Showing 123001 words to 126000 words out of 145791 words

Chapter 42 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

333

gani ta ke yi abinda IfaGbemi ya gaya ma ta ba mai yiwuwa ba ne. Tun da ta ke ba ta taSa ganin Najeeb yai fushi da Farida ba. They are inseparable. They are madly inlove.

Wannan weekend Win da ta wuce ta je jahar Ekiti chan cikin wani ?auye tareda ?awarta Maureen.
Ba komai ne ya kaita wajen ba sai saboda Najeeb W. Tsawon watanni tana dakon soyayyarsa amma shi kam bai ma san tana yi ba. Har aranta ta ?udura idan har Najeeb zai so ta to za ta bar kiristanci ta koma musulunci.

Maganganun Ifagbemi na ma ta yawo a ka lokacin da ta ke jujjuya kwallin da ya bata a hannunta.

"Mace Waya aka rubuta mi shi a gaba Waya rayuwar sa. Duk inda zai je ya dawo mace Wayan nan ita ce ?addarar sa"

"Baba to ya zan yi kenan? Ba zai taSa sona ba kenan?"

Bokan yai wata ba?ar dariya ya ce " idan ki na so ya so ki sai dai ya gan ki a matsayin matar da ya ke so. Idan ki ka yi kamaceceniya da ita zuciyar sa zai so ki"

Maureen da Naomi su ka haWa baki wajen faWin "ba mu gane ba"

Wata ?warya da aka lulluSe da jan ?yalle ya Wauko sai da yai ta surkullen sa sannan ya buWe ?waryar sai ga kwalli a ciki.
Ya Wau kwallin da hannun hagu ya mi?awa Naomi ya ce ta amsa da hannun hagu.
Naomi ta amshi kwallin tana jujjuya shi.

"Duk ranan da yai fushi da matar sa, ki saka wannan kwallin a idon ki ki ?yafta ma sa ido ki kwantar ma sa da hankali. Zai dinga kallon ki a matsayin matar sa, duk soyayyar da ya ke mata zai dawo kan ki Amma..."



"Naomi" muryan Farida ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

"Yes ma" ta faWa da muryan girmamawa.

Akwai Dr Lukman da zai zo wajena anjima ki barshi ya shigo.

Naomi ta gyaWa kai...

Najeeb ya fita supervision. Ita kaWai ke office. So ta ke ta surprising Najeeb amma bayan Lukman ya amince za ta sanar da shi komai.

Ba'a jima ba sai ga Lukman ya shigo.

"Hajiya Farida ya aiki"

"Lafiya Dr, ya hanya"

"Alhamdulillah"

"Ya ha?uri kuma na ji ance Alhaji Magaji ya rasu"

"Hakane kusan 5weeks ma yanzu"

Farida ta ce Allah ji?an sa.

Shiru ya Wan ratsa office Win. Kafin daga baya Farida ta ce " Doctor har yanzu ka ?i aure"

Lukman yai murmushi mai Waci ya ce " har yanzu Allah bai nufa ba. Kowacce mace ba ta son auren Wan shege"

"I'm sorry" Farida ta faWa cike da tausayin shi.

"No dont be. Allah ba ya taSa Waurawa bawa jarrabawar da ta fi ?arfin sa"

Farida ta ce hakane.

"Amma ba ka sake nema ba ne ko ya?"

Lukman ya nisa ya fara ba ta labarin yadda yai sanadin musuluntar da wata colleage na shi Dr Jennifer, har sun tsara za su yi aure ta amince da shi duk da ya gaya ma ta matsayin shi. ?watsam wani abokin aikin su wanda ya ke da mata biyu fa Dr Faisal ya shiga nemanta yai ta hure ma ta kunne da ma ta burga da asalin sa yana kushe Lukman a matsayin sa na shege. ?arshe dai Dr Faisal ta aura.

"Kai duniya, yanzu musulmi Wan uwan musulmi amma sai ya ha'inci Wan uwan sa. Shi da ke da mata biyu amma ba su ishe shi ba sai sun hanaka samun mata?"

Lukman yai dariya mai ciwo ya ce " mi za ta yi da shege bayan ga cikakken namiji mai asali"

Jikin Farida yai sanyi. Yadda ta tsara anya zai yadda da shawaranta kuwa? Dama so ta ke ta ma sa maganar Sabreen. Sabreen tana bu?atar aure sannan tana bu?atar auren mai addini wanda zai kula da ita. To kuma Lukman shi ne candidate Win da ta ke ganin ya dace ya auri Sabreen dan ya ?ara gyara ma ta rayuwar ta...

Shigar Dr Lukman office Win Farida ya sa Naomi ta sa do not disturb tag a jikin ?ofa tana addu'ar Allah ya sa Najeeb ya dawo da wuri.

Tana zaune kuwa sai ga Najeeb, as usual ko kallon ta bai yi ba ya zo zai shige office sai ya ga tag Win da ta sa.
Ya juyo a fusace yana tambayar dalilin saka tag Win.

"Sorry Sir, Madam ce ta ce na sa dan ta yi ba?o. Tun tafiyar ka su ke tare"

Najeeb bai kawo komai a ransa ba ya buWe office ya shiga. Ta glass Win da ya raba office Win sa dana Farida ya hango Farida da Lukman su na zaune. Zahiri ba wai su na wani abu ba ne. Magana ce su ke yi amma fiskan Farida Wauke da murmushi.
SheWan ne ya tunzura shi a wannan lokaci. Har zai buWe office Win ya shiga sai kuma ya juya ya fita, Kan sa ke wani irin ciwo. Idon sa ya yi ja zir.
Yana fitowa ransa a Sace zai tafi Naomi ta kira shi.

"Sir"

Ya juyo a fusace ya kalleta. Naomi ta fara ?yaf?yafta ido, ta taso ta zo gaban shi har lokacin bai iya janye idon sa daga na ta ba. "dear ka yi ha?uri. Ka kwantar da hankalin ka, ina tareda kai"...


*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 5?? 1??






Naomi ta sa hannu ta fara shafa ?irjin Najeeb. Bai motsa ba bai kuma hana ta ba. Ganin bai yi masifa ba yasa wanni daWi ya ziyarci zuciyar Naomi. Ta kwantar da kai jikinsa tana cigaba da shafa shi. Najeeb dai yana tsaye kaman gunki bai iya aiwatar da komai ba.

"Sweetheart ka yi ha?uri ka ji"
Najeeb ya tsinci kan sa da gyaWa ma ta kai...


Farida ta ji farin ciki sosai da amincewar Lukman. Tanada ya?inin Sabreen za ta amince da shi musamman idan Najeeb ne ya ma ta maganar.

"Barin kira mijina yanzu na san ya kusa dawowa"
Ta Wau waya ta fara kiran numban Najeeb. Sau uku tana kira sau uku wayan na tsinkewa ba tareda an Wauka ba.
Duk da gabanta ya faWi da hakan amma ba ta nuna ba.

Ta yi murmushi ta ce "?ila wayar ba ta kusa da shi ne, bari mu Wan hira shi"

Lukman ya mi?e tsaye ya ce "Aishah zan wuce, kawai duk yadda ku ka yi da shi sai ki sanar da ni"

"Insha Allahu wannan karan za a dace"

A zuciyar sa ya amsa da amin amma a fili murmushi kawai yai.

Har ga Allah tausayin shi ta ke ji. Lukman ya haWu ta ko'ina musamman ma da ya kasance mutum ne da ya ke da tarin ilimi a Sangaren addini, hakanan yana da kyawawan halaye...

Ta cigaba da kiran Najeeb amma shiru. Hakan ya sa ta kira Abdullahi. Bugu Waya ya Wauka. Ta tambayeshi ko har yanzu Najeeb bai gama abunda ya ke bane. Abdullahi ya ce yanzu ma muna hanyar gida ne.
"Gida kuma?" Farida ta faWa cikin rashin fahimta.
"Hajiya ai daga kamfanin ne ya ce mu wuce gida" ya amsa ba tareda ya fahimci mi ke faruwa ba.
Farida ta kashe kiran ta cigaba da kiran Najeeb amma still bai Wauka ba.

Jakarta ta Wauka ta fito.
"Ma, za ki fita ne?" Naomi ta faWa tana murmushi.
Farida ba ta kulata ba ta cigaba da tafiya, har ta kai ?ofa sai kuma ta juyo ta ce "Naomi miji na ya zo ne?"

Naomi ta yi saurin cewa "No ma"
Farida ta fita cike da tunani a ranta...

............................

Tunda ya fito daga cikin Kamfanin ya ke jin shi kaman marar lafiya. Yana ganin kiran Farida amma ya ka sa Wauka. Daga an kira wayan idan ya duba ya ga My Queen sai ya maida ta ya ajiye.
Ko wanka bai yi ba da ya shiga Waki ya kwanta a kan gado. Jin jikinsa ya ke kamar ba shi ba, kamar akwai abinda aka cire ma sa a jiki.
Yana kwance a haka har Farida ta shigo. Ganin sa kwance da kayan office a jiki ya sa ta san ba lafiya ba. Du?awa ta yi ta cire ma sa takalman sa kafin ta ?arasa dai-dai kan sa tana faWin " miji na lafiya? Are you Ok?"
Bai ce komai ba sai ma juya ma ta baya da yai.
Tunanin ta ko ciwon kan sa ne ya tashi. Dan tunda aka sallameshi daga asibiti yake fama da ciwon kai amma ya fi tashi ma sa idan ran sa ya Saci ko kuma he's stressed. Likita ya ce a hankali ciwon kan zai tafi gaba Waya, amma kuma ya dinga samun isashshen bacci, sannan duk lokacin da ya jima yana aiki to ya tabbatar ya ware lokacin da zai kwanta dan ya huta. Hakanan ya guji duk wani abu da zai Sata ma sa rai.


"My Champ dan Allah mi ya sameka? Wa ya Sata maka rai?"

" ba na son surutu" ya faWa a hankali

"Shikenan tunda ba za ka gayamin miya faru ba, amma dan Allah ka tashi ka rage kayan jikin ka za ka fi jin daWin baccin"

Mirginawa yai Waya Sangaren ba tareda ya amsa ma ta ba.
Ganin dai ba tashi zai yi ba ya sa ta tashi ta fita tunanin ta idan ya huce zai gaya ma ta koma minene.

?akin ta ta wuce ta je ta yi wanka ta chanja kaya. Sai da ta kira Ummi su ka gaisa kafin ta wuce kitchen dan ta taya Tasallah aiki...

Su na jera abinci a dining ya fito ya sha wanka. Ba?in riga da wando ya sa sai ya Waura farin blazer a kai.

"My Champ fita za ka yi ne?"

"My Champ...My Champ" ta cigaba da kira har lokacin da ?ofar ta rufu. Baki tasake tana bin ?ofar da kallo. Ya kalleta sun ma haWa ido kuma ya ji maganar da ta yi amma ya shareta.
Mi ke faruwa, abinda ta tambayi kan ta kenan.

Tun tana jiran shi nan da awa biyu har ta koma cewa nan da ?arfe takwas na dare zai dawo amma shiru. Ta kira duka nambobinshi amma a kashe.

Tana kwance a kan kujera da ke falon ta ji takun sa. Ta yi firgigit ta tashi dan dama ba wai ta jima da bacci ba ne, baccin ma rabi da rabi ta yi.

"My Champ, My Champ" da sauri ya dinga taka stairs Win har ya ?ule ma ta.
Agogon falon ta duba ta ga ?arfe goma har da rabi. Tunda su ka dawo gidan su bai taSa wuce ?arfe tara a waje ba...
Tashi ta yi ta bishi dan ba ta ga ta zama ba. Yana banWaki lokacin da ta shigo. Itama banWakin ta je za ta shiga dan ta taya shi wanka ko za su shirya daga nan amma ta ji banWakin a rufe. Mamaki ya kamata dan indai wanin su ya shiga banWaki yo baya rufewa tunda su biyu ne a gidan Tasallah Wakinta na ?asa.

Ta zauna a bakin gado tana jiran fitowar sa. Tana zaune ya fito, ya shirya yai Wan shafe-shafe da feshe-feshen sa ya zo ya kwanta.
Mamakin yadda yai kamar babu mutum a Wakin ya sa Farida ka sa magana. Ganin ya ja bargo ya kwanta ya sa ta lalubo sauran maganan da ke bakin ta ta ce "My Champion dan Allah ka yi ha?uri, idan ma wani laifin na maka ka yi ha?uri ka yafemin. Dan Allah miji na ka min magana. Ka gaya min laifina" tana maganan ne kaman za ta yi kuka

"Idan ba za ki iya kwantawa shiru ba, to ki koma Wakin ki"

Kan ta ya Waure. Najeeb ba zai taSa gaya ma ta haka ba, ko lokacin da ba sa shiri ma duk shirmen ta ba ya cewa ta bar Wakin.

"Miji na dan Allah, hankalina ba zai kwanta ba idan ban san laifin da na yi ma ka ba"

tsaki yai ya tashi ya Wau pillow ya koma kan kujera ya kwanta.

Haushi ya cikata. Idan ma laifin ta mishi bai ci ya ma ta wannan wala?ancin ba. Ta ja tsaki itama ta kwanta, a zahiri ranta na raya mata kar ta kuma bashi ha?uri zai zo da kan sa ya bata amma kuma chan cikin ranta tana tsoron wannan chanji bagtatan da Najeeb yai ma ta. Ta dinga tariyo abubuwan da su ka faru ko za ta tuna wani furuci ko wani abu da ta ma sa da zai iya Sata ma ta rai amma ba ta gano komai ba. They are just fine, tun jiya har safiyan yau, infact san da zai fita a office ma sai da ya kissing Win ta sannan ya kissing cikin ta amma komai ya wargaje ne tun daga tafiyan sa. To ko a inda ya je ne aka Sata ma sa rai? To ai koma wani ya Sata ma sa rai bai kamata ya sauke fushin a kanta ba musamman saboda condition Win da ta ke ciki.
Da ire-iren waWannan tunani ne bacci ya sace Farida.

Da asuba ma gum ya ma ta ba magana. Bayan ya dawo daga masallaci ta gaishe shi amma bai amsa ba. Haka kawai jikinta yai laushi ta fashe ma sa da kuka. To her uttermost shock maimakon ya rikice ya fara ba ta ha?uri sai ya shige banWaki ya barta zaune tana kuka.

Innalillahi kawai ta ke ta maimaitawa a fili.
Najeeb ne zai ga tana kuka ya share, yai kaman bai ganta ba, gaskiya da matsala.

Ta zauna har ya fito ya fara shirin fita office still ignoring her. Tsoro da fargaba su ka cika ma ta zuciya.
Ba ta san ma ya za ta fassara wannan yanayi ba. Wannan yanayi mai kama da mafarki ko almara.
Wai Najeeb Win ta ke ma ta wannan wala?ancin. Yadda ta ke zaune tana kallon sa haka ya ?arisa shiryawa ya fita daga Wakin. Tunda su ka shirya ya dena fita da sassafiya haka, tunda tare su ke fita office Win, amma sai ga shi bayan ma yai fitar sassafiya bai ma damu ya san ko wani hali ta ke ciki ba balle ya ji ko za ta fita office ko ba za ta je ba.

Farida ta jima zaune a kan sallaya ta rasa ma abinyi Allah kawai ta ke kira a ranta. Dan wannan sauyi ya fi ?arfinta, nan gaba kaWan za ta iya shiga wani hali...


Shi kuwa Najeeb yana shiga mota ya ce Abdullahi ya kai shi gidan su Naomi. Tun jiya Abdullahi ya shiga ruWu, ya kai Najeeb kamfani inda ya Wau Naomi su ka fita, wani haWaWWen restaurant su ka je daga nan ya kai su wata babbar shopping Mall inda su ka fito da kaya ni?i-ni?i. Gidan su Naomin ya kai su ta shiga ta ajiye kaya sannan ta sake shiryawa cikin wassu matsatstsun kaya ta fito.
Sunan hotel Win da Naomin ta faWa ne ya sa shi sake maimaita sunan da Wan ?arfi alamun mamaki.
Najeeb ya ce ya kai su inda ta ce. Lokacin kusan shida na yamma ta wuce, har ma wassu wajen ana kiraye-kirayen sallan magriba. Sun kusa isa hotel Win Daddy ya kira Najeeb akan ya zo yanzu-yanzu.
Najeeb ya cire kuWi ya bawa Naomi akan ta je ta jirashi. Idan ya dawo daga wajen Daddy zai zo.
Bai bar wajen Daddy ba sai ?arfe tara na dare. Har sun kama hanyar hotel Win Naomi ta kirashi akan ta koma gida an kirata mamanta ba lafiya. Wannan ya sa su ka dawo gida...

Naomi ta shiga mota tana zuba murmushi. Cikin kayan da su ka siyo jiya ta sa wani shegen gown Wan guntu da shi. Har gashin wig da ke kamta ta chanja shi. Ta kamo hannun Najeeb tana kaiwa kan nonuwanta tana shashshafa su. Najeeb bai hana ta ba bai kuma yi yun?urin yin wani abu ba. Kallon ta ya ke yi zuciyar sa na raya ma sa abubuwa dayawa. Naomi ta kai baki za ta kissing Najeeb Abdullahi ya ce " Alhaji yau Hajiya ba za ta aiki ba ne?"

Naomi ta koma baya tana hararan ?eyar Abdullahi ita shaWaf ta manta da wani driver. Abinda ya cika ma ta zuciya shine yadda za ta ji idan Najeeb ya shigeta. Yau kan ko ma wani irin uzuri ne ba za ta yadda ba sai ta san yadda za su je hotel su je su yi abubuwa...

Farida kam wani zazzaSine mai zafi ya rufeta.
Kusan ?arfe shaWaya sai ga Sabreen ta kirata.

"Mi ya sa za ki min haka? Ba na son shiga rayuwar kowa Ayshah"

Ta sani ?ila Lukman ya kira ta ne dan jiya ta bashi numbar Sabreen Win.

Ta danne duk wani ba?in ciki da ke ranta ta shiga ba ta labarin Lukman a ta?aice. Ta ?are da cewa " Sabreen kince kina son gyara rayuwar ki. Shiyasa na miki kwaWayin ki kasance tareda mutumin da zai taimaka miki wajen cimma burin ki. Lukman mutum ne da zan iya bugan ?irji na ce shi Win namiji ne na gari wanda ya san kima da darajar mace. Wanda ya ke da ilimi ya ke kuma ?o?arin amfani da wannan ilimin da Allah ya bashi. Amma idan kina ganin na miki shishshigi a rayuwar ki to kiyi ha?uri"

Shiru Sabreen ta yi na kusan rabin minti kafin ta ce za ta yi tunani a kai. Farida ta kashe wayar tana fatan Sabreen ta amince da Lukman. Bayan wayan su da Sabreen shiryawa ta yi dan ta je gida. Ko idan ta ga Ummi hankalin ta zai kwanta har ta iya tambayarta shawara bisa yadda za ta Sullowa wannan ba?on lamari da ta tsinci kan ta a ciki...



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 5?? 2??








Aure Rahama ne, musamman idan ka samu kwanciyar hankalin mijin ka. Ummi har wani ?iba ta ?ara ga haske da ta yi, annurin fiskar ta ya ninka na da.

Kunun Aya da Ummin ta yi ta kawowa Farida. Farida ta ?arSa ta tsiyaya a kofi. Ta ri?e ?ofin amma ba ta kai baki ba. Zuciyarta ne ya tafi ga abinda ke faruwa da ita tsakanin jiya da yau.

"Farida lafiya?" Ummi ta tambaya ganin 'yarta ta yi nisa cikin tunanin da ta ke.

"Dan Allah Hajiyata ina da tambaya"

"Minene?"

"Shin dama akwai lokacin da Namiji zai juya ma ka baya ne bayan kuna zaune lafiya?"

"Kin yiwa mijin ki laifi ko?"

"Ummi ba abinda na ma sa fa, idan ma akwai to ni duk iya tunani na ban gano ba. Ummi na bashi ha?uri amma ko kallo ban isheshi ba"

Ummi ta yi shiru tana nazartar Farida wanda damuwa ya bayyana ?arara a fiskarta.


"Yanzu haka cikin yawar maganar ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login