

"Iyi"

"Sir Najeeb ya kawo mi ki waya har gida"

"To miye aciki, ni ba sakatariyar sa ba ce"

Shiru Yakubu yai yana tunanin ko dai gulman da ake yi a office gaskiya ne. To idan ba haka ba Sir Najeeb Win da ya sani a da kam bai damu da damuwar kowa ba, kan sa kawai ya sani. To idan kuma akwai abu a tsakanin su fa? Baba ya ce a ?arshen watan December za ayi bikin Farida.
Farida ce ta katse shi da cewa "yawwa Yakubu ka san numbar nan?" Ta nuna ma sa numbar NJ. ?aukan numbar yai ya sa a wayarsa sai dai bai da irin numbar ma a wayarsa...

...................

Fitowar sa kenan daga wanka ya ganta zaune abakin gadon sa.

"What are you doing here?"

"Son, Kakan ka ya rasu da safiyar yau" ta faWi cikin muryan kuka


"Allah ya ma sa rahama"

"Zan wuce Bahrain gobe. Za ka je?"

"i'm busy" ya faWa a ta?aice

"Saboda ni ko saboda Sabreen ne ba za ka je ba"

"Enough Justice Nabilah. Ki fita min a Waki"

"Najeeb please" Mom ta faWa kamar za ta yi kuka.

"Ke ko Sabreen, ba ku da wani matsayi da zai sa na yi abu ko kar na yi abu"

Hawaye ne ya gangarowa Mom ta yi saurin sharewa ta ce " sai yaushe za ka yafe mi ni"

"When you are ready to tell the truth"

"Najeeb!" Ta faWa da ?arfi.

"Oh, Justice ki na tsoron gaskiyan ne?"

Shiru Mom ta yi tana ?o?arin maida hawaye.

Sai da ya ga ta fice Wakin sannan ya sauke numfashi, zama yai a bakin gadon lokaci guda jikin sa ya fara ma?yar?yata, abinda ya gani shekaru ashirin da Waya da su ka wuce ya fara dawo ma sa. Duk yadda yai ya manta da komai ya ka sa. He was only thirteen amma yana iya tuna komai harta fiskar wanWanda su ka Wau gawan a ranan...


...............


Washe gari da wuri Farida ta je office ta ajiyewa Najeeb takarda a table Win sa. Bai fi minti shabiyar da isowarta ba sai ga shi ya zo. Tana gaishe shi ma amma ko kallon ta bai yi ba. Sai da ta bashi minti biyar sannan ta bi bayan shi. Takardar ne a hannunsa lokacin da ta shigo.

"Sir na san na yi laifi amma ka yi ha?uri dan Allah"

Ya na so ya ma ta faWa, ya na so ya nuna ma ta ko shi waye, amma ba zai iya ba saboda ransa da ke a Sace saboda kuma...

Cillar da takardar ba da ha?urin da ta rubuto yai sannan ya ce " get back to work"

Ta yi mamaki da bai yi masifa ba ita kam hutarerenta ai. Har za ta fita sai kuma ta lura da yanayin sa kaman ba shi da lafiya ko kuma akwai abinda ke daminsa dan tsakanin jiya da yau ya chanja ma ta gaba Waya.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?"

"Get out Miss Salihu"

Simi-simi ta fita kar ma ta tunzura shi ya ce zai hukuntata.

Ya fara duba wasu takardu amma hankalinsa ya kau, tunanin kyakyawar fiskarta ya ke da murmushinta mai shiga zuciya. Ya missing Win ta sosai, *Aysherh* ya furta a hankali.

Ya na mamaki da Aysherh Farida ba ta da sanyi da ha?uri irin na Aysherh. Halin su ya sha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login