Showing 93001 words to 96000 words out of 145791 words

Chapter 32 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

338

kan hiran da ta ke yiwa Najeeb...



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 3?? 7??



Tana tareda Najeeb, Anas da Daddy su ka shigo Wakin.

"Masha Allah 'ya ta Allah ya mi ki Albarka" Daddy ya faWa lokacin da ya ?araso.

Ta amsa da Amin tana murmushi.

"Son ka ga abinda matar ka ta yi ko? She is a fighter, she's a winner. Matar ka iron lady ce. Ka tashi ka ji, ka tashi ku gina rayuwar ku tare" ya kissing goshin sa yana shafa gashin sa.

"Daddy Mom ta dawo?"

"Sai next week" ya amsa ma ta.

"Allah ya dawo da ita lafiya"

Su ka amsa da Amin.

Anas kam kunya ta hanashi magana sai kau da kai ya ke. Daga baya Daddy ya bar su ya ce zai je yai magana da likita.

"Ya hanya" Anas ya katse shirun na su.

"Alhamdulillah mun je lafiya mun dawo lafiya. Sauro bai cize mu ba haka Cinnaka ba ta cize mu ba balle ayi tunanin mun wahala. Kuma dai girma ya faWi"

"Farida dan Allah ki yi ha?uri. Na san ba ni da hujja akan abin da na aikata amma ki yi ha?uri ki yafe mun"

"Ya Anas a nan ka zo ka ro?e ni Allah Annabi akan na zama CEO amma mi ka yi bayan na zama CEO. Ka bauWe min, ka ?i goya min baya har ka na ganin gara ka bar aikin da zama na CEO ko?"

"Ba haka ba ne Farida, kawai dai ba na so kamfani ta shiga matsala ne"

"Da kyau, saboda ga Aisha Farida mai farar ?afa ko?"

"Duk abinda ki ka ce i deserve it. Ban ri?e amanar abokina ba, i'm truly sorry"

"Ka san mi ake cewa namiji matsoraci? To Ya Anas kai matsoracin namiji ne kuma ragon namiji. Idan ba ka dena sa tsoro a lamurran ka ba to ba inda za ka je a rayuwa. Kuma ko a gidan ka za ka samu matsala. Kana ganin da ina da tsoro zan kai yadda na kai da Najeeb, ka san da ni matsoraciya ce da tun ranan da Najeeb ya koreni da na bar aiki a kamfani kenan. But i fight back, na nuna ma sa ni ba ?wallo ba ne da zai dinga bugawa duk lokacin da ya ke so. Ka san miyasa Najeeb ya ka sa korata? Because he needs me. Najeeb na son mutum mai zafi, mutum da ba ya da tsoro ko kaWan"

Ya ji haushin kiran sa rago da ta yi amma kuma gaskiya ta faWa, sau tari ta inda su ke samun matsala da Najeeb kenan.

"Ki yi ha?uri dan Allah"

" na ji haushi kuma har yanzu ina jin haushin ka. Ka bani lokaci na huce tukunna"

"Ba komai, amma dan Allah ki yafe min"

"Na yafe"

Ba su sake wani maganan ba har Daddy ya dawo su ka tafi.


"My champ ka ga abokin ka ko, ka ganshi ko" ...

......................
Washe gari tana shigowa kamfani aka fara tafi, ana ma ta congratulations.
Duk wanWanda su ke ma ta wani gani-gani to yanzu sun sha jinin jikin su. Madam Farida kamar yadda yanzu aka fi kiran ta ta zama Boss lady. Tundaga lokacin da ta ?arSi matsayin CEO kowa ya shiga taitayin sa saboda ita ma zafi gareta kamar Najeeb. Wani zubin ma gara Najeeb Win dan shi idan ya ma ka tsawa shi kenan amma wannan sai ta bika da ba?ar magana wani lokacin idan ta yanko ma ka magana sai ka ji kamar ka kama kai ka rusa kuka.
Ga wanda ya bita sannu kuma tana da sau?in kai...

Su Mr Vladimir bayan ya tabbata Farida ta leading team kuma anci gasa ba ?aramin ba?in ciki su ka yi ba. Neman sulhu su ka fara yi dan kar su rasa 5% da au ka yi al?awari amma kuma Farida ta ce bata san zance ba. Su su ka faWi sharaWi kuma dole su bi shi yadda ya ke. Haka dai ba tareda sun so ba su ma sa hannu a takardar da ke shaidar sun ba da 5% shares Win su a Najeeb. Ranan Farida sai da ta yi hawaye saboda hango farin cikin da ta yi a idon Najeeb idan ya farfaWo ya ji abinda ta yi...


......................

Gidan AbdulWahab kam yanzu zaman lafiyan ba kamar da ba. Tunda Aneesa ta dawo Lagos da aiki sai komai ya chanja. Kullum cikin ta?alar Maijiddah ta ke yi, duk da ma yanzu Maijiddan ta dena tsoron ta kuma ta na Wan maida ma ta magana amma still wassu lokutan shiru ta ke ma ta. Aksarin lokaci Maijiddah tana burin inama ace itama ta iya magana kaman Farida da za su dai-dai ta tsakanin ta da Aneesa.

Haka kawai ta hana yaran shiga harkan ta, duk da yaran na so amma abinka da uwa da Wa sai ya zamana ta yi musu tsawa shikenan. ?an gara ma Alizah wani lokacin tana ?in bin umurnin Maman na su.

AbdulWahab na iya ?o?arin yin adalci tsakanin su duk da ma yanzu Maijiddah ta fara ganin chanji a tattare da shi lokacin da Aneesa ta dawo. Tana renon cikin ta lafiya amma wani lokacin gani ta ke tunda Aneesa ta dawo kaman yanzu AbdulWahab ya rage ba ta kulawa da kuma Wokin cikin da ta ke Wauke da shi.
Cikin ta na wata bakwai Aneesa ta fara laulayin ciki. Ta gano hakan ne ranan su na zaune suna cin abinci ta fita da gudu tana amai a banWakin da ke guest room.
Daga baya kuma Aneesan ta fara tsirface-tsirfacen abubuwa irin na ma su ciki.

Lokaci guda hankalin AbdulWahab ya koma kan Aneesa. Ranan su na cin abinci da ke Maijiddan ne ta yi girki, Aneesa ta fara kushe abincin akan an hana ta yawan cin mai a asibiti kuma ga shi abincin Maijiddan ya cika mai.

"Sweetheart ba ka gaya ma ta abinda likita ya ce ba ne?" Ta faWa tana kallon Maijiddah.


"Anny zan gaya ma ta ba yanzu ba akwai yara a nan"

"Na san ba za ka iya gaya ma ta ba. To Malama Maijiddah ciki ne da ni kamar yadda ki ka sani, kuma likita ya ce saboda mahaifata tana da rauni na guji aikin wahala da yawan stress na kuma rage cin wassu abubuwa saboda kar cikin ya zube. Sai ki kiyaye nan gaba"


Maijiddah ta buWe baki da hanci tana ganin wannan cin fuskan. ?arin haushin ma AbdulWahab bai yi magana ba.
Ajiye cokali ta yi ta bar wajen. Da ya ke kwanan ta ne AbdulWahab da ya zo sai ya ke ?ara gaya ma ta report Win da likita ya ce gameda cikin Aneesa.

Haushi ya kawo ma ta har wuya, ka sa shiru ta yi ta ce "amma Abban Alizah ni ma fa ciki gare ni kuma ko da babu likitan da ya gindayamin sharaWi, dai a matsayin da na ke yanzu ina bu?atar kulawa ta musamman"

"Hauwerh dont get me wrong please, ba wai ina nufin ke baki bu?atar kulawa ba ne..."

"Sai yanzu na gane gaskiya. Dama saboda matar ka ba ta nan ka auro ni, to yanzu ta dawo ban da matsayi ko?"

"Shhhhh, kar ki sake faWin haka Hauwerh ki na da matsayi babba a rayuwata"

" a rayuwar ka haka ne amma a zuciyar ka Anny ce kaWai"

Kamo hannun ta yai ta wafce hannun.

"Plz Gimbiyata, ki yi ha?uri. Ki na da matsayi a zuciyata da rayuwata gaba Waya"

Ranan dai AbdulWahab da ?yar ya shawo kan amaryar sa...

.....................


Ko mi zai ma ta ba za ta koma Lagos ba. Gara ya dinga zuwa yana dubata duk ?arshen wata. Ta bar mu su waje su sakata su wala yadda su ke so. Sai da motar su ta Wau hanya sannan ta jingina kanta da seat tana hawaye. Babbar motar Macapolo ta shiga da zai je Kano daga Lagos. Duk da kasancewa dare ne hakan bai sa ta ji wani fargaba ba. Su na tafiya tana tuno maganganun AbdulWahab...


Sai da su ka dawo daga asibiti sannan ya je Wakin Maijiddah dan ya bata ha?uri tsawan da ya ma ta Wazu. Ya sani sarai bai kyauta ma ta ba. Duk abinda ya faru bai kamata ya gaya ma ta magana haka ba.
Wayam Wakin ba kowa. Ya duba ko ina ba ta nan. Mai aikin su dama ba ta nan ta yi tafiya. Fita yai ya je ya samu mai gadi inda ya sanar ma sa Maijiddah ta fita. FaWa ya fara ma sa akan miyasa zai barta ta fita ita Waya da tsohon ciki. Maigadi ya ce shi ya je ya samo ma ta taxi ma domin kuka ta ke yi ta ce an musu rasuwa ne za ta je gida kuma kai ka ce ta tafi saboda kun fita da Madam Babba.
Tsaki yai ya koma ciki. Ya kira numbarta sau ba adadi amma a kashe. Ba dai Maijiddah gida ta tafi ba.
Aneesa na kwance sai nishi ta ke ita a dole ta yi Sarin ciki kuma kishiyar ta ce sanadi. AbdulWahab ya shiga tashin hankali sosai ina ya san zai nemi Maijiddah da daren nan...

Washe gari da safe ya samu labarin ta shiga mota ta tafi Kano. Kiran Hajiyar sa yai dan ya ji ko ta iso sai ya ga Hajiya ba ta ma sa maganar ba sai ma tambayar sa da ta ke ina Maijiddah. Sai alokacin ya waske da cewa ai tana hanyan Kano ma yanzu.

"Ko kai fa amma ka ce wai ta zauna a chan ta haihu"

Dama Hajiya Yelwa ta nemi ya bar Maijiddah ta haihu a kano ya ?i shiyasa ba ta kawo komai aran ta ba.

?arfe goma na safe su ka isa Kano inda direct gidan su mijinta ta wuce. Yanayin yadda Hajiya Yelwa ta ganta ya sa ta gane ba tafiyar jirgi ta yi ba.

"Lafiya Hauwa na ga kin kumbura, duba ?afafuwa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n ki"

"Ba komai Hajiya zama ne kawai ya sa yai haka"

Hajiya Yelwa ta kira AbdulWahab tana ma sa faWa akan barin Maijiddah da yai ta zo ita Waya sannan a mota ba a jirgi ba.

Hamdala yai lokacin da ya ji Maijiddah ta isa gida lafiya. Ya bawa Hajiya ha?uri akan ayyuka su ka ma sa yawa.

"Hajiyata ki Wan bawa Hauwa wayar na kira numbar ta baya shiga ina ga wayan ya mutu ne"

Hajiya ta mi?awa Maijiddah wayar wanda ganin idon Hajia ya sa ta karSa.

"Haba Hauwerh kin min adalci kenan, idan wani abu ya same ki fa."

"Na isa gida lafiya a gaida marar lafiya" ta kashe wayan saboda Hajia ta fita a Wakin...


Kwanan ta na uku sai ga AbdulWahab. Tana zaune tana cin abinci a Wakin Hajia sai ga shi ya shigo.
Ganin sa da ta yi sai da ta Wan yi jim amma ta dake.
Zuwa yai ya zauna gefen ta ya kamo hannunta Waya ya ce "Gimbiya ta haka kike da zuciya dama. Haba dan Allah, kin san ina son ki kuma ba zan taSa yin abinda zai Sata miki dai ba"

"Amma ai ka yadda ai lokacin da matarka ta ce na tureta ta faWi. Na yi sanadiyar rasa cikin Wan Lele ko"

"Na san na yi kuskure Gimbiyata a min ha?uri"

Namiji dai da daWin baki haka ya gama kwantar ma ta da hankali da kalamai ma su daWi. Dole dai ta mi?a wuya ta ha?ura ?arshe ma ita ta koma tana bashi ha?urin kan tahowa da ta yi cikin dare ba tareda ya sani ba...
Washegari ya tafi dan ya san tunda ta riga ta zo sai ta haihu tunda dama tun farko Hajiya Yelwa ta nemi hakan...



.......................

Sati biyu da zuwan Maijiddah kano ta haifo santalelen Wan ta mai kaman uban sa. Haihuwan nan ya sa Aneesa ta tada daru akan AbdulWahab dole ya bi ma ta hakki tunda Maijiddah ce ta yi sanadiyar zubewar cikin ta. Shi kam bai biye ma ta ba dan sai a lokacin yake ganin wautarsa ranan. Domin ya san Maijiddah ba ta da faWa kuma yadda ta ke Wan jin tsoron Aneesa haka kawai ba za ta tureta ba dan dai maganar fatar baki. Balle Maijiddah na da tsohon ciki ita kuma Aneesa cikin ma wata biyu ne.
Ana saura kwana biyu suna ya tattaro yaran sa su ka zo Kano. Aneesa kam Abuja ta wuce ta ce ba za ta je sunan ba...


Daga gidan suna ta wuce asibiti.

"My Champ ka ga babyn Maijiddah kuwa? Wallahi kyakykyawa da shi. Ka tashi muma mu yi abubuwa na samu ciki na haifi Baby mai kaman ka. Ka ji miji na"
Ta ?ara kissing hannun sa tana faWin "sunan Babyn na su Muhammad Al'amin, nima My Champ ina son suna Muhammad. Sunan Wan mu na farko kenan Insha Allah"...


?ar?ashin jagorancin Madam Farida Najeeb Constructions ta samu cigaba sosai kuma an samu gyararraki kan abubuwa dayawa.
Yau ma wassu ba?i ta ke meeting da su da su ka zo daga Kaduna.

Tana shiga office Win ta Anas ya shigo.
"Farida ba ki sa hannu a wannan takardan ba"
Ya mi?o ma ta wani takarda. Ta ?arSa ta yi signing sannan ta mi?a ma sa.

Tana zama sai ga kiran sakatariyar ta.

"Hello Madam, Mr Rayyan Abdullahi is here to see you should i send him in?"

"Rayyan Abdullahi?"...

Mi Rayyan zai zo yi wajen ta. Rabon ta dashi tun ranan da ya zo office Win ta Najeeb ya ma sa kora da hali...






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0?? 3?? 8??



"Faridah" muryan Rayyan ya doki kunnen ta. Ta Wan Wago ta kalleshi, kallonta ya ke yi mai cike da ma'anoni.
Da yatsar ta ta ma sa nuni da ya zauna ba tareda ta kalle shi ba. Har ya zauna bai Wauke idon sa a kan ta ba. Ita kuwa tunda ta Wago sau Waya ta maida kan ta ga takardun da ta ke dubawa.

"Farida" ya sake kira

Ta Wago kai tana juya biron da ke tsakanin yatsunta biyu.
"Mr Rayyan what can i do for you?"

"Farida ni Win, ni Win ne Mr Rayyan" ya faWa yana nuna kan sa.

" ok to Malam Rayyan mi zan iya ma ka"

"Lallai duniya!"

"As you can see aiki na ke yi. Idan ba ka da abin faWi dan Allah ka ?ara gaba"

Jijjiga kai yai sannan ya ce "ya jikin Mijin ki?"

"Alhamdulillah da sau?i"

"Stop pretending Farida, waye bai san halin da Najeeb ya ke ba a garin nan. He's being in coma for months now, ba alaman zai farfaWo balle..."

"Balle me? Balle me?" Farida ta daka masa tsawa.

"Kwantar da hankalin ki Farida ba faWa na zo ba. Ina so ki sani cewa har yanzu ina son ki kuma ina son auren ki. An sa aure na da mai sunan ki nan da 2 months. Amma na ro?i Umma ta bar ni na aure ki bayan na auri 'yar uwata Aishatu kuma ta amince. Kin ga by the time kin gama iddah sai mu maida auren mu"

"Ban san ka da shan giya ba Rayyan, ko dai ka fara ne bayan rabuwar mu?"

"Farida ke kan ki kin san har yanzu ina son ki..."

"Rayyan idan ba giyan wake ka sha ba ya kamata ?wa?walwar ka ta gaya ma ka ni matar aure ce, ni matar Najeeb ce"

"Wanni Najeeb Win, Najeeb da ke chan kwance kamar gawa. How long has it being, kusan 8 months fa"

"Yes Rayyan. Yana chan kwance for 7months 9 days, kuma zan jira shi ko da zai Wau shekaru kafin ya farfaWo. I love him and i will wait for him till the end of my life. Get that into your thick skull Rayyan" ta faWa tana mi?ewa tsaye.

"Far..."


"Leave!" Ta daka ma sa tsawa

"Farida ki..."

"Get out! Ka fita na ce!" Yadda ta yi tsawan wannan karan sai da ya Wan tsorata.

Ba tareda ya sake yun?urin magana ba ya tashi ya fita.

Zama ta yi ta fashe da kuka. Miyasa kowa ke ganin Najeeb ba zai tashi ba, miyasa su ke ganin a haka zai ?arasa rayuwar sa. Haka jiya da su ka yi waya da Ummi ta ke ce ma ta ance ba lalle Najeeb ya farfaWo ba, ko za a raba auren su. Miyasa ita ba ta gaji da jiran sa ba amma su sun gaji. Akwai wanda ta farfaWo daga coma bayan shekara ishirin, ko da Najeeb zai shekara ishirin a haka za ta jira shi. Balle ta san ya na chan ya missing Win ta yana ?o?arin dawowa gareta...

.....................

A gajiye ta shigo Wakin na su saboda aikin abincin sadaka da su ka yi. Duk Jummu'a ita ke zama da su Adama su girka jollof rice da naman rago su sa a take away guda dubu a kai wa almajirai da mabu?ata. Kullum sun sa ana mu su sadakan kunu da ?osai da Masa.
Mom ma ba a barta a baya ba wajen sadaka. Ranan su Adama su ka tayata fitar da kusan duka kayayyakin ta da ke closet, wassu kayan ma ba ta taSa sakawa ba, ga su kaya ne ma su matu?ar tsada, ta sa aka rabar sadaka. Mutum goma ta biyawa Umurah da lokacin azumi. Shi Daddy kam ba irin sadakan da yai Allah ne kaWai ya san adadin sa. Ba wai dama ba ya taimako ba ne, amma abinda ya faru ya sa ya ?ara buWe hanyoyin taimakon al'umma...

A Desk Win sa da ya ke zama yai aiki idan yana Waki ta zauna. Wani brown envelope ta gani, ta jawo shi. Wayoyin Najeeb ne guda biyu a ciki. Sai yanzu ta tuna cewa ita Win ce ta saka a wajen ranan da Anas ya kawo ma ta. Anas ya sa an buWe wayan domin a duba wassu sa?onni. Ko lokacin da za aje Bank da Court wajen authorizing signature Win ta ya zama bayan Najeeb da Anas har da na ta signature Win wajen sarrafa abubuwan Kamfani har da wayan nan aka je. Ta tuna sai da ta yi rantsuwa a kotu sannan aka gama haWa komai, abin tausayin ma maimakon signature Win Najeeb dole thumb print na sa aka sa.
Ranan da Anas ya kawo wayan tunda ta ajiye su a kan table Win ba ta sake bin kan su ba.

Ta Wauki babban wayan ta kunna. Hoton sa ne a screen Win duk da ma screen Win ya Wan tsatstsage. Ta ?urawa hoton sa ido, ta sa hannu tana shafa kyakykyawan fiskar sa. Ta shiga gallery tana kallon hotuna wanda yawanci hotunan zane-zane ne, sai wani folder wanda hotunan Najdah ne da hotunan sa wanda su ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login