Showing 12001 words to 15000 words out of 145791 words

Chapter 5 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

319

kanta ma ya zame.
"Duk a dalilin kyanwa ki ke son hallaka kan ki. Miye abin gudu a jikin kyanwa?"

Ba ta bashi amsa ba sai ma ta sunne kanta cikin cinyoyinta. ?ananun ?itson kalaba (braids) da ta yi su ka zubo.

Ganin yadda gashin ke da tsantsi ya sa shi taSawa dan ya tabbatar gashin kanta ne ba na aro ba (wig). Yana son mace mai gashi, haka nan ya tsani mace ta ?ara gashi abinda har yau matarsa Aneesah ba ta dena sawa ba kenan tun yana faWan har ya gaji.
Tabbas gashin ta ne ya faWi a ransa. Ga shi ba?i ga tsawo ga tsantsi.

Shigowar Hajiya Yelwa ya sa yai saurin cire hannunsa.

"Alhamdulillah!, ka ga yadda na tsorata da Alizah ta ce wai Hauwa'u ta mutu"

Yai saurin mi?ewa ya ce " ai Hajiya ba dan ina wajen ba ?ila mutuwar za ta yi. Kin ga yadda ta firgita kuwa, sumewa fa ta yi"

"Ai Hauwa'u kam sai dai Allah shi albarka kawai. Tukunna ma waya fito da kuliyar ne?"

Alizah ta Suya bayan Daddynta dan ta san ita ce ta tafka aika-aikar nan. Tun kafin Maijiddah ta zo Hajiya Yelwa ta sa aka rufe kuliyar kuma ta mu su kashedin kar su yadda su buWe ta.

Hajiya ta kama hannun Maijiddah ta ce " dan Allah ki yi ha?uri kin san sha'anin yara. Fatan ba ki ji ciwo ba?"

Maijiddah ta girgiza kai sannan ta lalumo hijabinta ta saka.

Yana tsaye ?ikam yana jira ta Wago yaga fiskarta da kyau, Wazu cikin ruWu ya ke bai tsaya ya kalleta sosai ba. Sai da ya ?are ma ta kallo sannan ya ce "Hajiya an gama haWa kayan ne?"

"Angama Yaya, na ce da Faty ma ta kai su cikin mota"

"Barinje in gani kar su yi mantuwa"

Har ya kai bakin ?ofa sannan ya sake juyowa ya kalleta, har a lokacin bata gama nitsuwa ba jikinta na Wan kakkarwa, yai murmushi sannan ya fita...

Hajiya Yelwa sai da ta tabbatar Maijiddah ta nitsu sannan ta sa autarta Faty ta raka ta har bakin gate duk da kuwa Fatyn ta tabbatar da an sake kulle kuliyar.

Hannunta ri?e da ledar da Hajiya Yelwa ta bata su ka fito da Faty.

Yana gindin mota ya ga fitowar su dan haka yai saurin Waga wa Faty hannu alamar ta zo.

"Kinga barinje Yaya na kira na" Faty ta gayawa Maijiddah.

" Lah ba komai, sai anjima" Maijiddah ta faWi ta yi hanyar gate Winsu. Ba ta yi wasu taku mai yawa ba ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Faty ta ?wala ma ta kira.
Da ta juyo ta ma ta hannu alamar ta zo. Tsayawa ta yi ta rasa mi za ta yi. Ga Daddyn su Alizah ya ?ura ma ta ido.

"Ki zo inji Yaya" Faty ta faWi da Wan ?arfi. Ba yadda za ta yi haka ta fara taku a hankali har ta kai wajen motar, gefen Faty ta tsaya tana kallon ?asa a hankali ta furta " ina kwana"
"Ki shiga ya kai ki a mota" Faty ta faWi tana Wan murmushi ?asa-?asa.

A hankali ta ce " Lah Faty sai ka ce ba ki san gidan mu ba, ?asan layi ne ba nisa"

"Wato dai ladar ne ba kya so na samu" Ya katse ta

"A'a Yaya, Allah ba nisa. Na gode"

" ki shiga mota ko na sa akawo kyanwar Wazu"

Ai cikin firgici ta kama handle Win ?ofa tana kokawa da shi. Faty ta fara ma ta dariya.
Shi ma murmushin yai sannan ya danne key Win hannunsa ?ofar ta buWu...


Sai da su ka fita daga cikin gidan ya Wan kalleta ya ga ta takure gefe ya ce " ki na tsoron kar na sayar da ke ne?"

Ta girgiza kai

"Ko nima ina da kamannin kyanwa ne"

"A'a"

"To ya kika takure, kin ?i ki sake jiki haka nan ba Wan hira"

Shiru ta yi dan ba ta san mi za ta ce ba. " ashe ke ce me yiwa Hajiyata kitso. Kin san yadda ta ke yabonki kuwa. Ga ki 'yar ?arama da ke, anya kin kai shashida kuwa?" Yai tambayar ne dan samun damar gabatar da ?udirinsa, yanayin tsayinta da ?aramin fiskarta ya ke ganin kamar ba za ta kai 18yrs ba shi kuma a gaskiya ba zai iya auren under 18 ba.

"Na wuce mana" ta faWa a hankali

"FaWamin gaskiya, shekarun ki nawa?. Idan ki ka min ?arya ma zan gane"

"20"

"Ishirin! Kai yarinya ba ki kai ba"

"Yaya kawai ?aramin jiki ne dani fah, amma anyi auren ?annena har biyu yanzu ma an kusa wasu biyun" sai da ta yi maganar sai kuma taji haushin maganar da ta yi.

Cikin zuciyar sa ya ke jimami sai dai bai bayyana ba ya ce " ke mi ya hanaki auren? Karatu ki ke?"

Shiru ta yi ta juyar da kanta wajen glashi tana kallon waje.

Bai sake tambayarta ba yana dai sake karantar yanayinta. Sai da su ka iso ?ofar gidan su sannan ya mi?a ma ta wayarsa ya ce " sa min numbar ki anan"

Kwarjininsa da girmansa shi ya hana ta mishi musu. Ta ?arSa wayar ta saka nambobin ta.

Mi?a ma ta kuWi yai ta ?i ?arSa.

"KuWin ?itson da ki ka yiwa su Baby ne"

"Hajiya ta bani ai"

"Hajiya daban ni daban. Ki ?arSa ko na sa a kawo kyanwar gidanmu na Waure mi ki ita a ?afa"

Ta ?arSi kuWin ta ce " na gode Allah ya saka da alkhairi" ya amsa da amin. Sai da za ta fita ya ce " a samu a addu'a, Insha Allah anjima zamu hau hanya"

"Allah ya kaiku lafiya ya tsare mu ku hanya"

"Amin"

...........................

Su Faridah ba su dawo ba sai yamma lis, da su ka dawonma hidimar gida ya sa ba su zanta da mutuniyarta ba. Sai da ?arfe goma ta gota na dare bayan ta gama goge doguwar rigar da za ta saka gobe sannan Maijiddah ta fara ma ta bayani.

"Anty Farida barin nuna mi ki wani abu"

Ta mi?a ma ta wayarta. Farida ta amsa wayar tana faWin " wannan tsohuwar wayar ta ki ma ya kamata ki chanja ta"

*Alhamdulillah! ni da yara na mun sauka lafiya. Na gode da addu'arki gare ni*
*AbdulWahab Bello Hassan*

"Weeeeeehuhu. Waye wannan dan Allah? ki ce addu'ar mu ta kusa karSuwa"

"Kayya Anty, Wan Hajiya Yelwa ne fa"

"Sai aka yi me. Abeg gist me, ya akayi ya samu numbar ki?"

Maijiddah ta labarta ma ta duk abinda ya faru.

"Ai Insha Allah mun sameshi 'yar uwa ki dai cigaba da tashin dare da kikeyi. Allah ya kusa amsar addu'ar mu. Tukunna ke da me ki ka ma sa reply?"

"Ban ma sa ba"

" amma anyi 'yar ?auye anan"

"To Anty mi zan rubuta?"

"Mtsssw, give me the phone jooor"...


.........................


Doguwar riga ta atamfa ta saka kalar atamfar ja ce da ratsin fari dan haka ta saka ?aramin gyale fari. 'Yar powder ta murza sannan ta goga jan janbaki kaWan wanda ya ke ?ara haska fiskanta.

A karo na biyu Yakubu ya aiko ta fito shi zai tafi.

"Jiddah wannan yayan na kun ko"

Maijiddah dai sai dariya ta ke ma ta...

Su na tafiya Yakubu na ta yiwa Farida faWa akan indai haka za ta dinga makarar da su to zai dena tafiya da ita kowa yai hanyar sa. "Haba ?an Musa, sai kace wanda mu ke aikin asibiti. Ban isa na fito ban karya ba, Allah na gani"

"Lallai kuwa, Sir Najeeb zai samu dalilin koran ki cikin sau?i kenan"

"Ba Sir Najeeb ba Allah ya sa Sir Salihu ne"...


Office Win Anas ta fara zuwa dan ta gaishe shi ta samu cleaner tana shara.
Ta juya za ta fita sai ga Anas Win ma ya shigo.

"A'a ?anwar mu ce da wurwuri haka, ashe da dai ba za kuyi faWan latti da Ogan ki ba"

"Ina kwana Ya Anas"

"Lafiya Aisha Farida"

Bayan sun gaisa sannan ta wuce na ta office Win.
Nan ma Win ana kan gogewa ne hakan ya tabbatar ma ta Ogan na ta bai ?araso ba, ta zauna tana danna wayarta...

Cikin takunsa na ?asaita wanda ke ?ara ma sa kyau da kwarjini ya shigo kamfanin na sa. Duk inda ya wuce gaishe shi ake yi sai dai fuskarsar nan mur ta ke balle ma asa ran zai amsa gaisuwar. Dama idan da sabo to sun saba. Sir Najeeb ba ya amsa gaisuwa.

Yana shiga lifter ya danna 3rd floor wanda nan ne za ta sada shi da office Win sa.

Ya ma manta batun yau sabuwar sakatariyar sa za ta fara aiki dan haka kai tsaye ya shiga office Win, sai dai tundaga bakin ?ofa muryarta ya fara dokan kunnensa.

"No it cant be her" ya faWi lokacin da ya tako cikin office Win. Sai dai itan Win ce dai ya gani, ba ta san ya shigo ba saboda hankalinta na kan wayar da ta ke yi.
?anshin turarensa da ya cikata ne ya sa ta Wago da idon ta.

"And who are you?" Ya faWi yana ?are ma ta kallo.

" The new secretary" ta amsa ma sa

" This is bullshit" abinda ya iya faWi kenan ya nufi hanyar office Win sa.

Tunaninta ba?on Oga ne dan haka ta yi saurin tsaida shi. Cikin bayanin da Anas ya ma ta. Bai kamata wani ya shiga office Win Oga ba tareda izininta ba.

" Mr Arab you cant enter the office, my boss is not around" ta faWi da ?arfi.


Tsayawa yai da buWe ?ofar Office Win ya juyo ya kalleta, lokacin ta baro wajen kujeran ta ta nufo shi.

" you can seat and wait for him there" ta nuna ma sa kujeran da ba?i za su zauna Idan sun zo.

?ura ma ta ido yai, itama idon ta na cikin na sa. Hazel eyes na shi ta ke kallo wanda ya sa ta ji wani kasala nan da nan ta yi saurin Wauke na ta idon. Ta yi gyaran murya sannan ta ce
" please go and wait for him"

Girgiza kai yai ya sa hannu zai buWe ?ofar Farida ta yi saurin buge hannun sa ta shiga gaban sa ta stretching hannayenta tana tare ?ofar da su. "Dan Uban ka, dan kana balarabe sai ka ce ba za ka bi doka ba, to ba ka isa ba"
Idonsa ne su ka firfito lokacin da ya ji abinda ta faWi.

Ta kalleshi ta ce " you will not enter this office. Anta La adkul.....a'a ba haka bane, Anta La Tadkulul Bab.... mtsww, yau ga ranan zuwa Islamiyya nan, ni Aisha Wan Larabcin ma ta gagareni"

Hannu ya sa a aljihu ya zaro waya ya kira wata number, ana Waga kiran ya ce da kakkausar murya "Come to my office now"

Mamaki ne ya mamaye fiskan Farida lokacin da taji abinda ya ce sai dai ta dake a wajen ba ta matsa ba.

Suna tsaye a haka Anas ya shigo. Ganin yadda Farida ta yi kane-kane a bakin ?ofar office Win Najeeb ya sa shi fashewa da dariya.

"Tell this crazy girl to get out of my way" Najeeb ya faWi cikin tsawa.

Anas ya dubi Farida wanda jin abinda Najeeb ya ce ya sa jikinta yai sanyi, ta sauke hannayenta amma ba ta matsa a bakin ?ofar ba.
Ya ce " Aisha ya ki ka hana Ogan na ki shiga office? ko salon na ki aikin kenan?"

"Ya Anas ni ban san shi bane ai. Akace sunan Oga na Najeeb Jibo, kuma na ga wannan balarabe ne. Suna *Jibo* kan ba na fulani ba ne?"

Anas ya fashe da dariya ya ce " kuma da gaskiyan ki fa. Sai dai wannan bafulatanin ruwa biyu gareshi, ruwan fulani kuma ruwan larabawa"

"Ya Anas ina dai ba ya jin Hausa?"

"Hausa kai, hausa kamar Jakar Kano ma"

"Shikenan ni Aishatu, daga fara aiki har na tafka katoSara"

"Fatan dai ba ki zage shi ba?"

A sanyaye ta ce " sai dai gobe kar a ?ara"...

"Barin ji mi Ogan zai ce" Anas ya faWi tareda shigewa office Win Najeeb. Dama tuni Najeeb ya shige ya barsu su.


Yana zaune kan kujerar sa ya na kallon ?ofa lokacin da Anas ya shigo.

" lokacin da na ce ka nemo min secretary, ban ce ka nemo mahaukaciya ba. She's fired, find another one" abinda ya faWi kenan lokacin da Anas ya ?araso wajen sa

Maimakon Anas ya bashi amsa sai ya sa dariya har da ri?e ciki.

"This not funny, da na yi aiki da wannan gara na dawo da Joseph"

Har lokacin Anas bai bar dariya ba, sai da yai mai isar sa sannan ya zauna ya kalli Najeeb da ya cika yai fam.

"First of all Aisha ba mahaukaciya ba ce, secondly, a iya sanina da Najeeb na san girman kan sa ba zai taSa bari ya dawo da Joseph ba. Thirdly idan ka kori Aisha, kai za ka Wau nauyin neman wata ko wani da kan ka. Aisha ?anwar Architect Yakubu Musa Wase ne, and as far as i know Yakubu is like a brother to me dan haka ?anwarsa ?anwata ce"

"Wow! Ban san ka fara kalen dangi ba ai"

"Ni ma kuma ban san ka fara tsoron mata ba"

"What do you mean?" Najeeb ya faWa a fusace

"Na san ka gane Aisha ita ce yarinyar da ta tada hayaniya a restaurant ranan. Shi ya sa ka ke tsoron aiki da ita"

"Tsoro?" Ya furzar da iska daga bakin shi sannan ya ce " i'll give her a chance, idan ba ta iya aiki ba zan koreta. And i dont care who's sister she is"

"Ko kai fa mutumina" Anas ya faWi tareda tashi tsaye. Har ya fara tafiya ya juyo ya ce " Dan Allah, ya ka ji da ta hanaka shiga office Win ka?"
Najeeb ya jefe shi da biro, Anas ya goce yana dariya...

Yana fita ya samu Farida tana zaune hankalinta kwance kamar ba laifin da ta yi.

" ?anwata na ro?a miki shi, dan haka ba wata matsala amma ki bishi a hankali"

"Na gode Ya Anas"...
Ta so jin maganarsu, amma bangon office Win sa soundproof ne ba abinda ta ji shiyasa ta ha?ura da laSen da ta yi ta je ta zauna...
Fitan Anas ke da wuya telephone Win office Winta ya fara ?ara. Ta san shine, dan ta nan Anas ya ce za ta fi comminicating da Ogan ta.
Ba tareda wani tsoro ko fargaba ba ta amsa kiran.

"In my office now" abinda ta ji ya faWa kenan da kakkausan murya..........



*=خ?SAKATARIYA TA=خ?*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0?? 0?? 6??


Ta fi Minti biyar a tsaye bai ce ma ta komai ba, aiki ya ke yi ma a system na shi.

"Sir kai ka kirani kuma ka shanya ni kamar kayan wanki, idan ba abinda zan yi zan koma dan bana iya juran tsayuwa"

?ago ido yai yana kallonta. Lallai ma yarinyar nan, shi a tunaninsa da ta shigo office Win sa za ta bashi ha?uri sai ta yi ?um da bakinta ko gaishe shi ba tayiba.

"Let me make this clear to you..."

"Sir Najeeb ka yi Hausa kawai zan fi ganewa, turancinkan nan ban faye ganeta ba. Lan?washe harshe ka ke kamar bature"

Bai ji mamakin maganarta ba duba da yadda ya san halinta.

" i will say this only once Miss Salihu. I do not tolerate laziness. This is an office, you should learn to behave yourself according to this company's rules. Is that clear?"

Kallon sa kawai ta ke yi ba ko kiftawa

"Miss Salihu is that clear!" Ya daka ma ta tsawa.

"Yes...yes Sir"

"Good, now get out of my office"...


Tafi minti goma ta rasa yadda za ta arranging files Win da ya bata, kamar da gayya aka hargitsa files su ka zama haka. Tana cikin yi kira ya shigo, ta yi tsaki kafin ta Wauka.

"In my office now"

Doguwar tsaki ta ja sannan ta tashi ta wuce office Win sa.

Ce ma ta yai yana da meeting ?arfe shabiyu. Ba?in ciki ya zo ma ta har wuya. Maimakon ya gaya ma ta da ya kira sai da ya bari ta sha wahala ta zo har office Win sa.

"Why are you still standing, get out?"

"Sir, na san kai Oga na ne kuma zan ba ka girman ka amma kuma wallahi ba zan Wau wala?anci ba. Sir daga zuwa na na yi jelen tsakanin office Winka ya fi sau goma. Haba dan Allah, indai sa?on magana ne idan ka kirani sai ka gaya min ba wai sai na zo har nan ba. Wannan ai salon mutum ya samu ciwon baya ne"

Ganin ya mi?e ya sa tai shiru. Har gabanta ya tako ya tsaya. " Miss Salihu, i know you are a lousy crazy girl but that should stop outside this company. Here, you are just a secretary, so work like one" yana gama faWin haka ya fice daga office Win ya bar Farida baki buWe.

"Allah ya isa na, mugu kawai. Daga ranan farko a addabi mutum da aiki kaman Jaki" ta yi tsaki sannan ta fice daga office Win...


...........................

?arfe sha biyu saura minti biyu ya fito daga office biye da shi kuma sakatariyar sa Farida, tana Wauke da wasu files a hannunta. Lifter su ka shiga saboda a second floor za a yi meeting Win. ?anshinsa ne duk ya bi ya cikata, ta rasa wannan ?anshin na shi, its so inviting, so cool.

Kiiiinnnnn. lifter ta tsaya su ka fito yana gaba tana bin bayan sa har su ka shiga hall Win.
Kowa ya hallara a wajen dama shi ake jira. Dokar Najeeb ne lateness is a punishable offence.

Ta samu kujera kusa da mace Waya da ke wajen ta zauna bayan ta ajiye files a gaban Najeeb.

Duk yawancin bayanan su ba ganewa ta ke yi ba, ko dan maganar ta fi karkata zuwa ga ayyukan gine-gine da kamfanin ke yi ne...
?arfe Waya saura minti biyar aka rufe meeting,su ka fito.

Yanzu ma bayanshi ta bi su ka haura. Sai dai ta yi laushi sosai tana ajiye files akan table ta kwantar da kanta.

Rufe ?ofar da yai ya sa ta Wago idon ta. Ya cire suit Win sa, farar shirt Win ne kawai ajikinsa yana warware hannun rigar da alama dai alwala yai. Su na haWa ido ya ?ara haWa rai...

Sai da ya tafi ta fara ?o?arin neman banWaki dan ta yi tsarki ta yi alwala. Office Win ta dai babu, ?o?arin fita ta ke matar Wazu ta shigo office Winta.

"Assalamu Alaikum sister"


"Wa'alaikissalam, 'yar uwa sannu da zuwa"

"Suna na Munibat AbdulHamid, i'm an Engineer. Office Wina na second

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login