Showing 57001 words to 60000 words out of 145791 words

Chapter 20 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

331

ka yi da dattijon sannan su ka gaisa.

"Yi ha?uri ban ganeka ba"

Ya mi?a masa envelop sannan ya ce " Wan ka zai yi aure ranan Asabat Win nan ko?"

"Insha Allahu"

"Matar da zai aura ba matar aure ba ce"

"Ban gane ba"

"Ka dubi cikin envelop Win nan za ka ga zahiri" daga haka ya juya ya tafi.


.....................


Anyi friends day lafiya kuma ba laifi ?awayen ta na Jos sun zozzo, anci an sha kuma an girgije.

?arfe goma sha Waya na dare lokacin ba ta fi 'yan mituna kaWan da kwantawa ba kiran Rayyan ya tashe ta. Tana Wauka ya ce ta fito waje yana ?ofan gidan su.

"My Ray lafiya ka zo da daddaren nan?"

"Ki fito Farida akwai sa?on da zan ba ki ne"

Maganar sa?o da ya ce sai ta ji zuciyar ta ya buga. Ta tashi ta sa hijabi ta fito.
Akwai wa su ba?i da ke kwance a barandar tsakar gidan su na hira, da ke ba su jima da tattara tsakar gidan ba.

"Amarya ina zuwa haka?"

"?ofar gida zan je an kawo min sa?o"

"Samarin zamani dai, angon ne ya ka sa hakuri haka"

Ita dai ba ta sauraresu ba ta fita.

Wajen motar sa ta je ya buWe ta shiga.

"My Ray minene, hankalina ya mugun tashi fa"

Da ke dare ne ba iya kallon fiskarsa ta yi sosai ba balle ta ga yanayin sa.

"Farida ashe za ki iya cin amana ta"

Dum ta ji ?irjin ta ya yi.

"Wallahi ban Wauka za ki min haka ba"

"Na shiga uku ni Farida ba dai za a kuma ba. Rayyan mi na yi?"

"Ashe soyayya ku ke da Ogan ki. Ashe duk yadda ki ke zagin sa a gabana iya fatar baki ta tsaya"

"Rayyan dan Allah kar ka sa zuciyata ta buga yanzu. Idan ma wasa ka ke ka dena please "

"Da kan sa ya je gida ya ce wa Baba ke karuwarsa ce"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun, Lahaula wala ?uwwata illa billah. Sir Najeeb ne ya faWi hakan?"


Mi?a ma ta wayarsa yai ya ce ga hotunan da ya kawo. Ina tunanin ma waWannan lokacin da ku ka je Lagos tarene ku ka yi holewarku achan.
Ta amshi wayar ta fara kallon hotunan. Hoton farko tana zaune kan cinyar Najeeb ta sa hannayen ta a kafaWun sa tana murmushi, Waya kuma suna tsaye ya rungumeta ta baya, lips Win sa a daidai wuyan ta. Ta swipping na gaba wanda tana kallo hawaye na Wiga a jikin wayar. Suna rungume da juna bakinsu a haWe kamar suna kissing.

"Ba ni bane, wallahi ba ni bane. Wannan sharri ne. Rayyan ka yarda da ni"

"Dama na zo na faWa miki ne da kaina kafin gobe a zo gida a faWa. Na fasa auren ki Farida, ina son ki amma ba zan iya auren ki ba. Najeeb yana da kyau yana da kuWi, ko bayan mun yi aure idan ya neme ki za ki amince da shi. Ba zan iya aure da zargi a ciki ba"

Bakin ta ne ya fara rawa, tana so ta yi magana amma ko me ya taho zai fito sai ya ma?ale a wuyan ta. *"Na fasa auren ki Farida"* shine maganar da ke ta maimaituwa a ?wa?walwarta.

"Gobe za su zo su karSi sadaki da lefe, sauran abubuwan na yafe. Na gode da Allah ya tona asirin ki kafin ma ayi auren, dama Umma ta sha faWamin ba ta yarda da ke ba dan 'yan Jos Win nan yawancin ku 'yan iska ne"...

Ba ta san ya akayi ta buWe ?ofa ba, ba ta san kuma ya akayi ta shiga gida ba. Zuwa ta yi ta zauna a bakin gado hawayen da ta ke yi ma ya tsaya. So take ta gane mafarki ta ke yi ko gaske ne. Bacci kam ranan ba bu shi a idon Farida.

Washe gari da safe aka tashi da shirye-shiryen walima. Farida ta kasa magana ta kasa faWan abinda ya faru jiya, ita har lokacin gani ta ke mummunan mafarki ta yi jiya da dare.

Zuwa ?arfe goma sai ga Baffa ya shigo yana faWace-faWace. Kiran Ummi da Nanna da Baaba Sabuwa yai zuwa falon sa. The next thing da akaji sai kukan Ummi. 'Yan gulma su ka yi falon da sauri Baffa musa ya fatattake su.

"Amina ki dena kuka, ni ban yarda da abin da su ka ce ba, kuma koma hakanne dole sai na aurar da 'ya ta gobe. Ba zai yiwu a fasa aurenta har sau biyu ba, sai duniya ta zageni. Ni nawa 'ya'yan ina aurar da su lafiya ita kuma da ta ke amana gareni ake samun matsala duk lokacin bikin ta"

Nanna da ita kaWai ce ba ta fara kuka ba ta ce "yanzu wa za ta aura?"

"Yakubu, Yakubu zai aureta, ku cigaba da shirye-shirye Allah ya kaimu goben"...

Farida na Waki har lokacin tana zaune jugum, Maijiddah ta yi tambayar duniyar nan amma ba ta kulata ba.

Ummi ta shigo Wakin tana hawaye. Zuwa ta yi ta tsugunna gaban Farida ta ce "faWa min gaskiya Farida, akwai abinda ke tsakanin ki da Ogan ki?"

Farida ta kalli Ummi da rinannun idanuwan ta ta ce "da gaske ne ko? Da gaske Rayyan ya fasa aurena?. Ummi banida sa'a a rayuwa kenan? Ummi ina son na yi aure, ina son na samu gidan kai na, ina so na haihu na tara 'ya'ya, ina so na samu ladan biyayyar aure, ina so na cika miki burin ki Ummi. Ummi ko dai aure ba ya cikin ?addara ta ne?"

Ummi ka sa magana ta yi sai kuka.....

Zuwa ?arfe shabiyu 'yan gidan su Rayyan su ka zo karSan kaya. Daga wajen ma su ke cewa aje a kwashe tarkacen da aka jera a gidan Wan su. Abubuwa dai su ka rinchaSe a wajen.

Kowa a gidan da abinda ke ran sa, wassu ba?in na shirin komawa amma da su ka ji Baaba Sabuwa ta ce aure ba fashi za ayi, sai su ka tsaya dan su ga ?arshen Farida.

Farida tun safe ko sau Waya ba ta fito a Waki ba, ko wanka ba ta iya yi ba balle abinci kam ba a zancen sa.
Da yamma Yakubu ya dawo daga wajen aiki sai a lokacin ya ke jin labarin abinda ke faruwa. Baaba Sabuwa ce ta ma sa maganar auren Farida da ya koma kan sa. Duk da bai shirya aure yanzu ba sannan bai taSa kawo auren Farida a ransa ba amma indai dan ya cececi mutuncin 'yar uwar sa ne to zai aureta da gudu ma. Abinda ya ?ara Waure ma sa kai baifi yadda aka ce wai 'yan gidan su Rayyan sun ce wai FARIDA karuwar Ogan ta ba ne. Ya san Farida kuma ya san Sir Najeeb, ko da dai chan ?asar zuciyar sa yana zargin Sir Najeeb na son Farida amma bai kai har ace wai suna neman junan su ba.

Yana cikin wannan tunanin ya ji wayar sa na ringing. Yana dubawa ya ga Farida ai da sauri ga Wauki kiran.

"Dan Allah Yakubu ka sameni a ?ofar gida"

Da sauri ya tashi ya fita.
Lokacin da ya ganta wani tausayinta ne ya kuma shigan sa. Lokaci guda Farida ta chanja ta zama wata iri, fiskanta ya kumbura ga idon ta da su ka ?an?ance saboda kuka. Tunowa yai da shekara uku da su ka wuce exactly haka ta lalace lokacin da aka raba aurenta da Lukman. Gara lokacin da sau?i tunda matsalar daga Lukman ne to yanzu fa.

Ya ?arasa wajenta yana faWin "Farida dan Allah ki yi ha?uri, ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce"

"Ka kaini gidan su Sir Najeeb" abinda ta faWa kenan cikin muryarta da baya fitowa sosai saboda dashewa da yai...


Adama ce ta buWe ?ofa lokacin da ta danna doorbell Win.
"Daddy na nan?"

"Eh ki shigo"

A tsaye ?i?am ta tsaya idon ta na kallon ?asa, kan ta ke sarawa, duk yadda ta Waga kan sai ta ji wani raWaWi.

Mom ce ta fara saukowa ganin yadda Farida ta ke ya sa tasan yarinyar na cikin damuwa.

" 'yan mata ki zauna mana" ta faWa da Hausanta da bai gama nuna ba.

Farida ba ta ce komai ba sannan ba ta zauna Win ba. Kitchen Mom ta wuce ganin Farida ba ta cikin hayyacinta.

Minti huWu sai ga Daddy ya sauko.

"Ina wuni Daddy" ta faWa da disashshiyar muryarta.

"A'a Aisha Amarya?"

"Na'am Daddy"

"Lafiya dai ko?, shekaranjiya Baban ki ya kawo min katin biki, ina ce ba wata matsala ba ne ta taso ?"


"Daddy kai uba ne na gari amma Wan ka bai Wauko hali na gari ba. Najeeb ya min sharri, ya raba ni da farin ciki na. Ya sa min tabo a rayuwata wanda ban san ranan da wannan tabo zai gogu ba. Ni marainiya ce, ba ni da gatan da ya wuce Allah, kuma na haWa Najeeb da Allah. A kamfanin sa ban tsira ba, na bar aiki da shi ma ban tsira ba. Allah zai saka min" ta fashe da kuka ta fice daga gidan da gudu. Daddy yana kiran ta amma ba ta tsaya ba. Daddy kan shi ya Waure dan bai gane ina maganganun Farida su ka dosa ba.

Tana fitowa ta tsaya ta goge hawaye sannan ta fara tafiya duk da kuwa ba ta da ?wari a jikinta. Ta kusa isowa wajen Yakubu da ke jiran ta jiri ya Webeta ta faWi ta suma. Yakubu ya yiwo kan ta da gudu...





*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0?? 2?? 3??








Maigadi da dreba da su ke zaune a benchi su ka taso da gudu.
Ce ma sa su ka yi ya kai ta mota yayinda Iliya dreba yai sauri ya shiga gidan don ya faWawa Daddy.
Daddy na falo har lokacin yana waya da Anas.

Ya na ma sa bayani Daddy ya ce muje-muje.

Daddy na gaba Yakubu na baya Wauke da Farida wanda har lokacin ba ta farfaWo ba duk da kuwa sun yayyafa ma ta ruwa. Kafin su isa asibitin ta farfaWo amma ba ta san inda ta ke ba....

Chan gida kuma Baffa ne ya ke ta faWa kan miyasa za'a bar Farida ta fita a wannan halin. Maijiddah ne ta ce tare su ka fita da Yakubu. Sai a sannan yai shiru ya zaro wayar sa a aljihu ya fara kiran numbar Yakubun amma bai Wauka ba.

"Shima Wan gatan'wa, ko ina ya shiga oho"...



Ruwa aka Waura ma ta aka ma ta alluran bacci dan sun ce jinin ta ne ya hau. Sai da ta fara bacci tukunna Yakubu ya samu damar kiran gida ya faWa mu su.

Daddy ya dubi Yakubu ya ce " mi ya ke faruwa ne? mi Najeeb ya ma ta?"

Da kaman ba zai faWa ma sa ba,sai dai girman Daddy da kwarjininsa ya fi gaban ya ?i ma sa magana. Duk abinda ake ciki ya tsirge mi shi tundaga farko har ?arshe.

Da ya gama bashi labarin Daddy ya Wauko waya ya kira wata number.

"Anas ka na ina ne?"

Yakubu bai ji mi ake ciki ba ya dai ji ya ce "muna room 18 a sama"

Ba'a jima ba sai ga Anas ya shigo. Ganin Farida a kwance ya sa shi mamakin mi ya faru.

"Yakubu ya jikinta?, mi ya sameta?"

Da sau?i kawai Yakubu ya iya ce masa.

"Ina Wan banzan nan ya ke?"

Daddy ya tambayi Anas.

Ya gane Najeeb ya ke nema dan haka yai saurin cewa yana office nima daga office Win na ke.

"Har da kai ake rusa rayuwar mutane ko?"

Anas ya zaro ido ya ce "A'a Daddy"

Daddy ya mi?e ya ce "Yakubu Allah ya bata lafiya, ina nan dawowa anjima"

Yana Fita daga Wakin Anas ga bi bayanshi da sauri.
A motan Anas Win su ka wuce Najeeb constructions.

Ya jima yana tunanin ko wani hali ta ke ciki. Wani Sangare na zuciyar sa na faWa ma sa bai kyauta ba wani Sangaren na nuna ma sa ya yi dai-dai.
"She deserve it" ya furta a fili.
Yana ?o?arin duba wasu takardu da aka submitting ma sa tun da safe amma ya kasa fahimtar komai. Haka kawai zuciyar sa ke ma sa ?unci....

A hanya Daddy ke sanar da Anas abinda Najeeb yai, Anas ya kaman salati yana salallami.

"Daddy ban san Najeeb zai iya yin haka ba especially saboda zargin da na ke masa akan yana son Faridan"

"Dan uban sa dan yana son ta sai ya mata sharri"

Anas dai shiru yai yayinda Daddy ke ta surfa ma sa masifa kaman wanda shi yai laifin.

Da ke an riga an tashi wajen shiru ka ke ji. Daddy da Anas su ka haura third floor.

Ya kifa kan sa akan kujera saboda wani zazzaSi da ya rufeshi lokaci guda, ya rasa mi ya sa shi shiga wannan yanayi. He supposed to be happy ya rama kaWan daga cikin asaran da Miss Salihu ta sa ya yi. But instead his sad.

BuWe ?ofar office na shi da aka yi ya sa ya Wago kan sa da sauri.
Ganin Daddy da Anas sai ya mi?e. "Dad " kaWai ya iya faWa kafin saukan mari ya sa ya haWiye koma mi ya ke shirin faWa.
A karo na biyu Daddy ya kuma marin sa, ji ka ke taas. Anas na gefe ya sha jinin jikin sa dan faWan uba da Wa sai Allah.

"I'm ashamed to call you my son"

"Dad" Najeeb ya faWa a hankali

"Ashe tarin shekarun ne kawai akan ka ba hankali. Mahaukacin banza Mahaumacin wofi. Sai ka samu me idan ka hanata auren? Tukunna ma, miye dalilin yi ma ta sharri? Miye dalili? "

"she deserve it Dad, she wanted to ruin me. Na rasa big contract saboda ita saboda haka 2 project da mu ka fara su ka soke contract da mu. She tarnished my image and the repeatition of my company"

Wani marin Daddy ya kai ma sa. " i didnt know i have a monster son. Asaran kamfaninka yana dai-dai da ruguza mutuncin mutum kenan?. Shin ka yi tunanin halin da yarinyar nan za ta shiga? What if she died of shock, sai ka haWa party kana murna ko"

Ya nuna shi da Wan yatsa yace " Anas, kalli banzan yaron nan fa,8yrs ago da Sabreena ta gudu ta barshi kafin auren su he almost died, he was depressed for months. Ya je theraphy section na watanni huWu kafin daga baya ya warke ya dawo Nigeria. Do you know that this fool here yana shan antidepressant drugs har yau saboda ba?in cikin yarinyar nan. Amma shi ne ya ke da guts da zai je ya hana auren 'yar mutane"

"Najeeb" ya ka sa magana ma saboda ba?inciki da ya tokare ma sa wuya.
Daddy juyawa yai ya fita, Anas ya kalli Najeeb, kallon ka bani mamaki sannan ya bi bayan Daddy da sauri.


Gidan su Rayyan Daddy ya ce Anas ya kai shi. Da su ka je su ka sa a yi sallama da Baban Rayyan Win, aka ce mu su yana kasuwa. Numbar sa su ka karSa su ka kirashi jin sunan Alhaji Adam Jibo ne ya sa mahaifin Rayyan ya ce yana nan zuwa. Haka su ka zauna zaman jiran sa, kafin ya dawo ma an fara kiran sallan maghrib su ka yi sallah a masallacin anguwar.
A ?ofar gidan aka shimfiWa mu su tabarma lokacin da Baban Rayyan ya zo.

Daddy bai Sata lokaci ba ya ma sa bayanin ko shi waye da kuma abinda ya ke tafe da su.

"Malam Abdullahi, wannan hoto da aka kawo muku ba tare su ka Wauka ba, editting na shi aka yi, kasan yanzu fasahar zamani ba abinda ba ayi. Wannan yarinya ta na da tarbiya kuma kowa ya shaideta da haka. Duk abinda Najeeb ya zo ya faWa muku to wallahi ?arya ne, ya yi hakan ne dan ya cimma wani banzan burinsa. Ku yi ha?uri a maida maganar auren yaron ku da Aisha"

Yadda Daddy ya ke magana cikin kwantar da murya ya sa Malam Abdullahi yarda da maganar sa domin Daddy babban mutum ne a gari kai a ma ?asar gaba Waya ba zai yiwu ya zo wajen sa dan kawai ya ma sa ?arya ba.

"Alhaji na fahimceka, sai dai gaskiya al'amarin nan ya riga ya Saci. Ni da Alhaji Musa mun samu saSanin harshe a yau Win nan saboda wannan magana. Yanzu haka maganar da na ke maka an riga an dawo mana da sadaki da kuma kayan lefe da aka kai. Harta kayan yarinyar da aka kai gidan yarona sun je sun kwashe. Al'amarin ya Saci sosai gaskiya"

"Malam Abdullahi a duba dan Allah. Auren nan idan aka fasashi alhakin yarinyar nan zai bi Najeeb 'ya'ya da jikokin sa"

"Gaskiya zan faWa ma ka Alhaji ko da za a dawo da bikin nan to ba gobe ba"

Shiru Daddy yai na tsawon lokaci kafin ya ce wa Anas su tafi.

...........................


Su Baffa da su Ummi sun zo asibitin da aka kwantar da Farida. Baffa kam a lokacin ma ya ?ara tabbatarwa kan sa ko mi zai faru to gobe sai ya aurar da Farida, domin idan gobe ta wuce bai san halin da Farida za ta shiga ba, balle ya san halinta yanzu sai ta ce ta ha?ura da aure gaba Waya ta ce karatu za ta cigaba da yi.

Bayan ya tabbatar da ankawo duk abubuwan da za su bu?ata sannan ya musu sai da safe saboda ance sai gobe za a sallameta. Ya zo zai fita daga asibitin da shi da Yakubu su kuma su Daddy su ka shigo.

"Alhaji Musa dan Allah ka tsaya" Anas ya faWa lokacin da ya ga Baffa Musa ya gan su amma sai ya kau da kai yai kamar bai gan su ba.

Baffa Musa ya juyo ya kalli Daddy yana ?arasowa wajen su, girman sa ya sa ya fasa masifar da ya ke shirin yiwa Anas.

"Alhaji Musa dan Allah ko za mu iya magana da kai"

"Ni yanzu gida zan wuce Alhaji, ina sauri"

"Ba komai Alhaji Musa za mu bika gidan"

Baffa Musa dai bai so ba amma ba yadda ya iya. Haka su ka wuce gaba, su ma su Daddyn su ka bi bayan su.

Daddy da Baffa Musa ne a falon. Yayinda Anas da Yakubu ke ?ofar gida suna tattauna wannan abin al'ajabi mai kama da almara.

Duk girman Daddy da matsayin sa haka ya fara yiwa Baffa Musa magana cikin sanyi da harshe mai taushi.

"Alhaji Musa dan Allah ka duba wannan al'amari. Na yiwa Malam Abdullahi magana kuma ya ce za su duba, kar a fasa auren nan gobe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login